chapter 5-6
by @autarmama
PRINCE SAPWAN👑
*STORY AND WRITEN BY SALMEERT (AUTAR MAMA, ƳAR LELEN ROYAL STAR) AND MARYAM YUSUF (OMMU JUJU)*
*YARDA MUKA FARA LITTAFIN NAN , RANAR 20 MAY 2022, ALLAH KA BAMU IKON GAMAWA LAFIYA.*
*WANNAN LITTAFIN ƘIƘIRARREN LABARINE BA MUYISHI DAN CIN ZARAFIN WANI KO WATA BA, IDAN YA YI ,DAI-DAI DA TSARI KO HALIN GIDANKU KO MASARAUTARKU TO AYI MANA AFUWA BA DA SANI BANE*
*BA MU YARDA WANI KO WATA YA CHANJA MANA TSARI KO YANAYIN LABARINMU BA*
*WANNAN LITTAFIN NA KUƊINE #200 NE KACHAL KUƊINSHI ,KI BIYA KI KARANTA HANKALI kwance*
Assalamu alaikum,ma Abota bibiyar litattafan Salmeert Sani Salman(Autar Mama, Ƴar Lelen Royal Star🧚♂️🧚♂️🧚♂️)to yanzu ma ina farin cikin sanar daku littafin na , na YAR GAN-GAN.
littafin na kuɗine idan kina bukata zaki iya fara biya tunkafin free page yaƙare,gamai son littafin Yar gan-gan zai turo da kuɗinsa ta wannan account din👇
Umma Salma Sani access bank 1499884120
idan kuma kati ne zaku turo katin MTN ta wannan number ***
Bamu son VTU ba zamu kar ɓaba.
idan kin turo kuɗin zaki turo mana da shaidan kin biya ta wannan number ***
Normal group 200 only zakuna samun page daya (1) a rana
Special group 300
zakuna samun page (2) a rana duk wanda ki kaga ya miki sai ki shiga.
bashi kaɗaiba zaku ringa samun litattafai na irin su.
1)Rayuwarmu Ayau.
2)Bara gurbi.
3)Amaryar Zamani.
4)Rayuwar Farouq.
Assalamualaikum barkan mu da wannan lokaci *ABMAR COLLECTION* ina nan na kawo muku kayana masu kyau da sauki👌🏻
KAMAR SU:-
Atamfa, Atamfa Mai golden,💁♀️
Lace ,Shadda lace
Yadi, Shadda
Abayas💥
Kids wear
Takalmi, jaka, mayafai💥
Sleeping dress, kananan kaya na gayu🔥kayan kitchen,
DA DAI SAURANSU ina Sokoto ina tura kaya ko ina da izinin ubangiji mai son kayana pc ina maraba daku siyan daya ko sari👏🏻domin neman karin bayani sai ku neme ni ta wannan number waya👉***
nagode kwarai da gaske💃💃
*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}
***
```MARUBUTA MASU AIKI DA FASAHA DA ZALLAR TSAKWARON AMANA, FAƊAKARWA HAƊI DA NISHAƊANTARWA GAMI DA WA'AZANTARWA HUNM WANI ABU SAI ROYAL STAR'S WRITER'S✍🏻📚✨⭐✨ ASSOCIATION RUWA ƘAƊAI KE MAGANIN ƘISHI (R..S..W..A) / 💪💪💪
UP-UP-UP BEST WRITER'S EVER💖 ```
*ALƘALAMINMU ƳANCIN*
*BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
*PAGE 5&6*
""""""""""""""""""""""Masu busa sigari nayi, gefe ta samu, ta zauna tare da babban robar Abincin da take siyarwa.
***************
"Hhhhhhhhh, to yanzu dai Yarima Sap, ya zama mutum-mutumin, saidai har yanzu hakan bai yi min ba, so nake na batar dashi gaba daya, domin ko photonshi banason gani balle sunanshi, dan haka duk yarda za'ayi , kayi Waziri dan so nake a batarmin da Labarinshi ma acikin masarautar nan", Fulani ta fada tana dariya.
"karki damu, Gimbiya Fulani, kamar anyi angama wannan zance, ki kwantar da hankalinki",
ya fada yana dalla mata harara kasa-kasa
**************
Gimbiya Khadija ce zaune kan prayer mat, Addu'o'i take jerowa na samun Lafiyar gudaliyar dan nata, sosai take kuka, Mai martaba ne ya bude idonshi ya daurasu akanta, ganinta zaune tana kuka, da sauri ya mike, ya nufeta rungumota ya yi, yana share mata hawaye, hakuri ya shiga bata yana lallashinta dakyar ta tsaida kukan da take.
**************
wani matashin saurayine ya nufo gurin da take, wanda da gani kasan irin yan iskan samarin nan ne, zama ya yi, kafin yace abashi Abinci.
bashi tayi, bayan ya gama ci ne, ya tashi ya tafi, Sapna ce, tace "Malam kuɗin fa?", ta fada tana kallon bayanshi.
"Anci Allah buɗa, ko da yarda za'ayi ne?" ya fada da maganarsu ta yan daba.
"Dan Allah, ka bada, karkajamin bala'i ", ta fada tana hawaye dan tasan indai bai bataba to ta shiga uku, da Inna yau dan saita kusan kasheta.
"kika kara yimin magana, sai na daddala miki mari", ya fada yana wucewa .
haka tanaji tana gani, ya tafi bai bada kuɗin ba, sai 10pm ta tashi, daga tallah .
gida ta nufa da zullumi cikin ranta, dan tasan yau babu mai hana Inna dukanta, saboda yau batayi mata ciniki sosai ba, gashi anci ba'a bata kuɗiba.
"Assalamu Alaikum" ta fada tana shiga cikin gidan.
Inna ce, ta fito daga ɗaki da sauri, tana cewa "Munafuƙa ni kawomin kuɗina", ta fada tana harararta .
a sanyaye ta kasara kusa da Innar tare da ajiye mata babbar robar abinci.
"ke! mai nake gani haka?", ta fada a tsawace.
jiki na bari tace "Wallahi yau babu ciniki Inna", ta fada hawaye na ziraro mata.
dukanta ta farayi baji ba gani, harda icce dakyar Ummi ta kwaceta , "to wallahi sai kin sayarda wannan Abincin gwarama ki fito, dan wallahi ko abinci baki dashi yau a gidan nan, shegiya mai bakin jini, dangi mahaukata a haka zaku ƙare kuma kizo ki fita, ko inci ubanki, shima sallamame da baya iya taɓuka komai, kuma wallahi karki dawo sai kin saidashi inba haka ba saina kasheki, ta fada da hargowa.
Sumi-sumi ta fito jikinta duk ba kwari, abincin ta dauka tare dayin hanyar waje.
Kofar gidansu ta fita, ta ajiye abincin kuka ta fara rairawa, a hankali cikin muryarta mai amo da dadin saurara.
Dafata taji anyi, da sauri ta dago, tana kallon wanda ya dafanta.
Da sauri ta mike tana kallonshi, "Lafiya Sapna? kikazo nan kinayin kuka", ya fada da alamar tausayawa.
Kuka ta kara ɓarkewa dashi kafin tace" Inna ce tace, kar na dawo sai na siyarda abincin, "haba shi ne kika zo nan kina kuka, toh kiyi shiru ni zan baki kudin abincin sai kiyiwa almajirai sadaka dasu, kin san bana son ganin ki cikin damuwa, cewar wannan saurayin,
Sosai Sapna taji dadi, godiya tashiga yi masa, nan take ya kirga dubu goma ya bata, Sapna kin amsa tayi, tace "Wallahi sunyi yawa abincin duka fa na dubu shidda ne, kawai ni ka bani dubu shidda kar Baba ya mun fada,
"Toh shikenan ga dubu shidda din tunda bazaki amsa ba duka" cewar saurayin "Eh nagode sosai dubu shidda ma sun isa, bata kudin yayi, ya wuce abun sa, Sapna kuwa murna take kamar ta zuba ruwa kasa tasha,
Domin kuwa ita har ga Allah bata san a ina zataje ta samu kudin ba, ai kuwa ba bata lokaci ta shiga rarrabawa almajirai abinci, daman tana kusa da wata makarantar allo ne na almajirai,
****************
Yau ma kamar kullum Sapna ce zaune ta buga uban tagumi tamkar zatayi kuka domin kuwa tunda ta fito kasuwa ko mutum daya bai saye abinci ba, ai kuwa kiris kawai ya rage ta fashe da kuka don ta san yau kashin ta ya bushe jiya ma da ta dan yi cikini sai da Inna ta maido ta belle yau da ko kwandala batayi ba,
Wata tsohowa ce ta zo wucewa sai ga wani katoton dutse sam tsohowar bata lura dashi ba, ita kuwa Sapna tun da nesa ta hango dutsen da sauri ta tashi zata je ta taimaka wa yar tsohowa, ai kuwa ta janye dutsin kenan sai ga wata motar ta zo ba tareda ta lura dashi ba kittttttt kawai kake ji ai kuwa sai ga Sapna kwance kasa sumamiya ba ko alamar numfashi tattare da ita, da saurin tsohowar taje ta rungume Sapna tana kiran dogarai su zo su taimaka a sakata a motar su kai ta asibiti,
Sapna kwance saman gadon asibiti sai hawaye take tayi tana fadin "Yoo na shiga uku sai Inna ta kashe ni, na bar roban abincin ta kasuwa, kuka tashiga yi wiwiwi tamkar ba gobe, Tsohowar zatayi magana kenan sallamar Sarki ya katse mata hanzari,
Sarki gaida ta yayi tareda cewa sannu yarinya kece kika taimaka wa Maman Sarki, sannu zaki ji sauki da yarda Allah, ita dai Sapna bama jin su take ba, abun duniya duk ya dame ta, tunanin ta guda ina robar Inna, sannan bata yi cinikin komai ba, shin ya kenan?
Fada sarki ya shiga yiwa dogaran da suke tareda Tsohowa yana cewa "Kuna ina ne lokacin da abun ya faru kenan saboda me nace a dinga rakiyar ta idan zataje sayyaya a kasuwa, Hakuri suka dinga bashi ya yinda yayi shiru, sai ga likita ya shigo cikin girmamawa ya gaida Sarki tare da basu takardar sallama,
Ai kuwa Sapna na jin an sallame su fashewa kawai tayi da kuka tana fadin don Allah kar ku maida ni gidan Inna wallahi kashe ni zatayi, don Allah kar ku maida ni gida, sosai mamaki ya kama su in da tsohowa tace "Yarinya ki kwantar da hankalin ki karki damu kinji ki gayamin damuwar ki in ma bakya son zama a gidan ku ne, ni a shirye nake na tafi dake gida na, tunda kika taimaka min nima ya zama dole na taimaka miki,
**************
Inna tun daga nesa ta dinga kwasan gaisuwa, Ashe fadawan sarki ta hango, sai ga Sapna ta shigo gidan daure da bandeji saman kai, "Toh shikenan ta faru ta kare yau kuma masifar da kika janyo muna kenan, wallahi ga ta nan ku ta tafiya da ita daman batada Uwa batada Uba na gaji da ci she ta, na baku ita ku tafi da ita, shegeya bakar annoba wane kalar masifa kuma kika janyo muna yau,
Su dai dogarai zuba mata na mujiya sukai suna jiran isowar sarki, Tsohowa ce ta shigo Inna ta shiga gaishe ta tareda bata hakuri "Don Allah kuyi hakuri Wallahi bani na haife ta ba ku min rai Uban ta baya kusa idan ya dawo zan isar da sakon ku in yaso sai kuzo ku kama shi ku tafi dasu duka, amma don Allah ku min rai, Inna ta fada tareda fashewa da kuka, kamar wace aka yiwa wani mugun abu,
Daga Sarki har Tsohowa dariya ma abun yaso basu, nan take suka shaida mata ba abunda Sapna ta musu face taimaka mata da tayi, kuma tana son abata Sapna ta dawo da zama gidan ta, ai nan take Inna tace "Ku tafi da ita na baku, na sallama muku ita halak malak, ku jira na kwaso muku kwamacalan ta, mamaki bayyane a kan fuskar tsohowa tace ai baza ayi haka ba, ina Baban nata ai shine yakeda ikon bada izini mu tafi da ita ba ke ba,".
"ku tafi da ita, kwai ai shi Uban babu abinda zai ce ku tafi, da ita dama shima ba iya ciyar da ita yakeyi ba, ni nake taimaka musu ina basu abinci", ta fada tana jefawa Sapna harara.
batayi mamaki ba dan tasan mafiyin haka Inna na iya yi mata, kuma ba bincike ba komai zata badata ga mutanan da bata sani ba, amma ba komai, zata zauna dasu ko da zasu ringa yankar naman jikinta.
"to shikenan babu damuwa , ko ban zoba zan yo mishi ake, Nainah muje" , ya fada yana yin hanyar waje, dukansu binshi sukayi a baya.
fifita sukayi, cikin motocinsu farare masu masifar kyau suka shiga suka tafi abinsu.
saida suka tafi kafin Inna ta fara cizon yatsa , tana cewa "mai ma yasa na basu ita,shikenan zata shahara ni nawa ahalin nanan, inama ace Ummi suka naimi na basu ko Abasiyya, Allah yasa tayi musu wani abun su korota kowa ma ya rasa". ta fada tana cizon yatsa fuska cike da bakin ciki da hassada
Baba ya shigo gidan fuskarshi a washe babu alamar wani tashin hankali, da yake sun haɗu da mai martaba ya yi, mishi bayanin komai, amma bazai taɓa nunawa Inna ya sani ba.
"Lafiya dai Tabawa maike faruwa kiketa safa da marwa" batayi mishi magaba ba sai wata uwar harara da ta dallah mishi.
"Allah ya baki hakuri", ya fada yana shigewa ɗaki.
**************
basu tsaya ko ina ba sai, kofar part din Nainah kama hannun Sapna tayi suka shiga part dinta, shima tsararen part ne mai masifar kyau..........
*muje zuwa......*
*ZAKU IYA TURO DA KUƊINKU TA WANNAN ACCOUNT NUMBER DIN*👇
*1499884120 UMMA SALMA SANI ACCESS BANK.*
*KO KUMA WANNAN ACCOUNT DIN👇*
*2153892190*
*U.B.A BANK*
*MARYAM YUSUF*
*IDAN KUN TURO TO KU TURO SHAIDAR BIYA TA WANNAN NUMBER👇*
*0703371851*
*KO KUMA WANNAN NUMBER DIN👇*
*****
*ƳAR LELEN ROYAL STAR CE🧚♀️🧚♀️, TARE DA SAHIBAR ROYAL STAR💫*