11-12
by @autarmama
_👑👑PRINCE SAPWAN👑👑
*STORY AND WRITEN BY SALMEERT (AUTAR MAMA, ƳAR LELEN ROYAL STAR) AND MARYAM YUSUF (OUMMU JUWAIRIYYA)*
*YARDA MUKA FARA LITTAFINNAN RANAR 20 MAY 2022, ALLAH KA BAMU IKON GAMAWA LAFIYA*
*WANNAN LITTAFIN ƘIƘIRARAN LABARINE, BA MUYISHI DAN CIN ZARAFIN WANI KO WATA BA, IDAN YA YI DAI-DAI DA TSARI KO YANAYIN GIDANKU, KO MASARAUTARKU TO KUYI MANA AFUWA, BADA SANI BANE*
*BAMU YARDA WANI KO WATA, SU CHANJA MANA TSARI KO YANAYIN LABARINMUN BA*
*WANNAN LITTAFIN NA KUƊINE #200 KACHAL NE KUDINSHI KI BIYA KI KARANTA, CIKIN KWANYAR HANKALI*
*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}
***
```MARUBUTA MASU AIKI DA FASAHA DA ZALLAR TSAKWARON AMANA, FAƊAKARWA HAƊI DA NISHAƊANTARWA GAMI DA WA'AZANTARWA HUNM WANI ABU SAI ROYAL STAR'S WRITER'S✍🏻📚✨⭐✨ ASSOCIATION RUWA ƘAƊAI KE MAGANIN ƘISHI (R..S..W..A) / 💪💪💪
UP-UP-UP BEST WRITER'S EVER💖 ```
*ALƘALAMINMU ƳANCIN*
_________________________
Assalamu alaikum,ma Abota bibiyar litattafan Salmeert Sani Salman(Autar Mama, Ƴar Lelen Royal Star🧚♂️🧚♂️🧚♂️)to yanzu ma ina farin cikin sanar daku littafin na , na YAR GAN-GAN.
littafin na kuɗine idan kina bukata zaki iya fara biya tunkafin free page yaƙare,gamai son littafin Yar gan-gan zai turo da kuɗinsa ta wannan account din👇
Umma Salma Sani access bank 1499884120
idan kuma kati ne zaku turo katin MTN ta wannan number ***
Bamu son VTU ba zamu kar ɓaba.
idan kin turo kuɗin zaki turo mana da shaidan kin biya ta wannan number ***
Normal group 200 only zakuna samun page daya (1) a rana
Special group 300
zakuna samun page (2) a rana duk wanda ki kaga ya miki sai ki shiga.
bashi kaɗaiba zaku ringa samun litattafai na irin su.
1)Rayuwarmu Ayau.
2)Bara gurbi.
3)Amaryar Zamani.
4)Rayuwar Farouq.
Assalamualaikum barkan mu da wannan lokaci *ABMAR COLLECTION* ina nan na kawo muku kayana masu kyau da sauki👌🏻
KAMAR SU:-
Atamfa, Atamfa Mai golden,💁♀️
Lace ,Shadda lace
Yadi, Shadda
Abayas💥
Kids wear
Takalmi, jaka, mayafai💥
Sleeping dress, kananan kaya na gayu🔥kayan kitchen,
DA DAI SAURANSU ina Sokoto ina tura kaya ko ina da izinin ubangiji mai son kayana pc ina maraba daku siyan daya ko sari👏🏻domin neman karin bayani sai ku neme ni ta wannan number waya👉***
nagode kwarai da gaske💃💃
_________________________
*BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
*PAGE 11&12*
"""""""""""""""""""""""""To , naji korafinki, amma zanje na tuntuɓi, Nainah naji yarda za'ayi", ya fada yana gyara Alkabbar jikinshi tare da ficewa dan dama shiri ya gama zai fita fada.
ita kuwa murmushi kawai ta saki, dan tasan tabbas Nainah, zata Amince dan tana matuƙar kaunar Yarinyar, tana cikin tunani ne Sapna ta shigo part din da Sallama, kusa da Gimbiyar ta zauna tare da gaisheta, Ansawa tayi tare da tanbayarta ya Nainah, da "Alhamdulillah", ta ansa mata.
tsigul kamar an tsunkuleta, ta tashi ta nufi ɗakin Prince ,bacci ta tarar dashi yanayi, zama tayi, kusa dashi dan kishingiɗa tayi, itama baccine ya yi gaba da ita.
Mommy ce taji shiru-shiru bataji motsin Sapna ba hakan yasa ta nufo dakin dan ganin ko lafiya, bacci ta tarar dasu kowa nayi, cikin kwanciyar hankali, inda shi kuma Prince da ka kalli yarda yake baccin zakasan ba cikin hayaccinshi da natsuwarshi yakeyi ba.
murmushi tayi,tare da girgiza kai, fita tayi tare da janyo musu kofar ta koma parlour tare da maida hankalinta kan, mujallar da take, gani.
har kusan magrib sannan, Sapna ta tashi, ido biyu taganshi, a kwance ya kafeta da ido kamar yasan mai ake ciki, ga miyau duk ya zalalo ya ɓata mishi cute face nashi, murmushi tayi kafin ta dauko towel ta goge mishi, gyara shi tayi, kafin ta fito daga ɗakin, dai-dai kuma lokacin da Ɗan Waziri, da yazo duba Prince, da yake duk Sa'annine yanason, suyi Abota da Prince amma shi kuma baya kulashi, hakan yasa tun yana sonshi, yaji ya tsaneshi, saboda halin ko in kula da yake nuna mishi, tare da zugar Waziri .
wani mayataccen kallo ya aika mata dashi, yana lashe lips dinshi, wanda da ka kallesu zaka gane yanashan sugari, saboda yarda sukayi baki, ga idannunshi da suka, dan ja alamar dai, tabbas yana shan wani abu.
gaishe shi, tayi tare da wucewa, wani kallo yabi bayanta dashi, tare da haɗiyar miyau makuttt.
ita kuwa batama san yanayi ba Gimbiya tayi ma Sallama tare da fita, dan magrib ta kusa.
saida ta fita kafin, ya dawo hayyacinshi, juyowa ya yi, Gimbiya ya kalla itama kallonshi tayi, durkusawa ya yi tare da gaisheta, yana sosa keya.
Ansawa tayi, ya mai jiki ya yi mata, shima ta amsa kafin ya tashi ya fita,10 minutes tsakani saiga, Kilishi ta shigo tana karairaya tare da tausar cingam kas! ƙas!! ƙaƙaƙas!!! , kamar wata budurwa.
ita kuwa Gimbiya bata ko ɗaga ido ta kalleta ba tunda ta kalleta so daya, takawa ta farayi har saida tazo gaban Gimbiyar kafin tace ,"Sannu fah Uwar Prince, ko ince nakasashe, wanda baya iya haddasama kanshi komai, ai kaɗan kuka, gani badai ku masu mulki ba, to ayi mulkin mu gani", ta fada tana dariyar shaƙiyanci.
ita dai Gimbiya batace komai ba, sai kallon Kilishi take .
ita kuwa kaɗa kai tayi tare da cewa, "toh bari ki jiya a haka zaku kare kaskance daga shi har ke, ni nan da kike gane ni yar gidan sarauta ce dole ya zamato ni ne shugabanku a fadar nan, amma saboda kina wulakantaciya har wani dadi kike ji, don za'a nade dan ki a matsayin Sarki, toh wallahi kunyi kadan,
Ai ba'a nade mai zubar miyau a baki a matsayin sarki wanda baya iya yiwa kan sa komai, ya riga da ya zama wawa, dolo, samna, Hahahahaha, ai duk wanda yaci tuwo da mu toh wallahi miya yasha, Kilishi haka ta cigaba da furta kalamai marasa dadi ga Gimbiya Khadija wanda sai da ta saka Gimbiya kuka sosai,
******************
Kamar kullum yanda Naina ta saba kyautatawa Baba tun bayan dawowar Sapna gidan ta, ko yau ma haka ne, buhun shinkafa da na Alkama da na Gero, ga galan-galan na man gyada da man ja an kawo gidan Malam, sosai Baba ya shiga musu godiya yana mai jin dadi,
Ya yinda bakin ciki ya taru yayiwa Inna yawa, wai duk wannan abubuwan da ake musu sanadiyan Sapna ce, albarkacin ta ne suke ci, ina ma ace Abbasiyyah ce, ai yau da ta fi kowa murna, don ko kadan bata fatan ace Ummi ce, acewar ta ai bata biyo halin ta ba, tamkar ba ita ce ta haife ta ba, ni kuwa Ummu juwairiyyah na kalle Yar lelen royal tareda cewa kaji su Inna anga banza dole ayi sakin layi,
Wani irin sauti na dinga jiyowa daga cikin dakin shiyasa na kara hanzari domin na dauko muku rahoto shin ko meke faruwa??? Waziri na hango saman Fulani turmi da tabarya, tamkar mata da miji, wal iya zubillah, Allah ya tsare muna imanin mu, tamkar ba matar aure ba, sai da ya gama biyan bukatar sa sannan ya iya rabuwa da ita,
"Ni dai Inna yau gaskiya bazan iya je kauyen illo ba, wallahi ina son naje naga yar uwata ace yau kusan mako hudu kenan ban saka ta a ido ba, haba Inna ai da ace Abbasiyyah ce tun ban furta ina son zuwa ba zaki ce naje amma da yake yar kishiya ce dole kiyi shiru ba tareda kin san a ina ne take rayuwa ba, ni dai na gaya miki yau wallahi gidan sarki zani naga yar uwata,
Inna sakin baki tayi karara, kafin daga bisani ta fara magana "yoo ni jikan Manu naga ta kaina, Ummi ni kike gayawa magana kai tsaye ba tareda kin ji shakka ta ba" ai kuwa ko Uban ki Ahmadu zai miki tsaye ba inda zaki, idan ma magani tayi miki toh wallahi ahirrrrrr dinta, don ko mai zaki ce min ba bu inda zakije, saboda haka tun ban saba miki ba na tsine miki ki shirya zuwa illo,
*MUJE ZUWA...........*
*ZAKU IYA TURI KUƊINKU TA WANNAN ACCOUNT NUMBER DIN👇*
*1499884120 UMMA SALMA SANI ACCESS BANK*
*KO KUMA WANNAN ACCOUNT DIN👇*
2153892190
*U.B.A BANK*
*MARYAM YUSUF*
*IDAN KUN TURO TO KU TURO MANA DA SHAIDAR BIYAN TA WANNAN NUMBER DIN👇*
***
*KO KUMA WANNAN NUMBER DIN👇*
***
*ƳAR LELEN ROYAL STAR CE🧚♀️🧚♀️🧚♀️, TARE DA SAHIBAR ROYAL STAR💫💫💫*