13-14
by @autarmama
👑👑PRINCE SAPWAN👑👑
*STORY AND WRITEN BY SALMEERT (AUTAR MAMA, ƳAR LELEN ROYAL STAR) AND MARYAM YUSUF (OUMMU JUWAIRIYYA)*
*YARDA MUKA FARA LITTAFINNAN RANAR 20 MAY 2022, ALLAH KA BAMU IKON GAMAWA LAFIYA*
*WANNAN LITTAFIN ƘIƘIRARAN LABARINE, BA MUYISHI DAN CIN ZARAFIN WANI KO WATA BA, IDAN YA YI DAI-DAI DA TSARI KO YANAYIN GIDANKU, KO MASARAUTARKU TO KUYI MANA AFUWA, BADA SANI BANE*
*BAMU YARDA WANI KO WATA, SU CHANJA MANA TSARI KO YANAYIN LABARINMUN BA*
*WANNAN LITTAFIN NA KUƊINE #200 KACHAL NE KUDINSHI KI BIYA KI KARANTA, CIKIN KWANYAR HANKALI*
*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}
***
```MARUBUTA MASU AIKI DA FASAHA DA ZALLAR TSAKWARON AMANA, FAƊAKARWA HAƊI DA NISHAƊANTARWA GAMI DA WA'AZANTARWA HUNM WANI ABU SAI ROYAL STAR'S WRITER'S✍🏻📚✨⭐✨ ASSOCIATION RUWA ƘAƊAI KE MAGANIN ƘISHI (R..S..W..A) / 💪💪💪
UP-UP-UP BEST WRITER'S EVER💖 ```
*ALƘALAMINMU ƳANCIN*
_________________________
Assalamu alaikum,ma Abota bibiyar litattafan Salmeert Sani Salman(Autar Mama, Ƴar Lelen Royal Star🧚♂️🧚♂️🧚♂️)to yanzu ma ina farin cikin sanar daku littafin na , na YAR GAN-GAN.
littafin na kuɗine idan kina bukata zaki iya fara biya tunkafin free page yaƙare,gamai son littafin Yar gan-gan zai turo da kuɗinsa ta wannan account din👇
Umma Salma Sani access bank 1499884120
idan kuma kati ne zaku turo katin MTN ta wannan number ***
Bamu son VTU ba zamu kar ɓaba.
idan kin turo kuɗin zaki turo mana da shaidan kin biya ta wannan number ***
Normal group 200 only zakuna samun page daya (1) a rana
Special group 300
zakuna samun page (2) a rana duk wanda ki kaga ya miki sai ki shiga.
bashi kaɗaiba zaku ringa samun litattafai na irin su.
1)Rayuwarmu Ayau.
2)Bara gurbi.
3)Amaryar Zamani.
4)Rayuwar Farouq.
Assalamualaikum barkan mu da wannan lokaci *ABMAR COLLECTION* ina nan na kawo muku kayana masu kyau da sauki👌🏻
KAMAR SU:-
Atamfa, Atamfa Mai golden,💁♀️
Lace ,Shadda lace
Yadi, Shadda
Abayas💥
Kids wear
Takalmi, jaka, mayafai💥
Sleeping dress, kananan kaya na gayu🔥kayan kitchen,
DA DAI SAURANSU ina Sokoto ina tura kaya ko ina da izinin ubangiji mai son kayana pc ina maraba daku siyan daya ko sari👏🏻domin neman karin bayani sai ku neme ni ta wannan number waya👉***
nagode kwarai da gaske💃💃
_________________________
*BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
*PAGE 13&14*
______________✍️Ummi shiru tayi, tana tunanin mafita, domin kuwa in ana ha maza ha mata ita sai taje fadar Sarki domin ganin yar uwarta, tunda ta kudurta aniya, don kuwa tasan da ace Abbasiyyah ce da kullum sai Inna ta dame ta da taje, amma da yake, ita Sapna yar kishiya ce, dole Inna ta nuna banbanci, duniya kenan, budurwar wawa,
*****************
"Ke bakida hankali ne, ni nake gaya miki magana kina nuna min iyayi, toh bari na gayamiki koh Uwar ki Saudi bata isa tayi sa in sa dani ba, Fulani ta fada afusace,
Jiki na rawa, tace "Kiyi hakuri Mama Fulani na daina, amma sai nake ganin Yarima yafi karfi na, ba zai amince da aure na ba, kuma ni Mama Fulani, me zanyi da Yarima yanzu wanda bayada amfanin komai kuma ma..., wani irin wawan tsawa Fulani ta buga mata, tareda cewa,
"Ke dabban ina ne wai, bakida wayo sam, toh an gaya miki da ace Yarima na lafiya shima zai amince da aure ki ne? Amma har zan hada ki da Yarima saboda wani biyan bukata na shine kike gaya min magana, toh ki shiga taitayin ki, tun ban saba miki ba, kuma ko ki so ko ki k'i dole ne ki amince da auren Yarima kuma duk abunda na saka ki dole ne kiyi"
Luba saura kadan fitsari ya kubce mata saboda, tun fil azal tana mugun tsoron Fulani, ko kadan bata bukatar abunda zai hada ta da ita, don koh Maman ta Saudi tana mugun shakkar Fulani belle ita, toh dai ko Luba bata da mutunci domin kuwa ta iya rashin kunya kala-kala, amma duk rashin kunyar ta ko alama bata son shiga zabgar Fulani,
Don acikin yan uwan Maman ta babu wace ta tsana irin Fulani, ko mai irin sunan Fulani bata son a fadi sunan sa idan har tana kusa, don Fulani muguwa ce na bugawa ga jarida,
*******************
Sapna ce zaune sai magiya take tayiwa Naina "Don Allah Naina ki bar ni naje gefen can, Allah daga gani awajen akwai ni'ima sosai, bazan jima ba Allah Naina nayi alkawari" cewar Sapna ta dan shagwabe fuska har sai da ta soma ba wa Naina dariya, "Ni ban ce karki je ba amma ki kula sosai kinji yar kwarai, kuma kinyi alkawari bazaki jima ba, saboda haka, karki jima,
"Insha Allah tsohowa" daga Naina har ita dariya sukayi, daga bisani ta tashi zuwa part din su Kilishi, a wajen wani gindin bishiya ta zauna tana shakar iskan wajen, tareda yin wasa da ya'yan margaryar da suka fado, ji tayi an dafa ta, a dan zabure ta juyo domin taga ko wace ta dafa ta,
Luba murmushi ta sakan mata nan take kuma ta daure fuska, domin ita Luba tanada tsananin assada da bakin cikin farin cikin wani, tunda take duniya bata taba ganin mai irin kyawun Sapna ba, ita ko kadan bata son taga wani ya fita, "ke! wace ce ke?" Cewar Luba, "tambaya ko kuma neman sani?" Sapna ta fada ba tareda ta kalle ta ba,
Lubu dariyar mugunta tayi tareda cewa, "kiyi hakuri ina son mu zama kawaye, masu gayawa juna sirrin su, kin fahimce ni, yanzu ki bani tarihin rayuwar ki ke wacece? Cewar Lubu tana mai zama kusa da Sapna, "sunana Sapna Ahmad ni haifafiyar yar garin..... Sapna ko me ta tuna, shiru tayi ba tareda ta sake furta komai ba, Lubu kallon kurilla tashiga yi mata, can tace "Eh ke ki fara bani labarin rayuwar ki,
**********************
"Yanzu babu wani maganin da zaka iya taimaka ka bani?" Cewar Fulani tana zaune agaban boka, wani irin wawan murmurshi boka ya yi kafin yace, "lalle nagaya miki babu abunda zamu iya masa face wannan kwalban ruwa da na baki, ki tabbatar da an shafa mishi aduk ilahin jikinsa, kuma wannan kullin magani, matar sa zata tura agaban ta sai ya sadu da ita,
Toh ina mai gaya miki, bazai kara numfashi ba aduniya idan har ya kusanceta, boka ya fada tareda fyace majina, Fulani duk ta takura, domin warin dakin duk ya ishe ta, amma saboda bakar jaraba daurewa tayi tace "bashida mata faa, taya za'a yi kenan?"
"Wannan kuma matsalar kice, amma idan har kina son kashe shi a gaggauce, toh kiyi yanda nace kawai" cewar boka, "toh insha Allah...... "Dakata munafuka, karki sake kiran wannan suna a nan" "Yi hakuri boka mantawa ne nayi" Fulani ta fada tareda ficcewa daga dakin,
************************
"Ku banzaye ne wallahi nace duk rai daya zan baku million biyar idan har zaku iya yin kidnapping din shi, daga shi har ita amma kun tsaya kuna kawo min kabli da ba'adi, idan bazaku iya bane ku fada mun sai na saka wasu su min iyeeee" cewar Kilishi afusace, idan ran ta yayi dubu toh ya baci, domin kuwa wani irin bakin cikin Yarima da Gimbiya Khadija take, ji take duk sun addabe rayuwar ta, idan har ba kashe su akayi ba toh lalle batada sukuni,
***********************
"Nima na jima ina wannan tunani domin kuwa su din sun dace da junan su, kuma na yaba da tarbiyar yarinyar nan tun aranar da na fara dora ido na akanta, Gimbiya ashe kema haka ne a gunki, toh Allah yasa Naina ta amince" cewar Sarki, "ka kwantar da hankalin ka Mai martaba nasan Naina ita ma zatayi kwadayin Sapna ta zama matar jikan ta, bazata so Sapna tayi nisa da ita ba, domin na fahimce akwai shakuwa atsakanin su sosai,
"Naina da fatan kin wuni lafiya, nace ya maganar mu dake, naga banji kira daga gare ki ba, koh har yanzu bakiyiwa Mai martaba magana bane? Ko kuma bakya ra'ayin Lubabatu amatsayin surukar ki? Haka Fulani ta dinga jerawa Naina tambayoyi batareda ta dasa aya ba, har sai da ta kai karshen tamboyoyin nata, Naina shiru tayi batareda tasan mai zata ce ba, can ta numfasa tareda cewa.....
*MUJE ZUWA...........*
*ZAKU IYA TURI KUƊINKU TA WANNAN ACCOUNT NUMBER DIN👇*
*1499884120 UMMA SALMA SANI ACCESS BANK*
*KO KUMA WANNAN ACCOUNT DIN👇*
2153892190
*U.B.A BANK*
*MARYAM YUSUF*
*IDAN KUN TURO TO KU TURO MANA DA SHAIDAR BIYAN TA WANNAN NUMBER DIN👇*
***
*KO KUMA WANNAN NUMBER DIN👇*
***