15-16
by @autarmama
👑👑PRINCE SAPWAN👑👑
*STORY AND WRITTEN BY SALMEERT (AUTAR MAMA, ƳAR LELEN ROYAL STAR) AND MARYAM YUSUF (UMMU JUWAIRIYYA)*
*YARDA MUKA FARA LITTAFINNAN RANAR 20 MAY 2022, ALLAH KA BAMU IKON GAMAWA LAFIYA*
*WANNAN LITTAFIN ƘIƘIRARAN LABARINE, BA MUYISHI DAN CIN ZARAFIN WANI KO WATA BA, IDAN YA YI DAI-DAI DA TSARI KO YANAYIN GIDANKU, KO MASARAUTARKU TO KUYI MANA AFUWA, BADA SANI BANE*
*BAMU YARDA WANI KO WATA, SU CHANJA MANA TSARI KO YANAYIN LABARINMUN BA*
*WANNAN LITTAFIN NA KUƊINE #200 KACHAL NE KUDINSHI KI BIYA KI KARANTA, CIKIN KWANYAR HANKALI*
*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}
***
```MARUBUTA MASU AIKI DA FASAHA DA ZALLAR TSAKWARON AMANA, FAƊAKARWA HAƊI DA NISHAƊANTARWA GAMI DA WA'AZANTARWA HUNM WANI ABU SAI ROYAL STAR'S WRITER'S✍🏻📚✨⭐✨ ASSOCIATION RUWA ƘAƊAI KE MAGANIN ƘISHI (R..S..W..A) / 💪💪💪
UP-UP-UP BEST WRITER'S EVER💖 ```
*ALƘALAMINMU ƳANCIN*
_________________________
Assalamu alaikum,ma Abota bibiyar litattafan Salmeert Sani Salman(Autar Mama, Ƴar Lelen Royal Star🧚♂️🧚♂️🧚♂️)to yanzu ma ina farin cikin sanar daku littafin na , na YAR GAN-GAN.
littafin na kuɗine idan kina bukata zaki iya fara biya tunkafin free page yaƙare,gamai son littafin Yar gan-gan zai turo da kuɗinsa ta wannan account din👇
Umma Salma Sani access bank 1499884120
idan kuma kati ne zaku turo katin MTN ta wannan number ***
Bamu son VTU ba zamu kar ɓaba.
idan kin turo kuɗin zaki turo mana da shaidan kin biya ta wannan number ***
Normal group 200 only zakuna samun page daya (1) a rana
Special group 300
zakuna samun page (2) a rana duk wanda ki kaga ya miki sai ki shiga.
bashi kaɗaiba zaku ringa samun litattafai na irin su.
1)Rayuwarmu Ayau.
2)Bara gurbi.
3)Amaryar Zamani.
4)Rayuwar Farouq.
Assalamualaikum barkan mu da wannan lokaci *ABMAR COLLECTION* ina nan na kawo muku kayana masu kyau da sauki👌🏻
KAMAR SU:-
Atamfa, Atamfa Mai golden,💁♀️
Lace ,Shadda lace
Yadi, Shadda
Abayas💥
Kids wear
Takalmi, jaka, mayafai💥
Sleeping dress, kananan kaya na gayu🔥kayan kitchen,
DA DAI SAURANSU ina Sokoto ina tura kaya ko ina da izinin ubangiji mai son kayana pc ina maraba daku siyan daya ko sari👏🏻domin neman karin bayani sai ku neme ni ta wannan number waya👉***
nagode kwarai da gaske💃💃
_________________________
*BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
*PAGE 15&16*
______________✍️"Fulani kin ga dai Yarima bashida lafiya, ai ba yanda za'a yi kuma a masa aure yanzu, shiyasa kawai ni bangaya ma Sarki ba, in da dai kin hankura har ya samu lafiya, sai a tambaye shi idan har yana ra'ayin ta, ai Lubabatu tamkar jikanyata ce, bazan ki auren ta da Yarima ba" Naina ta fada, da alamar tsoro a fuskar ta,
Fulani kanzil bata ce da ita ba, fuuuu ficcewa tayi daga cikin dakin Naina ta nufa ɓangaren ta, "Hmmmmmmm" Naina duk abun duniya ya ishe ta, tama kasa gane kan Fulani, yaushe za'a yiwa marasa lafiya aure, salon aje a aure masa wace zata dinga cin amanar sa, tunda komai baya iya yiwa kan sa, tabbas idan har za'a yiwa Yarima aure yanzu,
Toh ya zama dole a nema masa mace kamila, jaruma mai amana wace zata so shi saboda Allah ba wai don komai ba, domin kuwa duk macen da zata zauna dashi, toh zata kai zuciyar ta nesa, kuma ya zama dole ta zama mace mai hakuri, Fulani ran ta ya baci ba kadan ba, daman tasan duk shirin da zatayi, Naina sai taso ta bata matsala, amma zatayi maganin ta ne,
***********************
_____________Sai da Ummi ta tabbatar da Inna tayi nisa a bacci, sa'anan ta tashi daman a shirye take, wufff tayi hanyar waje, karo taci da Baba, har ta dan tsorota don batayi tunanin shine ba, "Ummi ina zuwa haka? Naga sai sauri kike tayi" cewar Baba "Eh daman Baba fadar Sarki zani, naje naga Sapna, tun fa sanda ta bar gidan nan ba wanda ya taba je ganin ta, haba sai kace wace batada dangi,
"Kinyi gaskiya Ummi je ki Allah ya miki albarka, amma kin gayawa........... koh? "eh Baba na gaya mata, Ummi ta fada tana waiwaya baya koh Inna bata fito ba, "Toh ina gaida Mai Martaba da su Gimbiya, Ummi maza kije karkiyi dare, kice ina gaida Mamana, Allah ya yi muku albarka baki daya,
"Haha Inna ina kike ana nan ana munafucinki, cewar Abbasiyyah da yanzu nan ne shigowar ta gidan, Allah kadai yasan daga ina ne ta fito, Ummi ko kallon ta batayi ba tayi sauri ta fice daga gidan gudun kar Inna ta tashi ta hana ta zuwa a karo na biyu,
*************************
Kamar kullum kwance yake saman tafkeken gadon sa mai dankaran kyau, sai miyau ke malalowa daga cikin bakin sa, sanye yake da farin singlet da gajeren wando (short niker), sallama dauke a bakin ta ta shiga dakin, ganin tayi ba kowa adakin nashi,
Da sauri ta juya zata fita daga cikin dakin ganin cewa daga shi sai singlet da gajeren wando, toh gaskiya ita bazata iya jure kallon sa a hakan ba,
"Sapna ina kuma zuwa, ta jiyo muryar Gimbiya daga cikin bandaki, au daman ashe tana ciki, sunkuyar da kai tayi kasa tareda cewa, "Daman...daman... gani nayi ba kowa a dakin" sarai Gimbiya ta gano ta amma sai bata ce komai ba, sakawa Prince kayan sa Gimbiya tayi sannan ta kalle Sapna tareda cewa
"Toh yanzu shikenan koh? Sapna rufe fuska tayi da dukkan tafin hannun ta, alamar taji kunya, ita dai Gimbiya sosai Sapna ke burge ta, Allah dai ya cika mata nufin ta, amma tabbas sosai take kwadayin Sapna ta zama matar Dan ta tilo daya,
Kamar kullum ko yau bata bar part din *PRINCE SAPWAN* ba har sai kusan 9:00, sosai Yarima yake kallon ta kamar wani zai kwace masa ita, komai baya ganewa haka zalika komai baya iya yi wa kan sa, sai miyau dake ta malala a bakin shi, ita kuwa bata gajiya da goge masa,
*************************
Sosai Sapna ta ji dadin zuwan Ummi domin kuwa sunyi firar yaushe gamo, har sauyin da suka samu agidan duk Ummi ta bata labari, ta ce kusan kullum sai Mai Martaba ya saka a kawo musu abinci, yanzu sam ba su da damuwan abinci, sai dai har yanzu Inna na nan yanda ta ke babu wani sauyi tattare da ita,
Nan dai suka dinga firar su, suna dariya harda Naina a firan na su sai kusan magariba Ummi ta koma gida tana mai kewar Yar'uwa ta ta,
Tun kafin ta shiga gida ta ji Inna na ta zagin Baba, "E mana wallahi tunda na ce kar Ummi taje amma ka tilasta mata zuwa ganin yar iskar nan to banga uban da zai mata tsayi ta kwana a gidan nan ba yau, ai sai dai ta kwana a gidan Uban wanda ya aike ta", ba dai a wannan gida ba, Ummi dauke da sallama a bakin ta ai bata ida sallamar ba, Inna ta nufe ta gadan-gadan ji kake fuuuuuu!!!!
Inna fadi tayi kasa, da yake Abbasiyyah bata share ruwan da suka zuba a kasa ba alokacin da ta gama wanke-wanke ba, tsantsin ruwan ne ya ja ta, ai kuwa wani irin wawan ihuuu Inna ta kwala tana neman agaji, Abbasiyyah me za ta yi ban da dariya, ai kuwa dariya ta shiga kyalkyalawa son ran ta,
Da sauri Ummi ta je ta nufe ta domin kai mata agajin gaugawa, amma da yake Inna karshe ce ababin rashin mutunci, duka ta kai wa Ummi ta na fadi "Kar ki kuskura ki taba ni da wannan hannu na ki, wallahi Ummi zan yi mummunar bata miki rai" tana fada ta na citzon kasan lebon ta, da dukkan alamu ba kadan take jin jiki ba,
Muje zuwa......... Yaseen an kusa gama free page😂🤪😝 Hajiyata kar fa ki bari ayi wannan tafiya ba ke, domin kuwa yanzu ma aka soma labarin, wannan salo na daban ne da saura ina gaya miki🥳💃
*ZAKU IYA TURI KUƊINKU TA WANNAN ACCOUNT NUMBER DIN👇*
*1499884120 UMMA SALMA SANI ACCESS BANK*