19-20
by @autarmama
*LAST FREE PAGE🤣🤣🤣🤣*
*PAGE 19&20*
""""""""""""""""""""""""""""Bakin part din ta tsaya, Sallama sukayi kafin ta juya.
ita kuwa Sapna saida ta goge hawayen fuskarta sosai, kafin ta karasa shiga parlourn da sallama murmushi malale akan fuskarta, amma kallo daya zakayi mata kasan tayi kuka.
Ansawa Nainah tayi, tana kare mata kallo, chan kuma sai tace " Lafiya kuwa, Sapni?," da yake kusan lokuta haka take kiranta dashi.
"Lafiya lau mana, Yar tsohuwa, mai kika gani?", ta fada tana zama kusa da ita.
murmushi tayi kafin tace,"naga kamar kinyi kuka ne", ta fada tana kwanto da kanta kan cinyarta dan itama ta saba da ganinta kullum saman cinyar tata.
kwalla ce ta zubu, mata sharrr kafin tace , "Inason inje gida naga Abba ne", ta fada tana goge hawayen.
sosai tausayinta ya kamata dan tasan, wani abun akayi mata, ta boye tace gida takeson zuwa.
"kwantar da hankalinki indai gidane, gobe sai mu shirya muje, tare ma zamuje kinji?", ta fada tana kallonta.
murmushi ne ya suɓuce mata kafin tace "to Allah ya kaimu goben" ta fada da farin ciki dan tunda tabar gidansu bataje ba .
da "Ameen" Nainah tace, kafin suka cigaba da fira, inda kasa-kasa Sapna take ansa mata, saboda tunanin Prince da ya addaba mata, kwana biyun nan, fuskantar hakan yasa Nainah yin , murmushi kafin tace.
"Tashi ki kawo mana , abinci dan yunwa nakeji, ke na tsaya jira dama ki dawo, ke kuma naga kamar kin ciko tunbinki, dan haka tashi ki zubomin ni", ta fada tana shafa cikinta.
yarda tayine ya yi, mugun bawa Sapna dariya hakan yasa ta dara, kafin ta , tashi ta nufi kitchen din.
********************
shi kuwa Prince tunda, Kilishi ta mari, Sapna ya waniyi hade rai kamar zaiyi kuka, nikuwa nace wannan kamar ya fara dawowa cikin sense dinshi.
daga karshema kafin Gimbiya ta dawo ma har ya yi, bacci hakan yasa ta gyara mishi kwanciya tare, da kashe mishi light.
*******************
Kilishi ce zaune, parlounta tana cin fruit din da aka yanyanka, aka ajiye mata a gabanta.
sai wani isa take, da takama ita daya, ni kuwa nace , kaga isar baka isaba🤣, ita tana ganin ta isa har take takama Alhalin bata kokai matsayin ba.
Sarkin kofane, ya shigo ko kallonshi batayi ba, shi kuwa taɓe baki ya yi, tare da zama yana cewa, "Allah ya taimakeki, naji ance kina naimana lafiya dai ko?", ya fada yana sunkuyar da kai , kasa dan kallon da Kilishi take aikamishi dashi ya tsoratashi.
"da saninkane wata, Bara gurbi, ta shigo cikin Masarautarnan amma baka fadamin ba", ta fada tana cigaba da shan yankakkun fruit dinta.
"eh to , Mai Martaba ne, da Naina suka kawota, saidai a bangaren Nainah take zaune, Ranki ya dade", ya fada yana sunkuyar da kai.
taɓe baki taji, kafin tace "mtswww, matsiyata, chan musu, ni yanzu tashi ka ciremin kayan nan ma jikinka", ta fada ba alamar wasa.
waige-waige ya fara jiki na kerma, saida ya tabbatar ba kowa kafin ya fara kwance ta zugen wandon, dake jikinshi.
bedroom ɗinta ta nufa, da sauri jiki ma mazari yabi bayanta.
kafin ya shiga bedroom din nata, har ta fara cire kayan jikinta, da sauri yazo ya karasa cire mata, ɓata lokaci suka fara romance din juna, sai wani shidewa sukeyi, aiki ya fara raba mata.
ganin hakan yasa da sauri, na fito tare da rufo musu kofar ,kafin nace Allah ya shiryaku.
******************
Inna ce zaune, tana wakarta tare da kaɗa kai, goro take ɓantala a hankali tana ci, dafsar goron kuwa, ta cika mata baki, dakyar take juya bakin.
Ummie ce gaban murhu
sai ƙaƙaniyar daura musu girki, take .
Abasiyya ce, ta shigo tana taubar chewgum, sai kakas , take kamar wata tsohuwar kilaki, ko sallama batayi ba ta zauna , kan kujera yar tsugunon dake gefe.
waya ta fiddo, yar rakani, kashi, waka tasa ta Ado gwanja, tashi tayi, tare da fara takawa , tana girgiza, Inna ma fara kaɗa kai tayi alamar kiɗan na kaimata,tun tana kada kai, har yakaida ta fara kada kafafu, chan tafiya tayi tafiya, saiga Inna an mike ana gwangwajewa, kamar wata Yarinya , (Allah ya shiryemu ya rabamu da irin wannan tsufan).
Ummie dai ko kallo, basu isheta ba, Aikinta kawai take.
Inna kuwa hardasu kwaso shoki, sai tafawa suke, suna hada jiki ita da Abasiyya kamar wasu kawaye.
Babane ya shigo da Sallama, amma ko kulashi basuyi, Ummie ce ta tashi ta , taroshi tare da Ansa Sallamarshi.
kayan Hannunshi ta ansa tana gaisheshi, ansawa ya yi kafin ya shafa kanta , tace "Allah ya yi miki Albarka".
"Ameen "tace kafin ta wuce ta kaiwa Baba kayansa ɗaki.
wajen ta dawo ta cigaba da aikinta dan dare ya yi, sosai dan kusan 10.
****************
bayan sun gama, cin Abincin ne, ta nufi ɗakinta, dan kwanciya.
wanka tayi, tare da dauro Alwala, saida tayi nafila, kafin tafara karatun Al-qur'ani, ta dade sosai kafin ta,kwantawa saidai fir bacci ya kauracewa idanunta, sai tunanin Prince take, ita kanta yanzu har mamakin , yawan tunaninshi da takeyi take.
sai gurin 1 kafin bacci barawo ya yi, awon gaba da ita, tana like da pillo a hannunta.
*WASHE GARI...*
tunda sassafe Sapna , ta tashi tare da fara shiri, kafin 9 ta gama shiryawa tsaf da ita, cikin Less Maroon mai, bala'in kyau.
Lifaya, ta daura kan kayan , takalmi kawai ta dauka, ta fito parlourn anan ta tarar da Nainah zaune, cikin shirin fita itama, Alkebba ce sanye a jikinta, sai kuma wata wadda take kusa da ita a ajiye.
kusa da Nainar ta zauna tare da cewa "Yar tsohuwa , an tashi lafiya?", ta fada tana murmushi.
itama murmushin tayi kafin tace "lafiya lau Sapni ya kika tashi?", ta fada tana shafa kanta da yake a kwance.
"Alhamdulillah", ta fada tana murmushi.
"wai wannan kan baki kitsashi kullum, kina yawo dashi haka", ta fada tana kallon wani gefen daban.
"yau zanyi ai", ta fada tana dariya.
tashi tayi, tana cewa "bari na dubo Prince kafin mu tafi", ta fada tana mikewa.
rike mata hannu Nainah tayi, juyowa tayi, lifayar jikinta , ta fara cire mata, ita dai tana tsaye batace komai ba, saida ta gama tas kafin, ta dauki Alkebbar ta sanya mata, a jikinta.
murmushi tayi kafin tace,"tayi miki kyau sosai", ta fada tana lotsa gefen kumatunta wanda ya lotsa sakamakon murmushi da tayi.
Sallamar Mai Martaba, ce ta katse musu firar tasu.
"Tubaraqallah Masha Allah", Mai Martaba ya furta cikin ranshi, dan ba karamin kyau Sapna tayi da Alkebbar ba.
gaisheshi tayi, tare da ficewa , ansawa ya yi, da murmushin , yana kallonta dan yasan inda zataje.
zama ya yi, suna gaisawa da Nainah , "an hada komai, ku kawai ake jira", ya fada yana mikewa.
"muma gamunan taje ganin Prince ne da ta dawo, zamu tafi", ta fada tana kallonshi.
"yawwa nima da anjima zanzo gidan, zamuyi maganar nan ", ya fada yana ficewa
*****************
da Sallama, ta shiga part din, Gimbiya ce ta ansa da murmushi, tana dakatawa da shiga ɗakin Prince da takeyi.
Ansawa tayi da murmushi, kan fuskarta ,karasowa tayi gurinta har kasa ta duka ta gaisheta.
ansawa tayi tana cewa "Tubarakallah masha allah , daughter kinyi kyau", ta fada tana murmushi.
murmushin tayi itama , a tare suka shiga ɗakin, kusa dashi ta zauna da murmushi , kan fuskarta.
da kallo ya fara binta, kamar gaula, sosai yake kallonta, Gimbiya kuwa toilet ta nufa, tana murmushi.
a hankali Sapna ta fara cewa," zamuje Unguwa nida Nainah , sai zuwa anjima zamu dawo, ka kula da kanka", ta fada tana shafa sajen fuskarshi.
Annuri kan fuskarshi ne ya fara dishewa amma, ita sam bata lura ba, lekawa tayi toilet din tayi tana cewa.
"Mommy zamuje gida nida Nainah sai zuwa anjima" ta fada tana murmushi.
fitowa itama tayi, Addu'ah tayi mata, kafin tace ta jirata ta fito.
da "to"ta bita, fitowa tayi tana cewa Prince by "byeeeee👋", ta fada tana daga masa hannu.
a parlour ta zauna, tana jiran Ginbiya ,bada dadewa ba, ta fito.
bedroom dinta ta nufa, abubuwan, amfani ta jido da yawa, da kudi, kafin tace akaiwa Ummie sosai tayi nata godiya kafin ta f............
to ko mai , Mai Martaba, zaije ya gayawa Baba???, uhmmm to kodai Prince ya fara dawowa ne cikin sense dinshi ne???, kudai ku cigaba da binmu dan jin ya zata kaya...
muje zuwa.........
*ZAKU IYA TURO DA KUƊINKU TA WANNAN ACCOUNT NUMBER DIN👇*
*1499884120*
*UMMA SALMA SANI*
*ACCESS BANK*
*KO KUMA WANNAN ACCOUNT DIN👇*
*2153892190*
*U.B.A*
*MARYAM YUSUF*
*IDAN KUN TURO TO KU TURO MANA SHAIDAR BIYAN TA WANNAN NUMBER DIN👇*
***.
*KO KUMA WANNAN NUMBER👇*
***
ƳAR LELEN ROYAL STAR CE 🧚♀️🧚♀️🧚♀️, TARE DA SAHIBAR ROYAL STAR💫💫💫