35
by @kitty
A CIKIN DUHU
BONUS PAGEđđ
35
***
Ahmad yana sauka kai tsaye office ya nufa ya fadâa aiki, gajiya ce a jikinsa sosai saidai aiki da âkasashen waje ba kamar aiki da nigeria bane kowane lokacinka cikin kudâinka yake, kwanakin da yayi baya nan saida aka zaftare awannin a albashinsa saboda haka ba zaiyi sanya ba.
Saida dare ya gama aikinsa ko tunanin komawa gida baiyi ba ya fita ya sayo abinci yaci ya shiga toilet dâinsa na cikin office ya kwanta kan kujera baccin gajiya yayi awon gaba dashi, kiran sallar asuba ne ya tadashi yayi sallarsa a office dâin domin yana da tabbacin kamfanin nasu a rufe yake, mamaki yayi ma da babu wanda ya nemeshi.
Yana idar da sallah ya sake komawa bacci bai tashi ba saida yaji bugun âkofa. A gajiye ya tashi dukda baccin da yayi ya kalli agogo yaga 9:30 na safe, zumbur ya miâke ya budâe âkofa ya samu manager dâinsu ne.
âAhmad youâre sleeping?â Managee ya tambaya yana nufar teburin Ahmad, sosa âkeya Ahmad yayi yace âsorry sir i was working till late I didnât know i slept here, but Iâm done with the files here they areâ. Ya miâkawa Manager dâinsu da ake kira da Hakeem files dâin, dubawa hakeem yayi yace ânicely done, sannu daâŠâkoâkari ko?â
Murmushi Ahmad yayi ya mishi alamar eh da kai domin tun zuwansa nigeria ya damu ya iya hausa kuma a hankali yana iyawa. Kallon office dâin Hakeem yayi yace âI think you can rest today we donât have much to do, but we have a meeting tomorrow with some of our clients so be here earlyâ.
Dadâi ne ya ziyarci Ahmad yace âthank you sir, i will insha Allahâ. Hakeem na fita Ahmad ya dâauki kayansa ya fice shima, mashin dâinsa ya dâauka har ya kunna zai tafi yaga fitowar Abbu, tsayawa yayi suka gaisa Abbu yace âya hanya? Naga shigowarka jiya ina shirin fitaâ.
âLafiya lau alhamdulillah, ai anan na kwana ma yanzu babu aiki na kammala jiya zanje na huta ne, na bar Inna a canâ.
âOkay..umâŠya kariman?â
âTana lafiya lauâ. Ahmad ya furta a taâkaice domin sam a yanzu baya so yana maganar karima da Alhaji Ismail musamman yanzu da yaje yaga new karima ba wadda ya saba gani ba.
âBabu wani matsala dai ko?â Abbu ya sake tambaya, Ahmad danne zuciyarsa kawai yayi ga gajiya ga kishi yace âbabuâ.
Sallama sukayi ya wuce gida Abbu kuma ya koma office yana tunanin hanyar da zaibi yaji daga bakin karima ko kuma ya ganta. Tun tafiyar Ahmad yake tunani akan maganar da yayi a station wadda itace kadâai mafita idan yana so ya mallaki karima ya dawo da ita kusa dashi, aurenta kawai zaije nema a bashi kuma a yanzu ya shirya aurenta idan yaso ko me zai faru daga baya sai su san hanyar warwareshi.
Saida Ahmad yayi kwana biyar da dawowa sannan Inna ta dawo, a ranar ta sanar mishi muradin karime da mahaifiyarta sannan ta dâauki kudâin da suka bata ta danâka mishi tace âAhmad mutanennan suna can wata duniya daban amma sun dâauki amana sun bamu saboda yarda, dan Allah ka kula musu da dukiyarsu kaji tsoron Allah a kan wannan amanar ka samo musu muhalli mai kyau wanda zasu sami sakewa a cikiâ.
Bakinnan nashi har âkeya saboda murna yace âinsha Allahu Inna zan riâke amana amma bansan nawa kudâin zai kama a naira ba idan aka juyasuâ.
âSunce ya kai dubu dâari biyu amma ka canza kaga abinda zaâa samuâ.
Zama yayi yace âto ai Inna dâari biyu ba zata sayi gida ba, me zai hana a kama musu haya na shekara guda, a zuba kaya a gidan da gyare-gyare da ragowar kudâin idan suka dawo daga baya sai mugani idan akwai halin sayenâ.
Zare idanu Inna tayi tace âkai Ahmad yanzu wannan uban kudâadâen kace ba zasu sayi gida ba?â Dariya Ahmad yayi yace âKai Inna kamar baki san tsadar rayuwa a yanzu ba? Ai yanzu ba kamar da bane. Wannan gidan namu ma sai kiji an kusan tayashi miliyan idan saidashi zaâayi. Gida a dubu dâari biyu saye gaskiya bazai siyu baâ.
Tagumi Inna ta zuba tace âidan kuwa hakane Ahmad akwai matsala babba. Ta yaya zasu dinga dâawainiyar haya ga kuma ta yau da kullum? Ba wata tsayayyar sanaâa garesu ba dukka zaman zai musu wahala faâ.
âInna a sama musu gidan dai idan suka dawo zasu iya samun sanaâar da ko ma menene amma bana son zaman karime a wannan garin, da ace inada daban bazan dawo ba tareda ita ba, yanzu kuwa tunda ga sauâki ya samu ai duk yanda zanyi naga ta dawo gareni zanyiâ.
Inna kawai jinsa takeyi amma a ranta tana tsoron zamansu a kano da wannan âkarma-âkarmar. Tunani take yanda zata sanar musu da abinda ake ciki saidai babu damar waya, kaf timiya babu sabis sai ka fito farkon bagzane wanda tafiya ce mai nisa ta kusa awa guda, gashi karime babu caji wurinta babu alamun caji ita kuma ba zata iya komawa Timiya nan kusa ba saboda yanayin jikin tsufa.
Kwana biyu da dawowarta tana zaune da yamma taji sallama, cikin sauri ta fita domin tace Ahmad ya turo mata mai ruwa fanfon gidanta ya dâauke, Alhaji Ismail ta gani a jikin motarsa wanda ya sanyata fadâadâa murmushin ta tace âsannu da zuwa Alhaji bismillahâ.
Cikin gidan ya shiga ta shimfidâa mishi tabarma ta kawo mishi ruwa sannan ta dâauko dabino ta ajiye mishi tace âwannan tsarabar mutanen Timiya ce dama inata cewa zan baiwa Ahmad ya kawo makaâ.
âMasha Allah sannu da âkoâkari fa Inna ana ta dâawainiya Allah ya saka da alkhairiâ. Abbu ya furta yana shan ruwan da ta kawo, wannan na dâaya daga cikin abubuwan dake âkara mishi girma a idanun Inna saboda bai taâba zuwa ta kawo mishi abinci ko ruwa yaâki amsa ba, ruwa ne ta dâebo daga randarta a kofi Abbu bai nuna âkyanâkyami ba ya dâaga ya sha abinsa sannan yaci dabino yace âdama nazo ne naji yarinyarnan tana lafiya dai ko?â
âLafiyarta âkalau wallahi tana tareda da uwarta ai hankalinta ya kwanta, saidai dake garin âkauye ne kuma kasan âkauyen can âkasar da namu akwai banbanci tace bata jin dadâin zaman garin, yanzu haka ma mahaifiyarta ta bada kudâi tace a nema musu gida a nan ko da haya ne su dawo saboda karatun ita kariman da sauran abubuwaâ.
Gyadâa kai Abbu yayi yace âokay, amma shi Ahmad bai fadâa min hakan ba koyaushe na tambayeshi ita zaice lafiya take kawaâ. Shiru Inna tayi bata amsa mishi ba yace âkuma ai haya abu ne mai wahala gaskiya, zaifi kyau ace sun mallaki gidan kansuâ.
âTo nima haka nake musu kwadâayi amma abinda ke hannunsu ne ba lallai ya kai ba, yanzu haka dubu dâari biyu suka bayar Ahmad na ta fafutuka a sami haya mai sauâki a ma gidan kwaskwarima a saka musu abinda ya samu kafin su âkarasoâ. Inna ta âkarashe maganar tana kallon Abbu da ya bata dukka hankalinsa.
Amsa mata yayi da âokayâ sannan yace âgaskiya haya bazai yiwu ba, zanga abinda zaâayi akan gidan insha Allah amma kafin wannan akwai magana mai muhimmanci da ta kawoni ina neman alfarma da kuma izniâ.
Inna tamkar ta sauko daga kujera tace âumarni daga garemu Alhaji?â Murmushi Abbu yayi harda Sunkuyar da kai yace âeh Inna tunda kusan dai anan kece kamar uwa a wurinâŠitaâŠyarinyar wato karima. Ina neman Izni a bani damar aurenta kuma ina neman alfarmar a shige min gabaâŠwurin..ummâŠsu nata iyayenâ.
Jim Inna tayi dukda ta jima da sanin maganar sannan tace âTo Alhaji ba wai naâki bane domin duk wanda yace yana son naka ai ya gama maka komai ga kuma dâawainiya da aka sha da ita wadda da ace da mu ka barta ba zamu iya ba, saidai yarinyarnan yanzu tana hannun iyayenta sannan tana da abubuwa da dama a gabanta, shigewa gaba zan iya shige maka amma idan har karime ta amince da kai a matsayin mijiâ.
Wani murmushi Abbu yayi ya duâkar da kai wai shi suruki sannan yace âHakane Inna ai nima babu dole a ciki idan ta amince zanfi kowa jin dadâi idan kuma bata amince ba ma duk babu matsala abinda nayi niyya zanyi musu insha Allah, dama ina tunanin zuwa can garin nasu na gabatar da kaina ne amma nace sai na fara neman izni gareki tukunaâ.
âBabu komai hakan da kayi yayi kyau sosai ya nuna kai dâin mutumin arziâki ne, Allah ya tabbatar da alkhairinsa duk abinda tace zan goyi bayanta dâari bisa dâari amma yanzu bazan maka alâkawarin komai baâ.
Godiya Abbu yayi ya fita daga gidan cikin murna, yana fita ya kira âkaninsa da yake harkar gidaje ya sanar dashi yana neman gida na sayarwa.
âIsmail me zakayi da gida kuma?â âKanin nasa ya tambaya, Abbu bai amsa mishi ba yace âdama akwai tsarin amsa tambayoyi irin d wadâannan idan mutum zai sayi gida? Kaga gida kawai nakeso madaidaici na mutum biyu ginin zamani wanda akwai ruwa da wuta babu matsalaâ.
âAkwai, miliyan dâaya da dubu dari biyuâ. âKanin Abbu ya furta, shiru Abbu yayi ya gama lissafi sannan yace âokay ka turo mun shi a waya naganiâ.
Abbu yana isa gida videon gidan da aka fadâa mishi ya shigo wayarsa. Gida ne âkarami ginin zamani da madaidaicin gate da âkaramin tsakar gida sai bandâaki dâaya a tsakar gidan. Babban palo ne daga gefen bandâakin wanda yake dâauke da dâakuna uku a ciki da kitchen. âDakuna biyu suna kallon juna da bandâaki a tsakiyarsu sai dâaki dâaya daga gefe. Gaba dâaya gidan an mishi sabon fenti milk and yellow yayi kyau sosai.
Abbu kiran âkaninsa yayi yace ânaga gida amma wacce unguwa ce? Banason nesa sosaiâ.
âBa nesa bane a cikin sharadâa gidan yake ai, idan ka samu lokaci kazo muje ka ganiâ.
âOkay zanzo amma yanzu zan maka wiring kudâin ka kular min da gidan na wani dâan lokaci wanda zasu tare basu kusaâ. âKanin Abbu dai tambayoyi ne fal ransa amma baida damar fito dasu domin ya san halin yayan nasa indai ba niyyar fadâin abu yayi ba bazai fadâa ba, tsoronsa dâaya Allah yasa ba aure Abbu zaiyi ba domin sarai ya san halin Amina ba zata taâba amincewa ba.
Abbu yana tura ma âkaninsa kudâin gidan yayi murmushi a ransa yace âna gama da wannan saura next kumaâ.
Zuciyarsa ce ta tunasar dashi âiyalinka fa?â Saidai Abbu yayi saurin kawar da wannan tunanin daga ransa, zaiyi dealing da wannan daga baya amma a yanzu zaiyi âkoâkari yaga ya mallaki karime kafin wani ya mishi shigar sauri.
Duk wasu ayyukansa dake gabansa ya hadâa ya âkarashesu a cikin kwanaki uku sannan yayi canceling duk wani meeting ya dâaga su zuwa lokacin da zai dawo daga timiya, masu muhimmanci kuma ya matso dasu kusa. Bayan ya tabbatar da ya zama free ya kuma bar komai a kan secretary dâinsa da sauran departments ya nufi gida da niyyar fadâa ma Amina tafiya ta kamashi, saidai a rayuwarsa ya tsani âkarya musamman da girman amma kuma gaskiyar a yanzu zata fi kawo mishi matsala, ta ina zai fara?â
Yana zuwa gida ya tarar da Zee da hammad suna coloring a parlor, da gudu suka nufeshi suna mishi oyoyo bayan sun gaisa yace âina Mumynku?â
âTana dâakin Yaya Fatimaâ. Hammad ya furta yana nuna dâakin tareda komawa kan littafinaa da yake coloring, da murmushi Abbu ya amsa mishi da okay sannan ya nufi dâakinsa. Yana ajiye jakarsa yaji sallamar Aminatu saidai yana kallonta yaji gaba dâaya shirin da yayi a waje na tunkararta ya wargajeâŠ