ZUMUNTA KO MUGUNTA

SHAFI NA 21

by @yarmutanargungu

``````ZUMUNTA 🤝 KO MUGUNTA 👺...✍️





MARUBUCIYAR...✍️



**Ashe ba so ba ne



**Bayan wuya**



**Zumunta ko mugunta on typing...✍️




          NA




Fatima Zara Alhassan ❤️



        (ƴar mutan Argungu)




ARGUNGU WRITER's ASSOCIATION...📚





GARGADI!



ƙagaggen labari ne. Ban yadda wani ko wata su juya shi,ba tare da izinina ba, akiyaye. Idan kuma ya zo dai-dai da rayuwar wa su, toh akasi ne!. 





GODIYA



Ga mabiya littafai na, Allah ya barmu ta re,ya kuma ƙara danƙon zumunci 💙❤️




K/wata/17/12/2022




FREE BOOK📚





SHAFI NA 21




BISMILLAHIR RAHMANIR-RAHIM



******************************************************* 


Ɗagowar da zai yi, su ka ido biyu, sai kawai ka ji fatatatattt...ya sa ki zawo



A gefe ɗaya kuma, ma'aikatan kamfani ne tsaye su na kallon ikon Allah.



Ka ma hannun sa Aneesa ta yi san nan ta ce "kawu sannu, zo mu je ka zauna.


ganin yadda ma'aikatan ke kallon su, shiyasa ita ma ta zuba mu su idanuwan ta, kafin ka ce kwabo kowa ya ka ma gaban sa.



Bayan ta kai kawu Tukur office ɗin sa, ta ce ya shiga toilet ya gyara kan sa.



Cikim firgici da bin umarnin ta, ya shiga toilet ya gyara jikin sa ya fito


Amma har yanzu mamakin ganin Aneesa bai sake shi ba. 



Shin gaskiya ne ko mafarki? Aneesa ce yau a gaban shi, ya aka yi ba ta mutu ba? bayan boka ya ce ba za ta taɓa dawowa ba! Shine kuma yau ta dawo har ta ke ba shi umarni? kai wallahi wannan mafarki ne



Murmushi ta yi ganin yadda kawu Tukur ya rikita kan sa



"kawu ina wuni ya bayan rabuwa?"



Cikin rawar jiki da munafurci kawu ya fara kuka..." Aneesa ɗiya ta ina ki ka shiga mu na ta neman ki ba mu gan ki ba? 


Ba bu inda ba mu duba ba, amma ba mu gan ki ba, har gidajen talabijin da rediyo ba bu inda ba mu kai cigiyar ki ba, amma shiru kamar an aika bawa garin su...



Mun shiga tashin hankali sosai ni da Adamu, a lokacin da mu ka ga gawar ɗan uwan mu shi da matar shi kwance a cikin jini ba bu rai a ta re da su, gefe ɗaya kuma ga ɓatan ki!"




"Allah sarki kawu, ita rayuwa da ma haka ta ke, na kuma gode da kulawar ku, kuma insha Allahu yanzu na dawo cikin ku ba bu inda zan tafi. 



Kuma a shirye na ke naga na ƙwato haƙƙi na, kuma ba zan ya fewa duk wanda ke da hannu wajen kisan iyaye na ba! 



Da sauri kawu ya ɗago kan sa ya na kallon Aneesa jin abun da ke fitowa daga bakin ta. To yanzu idan tasan su ne su ka kashe ma ta iyayen ta ya za ta yi? 



Kai ba zan taɓa ba ri ta sa ni ba.



Ya na son ya yi magana da ita, amma sai ya ga ta cika mi shi office sabo da kwarjini



maganar ta ce ta katse mi shi tunanin da ya ke yi



"Ni kuwa kawu, ya aka yi ban ga kawu Adamu ba? Ko ba ya nan ne?"



Cikin in,in,niya  kawu ya ce "ya na nan ba ri na kira mi ki shi."



Ya ce hakane sabo da ya samu hanyar guduwa.



Da ƙarfi ya turo ƙofar office ɗin kawu Adamu, kamar wanda aka tunkuɗo daga waje



A fusace kawu Adamu ya ɗago dan ganin wane ɗan rainin hankali ne ya shigo mi shi office a firgice haka!!



Ganin kawu Tukur ya yi tsaye a can gefe ya na mai da numfashi



Cike da mamaki ya ke kallon kawu Tukur wan da ya haɗa uban zufa, sai faman zare idanuwa ya ke yi kamar wanda ya yi wa sarki ƙarya



"Kawu lafiya? me ya same ka haka ka ke ta haɗa zufa?" 




"Adamu wallahi fatalwa na gani, ko kuma ince ma ka na yi gamo, wallahi yan zun nan na ga aljana da idona Adamu!!!"



"Bushewa da dariya kawu Adamu ya yi, har ya na duƙewa a ƙasa. Haba yaya, wane irin gamo kuma ana zaune ƙalau?  


yanzu dai zauna mu yi magana. Ta re da bushewa da wata dariyar...




Cikin fushi kawu Tukur ya ce wane irin zama kuma Adamu? ina yi ma ka maganar na yi gamo, amma ka ke ɗaukar magana ta kamar wasar yara! Shi ne har da yi min dariya! wato ga mahaukaci sabon kamu ko?!




Sallamar Aneesa ce ta katse maganar kawu Tukur...



Tashin hankali wanda ba a sa mi shi rana! 


A firgice kawu Adamu ya ke cewa," innahu sulaimanu wainnahu bismillahir rahmanir rahim!! lallai yaya da gaskiyar ka nima fatalwar ta fito min, dan Allah ki yi haƙuri wallahi ba da ni aka kashe iyay...



Wani mazga kawu Tukur ya kaiwa bakin kawu Adamu, sabo da kar ya fallasa asirin su.



A tunanin kawu Adamu fatalwa ce ta mazge shi, nan ta ke ya zube ƙasa ya na kuka, ya na dan Allah ta yi haƙuri



Cikin takaicin abun da ɗan uwan na shi ke yi, shiyasa kawu Tukur ya sa ke dunƙule hannu da niyyar ya kai wa Adamu naushi,


Aneesa ta ta re.



     "A'a kawu wanda ka yi mishi ya isa, dan Allah ka yi haƙuri"




Haka dai Aneesa ta yi mu su bayani, su bar tsoron ta ita ba fatalwa ba ce



Amma duk da haka ba su saki jikin su ba.



Haka dai su ka yanke shawarar Aneesa za ta koma gidan kawu Tukur da zama.



Bayan kwana biyu, Aneesa ta bijiro da maganar ta na son a buɗe case ɗin mutuwar iyayen ta.



Ba bu yadda su kawu ba su yi ba, akan tabar maganar sabo da ko an buɗe case ɗin ba ta da wani shaidu da za ta bai wa kotu, amma ta ce a tafau sai anbuɗe.



Su kawu ne zaune shi da Adamu, su na tattaunawa akan yadda za su ɓullowa lamarin Aneesa.



"Adamu mai zai hana mu kashe Aneesa har lahira, yadda za mu ci gaba da cin duniyar mu da sinke, ba ta re da kowa ya zarge mu ba.


Sabo da wallahi idan ba haka mu ka yi ba, to ina mai tabbatar ma ka yarinyar nan za ta ɓallo ma na ruwan dafa mu.



Ka duba ka ga yadda ta ke kallon mu, ba bu tsoro ko shakkun komai a ta re da ita, kai tsaye ta ke gaya ma na magana, wanda kai kan ka kasan da can ba haka ta ke ba."



"Yaya wallahi ni kam tsoron yarinyar nan na ke ji, da zarar ta kalleni sai na ji jikina kamar wanda aka tsoma cikin firiza( freezer) wani tashin hankalin ma, sai ka kalli cikin idanuwan ta. 



Gaskiya yaya kar mu kashe ta, tunda mun so kashe ta a karon farko ba ta mutu ba, kawai yanzu mu barta ta yi rayuwar ta,



Sabo da duk yadda za ta yi, ai ba za ta taɓa gane cewa mu muka kashe ma ta iyaye ba.


     Yaya kawai mubar ta, ta shigar da ƙarar idan ta ga ba bu wani shaidu, ai dole ta haƙura. Amma ya ka gani?"



"shiyasa aka ce yaro, yarone wallahi. Kar ka manta fa, ta re da kai mu ka yadda yarinyar nan a daji, yanzu kawai rana tsaka ta dawo ma na, ba ta re da tayi mana cikakken bayani ba, kuma kai kan ka kasan boka tsimmirarre ya tabbatar ma na zai haukata ta, amma kawai sai mu ka ga yarinya ta dawo, kuma cikin shiga ta kamala, ka dubi dalleliyar motar da ta zo da ita. Sabo da haka dole mu sa ka ma ta ido sosai akan duk wani shige da fic ce da za tayi, in har ba ta shiryawa wannan case ɗin ba, wallahi ba za ta ce a ta da shi ba. Amma ka yi tunani da kyau..



****************  ❤❤❤❤❤❤❤❤


❤❤❤❤❤❤        ************


**************          ************


Cikin shirin zuwa gona, malam kabiru ya fito, daga cikin ɗakin sa, ya tsaya a baranda ya na ƙwala kiran Murja..murja..



Na'am malam ga ni nan zuwa...



"wai dan Allah har yanzu ɗumamen bai samu ba ne? ban son rana ta yi ma na a gida."



Cikin ladabi inna murja ta aje kwanon samira a gaban mai gidan ta, ta na cewa 


" malam ayi haƙuri kasan yanayin itacen ba sa wani ci, ga shi kuma anyi mu su ruwan sama, da ƙyar na samu wutar ta kama.  Ta re da miƙewa ta ɗebo ruwa cikin kwanon sha, ta aje a gaban shi.




Godiya ya yi ma ta, san nan ya ce ta ɗauko mishi tabarma zai je waje su ci shi da baƙon sa.



Miƙewa inna murja ta yi, ta je ta ɗauko mishi. Karɓa ya yi, ya je ya shimfiɗa a cikin soron gidan. San nan ya fita ƙofar gida, akwai ƙaramin ɗaki a wajen, nan ya nufa ya na ƙwanƙwasawa. 


Wani dattijo ne ya fito daga cikin ɗakin, ɗauke da murmushi akan fuskar sa, wanda idan ka kalle shi da kyau kasan cewa damuwa ce ta tsofar da shi da wuri haka, 


ya miƙawa malam kabiru hannu su ka yi musabaha.


Bayan sun gaisa, malam kabiru ya yi mishi bismillah su je su ci abinci.


Wannan al'adar malam kabiru ne, kullum safiyar Allah, haka zai ɗauko mu su karin kumallo ya zo su ci ta re da baƙon sa.



Duk wanda ya ga yadda su ke gudanar da rayuwar su, zai ga shaƙuwa sosai a tsakanin su...


Bayan sun gama karin kumallo su ka yi wa inna murja sallama, su ka wuce gona.



Malam kabiru asalinsa ɗan garin KAITA ne wadda ke cikin jahar katsina.


Ya na zaune ta re da matar shi Murja, kusan shekarar su ashirin amma Allah bai ba su haihuwa ba.


Ba ya da wata sana'a wadda ta wuce Noma.


Kuma kunsan noma ga mai ɗan karamin ƙarfi akwai wuya. 


Shiyasa aminin sa malam sale, ya zo mishi da shawarar su je birni ko Allah zai sa, adace su samu wani aiki wanda zai fi noma samu.


Amma malam kabiru ya ce shi sam, ba bu inda zai tafi, sabo da ance mishi ƴan birni sun fiye walaƙalanci, gara ya yi zaman shi, ya ci gaba da noman sa zai fi mi shi sauƙi.



Bayan kwana biyu malam sale ya zo mishi da zancen cewa ya samu aikin tsaron maƙabarta a cikin garin katsina.



Malam kabiru ya yi mishi murna sosai, da kuma fatar alkhairi



Haka rayuwa ke tafiya, da daɗi da ba bu daɗi...



Kwatsam sai ga malam sale ya zo mi shi da wani zance , na cewa su taimaki wannan bawan Allah.san nan ya kwashe duk iya abun da ya sani game da wannan mutumin ya faɗawa abokin sa.



Wannan shi ne mafarin zaman malam Baƙo a gidan malam kabiru...





"ƳAR MUTAN ARGUNGU MUN JI SHIRU?


DAN ALLAH A CI GABA."



HAKA JAMA'A KE TA KIRA NA SU NA FAƊAMIN.


SHIYASA NI KUMA NA TATTAKE NA ZUBA MU KU RUBUTU MAI YAWA😜😍




MA SU KIRA NA A WAYA SU NA ƘARA ƘARFAFAMIN GUIWA WALLE NA JI DAƊI, KUMA ALLAH YA SA KA MU KU DA ALKHAIRIN SA❤  




         





KAR KU MANTA ƘOFA TA A BUƊE TA KE DOMIN BA DA GUDUNMUWA KO SHAWARWARI👇



*** KO KU TUNTUƁE NI AKAN LAYIN WHATSAPP 👇



    ***







KU DAI KU CI GABA DA SUBURBUƊAMIN



***COMMENT***



***SHARE***



***VOTE***



***LIKE***



  



ZA KU IYA SAMUN WANNAN LITTAFIN A #WATTPAD#




KO KUMA KU ZIYAR CI SHAFIN 



(AREWA BOOKS) 




GA DUK WAƊAN DA BA SU KARANTA 



(ASHE BA SO BA NE) MA ZA KU GARZAYA ***






TA KU HAR KULLUM, MAI SON FARIN CIKIN KU....





💖ƴar mutan Argungu``` 💝 💖