WANI RABON........

CHAPTER 8 (Gone for good )

by @deejasmah

WANI RABON.............🦋🦋🦋


Khadeejah Bint Ismail (deejasmah)


Elegant Online Writers (E.O.W)


In dedication to all single ladies out there 😍


CHAPTER 8 (Gone for good)



This whole chapter is exclusively dedicated to wani rabon fans club you guys are actually sweet and cute set of people thanks for your duas and well wishes Insha Allah me and my guys will surely make it........❤ jazakumullahu khair 



 Follow on wattpad @deejasmah15


Arewabooks @deejasmah



For inquires comments and more chat us on WhatsApp @ *** 


P.S WhatsApp only Don't call 




Ganin yanda suke ta ɗaura min laifi ne yasa na ɗauki aniyar bashi haƙuri akan kalmomi na bawai hakan yana nufin cewa zan amshi soyayyar shi bane nope kawai in share mai ɗacin harsh words ɗin da nai using a kanshi saidai kira har uku baiyi picking ba hakan ba ƙaramin ɓata min rai yai ba saidai little cewa tayi ma wai ai baikai abinda nai masa ba hararar ta nai ina sake dialing saidai kamfanin sadarwar sun shaida min cewa wayar a kashe take 

Taɓe baki nayi ina kallonta "you see what you cause right ?" na tambaye ta kamar zan sa mata kuka dariyar ta ta danne tareda cewa " what you cause dai Allah Addah in da bakiy mai wulaƙanci tun farko ba da bazai miki hakan ba he'll surely call you zuwa anjima it seems like ranshi a ɓace yake " 

Baki na sake taɓewa ina cewa " ya kira ko kar ya kira wannan damuwar shi ce what i know is na fita haƙƙin shi tunda har na kira shi fushin shi kuwa shi ya dama ba niba " tareda ajiye wayar gefena ina kishingiɗa yayinda Areepha ta kasa daure dariyarta sakinta tai tana cewa " hajiya Addahrmu kenan " ganin yadda nake overeacting ban ko kalleta ba nima na saki wata siririyar murmushi ina lumshe idanuna 

Ban sake bi ta kanshi ba na cigaba da hidindimuna yayinda bestie itama bata sake tanka ni akanshi ba kyale ni tai itama ta cigaba da harkokin ta hakan kuwa ba ƙaramin daɗi yai min ba dan haka nima na share kawai 

Through out this week ban haɗu dashi ba ko na shiga house ban ganinshi ko motar shi a tunanina ko hutu yaje haka ko kuma yana zuwa ni ce ban ganinshi "ki ganshi kiy masa mene bayan kinyi rejecting en shi " na tambayi kaina ban bawa kaina damar amsawa ba na kawar da tunanin ko secreteriat ban ganshi a can ba kawar da kaina nai daga kanshi ɗin saidai hakan ya gagara gareni domin kam yau kimanin 10days kenan ban ganshi ba kuma banji ɗuriyar shiba hakan ko ba ƙaramin sani a ruɗu yai ba don ko jikina ya bani cewa babu lafiya kam 



Monday da sassafe na shigo complex ɗin namu reception na fara zuwa dan nasan a bakin Aisha zan samu labari saidai ban ganta ba hakan na nuna bata zoba kenan hakan yasa na wuce sama har na shiga floor ɗinmu naji bazan iya wucewa ba yasa na dawo baya na hau izuwa floor ɗinsu babu kowa a wurin sai janitors da kuma securityn wurin kamar dai namu floor ɗin 

Securityn ne ya matso gabana tareda gaishe ni " good morning ma " amsa mai nai da morning tareda stating mai abinda ya kawoni wato Salem Mustapha shiru yai kamar mai tunani sannan yace "anya wannan floor ɗinne dan bana tunanin akwai wani maaikaci mai irin sunan nan " dafe goshi nai sannan nace "ba staff bane a nan shima bautan ƙasa yazo " 



A take yace "ayya wai corper Salem Allah sarki ai yau kusan 1 week kenan da barinshi nan office ɗin ya koma Abuja ai " shiru nai ina jinjinawa godiya nai masa tareda komawa unit ɗinmu ina jin babu daɗi a raina Allah dai yasa ba saboda ni yabar wurin nan ba zama nai ina ɗaukar wayata tareda dialling number bestie ringing biyu ta ɗauka tana mai cewa "bestie lafiya kuwa " sai yanzu na tuna cewa yanzu 7 tayi 

Ajiyar zuciya nai tareda cewa " lafiya lau bestie yakike?" itama ajiyar zuciya ta sauke tareda cewa "lafiya lau but you didnt sound well whats wrong babe?" ɗan shiru nai sai can nace " everything is okay ashe ɗanuwanki ya bar Kaduna ne babu labari " dariya ta kwashe dashi saida tai ma'ishinta sannan tace "so kinyi noticing cewa baya nan kenan? well ya koma inda aka san worth ɗinshi " dariya nima nai wato abin harda gayamin magana a ciki "babe bakida mutunci wallahi watau nice bansan worth ɗinshi ba okkkk naji wannan " na faɗa in between laughter




"Abi i lie?" ta tambaya nope na furta mata sannan na ƙara da " but hajiyata Allah yasa ba saboda ni ya tafi ba ?" shiru tai tareda cewa "kusan hakan babe in kin tashi da wuri ki biyo gida mana lets talk " ok na furta tareda ajiye wayar ina mai lumshe idanu ba'a daɗe ba office ɗin ya fara cika da mutane 

Yinin ranar haka nayi shi cikeda tunanin dalilin tafiyar shi da kuma neman da take yi min ji na nake sukuku kamar wacce bata da lakka a jiki bansan ya akai tafiyarshi ya tsaya min a raina ba amma na yarda dalilin tafiyarshi ba mai daɗi bane samun kaina nai da dialing number shi yau dai ya shiga saidai ringing biyu akai rejecting call ɗin don haka ban sake kira ba 

Around 4 na bar office ban jima ba na samu keke zuwa gidanta dake ƙasan Ishaku road dake Ung dosa koda na isa sallah na farayi sannan muka samu natsuwar zama kallona tayi tana murmushi " what ?!" saboda kallon is so unusual dariya ta fashe dashi mai sauti " wai kin kirani ne saboda ki tasa ni a gaba kina dariya ko me?" 



Haɗiye dariyar ta tai kafin tace " nope ke ɗin ce naga kamar kin damu da yawa akan ɗanuwa na ko dai anyi falling mai ne ?" nima dariyar na tayata dashi saida nai mai'shi kana nace " Allah ya yafe miki kam meyasa kikai wannan tunanin ? " ta bani amsa da " nothing it is just that naga kin kirani ne a kanshi ke da ko kaɗan ba ki son in kiraki akan maganar shi kinga ko ai dole inji mamaki " 



Ajiyar zuciya nai sannan nace "it is not like i care ko na fara sonshi nope ko ɗaya kawai dai kinsan a musulunce ya kamata in duba wanda na saba gani kullum kuma all of a sudden sai naji ɗifff babu ɗuriyar shi bansan ko laifi na aikata by checking on him ba " 



Kallona tai kafin tace " well Salem is gone.......like gone and for good....... a ranar da yai confessing soyayyarshi gareki kikai turning ɗinshi down ne ya kira ni bai ɓoye min komai ba saidai ma ya roƙe ni da in sanar mai da irin matsalar da kike tareda ita wacce tasaka kike ganin babu wani ɗa namiji da zai iya aurenki a yanda kike ban ɓoye masa ba nai briefing ɗinshi akan irin taki damuwar da kuma yanda hakan ya sakaki a matsaloli da dama 

Nuna min yai cewa shi a gareshi hakan ba damuwa bane kuma insha allahu zai aureki a dukkan yanayin da kike ciki hakan yasa nai ta kiranki ke kuma kina nuna min cewa you have already make up your mind ganin hakan yasa nace mai ya ƙyaleki ya turo iyayenki su nema aurenki hakan shi zai saka ki yarda da cewa shi ɗin ba ƙaramin mai sonki bane hakan yasa friday ya shirya ya tafi Abuja 

Saidai bai samu positive feedback daga wurin iyayenshi ba hasalima nunawa sukayi cewa bai isa ya aureki ba don aurenki a hakan tamkar zubda mutunci da kimar gidansu ne kirana yai ya zayyane min matsalar da yake ciki inda na ƙarfafa mai gwuiwa akan indai ke rabon shi ce sai kiga ya sameki a lokacin da baiyi tunani ba hakan yasa ya cigaba da bibiyarsu da nuna musu irin son da yake miki but to no avail

Monday da ya shirya zai taho ne babanshi yake sanar mai da cewa an dawo dashi abuja anan zai kammala service ɗinshi yayinda maman kuma tace in dai ya sake ya mu'amulance ki koda ta waya ne toh bata yafe mai ba hakan yasa ya haƙura though ko ɗazun da kika kirashi ya kirani ya shaida min cewa kin kirashi yayinda nai alƙawarin sanar dake abinda ke faruwa a tsakanin ku " 



Idona na lumshe ina jin hawaye yana taruwa a hankali nace "dama na san ba kowacce uwa bace zata yarjewa ɗanta ya aureni indai har tasan wacece ni ɗin saidai in itama tasan zafin halin da muke ciki amma wacce bata sani ba kam da wuya ta yarda da hakan well, Alhamdulillahi for that "



Shiru tai tareda nisawa sannan tace " kiyi haƙuri babe amma i assure you akwai wannan uwar akwaita kuma tabbas zaai aurenki a yanayin da ke ɗin baki taɓa zata ko tsammani ba duk wainnan da kikaga sunƙi aurensu is because ke ɗin ba tasu bace inda ke rabonsu ce toh da ko anaso ko baaso sai kin aure su so mu cigaba da addua insha allah zamu ga haske nan bada jimawa ba " 



Ameen nace ina mai jingina da sofa tareda runtse idona cikeda son hana hawaye zubowa cikin nasara kuma ya tsaya cak innalillahi na cigaba da ambata a zuciyata har zafin da nakeji ya lafa don haka na saki jiki muka dasa wata sabuwar hira har Sahal ya dawo muka dasa dashi ban baro gidan ba sai after maghrib tareda su har gida suka maidani nanma wani hira muka dasa dasu mamie sai wurin 9 suka wuce gidan su bestie..............


Follow

Comment 

Vote 


Deejasmah 🦋💖🌹