Chapter 20
MIJIN MACE ƊAYA
PART 2.
Da alkalamin Ummul khair Abba Muhammad.
Assalamu alaikum, 'yan'uwana masu daraja, a duk lokacin da zan yi posting kafin na kai da yi zan dinga tunatar da mu duk abin da zai amfanar da mu, taken shi ne MU ƘARU DA JUNA.
#Mu ƙaru da juna#
TSAFTACE HAMMATA.
*Charcoal(gawayi)
Kamar yadda muka sani ana amfani da gawayi wajen ƙara hasken hakori..to anan ma ana ƙara hasken hammata da shi.. za ki yi mixing dakakken gawayi da da ruwa kaɗan (kada ya yi tsululu) sai ki shafa a hammata na tsawon minti 10 sannan ki wanke da ruwan ɗumi.
Wallahi idan wata ta buɗe hammatanta sai kinyi amai.... Me kike yi kin bar gashin hammata kaman dajin sambisa?? Have time for yourself too...
Da sunan Allah Mai Rahama Mai jin Kai.
Chapter 20
WAIWAYE ADON TAFIYA.
Ya kamata mu waiwaya rayuwar Hafsy da Mus'ab kafin su zamo ma'aurata wanne irin gwagwarmaya da kalubale suka fuskanta kafin zamansu ma'aurata....
Alhaji Abdullahi, mahaifin Hafsy hamshaƙin attajiri mai kuɗi ne, mutum ne da ya kwankwaɗi boko kuma mai tafiyar da tsarin rayuwarsa na 'yan boko babban ma'aikacin gwamnati ne kana kuma shahararren ɗan kasuwa domin shi gida biyu ne maganin gobara, yana da tsatssauran ra'ayi kuma bai son wargi da raini.
Idan akwai abin da ya tsana a rayuwa bai wuce ƙulla alaƙa da talaka ba, don ko da iyalansa ya ga suna hulɗa da su sai ya tsawata musu tare da nuna ɓacin ransa. Matarsa kuwa Hajiya Maryam, mahaifiyar Hafsat ba ruwanta ba ta ɗauki duniya da zafi ba, ta wannan ɓangare sun yi hannun riga da mijinta tana da kyakkyawar mu'amala ga mutane ba ta kyamar talaka, kullum tana ƙoƙari wajen nutsar da mijinta amma ina wanda ya yi nisa baya jin ƙira. Da ta fuskanci idan har ta so tursasa shi za su iya samun saɓani ta rabu da shi, sannan duk wani abin da za ta yi idan ya jiɓanci mu'amala da talakawa takan yi a sirrance gudun saɓani. Muna iya cewa Hafsy mahaifiyarta ta gado ta wajen halayya.
Alhaji Abdullahi matarsa ɗaya ce mahaifiyar Hafsat sun yi auren saurayi da budurwa sai da suka shekara biyar babu haihuwa kowane lungu da sako sun shiga hatta ƙasa mai tsarki sun je roƙon Allah don neman haihuwa. Kasancewar Allah ma ji roƙon bayinsa ne a duk lokacin da bawa ya roƙi Allah wani Allah kan amsa masa nan take wani kuma ya jinkirta, to haka ya kasance ga Hajiya Maryam rana tsaka kwatsam ta tsinci kanta da yawan zazzaɓi, da tashin zuciya da amai, kullum jiki babu kuzari, Alhaji ya ce su ziyarci likita suna zuwa asibiti da aka yi gwaji aka tabbatar musu tana ɗauke da juna biyu, ai ko daɗi kashe ni suka dinga murna mara misaltuwa.
Kulawa da tarairaya da Hajiya Maryam ta dinga samu wurin mijinta jaririn goye albarka, cikinta na kai wa wata bakwai ya fita da ita ƙasar waje da ta haihu ma ya ce jinjirarsa sai ta yi kwari za ta zo ƙasa Nigeria a can suka yi budirinsu na suna, yayin da 'yan'uwansa da 'yan'uwanta ma ya tura musu kuɗaɗe ya ce su yi liyafar su a inda suke.
Ya sanyawa ɗiyarsa suna Hafsat tana da wata huɗu a duniya suka dawo ƙasarsu Nijeriya, nan ma ya haɗa manyan abokansa suka yi gagarumin party.
Alhaji ya ɗauki soyayyar duniya ya ɗora ma ɗiyarsa duk wani gata da kulawa yana ba ta, cikin ikon Allah kuma daga kan Hafsy mahaifiyarta ko ɓatan wata ba ta kuma yi ba ballantana ɓari.
FARKON HAƊUWAR HAFSY DA MUS'AB.
Ranar Asabar, rana ce da a ka wayi gari cikin lumshi wato ranar ta kasance ba ta fito da harshenta ba, kamar yadda a ka saba a kullum, yanayin garin sai ya zamo abin sha'awa ga kowa, saboda tsananin rana da ake ƙwallawa yakan galabaitar da al'umma.
Hafsat wani tsadadden lace Maroon color doguwar riga ta sanya, mai manyan duwatsu golden, wanda hakan ya sanya ta yi shigar komai golden wato gyale da takalmin ta half cover da hand bag nata duk golden hatta agogon da ke makale a dantsen hannun, sannan fuskar nan tata ta sha makeup wanda ya yi matuƙar yi mata kyau. Hafsat yarinya ce mai son ado da kwalliya don passion na ɗaya daga cikin abubuwan da take so a rayuwa.
Tabbas Hafsat idan ana maganar kyau tana layin farko, fara ce sol tamkar Balarabiya, bakinta ma daidaita ne, ga ta da dara-daran ido da kuma ƙaran hancin girarta cunkus masu ƙauri baƙaƙe wanda ya ƙara mata kyau.
Hafsat tun ba ta cika mace ba maza ke rububi a kanta ballantana yanzu da ta cika mace babu magana.
Sai dai ita kuma Allah bai ɗora mata rawar kai ba, kai ita kalmar soyayyar ma jin sa take kawai duk wanda ya tunkare ta da ita sai ta ce ita fa wannan soyayyar da ake iƙirari ba ta san ta ba a bar ta har zuwa lokacin da za ta san soyayyar sai a furta mata shi.
Ta feshi jiki da turarurruka iri daban-daban ta fito cikin fara'a ta durƙusa a gaban Ummanta, "Mummy barka da hutawa." Ta dube ta tare jinjina kai, "Barka dai, wannan ƙwalliya kuma haka ina za a je?"
Ta sosa keya tana murmushi, "Mummy super market zan je na yi sayayya duk yawancin kayan amfanina sun ƙare wasu suna daf a ƙarewa."
"Okay, to kamar nawa kike buƙata? Ko kuma na ba ki ATM card kawai."
Ta zaro ido, "ATm dai Mummy, akwai kuɗi a hannuna kuma zai ishe ni sayayya, ko kin manta kowane wayewar gari Daddynq ba ni kuɗi ni kuma kin san ba ni da kashe-kashe su na ɗauko zan je na yi siyayya."
Murmushi ta yi, "Yauwa ɗiyar albarka haka nake so ki kasance mace mai tattali, yau mu ne gobe ba mu ba ne duk wanda ya san farkonsa bai san ƙarshensa ba komai na rayuwa ka bi ta a sannu."
Ta miƙe, "Wannan haka yake Mummyna, Allah dai ya sa mu dace."
Mahaifiyarta ta amsa mata da amin, sannan ta ce, "Sai ki yi wa Manu driver ya kai ki ko."
A shagwaɓe ta ce, ,Mummy ni gaskiya Ni kaɗai zan tafi. Na tsoron da kike ban gama koya tuka mota ba ko? To yanzu na kware, na gama koya, an cire alamar L (learning) daga nan har Legas sai na kai ki no gada-gada."
Ta kyalkyale da dariya, ""Ah, lallai to congratulation." Ta ba ta key, ta miƙa hannu biyu ta karɓa. "Amma ni kam ba tafiyar ba, ina gujewa tsautsayi kar wani abu ya faru da ke, kin san halin Daddynki ni zai danganawa laifi."
"Mummy, babu abin da zai faru sai khairan in sha Allah, saboda haka faɗi abin da zan taho miki da shi?"
"To Allah ya sa. Duk abin da ya kika ga ya dace ki sayo zan so shi.'."
"To ai ko shike nan supermarket zam zan ɗauko na kawo miki." Ta fara waige-waige, "Na san ba za a rasa gurbin ajiye shi ba a wannan gida."
Ta tuntsire da dariya ta fice, haka Hafsat da mahaifiyarta suke idan suka fara wasa da dariya sai ka ce ƙawaye ne, amma duk da haka akwai girmamawa a tsakaninsu.
Hafsy ta shige motarta, ta ɗauki hanya tana tafiya a nutse ba ta ƙarasa supermarket ba mota ya yi gardama "Innalillahi wa inna ilahirraji'un." Shi ne abin da laɓɓanta ke furtawa, kawai sai ta fito tana cewa, "Lallai ƙarfen nasara ba ki da tabbas. Wannan motar nan kin gama da ni." Ta cija laɓɓa, "To ya zan yi?"
Ta waiga Gabas da Yamma Kudu da Arewa ba ta ga kowa ba, dama hanyar ma motoci jifa-jifa suke wuce wa, sit shirun wajen ya sa ta ɗan tsorata da ma kuma matsoraciyar ce.
a ɗaga Boot, ta ce a zuciyarta, "Ni, me na sani a kan abin da ya shafi mota me zan duba."
Gumi ya fara yanko mata ta nufi gaban mazauninta ta ciro waya tare da cewa, "Daddy zan ƙira ko Mummy?" Kai idan na ƙira Daddy na faɗa masa halin da nake ciki zai azalzale Mummy da faɗa me ya sa ta bar ni da ma ga kashedin da ta yi mini."
Wata zuciyar ta ce da ita, "To ki ƙira Mummy kawai Manu driver ya zo." Ta kuma cewa, "To Mummy ma da rikicewa abu ƙalilan idan na faɗa mata za ta shiga firgci."
Kawai ta kifa kanta a kan motar don takaici tare da faɗin, "Tsautsayi dai abin da mummyna ta yi gudu to ya Allah ka ba ni mafita."
Zuciyarta ce ta ba ta shawara da ta ƙira mahaifiyarta ta faɗa mata, yadda wannan wajen yake shiru kar wani mugun abu ko mugun mutum ya cutar da ita.
Ta ɗago kanta tana ƙoƙarin latsa number sai ta ji takun sawu ana tafiya gudu-gudu zuciyarta ta yi wani ras a razane ta ɗago kanta sai suka yi ido biyu da matashin saurayi haɗa ido da suka yi ta ji zuciyarta ya fara buga wa fat fat fat kamar ƙirjinta zai fashe zuciyar ta fito waje hannunta ya fara rawa ta gagara ƙirar da za ta yi.
Matashin saurayin ya fahimci yadda ta kiɗime dalilin kallonsa da ta yi, cike da murmushi ya ƙarasa gare ta.
"Baiwar Allah, kallona da kika yi yanayinki ya nuna mini kin tsorata da ni. To ki kwantar da hankalinki ba zan cutar da ke ba, hasalima duk abin da na ga zai cutar da ke zan yi ƙoƙarin ba ki ƙariya sai inda ƙarfina ya ƙare."
Ya shafi sajensa, "Da ganin ki kina buƙatar taimako ko za ki faɗa mini idan ina da dama na taimaka." Ya ƙarashe maganar yana murmushi kuma yana kallon fuskarta.
Ta sauke ajiyar zuciya ta ce, "Ka ga wallahi motata ce ina cikin tafiya kawai ta tsaya na yi na yi ya ki motsa wa."
Ya rausayar da kai, "Ikon Allah ni kuma ga shi ba makaniki ba, amma na ɗan taɓa sana'ar da jimawa na bari, bari na duba ko zan gano matsalar."
Ya dudduba, sai ya dube ta, "Ko kina da ruwa a tare da ke?"
Ta ce, "Babu gaskiya."
"To ki yi haƙuri ki jira ni zan je na nemo." Ya waiga, "Anya kusa nan za a samu ruwa kuwa?" Sai ya kalle ta, "Baiwar Allah area nan kamar ba alamar ruwa, saboda haka zan je na nemo a duk inda za a samu, na fahimci kina da tsoro saboda haka zan ba ki lakani ki dinga furta hasbunallahu wa ni'amal wakil. Da la'ilaha illa anta subhanaka inni kuntu minazzalimin. Bi'iznillah babu abin da zai cutar da ke." Ta amsa da to da yi masa godiya, ya juya yana tafe sauri sauri gudu-gudu tun tana hango shi har ya ɓace.
Bayan wasu 'yan mintina, sai ga shi ya taho da mai a daidaita sahu (keke napep) da ruwa mai a daidaita sahu zai juya ya tafi ta ce, "Dakata ka karɓi kuɗinka." Ya ce da ita tun kafin ya zo suka yi ciniki aka biya shi yana gama faɗa ya ja adaidaitarsa ya yi gaba, ta juya za ta yi magana ya yi mata ishara da ta yi shiru.
Cikin ikon Allah ya gyara mata motar ya umurce ta da ta je ta gwada tuki, tana farawa mota ta fara tafiya cike da fara'a tana mai jin daɗi ta, ce, "Alhamdulillah." Sai ta ta fito, tana murmushi ta ce, "Mota ya tashi wallahi gaskiya na gode ba don kai ba ai na kaɗe har ganye na."
Murmushi ya yi, "Ba don Allah ya so ba za ki ce."
Ta ce, "Haka ne amma ka san komai da sanadi kai ne sanadi. Ina godiya sosai."
Ta sa hannunta cikin mota ta ciro kuɗi ta miƙa masa, "Ban isa na biya ka ba, Allah kaɗai ne zai iya ba biyanka ni dai ba abin da zan ba ka face ihsani ka san shi kyautatawa na da kyau. Ka kyautatawa wanda ya kyautata maka Allah ne ya umurce mu da yin haka."
"Haka ne, amma ni nafi buƙatuwa da kyautatawa ta addu'ah a gare ki da wannan abin da za ki ba ni saboda haka na fanshe da addu'a ina sauraronki."
Murmushi ta yi, "Ba wani wayo ka yi mini kuma ka ɗaure ni da jijiyoyina ba ni da zaɓi face abin da ka ce, to ina roƙar maka Allah yadda ka taimake ni Allah ya taimake ka bisa dukkan lamuranka ta duniya da lahira. Yadda ka ji kaina kai ma ya ji ƙanka, yadda ka tausaya mini kai ma ya tausaya maka duniya da lahira. Idan iyaye na raye Allah ya ƙara musu tsawon rai mai amfani, idan ko sun riga mu gidan gaskiya Allah ya kyautata makwancinsu."
Ya amsa da amin tare da ce mata, "Wannan addu'o'in ya fi kyautar da za ki yi mini daraja. Duk ni kaɗai amma na ji daɗin wannan addu'ah ta ki."
Ta lumshe ido haɗe da murmushi, "Yanzu ina za ka nufa na rage maka hanya?"
"Na gode nama kusa zuwa in da za ni kinga wancan fili." Ya yi mata nuni da wani fili a can gaba, "To can zan je na motsa jikina."
" To kai motsa jikin naka da rana kake? Na ga masu yi da sassafe suke."
Murmushi ya yi, "To ai yanayin weather na yau za ki yi duba sai isa zan yi a warhaka, baya ga haka Allah ya ƙaddara za mu sadu da juna sai isa kuma hakan ta kasance."
Ta lumshe ido kana ta yi murmushi dimple nata suka motsa ta buɗe door, "Ba don ni ba don Allah don kuma soyayyarka da Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama ka shiga ka rakani inda za ni yau a haƙura da motsa jiki."
Shiru ya yi, ta katse shirun da cewa, "Kamar yadda da farko ka ce ba za ka cutar da ni ba, to ni ma ka sani alheri ke tattare da ni gare ka."
Ba tare da ya musa ba ya shiga mazaunin gaba ita ma ta zauna a mazauninta ta ja mota.
Suna cikin tafiya ta ce, "Sunana Hafsat Abdullahi ko ya sunan bawan Allah?"
Ya ce, "Ni sunana Mus'ab Adam Usman."
Murmushi ta yi, "Nice name, wannan babban suna ne ai, babban Sahabi da ya yi gwagwarmaya ya ba da gudunmawa ma addinin Musulunci."
Ya ce, "Haka ne ai Hafsatu ma babbar suna ce idan za a taɓo ahalin Annabi dole a sako ta, ta haɗa abubuwa biyu mata ga fiyayyen hallitta kana ɗiya daga ɗaya daga cikin khulafa'ur rashidun."
Ta ce, "Wannan haka yake mun kasance da sunayen mutane masu daraja, Allah ya sa mu yi koyi da su a ɗabi'u da halayya."
Ya amsa da amin sun zo daidai supermarket ta yi parking bayan sun fito ta ce bismilla suka shiga.
Ta yi siyayya kashi 2, bayan sun shiga mota sun zauna tana murmushi ta miƙa masa, "Na san halinka ba kai na sayawa ba, na san ba za a rasa ƙannai a gida ba to su na ba wa."
Murmushi ya yi, "Ba yadda na iya to an gode."
Ta ja mota suna cikin tafiya ta ce, "Ka yarda da ni cikin sauki, to ka sani ka hau motar 'yar killar kai yau kai da duniya kun yi sallama."
Cike da dariya ya ce, "Kai haba! Da ma
mata ma suna killar kai?"
"Ba ka sani ba da ma lallai yau za ka sani, ga shi na ga alama wannan kan zai kawo kuɗi."
Ya kyalkyale dariya, "Ke ba, na fahimci akwai ki da raha."
Ta sauke ajiyar zuciya, "Ina zan kai ka?"
"Ina dai za ki ajiye ni za ki ce."
"To na ce hakan."
" To ki sauke ni a post office. Akwai abokina da muka yi za mu haɗu za mu je specialist hospital duba mara lafiya."
Shiru ta yi a zuciyarta dai ba ta gamsu da maganarsa ba, amma ta haƙura suna zuwa post office ta sauke shi ta buƙaci phone number sa ya ba ta sai ta ce bari na yi flashing naka sai ka yi saving number ta, tana sa number sai ta ji a kashe ta dube shi yana sosa keya ya ce, "Ranki ya daɗe na bayar da caji ne kuma saboda kar a neme ni na kashe. Amma rubuta mini number taki a paper ina karɓar wayar na ƙira ki kafin ki kai ga ƙira na."
Ta rubuta ta miƙa masa tare da shopping da ta yi masa. "Yanzu da niki-nikin kaya za ka je asibiti ni kuma ga shi niyyata ma ƙannanmu na saya."
Ta ja mota ta tafi bayan ta furta haka. Mus'ab kuwa da ma ba dubiyar da za shi, baya so ta ce za ta kai shi har unguwarsu ne ya ƙirƙiri ƙarya.
Bayan ta ɓace ɓat ya tsayar da adaidata ya faɗi unguwar da za shi a ka ce ya shiga.