32-33
by @ayshercool
GABA DA GABANTA
AISHA ADAM (AYSHERCOOL)
PAGE 32-31
Duk da Amina ta sha jinin jikinta da irin kallon da Alhaji Ahmad ya yi musu, amma ta maze ta ƙi ko ɗaga kanta, balle ta nuna ta san ita yake yiwa wannan kallon.
Bilal ya gaida Alhaji Ahmad, amma ya amsa masa sama-sama ya fice, Amina na ganin fitar Alhaji Ahmad, ta yiwa Bilal sallama ta shige cikin gida.
Fadila kuwa tun da Kankiya ya Kori Yazid daga ajin, hankalinta yake a tashe, ta rasa meya kamata ta yi, tamkar a kan ƙaya take haka ta dinga jiran Kankiya ya fita ita ma ta fita, ganin ba shi da niyyar fita ne, ya sanya ta tashi ta nemi excuse zata fita, amma Fafur Kankiya ya hanata, ji tayi tamkar ta je ta shaƙe shi ta gwara kansa, wata irin tsanarsa ta ninku zuciyarta.
Sai da yayi kusan awa biyu da wani abu sannan ya bar ajin, yana fita Fadila ta fita, ta dinga duddubawa ko zata ga Yazid, amma babu Yazid babu dalilinsa, duk in da ta san zata ganshi ta duba amma bata ganshi ba, hakan ya sa tayi tunanin gida yayi tafiyarsa, alamar yayi zuciya.
Tunani ta dinga yi, wani irin hukunci yakamata ta yiwa Kankiya, wani mataki yakamata ta ɗauka a kansa, amma sai ta yi tunanin kar tayi wani abu a kai, ya kuma cutar da Yazid, haka nan ba tare da ta yanke shawarar komai ba, ta shiga motarta ta tafi gida cike da damuwa.
A gidanma kasa sukuni tayi, gashi ita ba lambar Yazid ba, balle ta kira shi a waya taji meyafaru bayan fitarsa daga aji ba.
Tana tsaka da wannan tunanin, sai ga kiran Kankiya, ji tayi kamar tayi jifa da wayar, amma tayi yaƙi da zuciyarta ta ɗaga.
"Amincin Allah ya tabatta a gareki amaryata" ji tayi kamar ya watsa mata wuta a zuciyarta, ko muryarsa ba ta ƙaunar ji sam.
"Me ka kirani kayi mini, wai ban maka kashedi a kan kirana ba?"
"Kina fushi da ni dan na kori saurayinki daga aji ko? Ai abinda na gaya miki ne Fadila, muddin ba zai rabu da ke ba, zan ta wahalae da shi ne"
"Wai kai waye ya gaya maka Yazid saurayina ne? Babu wani abu mai Kama da soyayya tsakani na sa Yazid, kuma bari in gaya maka wani abu, wallahi muddin baka kiyaye ni a kan batun soyayyar nan ba, sai na maka abin da har ka mutu ba zaka manta ba*
Yayi dariya ya ce "Ni ma kuma zan yiwa Yazid ba, dan naga a duniya idan ana son ɓacin ranki, to a taɓa Yazid"
Sai kuma yayi ƙasa da murya ya ce "Haba Fadila, duk ke kika saka al'amura suka zama so complicated like this, ni ina da kishi sosai da sosai, shiya sa ba zan iya jure ganinki da wani ba, wallahi idan Yazid ya fita daga harkarki babu ruwana da shi. Yanzu gaya mini yaushe zan zo gidanku?"
"Abudrrasheed Kankiya, banda ina ganin darajar alli da duster, da sai na nuna maka wacece Fadila, na lura rashin sanin wacece ni ya sanya kake mini karan tsaye yadda ka ga dama"
"Hmmm, koma dai menen ai nasan ke mutum ce, kuma duk matsayinki dole zaki aure wataran ƙarƙashin inuwar wani, Fadila mu daina samun wannan saɓanin, in daina wahalar da ɗan mutane, ki fita harkarsa ki bani dama in gwada miki soyayya"
"Shikenan, ni da kai mu zuba mu gani,ka koma ka ƙarewa kanka kallo, sannan ka ƙare mini kallo kasan wacece ni, kan kace kana sona ka san matsayina tukuna, wallahi ka cigaba da takura masa zan nuna maka abin da zan iya yi a kai"
Kankiya ya yi ajiyar zuciya ya ce "Saboda shi Yazid ɗin duk kike gaya mini wannan maganganun?"
"An gaya maka ɗin, kayi abin da zaka iya" daha haka ta kashe wayar , tana jin tamkar ta sa a ɗaure Kankiya, ita tausayin Yazid take ji, idan aka ɓata masa career an cuce shi, amma Kankiya na son amfani da wannan damar ya tilasta mata ta so shi, bata taɓa tausayin wani ɗan Adam a rayuwarta ba, kamar yadda take tausayin Yazid. Ita kawai kyawawan halayensa take kallo, sai taga kamar idan aka cutar da shi ba a yi masa adalci ba, yana da halaye masu kyau, ba ya cutar da kowa to shi mai zai saka a dinga cutar da shi.
Ta tuna irin kasadarsa mussaman a ɗakin jarrabawa, dan kar wani ya faɗi, da tsananin biyyarsa ga malamai, amma hakan bai hana a dinga dizga shi a gaban aji, ba tare da duba halayensa masu kyau ba.
Dafe goshinta tayi, ji tayi kamar kanta ya fashe Saboda rasa mafita.
Ɓangaren Khalil ma yana cikin ɗumbin damuwa, Hafsa ta buɗe what's app a wayar da ya bata, har tayi masa magana ta what's ɗin, sai wani ƙara lallaɓa shi take, tana bashi kulawa ta mussaman, da Adduoi, nasiha gami da kalaman soyayya, wanda hakan ke ƙara masa sonta a ransa. Gaba ɗaya Mummy ta ɗauke masa wuta, ta daina shiga harkarsa, duk dan saboda yana son Hafsa.
Gaba ɗaya fushin da Mummy take yi da shi, bai yi masa daɗi ba, hakan ya sanya, ya kuma ƙoƙarin zuwa ya rarrasheta, sannan yayi mata bayanin halin da su Hafsa ke ciki, ko Allah ya sa ta fahimce shi.
Da sallama ya shiga bedroom ɗin Mummyn, ya tarar da ita a kan gadonta, tana danna Computer, gefenta kuma ga calculator, da alama kuɗi take ƙirgawa.
Tun da ta ɗaga kai ta kalleshi sau ɗaya, ta mayar da kai ta cigaba da abin da take yi.
"Mummy sannu da aiki"
"Yauwa" ta amsa a daƙile ba tare da ta kalleshi ba.
"Mummy wurinki na zo"
"Ai na ganka, ina kuma jinka"
Khalil ya ɗan gyara zama tare da sosa kai ya ce "Mummy, dama game da Hafsa ne, yarinyar nan da aka ce miki an ganni a wurinta, Mummy yarinyar marainiya ce ne, Da mahaifinta mai abin hannunsa ne, kan ya rasu ya saya mata kadarori, sai dai bayan rasuwarsa dangin mahaifin suka ƙwace komai, shiyasa kika gansu a haka, amma tana da kirki da kuma hali mai kyau, ba ta da wata matsala yarinyar"
Ai tamkar dutse yayi wa wannan dogon jawabin, dan danna calculator kawai take tana shigarwa cikin Computer.
"Mummy ba ki ce komai ba"
"Me kake so in ce maka, ai kai an shanyeka, ni kuwa ba a shanye ni ba a hayyacina nake, nayi mamakin wurin wani malami suka je haka, da har ka iya zuwa ka tunkare ni ni Hajiya Zainab, kake mini wannan maganar banzan, ban sani ba ko orphanage Home ka buɗe, zaka fara rainon marayu da marasa galihu, da har zaka yayi mo min wannan shirgin tsiyar, Khalil banda rashin hankali irin naka, ina kai ina mai suyar Awara a titi, ba bu ilimi mai zurfi, ta gama zaman titi maza sun gama kalleta, in anjima ta ci kwalar namiji, kuma ka ce mini ita ce sirikata,ai kai ma ka san kayi ƙarya"
"Mummy wallahi ba haka Hafsa take ba, tana....
"Dalla rufe mini baki, ina magana kana wani kwantar da murya ce, cece, ni zaka lallaɓa in anince da auren 'yar matsiyata, ka buɗe kunnenka da kyau ka saurare ni, daga yau babu kai babu yarinyar nan, na yanke duk wata alaƙa da take tsakaninka da ita, wallahi na bibiya na tarar ba ka rabu da ita ba, hukuncin da zan yanke maka ba zai maka daɗi ba"
"Mummy dan Allah, ki duba lamarin nan"
"Ni kake cewa in duba lamarin nan, wato sihirin har ya kai ka fifita ta a kaina"
Cikin rauni ya ce "Ba haka bane Mummy, wallahi ba suyi mini asiri ba, suna buƙatar tainako ne Mummy, kuma muna son juna sosai"
Mummy ta jinjina kai ta ce "Da kyau Khalil, suna buƙatar taimako ko, sannu gwamnati kowa naka, tashi ka fita ka bar mini ɗaki" ta nuna masa hanyar fita.
Zai kuma magana, ta sake haɗe rai ta nuna masa hanyar ficewa, haka ya haƙura ya bar mata ɗakin zuciyarsa babu daɗi.
Amina kuwa ba ƙaramin haushin abinda Daddy yayi mata taji ba, haka ta shiga ɗakinta, tayi alwala tayi sallar magariba, ta shiga kitchen ta hau aikin Abincin dare, kasancewar Hajara ce tayi na rana tunda ita tana makaranta.
Gaba ɗaya Amina a gajiye take, tunda kusan wuni tayi aikin da Daddy ya sakata, aikin da a ƙarshe ya sakamata da direta a titi yayi tafiyarsa saboda tayi maganar matarsa.
Ta gama girkin, ta kai dining, ta ɗau na Baba ta tafi ta kai masa, ta tarar da Baban a cikin ɗakinsa na gadi, yana jin radiyo.
Har zata fita, Baba ya kirawota, ta dawo ta zauna tana kallonsa.
Ya ɗauko wata 'yar jaka ya miƙa mata, ta sa hannu ta karɓa, ta buɗe jakar wani babban kwalin waya ta gani a ciki, ta saka hannu ta ciro wayar tana kallon Baba.
"Baba wannan wayar fa?"
Baba ya ɗan yi shiru sannan ya ce "Alhaji Ahmad ne ya bani, ya ce in baki, wai saboda ki samu sauƙin karatu, sai dai har ga Allah ni bana son ki mallaki wayar hannu yanzu, amma bana son yi masa jayayya kuma naji ya ce saboda karatunki, ina fatan dai ba roƙonsa ki ka yi ba?"
"Haba Baba, ka san bana roƙo, wallahi ni ban roƙe shi ba"
"To sai kiyi masa godiya, duk da nima nayi masa"
"To, insha Allah zan masa"
Ta tashi tana jujjuya wayar ta bar ɗakin Baba.
Har ga Allah tana matuƙar son waya, mussaman duba da yadda ƙawayenta ke da wayar, amma ita ba ta da ita, sai dai da ta tuna da abin da Daddyn ya yi mata, sai haushi ya kamata har ta ce "Mayar masa zan yi, ban so" ta jiye wayar a gefen katifarta tana harar wayar tamkar Alhaji Ahmad ɗin ne a gabanta.
Washegari da Safe Amina bata da niyyar zuwa lesson, ta tashi ta hau aikace-aikacenta, ta shiga kitchen ta ɗora sanwa, ta yi girkin safe ta kammala, ta zo ta shiryawa masu gidan nasu Abincin, sannan ta kaiwa Baba nasa ta dawo, ta fara mopping ɗin falo.
Hajiya Zainab ce ta fara fitowa, Amina ta gaisheta ta amsa mata da ƙyar kamar an yi mata dole, sai kuma Fadila ta fito, Alhaji Ahmad ne ƙarshen fitowa, ba tare da Amina ta kalli in da yake ba, ta gaishe shi, yana jinta ya shareta, kamar ba da shi take ba.
"Good morning Daddy" Fadila ta faɗa tana ƙoƙarin haɗa tea.
"Morning sweetheart, how are you"
"Am fine Daddy"
Ya ɗan ƙara kallon Fadila ya ce "Meke damunki ne, you look dull today"
Fadila ta ɗan yatsuna fuska ta ce "Nothing much, stress ne na school kawai"
"To Allah ya bada sa'a, yau weekends ki samu ki huta sosai"
"Ok Dad"
Ya mayar da hankalina kan Mummy ya ce "My Z ina Khalil ne?"
Mummy da ta kai loma bakinta, ta ƙarasa taunawa sannan ta ce "ƙyale shi kawai"
'in ƙyaleshi kamar yaya, ban gan shi a wurin cin Abinci ba"
"Ka san halinsa wasu lokutan, maybe bacci yake yi"
"Is ok" Daddy ya faɗa yana cigaba da cin Abincinsa. Yana yi yana satar kallon in da Amina ke mopping, tayi kicin kicin da rai, ko kallon in da suke bata yi, aikinta kawai take.
Ɗan guntun murmushi yayi, ya cigaba da cin Abincinsa.
Bayan sun kammala ci, Mummy ta miƙe tsaye, ta kalli Fadila ta ce "Fadila je ki shirya muje ki rakani gidan Hajiya Turai"
Fadila ta ɗan tsuke fuska ta ce "Mummy ki je ki kaɗai, ni bana son fita"
"Aikuwa sai kin je, tashi maza muje"
Fadila tana tura baki, haka ta tashi, ya wuce ɗaki, dan ta fara shirin yiwa Mummy rakiya, idan ba haka ba ta san halin Mummy, idan ta dinga mata mita sai taji babu daɗi.
Suka wate suka bar Daddy a falo, Amina kuma na zaune na goge TV.
"Ke da waye jiya na gani a tsaye a gidan nan?" Amina ta ɗaga kai ta duba falon, amma bata ga kowa ba, dan haka ta san da ita yake, maida kai tayi ta cigaba da aikinta.
"Ko in zo in maimaita miki ne?"
Ta ce "Ba kowa"
"Kina nufin ƙarya nake kenan?"
Ta girgiza kai alamar a'a.
"Ke da waye?"
"Bilal ne, a nan layin yake, bayan ka ajiye ni a hanya, ya ɗauko ni"
Alhaji Ahmad ya ce "Ban tambayeki wannan ba, abu ɗaya nake son gaya miki, kar ki sake kawo mini wani gida, kin zo gidan nan ne dan kin yi aiki da karatu, idan saɓanin haka ne a ranki, to zan sanar da Malam Hassan tun wuri ya san matakin da zai ɗauka, karki ƙara kawo mini wani gida kinji na gaya miki, idan kuma aure kike so sai kiyi bayani, amma gidana ba wurin tara maza bane" kamar kibbau haka ta dinga jin maganganun Alhaji Ahmad, ba ƙaramin ƙona mata rai suka yi ba, ba tace masa uffan ba, sai wasu hawayen ɓacin rai da suka cika mata ido, bata son ya ga lagonta, dan haka ta tashi ta kwashe kayan aikin nata, ta bar masa falon.
Alhaji Ahmad ya shirya ya fita, sai dai ya ci karo da Wayar da ya sayawa Amina a cikin motarsa, ya ɗau wayar ya jujjuyata, ya ɗan yi shiru sannan ya jinjina kai tare da faɗin lallai ma yarinyar nan. Ya ajiye wayar ya cigaba da tuƙinsa.
Hajiya Zainab ce tare da Hajiya Turai a falonta suna hira, yayin da Fadila ke gefe a zaune tana latsa wayarta.
Hajiya Turai ta ce "Wallahi kar ki saurarawa yaron nan, kiyi dagaske ki miƙe a kan abinki, idan ba haka ba wallahi kina kallo za a shanye miki shi, sai yadda aka yi da shi"
Mummy ta ce "Wallahi Turai Khalil ya bani mamaki, ban taɓa zaton yaron nan zai kai kansa wurin maƙasƙanciya kamar mak awara ba, me aka yi a kai mai awara? Banda kalen tsiya da rashin sanin darajar kai, ya janyo mini abin faɗa a cikin ƙawaye"
"Bari Hajiya Zainab, yaran yanzu ka haifesu baka haifi halinsu ba, banda abin Kalil waye yake janyo talaka jikinsa, ai kowa arziƙi yake nemawa kansa, ai baki ga abin haushi ba yadda yarinyar ke washe baki, kamar gonar gyaɗa, Allah ya kashe ya bata"
Mummy ta ce "To wallahi yayi kaɗan, muddin bai rabu da yarinyar ba, zaiga abin da zan masa daga shi har ita"
Turai ta ce "Ai zuwa zaki har gida, mu kasawa yarinya warning ita da uwarta"
Fadila dai ba ta tofa ba, dan a ganinta Khalil shi ne ya janyowa kansa, ga Yusra nan, ba abin da Allah ya rageta da shi, amma ya watsar da ita ya ce baya so.
Turai ta kalli Fadila ta ce "Daughter, ke kuma wa zaki kawo mana, ina fatan dai ba wahalalle kema zaki kwaso mana ba"
Fadila ta ɗan kwaɓe fuska da murmushin gefen baki.
Turai ta ce "Ai ba murmushin ba, ni dai ɗana ya gani ya ce yana so, insha Allah da ya dawo zan haɗaku, dan har Babanaa ya zan zancen"
Mummy ta ce "Ai na fara mata zancen kwanaki, kin san yaran naki ne, miskilaine kamar ubansu, na fara mata maganar ba ta ce mini komai ba dai tukuna, amma dai na san zasu daidaita"
Fadila ta sake gyara kwanciyarta a kan kujera, dan wannan hirarrakin nasu ya isheta, so take su tafi gida kawai.
Sai da Khalil ya tabattar da Mummy ta fita, sannan ya shiga falon, ya saka Hajara ta kawo masa kayan breakfast ya karya, ya ci ne dan kawai yana jin yunwa, ba dan yana son cin Abincin ba.
Bayan ya gama ya fito daga ɗakin, ya haɗu da Amina a kan baranda, ya kalleta fuskarsa ba walwala ya ce "Daga yanzu idan kun gama girki a dinga zuba nawa ana kai mini ɗakina"
Amina ta ce "To insha Allah"
Fadila har suka taho gida, Mummy tana yi mata bayanin yadda ɗan Hajiya Turai yake, ita dai Fadila lissafin, yadda zata yi da Kankiya da kuma batun Yazid ne ya dame ta.
Khalil kuwa gidansu Abdul ya wuce, dan ba shi da aminin da yake gayawa damuwarsa wanda ya wuce Abdul ɗin.
Tun a kallon fako, da Abdul ɗin ya yiwa Abokin nasa, ya san tabbas akwai damuwa, dan a yadda Khalil ya saba, da yazo yake fara zolayarsa, amma yau yana shigowa, ya wuce kan gadon Abdul ya kwanta, yayi shiru ba tare da ya ce musu komai ba.
Abdul bai kula shi ba, sai da ya kammala abin da yake yi, sannan ya dawo ya zauna a kusa da Khalil, ya kalli Khalil ya ce "Kalil, meke faruwa ne, tashi kayi mini bayani"
Kamar Khalil na jiran ƙiris, ya tashi zaune, yana share gumin da ya tsatsafo masa, ya kalli Abdul ya ce "Abdul, na ga samu, ina shirin ganin rashi"
"Kamar yaya kenan?"
"Abdul, Mummy, Mummy"
Abdul ya sake gyara zamansa ya ce "Me ya faru? Me Mummyn tayi"
Kamar Khalil zai yi kuka ya ce "Bayan wahalar da na sha wurin farautar soyayyar Hafsa, na yi nasara na samu, tana sona mun shaƙu, sai dai ina shirin zuwar wa da Mummy maganar Hafsa, ƙawaywen Mummy sun gano ni a wurin Hafsat, sun sanarwa da Mummy, baka ga cin mutuncin da ta mini ba, yanzu haka ma ta ce lallai in rabu da Hafsa, dan Allah Abdul yanzu ta yaya zan koma in janye maganata da Hafsa, bayan ta gama bank dukkanin yarda, da saka ran samun salama a wurina tayaya Abdul"
Abdul ya jinjina kai ya ce "Akwai damuwa, ka san iyaye gaba suke da dukkanin wani abu na san rai da son zuciyarmu, amma kuma yakamata ita ma Hafsa a duba a yi mata adalci, kaima kana da ƙanwa mace, alhakin Hafsa zai iya kama Fadila da bata ji ba bata gani ba"
"Kai Abdul, ba zan iya haƙura da Hafsa ba, duk da ban san wane irin mataki Mummy zata iya ɗauka a kaina ba, bana jun zan iya rayuwa babu ita!!!
DOMIN SHIGA VIP GROUP, POSTING KULLUM KU TUNTUƁENI TA WANNAN LAMBAR
***