CHAPTER 11 (NEW JOB)
by @deejasmah
WANI RABON.........🦋🦋🦋
Khadeejah Bint Ismail (deejasmah)
Elegant Online Writers (E.O.W)
In dedication to all single ladies out there😍💖...........
Follow me on wattpad @deejasmah15
Arewabooks @ deejasmah
WhatsApp @***
N.B WhatsApp only not call😁
Chapter 11 (New job)
This whole chapter is dedicated to Maimoon Abdallah "Heroine" who has been a source of inspiration throughout the course of writing this book thanks for sparing a time to check on my write up ,thanks for the support and love Jazakirrahman ❤🔐
Monday tazo min cike da fargaba da tunanin abinda zan tarar a office ɗin kasancewar wannan ne karon farko da zan fara yin aiki a rayuwata tunda na farka nake jina wata kala banda ƙwari ko kaɗan a wurin breakfast ne Mamie ta lura da yanda nai wata kala kamar mara lakka a jiki tace " don't be nervous dear all will be well " haɗa baki mukayi a tare wurin cewa insha Allah Mamie
Sannan peacefully mukai breakfast a tare muka fito dukanmu Mamie ce ta fita damu fav kaɗai aka sauke a luggard roundabout kasancewar shi CBS yake zuwa while ni kuma sai a gate ɗin KASU inda zan hau keken karji ta ajiye su kuma suka shige school ɗin ita da Areepha
Keke na samu saidai kasancewar safiya ce babu masu tafiya sosai yasa na ɗauki drop har bakin companyn ya ajiyeni sallamar shi nai tareda ƙarasawa tundaga gate ɗin zaka tabbatar da cewa ba ƙaramin wuri bane dukda cewa safe ne amma harabar wurin cike yake da manyan motoci na alfarma kallon kaina nayi don in tabbatar da in na shiga ciki babu mai bina da ƙasƙantacce kallo
Yeah i'm looking good in one handcrafted egyptian gown cream colour nai rolling da veil ɗin kayan sai takalmina luxury sneakers maroon da side-chained Gucci bag itama maroon hamdala nai wa allah kana na nufi entrance door ɗin inda securities suke tsaye gaisheni sukai tareda buɗe min ƙofar amsawa tareda godiya kana na nufi cikin reception ɗin
Shade na gaggauta cirowa daga bag ɗina gudun kar inyi ƙauyanci sakamakon haɗuwa da kuma tsaruwar reception ɗin koina ƙal-ƙal kuma tsaf-tsaf kamar ba mutane counter na nufa ina mai knocking wata farar yarinyace ta leƙo ta ƴar gilashin wurin tareda cewa "yess" gaishe ta nai tareda cewa "I'm here to see Mr. Sahal Maikwanoni "
Ƙare min kallo tai sama da ƙasa kafin tace " so you are the new secretary ?" da sigar raini a maganar tata "yeah i am " na bata amsa ina mai gyara fuska ta gudun kar raini ya shiga cikin lamarin "ohhh i can see" ta sake faɗa tana wani yatsina ban tanka ba na sake gyara tsayuwata landline ɗin wajen ta ɗauka tareda danna no.2 tana mai karawa a kunnenta " sir, the new secretary is here.......ok sir " kallona tai tareda cewa "5th floor first office by your left " ta koma inda take tana latsa wayarta kirar Iphone Xmax
Kallonta nai ina ayyana rainin hankalinta a zuciyata ta ina zan gane kwatancenta girgiza kaina nai ina nufar staircase ɗin tareda lalubar number Sahal ɗin wanda tun wuri ya kamata nai hakan ɗauka yai da kanshi yai directing ɗina har zuwa office ɗin nashi inda yake tsaye a bakin ƙofa alamun ni yake jira
Cikin office ɗin muka shiga wasu takaddu ya miƙo min karanta su nai tareda signing inda ya dace sannan ya fara min bayanin yanayin aikin da komai " and sai kinyi takatsantsan da wurin nan domin kinsan yanayin aikin company sannan kuma dashi boss ɗin naki yanada tsari da yawa mutum ne mai matuƙar due process ba ƙaramin abu zakiyi ki burge shi ba amma with the uniqueness and smartness da kike dashi i'm pretty sure zakiyi more than expected from you "
Gyaɗa kai nayi cikeda gamsuwa da kalamanshi kafin nace " Insha Allah i'll do my very best saboda ganin cigaban companyn nan " murmushi yai tareda cewa " i also believe you can allah ya shige mana gaba " ameen na furta sannan muka fita daga office ɗin muka nufi Executive department wanda yake last floor wato 6th floor
Ƙasaitaccen floor ne da kaff companyn babu mai girman wurin cike yake da offices na ma'aikata sai office ɗin CEO din da ya cinye almost half na floor ɗin a gefenshi kuma ga wani small office made of glass which is more like a cubicle an rubuta "SECRETARY TO THE CEO " akwai wata glass door da take linking office ɗin da nashi office ɗinne last a floor ɗin a rufe yake ruff alamun baya nan
Glass office ɗin ya nuna min tareda cewa "this is your office mu shiga " da Bismillah na shiga office ɗin bayan nayi addua a zuciyata da allah ya tsareni sharrin dake wurin ya kuma sadani da alkhairin dake cikinta "Masha Allah " na furta a ƙasan maƙoshi a dai-dai lokacin da nai arba da cikin office ɗin
Faɗin haɗuwa da tsarin office ɗin ɓata baki ne da kuma lokaci domin banda kalmar da zan kwatanta tsarin wurin saidai ince "the office is very unique and stylish TV ce babba a bango sai ɗan gefenshi kuma fridge na ƙarami sai table mai girma a opposite ɗinshi ɗauke da system a gefe sai wasu files da suke a lode
A gaban table ɗin kujeru ne guda biyu sai wata white leather sofa tsari da haɗuwan wurin ya burge ni ko dan ban taɓa shiga irin wurin bane har na fara imagening yanda office ɗin CEOn zai kasance wata ƙofa ce kusa da TVn wanda toilet ce a wurin glass door ɗin ya nuna min yana cewa " wannan ne ƙofar ke kaɗai keda access da shi " gyaɗa kai nayi domin na fahimta fitowa mukai bayan ya bani card ɗin office ɗin saukowa mukai inda yake ce min " in boss baya gari ba'a shiga mai office sai ƙwaƙƙwaran dalili shima sai in shine wanda ya ɓukaci hakan ko kuma ni " nodding na sakeyi wasu departments ɗin muka shiga kamar su
Accounting,operating,legal da sauransu dama na shiga admin watau inda office ɗin Sahal yake saukowa mukai back to the ground floor a nan na lura ashe akwai wata stand mai nuna direction na kowani office baro cikin wurin mukai ya nufi wata hanya ta baya anan ne manufacturing department yake
(well matawalle global is a metal,steel and glass industry wanda suke samun kwangila daga wurin state and federal government akan buildings da kuma hanyoyi amma sunfi samun contracts daga constructions industries da kuma engineering projects kasancewar specialisation ɗinsu kenan)
Zamu shiga aka bamu wasu kaya muka saka da mask well i was impressed with what i see there wurin komai da tsarin shi babu hatsaniya fitowa mukai gefen wurin wani ƙaramin clinic ne sai mosque a gefen clinic ɗin ashe shima akwai gate ta wurin ta main gate muka dawo ya rakoni inda yake jaddada min "reporting nextweek sannan kuma in kiyaye dresscode ɗin da suka turamin ta email " godiya nai tareda tare keke inajin zuciyata wasai compared to yanda na fita da safe...............
Manage babu yawa i'll try to drop a new update gobe da safe insha Allah
love y'all
Deejasmah🔐🦋❤