Chapter 3 End
BA LABARI
By
Fadila Lamido
EXQUISITE WRITER'S FORUM.
Page 21- 22
Cikin dingishi yake tafiyan yayin da Suraj da Muftahu sukayi saurin kamashi, rikeshi sukayi yayin da Suraj yace, amman dai kasan yadda 'kafar nan take maka ko?, yanzun ne fa aka samu aka samu kanta, kuma ya bada sharadin ko kaji dama kada ka taka ta....
Ganin Modibo yana kokarin d'ingisawa yasa su kara tareshi da saurin su, kowanne fuskar sa dauke da firgici, muftahu ne yai saurin zuwa ya dauko motar yayin da Suraj ya taimaka masa har suka fito harabar gidan, Nan danan Suraj ya bude motar yayin da Modibo ya shiga gaba, Suraj ma zagawa yayi ya zauna a mazaunin driver shima Muftahu bayan motar ya zauna domin yanayin Modibo a yau ya basu Mamaki, bayan sun dauki hanya ma kowa da abin da yake sakawa cikin ransa, Modibo ma rufe idon sa yayi kawai tare da kwanciya jikin kujerar Motar.
Sannu ahankali suke tafiya sabo da ruwan saman da ake shekawa, tafiyan minti 30 ta kaisu kofar gidan, ganin Modibo na kokarin sauka Suraj yace ka zauna bara na dubo ta, kafin Modibo yace wani abu Saraj ya hangi ta tana tahowa, dan haka ya rike hannun Modibo yana fadin kaga gatacan ma tana tahowa.
Acikin ruwan nan?, Modibo ya tambaya.
Sauka Suraj yayi da saurin sa, ganin Suraj yasa ta tsaya cak tana kallon sa, saidai shi ko kada batajin tsoron sa domin ya jima yana zuwa gurin ta, kuma be taba matsa mata da karfi da yaji saita bude fuskarta ba Kamar yadda wadda suke Kira da sunan Modibo ke yi.
Suraj ne tsaye agaban ta cikin tsareta da kallon yace, daga Ina kike?, Ido yabita dashi tsayon lakaci batace komai ba, ganin yayyafin da ake danyi a yanzun yana jika su yasa shi saurin fadin, " toh kizo ga Modibo yazo duba ki hakawai yana zaune ganin wannan ba'kin hadarin ya matsa sai yazo ya ga halain da kike ciki, kinsan meye tunanin sa?, ganin ba amsa zai samu ba yaci gaba da cewa, " be taba rayuwa cikin irin wannan gidajen naku ba, atunani sa be yadda da ingancin ginin ba, sannan kuma Yana ganin cewa ke kadai ce a cikin gidan dan haka yake tausaya miki, yau na tabbatar lallai Modibo na tsananin tausayin ki tunda ya fito a irin wannan lokacin, ni abun da nake so dake ki bashi hadin kai, ki zama karkashin kulwarsa, Ina me tabbatar miki zai kula dake fiya da tunanin ki domin yayi mun gani"
Idan akwai abun da Unaisa tafi tsana a rayuwarta be wuce mgnr tabar dakin Innawuro ba, dan haka ma wannan lokacin ji take Kamar ta make Suraj, dan haka ta shiga tafiya kawai tana kokarin kasarawa gida.
Bayanta Suraj ya biyo yana fadin toh kije Modibo na mota yana Kiran ki.
Cak ta dakata tare da runtse Ido acikin zuciyarta tace, me ya dawo yi?, Ba tasowan hadarin nan ya wuce ba, nagaji da wannan zirga zirgar gaskiya.
Ganin ta tsaya Suraj yace, Muji ko?
Ba yadda ta iya dole ta fara takawa zuwa gurin motar su daya tal da sukazo da ita, domin tasan ko Bata tsaya va kota hadin yaye ne indai wancen motunin ne saya shiga gidan, Suraj ne ya nuna mata gefen da yake dan haka ta zagaya ta tsaya gaban kofar da gilashin sa yake rufe.
Ahankali taga gilashin nayin kasa dan haka tai saurin yin kasa da kanta, ajikin ta taji kallon ta yake yayin da hakan yasa ta duk taji ta daburce.
Daga Ina kie?
Cikin dakarkiyar muryan sa yai mata wannan tambayan dan haka taji Muryan sa ta daki dodon kunnen ta, wannan karon ya dawo da takama, tafada azuciyar ta, kafin ta dago idonta ta kalle shi.
Ba kallona nace kiyi ba, kuma bana son shiru lallai yan Ina son kimin mgn, daga Ina keke cikin irin wannan yanayin kina awaje.
Wasa ta fara da hannun ta dan haka yabita da Ido tsayon lokaci sannan yace, " Ina duka fa.
Cikin sauri ta kalle shi dan haka ya kara cewa eh da gaske Ina duka, idan na sake miki tambaya biki amsa min ba wlh saina dake ki, Ina jinki daga Ina kike?
Cikin sauri ta hada kanta da gefen window motar hakan yasa tai kusa da kunnen Modibo ahankali tace, Ni kaine ka bani tsoro.
Lumshe idonsa yayi jin muryanta cikin kunnen shi batare daya bude ba yace, meyasa nake baki tsoro aunty na. Sahima kasa kasa yai mgnr sosai, sai dai duk da haka suraj yaji abin da ya fada.
Bana son kacewa sai kaga fuska ta.
Lumshe Ido ya sake yi tare da fadin, sai kuma me?
Sannan kabar cewa zaka tafi dani.
Inajikin sai me kuma?
Kubar zuwa gaba dayan ku bana so.
Haba dallah?, da gaske mubar zuwa?
Eh.
Toh inajin ki sai kuma me?
Ni dai kubar zuwa kawai idai kuna zuwa ciwona bazai warke ba.
Hada dan Allah?, sabo dame?
Ni bazanbar dakin Innawuro ba, bazan iya bacci ko Ina ba inba gadon uwata ba, ban saba da kowa ba kuma bazan iya rayuwa da mutane ba.
Haba?, da gaske ko wasa?
Da gaske nake.
Toh Allah ya jikan ta, ya Kai haske kabarin ta, sannan nima zan sata cikin addu'ata, Allah ya jadda rahamar sa gare ta.
Lumshe Ido Unaisa tayi tare da fadin, Amin nagode
Ajiyan zuciya Modibo yayi sannan ya kara kasa da muryan shi tare da karkatowa gare ta, duk da cewa Yana zauna cikin mota, ahankali yace, " barin inyi mgn biyu zuwa uku dake, ni ban tabajin Ina son ganin fuskarki ba, dan ni bashi ne agaba na ba, kuma kema dai banda abun ki inda Ina son ganin fuskarki da tuni nagani, dan cire wannan kyallen ba abu bane me wuya awaje na, Koda kikaga kwanaki nacewa Magaji ya danna minke ya cire, bayi hakan ne nagane kinajin mgn kokuwa kurma ce, ganin fuskarki bashi ne abun da ya kawo ni ba, nazo in taimake ki ne ko aya kike.
Shiru kawai tayi tana wasa da hannun ta, tare da addu'a Allah yasa karya kara mata duk abun data lissafa masa.
Jinsa tayi ya cikaba da fadin, kinsan mene?, Ina son ki fahimce ni da kyau, dan uwa nake son ki daukeni ba ba abokin gaba ba, idan Kika bani hadin kai komai duk abun da zanyi sai da yardan ki, Ina son kisa azuciyarki nima Innawuro ce mahaifiya ta, bana neman komai agurin ki, baki da abun da zaki bani, asalima zuciyata a kulle take, amman naji araina lallai Ina son in kaiki cikin mu, domin kishiga ciki wata rayuwa ta daban, barin kwad'aita miki wani abu, ki kwatanta inda zan kaiki da aljanar duniya, Amman bawai dan dukiya, kudi, mulki, ya ko saurauta ba, duk Basu bane hujar da tasa na Kira inda zan Kai da aljanar duniya, nakirashi da hakan ne saboda muna da soyayyar dangi, farar sura tare da farar zuciya, amman baxa'a rasa bata gari ba.
Sosai Unaisa taji ta samu nutsuwa ta kallin sa, babban abun barin cikin ta da yace komai saida yardanta, muryan sa ya sake dukan kunnen ta.
Aunty zaki bini muje??
Kanta ta kirkiza har yanzun bakinta Yana saitin kunnen sa.
Komawa yayi ya jingina da kujer motar tare da lumshe Ido sannan ya dago ya kalleta tare da fadin shikenan kije abun ki.
Juyawa tayi batare da tace komai ba, murmushi Suraj yaja tare da fadin, Allah yayi abin inji mafadin auren sa.
Wani 'Kayataccen murmushin Modobo yayi, tare da fadin, "banda abin ka dawa Bata gama cin wutaba ai fara batayiwa 'yar uwar ta barka.
Ai naga kamar tayi mgn ne yau.
Da gira Modibo yabawa Suraj amsa cikin sauri Suraj yace me tace ne?
A'a mgnr muce nida ita.
Dariya Suraj yayi har hakoran sa suka bayya domin aganin sa narasan Modibo nasarsa ce.
Har suka kamo hanya Suraj murna yake hakama Muftahu farin ciki fal cikin sa, afalo suka samu Magaji yayin da suke kokarin shigo da Moddibo dan kin yadda sukayi ya taka kafar Kamar yadda yaso.
*****
Ina kukaje nadawo ban sameku agida ba.
Zama Modibo yayi ya lumshe Ido Yana jin Suraj na fadin, "Ina ka aje masa sandarsa, sanin kane cewa dole dasu yake amfani, ko bazai fita ba ai ya shiga toilet, amman dan ranshin hankali saikai nisa dasu.
Kashhh, wlh na manta Suraj, na manta na kaisu dakin sa.
Muftahu ne yace ai naduba duk dakin bangansu ba.
Sunanan gefen gado mana, Modibo ya kalla sannan yace, Modibo Sorry wlh mancewa nayi.
Ko Motsi Modibo meyi ba, idonsa lumshe.
Mikewa Magaji yayi ya fito dasu ya aje agefen Modibo, saidai tunkan ya cire hannun sa akan karfen yaji saukan wani gigitaccen mari akan kumatun sa,
Sosai Marin ya shigeshi, rabon da amai irin sa ya manta.
Suraj da Muftahu ne sukayi saurin rike Modibo wadda banda huci babu abun da yake yi.
Ahankali Suraj ke fadin, haba Mana Modibo, ka koma ka zauna kodan sabo da kafarka, Muftahu ma hakuri yake bawa Modibo daker ya koma ya zauna, Magaji kuwa yana rike da kumatun sa saidai ya kafe Modibo da ido, tsayon lokaci suka dauka a haka sannan Magaji yasa kafarsa ya daki karafunan suka watse a kasa sannan ya dauki key din mota ya nufi fita a fusace.
Suraj ne da Muftahu suka fara fadin Ina zaka?, Modibo ne ya daga masu hannu dan haka babu wadda ya sake cewa komai.
Sunaji ya tashi Mota yabar gidan.
Lumshe Ido Modibo yayi sannan ya dauki wayar sa ya shiga typing, bayan ya gama ya aje wayar a gefen sa ya lumshe ido, befi minti minti goma da aji wayar tasaba saiga Magaji ya dawo hannun sa cikin aljihu ya tsaya a tsakiyar falon tare da fadin, " Kai hakuri nayi suskure, daganin inda yai mgnr kasan tursasa shi akayi.
Adaren ranar ma Suraj ne da Modibo kwance wani dakin bacci, hira suke duk su biyun suna Kan gado, zuwa can Modibo ya daga waya ya kira Magaji da Muftahu, Nan danan sai gasu,
Tashi Modibo yayi zaune batare da ya kalli kowa ba yace"
Ina son in muku mgn akan yariyar nan ne, Ina son in dauketa muje da ita gida, abin da nake son kowa cikin ku ya sani, ni na dauki yariyar nan ne matsayi biyu kacal, kanwa ta jini sannan intaso Ina iya zama uba agare ta, idan nace uba, Ina nufin zan iya bada auren ta, sannan ni babu ruwana da fuskarta ko wani abu nata, rayuwarta kawai nake son taimakawa, dan haka banson wani cikin ku ya nunawarwa yariya irin wannan abun dana lisa.
Yauma kamar kullum motocin sune jare suke shiga cikin Unguwar su Unaisa, kofar gidan Malam Baba suka fara tsayawa yayin da Modibo ya fito, wannan karon cikin rakiyar Muftahu da Suraj suka shiga cikin dakin me maganin, Magaji kuwa daman har yanzun kunbure kunbure kawai yake yi.
Bayan an gama duba kafar tasa ne Modibo yace, Baba daman Ina son inma wata magana.
Toh toh inajin ka Ranka ya dad'e.
Kallon Muftahu da Suraj yayi sannan ya juya ya kalli Malam Baba, Baba akwai wata yariya ana tana makotaka da ita, na samu labari akan yariyar cewa bata da kowa, kuma ita daya take rayuwarta a inda naji ma duk cikin Unguwar nan babu wadda yake hurd'a da ita....
Gyara zama Malam Baba yayi sannan yace, " Wala Habaru kake mgn akai kenan.
Eh haka akace sunanta.
Jimmm Malam Baba yayi sannan yace me kake so sani game da ita?
Ni kawai Baba Ina son in dauki yariyar ne inriketa sabo da naga bedace ace 'yamace karama haka na rayuwa ita daya ba, inason kuyi min izini in tafi da ita, idan kuma tana dawani dan uwa duk inda yake zanje in nemo izinin tafiya da ita cikin dangi na.
Jimmm Malamin yayi zuwa can yace, " ai wannan yariyar da kake gani dangin ta nanan fal cikin wannan layin da kake gani, jikan Malam Bawace, kodaga Ina ka tsaya cikin garin nan kace gidan Malam Bawa za'a kawo ka har kofar gida...
[11/20, 11:16 AM] +227 90 16 59 91: BA LABARI
By
Fadila Lamido
EXQUISITE WRITER'S FORUM.
Page 23-25
Cikin tsanini Mamaki Modibo ya kalli Malam baba, bama Modibo kadai ba har Suraj da Muftahu kallon sskabi mutumin dashi.
Modibo ne yace, " Baba kana nufin tana kusa da 'yan, uwanta to meyasa zuka banzatar da ita?
Jimmm malam Baba yayi tsayon lakaci sannan yace eh to, ba'aji abakina ba, Amman dai koma menene akwai Malam Ayuba shine karamin kanin Innawuro Yana raye shi yake da damar baka Wala Habaru ko ya haana ka, amman shawaran da zan baka ka rabu da yariyar nan inda ka ganta.
Meyesa kace haka Baba?
Toh nidai abinda nafi gani kenan, sabo da bama muba mutunan unwar nan ba, danginta ma gudun ta suke.
Jimmm, Modibo yayi zuwa can yace, " nidai Baba banajin akwai abun da zai sani in janye kudirina, a takaice dai yanzun Baba ka hadani da iyayen ta.
Cikin wani irin yanayi Malam bawa yacewa Modibo toh shike Nan duk lokacin daka shirya kamin mgn saina kaika har gidan.
Aini Baba Koda yaushe shirye nake, ko yanzun ne ma muje.
Eh toh inaga Bari mu Bari zuwa gobe, dan yanzun da wuya a same shi agida wata kila ya tafi kiwo.
Dahaka sukayi Sallama suka wuce awannan karon Basu shiga gidan Unaisa ba, sosai hakan ya Basu Mamaki ganin Modibo bece su shiga ba.
*****
Washegari Kamar yadda malam baba yace, Modibo tare da mutanen sa suka sake shiga cikin Unguwar, gidan Malam Baba suka fara zuwa suka dauke shi sannan suka wuce gidan su Malam bawa.
Motocin sune jere kofar gidan Malama Bawa, Nan idon mutane da hankalin su ya dawo Kan motocin baki daya, kowa Mamaki yake me ya kawo wannan zuka zukan motocin kofar gidan Malam Bawa.
Jama'a da dama tsayawa sukayi domin ganin ikon Allah yayin da wasu ke tambayar lafiya, saidai Basu dame amsa masu.
Balam Baba ko Sallama yayi akofar gidan, wata yariya ce ta leko nan ya sanar mata tamai Sallama da Malam Ayuba.
Ba jimawa ya fitonganin manyan Motocin yafara binsu da kallo tare da bawa Malam Baba hannu suka gaisa.
Modibo ko wani mugun haushin Mutumin ne ya kama su, ganin tsakanin gidan su da gidan yariyar babu wani nisa amma aka barta ita daya.
Cikin gida Malam Ayuba ya koma ya dauko katowar tabarma ya shinfida ganin haka Modibo ya sakko shida Suraj suka zauna suka gurin.
Bayan sun gaisa ne Malam baba yaiwa Malam Ayuba bayani, saidai tun kafin Malam Baba yakai ga rufe baki Malam Ayuba yace mun bashi, ya tafi da ita daga nan har duniya ta shi.
Malam Ayuba beyi Mamaki ba jin wannan furucin daga bakin Malam a yuba , saidai Suraj da Modibo sunyi matukar Mamaki musamma da sukaji yace har Duniya ta tashi ma.
Nan danan idon Modibo ya kada yayi ja, yanzun ya fara fahimtan wani abu game da rayuwar yariyar, godiya yayiwa Malam Ayuba sannan yaciro kudi ya mika masa, godiya sosai Malam ayuba yayi sannan ya rakasu har bakin motar tare da tambayan Modibo yau zai wuce da Wala Habaru?
Zama Moddibo yayi sosai acikin motar tare da fadin" a'a bayau ba, Ina Amasa magani ne yanzun, dazaran nagana amsan maganin zan koma, amman insha Allahu duk randa zan tafi zan kawota tayi Sallama.
A'a basai kunzu ba kuje abin ku.
Sosai Modibo ya kara shiga Mamaki, tsintan kansa yayi da tamyan Malam Ayuba Yaya sunan yariyar ne, budar bakin Malam Ayuba sai fara dabur dabur daga karshe yace sunanta ya shige masa.
Jikin Suraj ne yayi sanyi sosai, dan haka bayan sun sauke Malam Baba yaso su tattauna zancen da Modibo saidai Modibon yaki hakan, nunawa yayi beson mgnr tare da komawa Kan kujerar ya kwanta, Koda suka koma gidama cewa yayi kansa na ciwo yake masa, dan haka Suraj ya shiga damuwa sosai, gashi yaso yasa idon sa akan yariyar sai dai Modibon yaki yadda hakan tsayon sati uku suka kwashe sai dai suke su amsa magani su wuce abun su, sosai hakan ya damu Suraj tun Yana boyewa har abun ya bafara gagaran sa, Muftahu ma can kasan ransa yake jin son sa yariyar a idon sa.
Magaji kuwa yanzun be cika biyo su ba saidai kullum su barshi a gida.
Yauma kamar kowacce alhamis Modibo zaune gaban Malam Baba bayan ya gama shafa maganin yace, " Ina ganin yanzun kuna iya komawa gida.
Alhamdulillah Modibo yafada sannan
Sannan yace kenan Nan da sati daya Ina iya aje sandar?
A'a kadan kara riketa har bayan ka koma da sati biyu, lokacin ta cika wata biyar kenan da fara magani guri na, insha Allahu babu matsala da zata kara tashi.
Cike da gamsuwa Modibo ya amsa sannan suka masa Sallama suka wuce, yauma Modibo bece zasu gun yariyar ba, dan haka Suraj yace yau bazamu leka gidan Nan ba kuwa.
A'a kawai Modibo yace, sannan suka wuce gida, tun daga wannan ranar Shirin tafiya kawai suke tare da tattare duk wani abu da suke bukata.
*****
Muftahu ne zaune shi da Modibo saman Mota, suna hira ahabar gidan su, Magaji ne yace, gobe war haka muna gida, bayan dan hutun kwana biyu kowa ya kama harkokin sa, Ina tabbatar maka na koma gida bazan sake yin tafiya ba.
Mum fa zaunu, gashi wadda mukeyi Dan shi din ma besan munayi ba, Nina fara cewa zanyi jinyan sa amman ya iya daga hannun sa ya mare ni.
Ya sani Mana, Yana sane dakomai, kai ai laifi ka masa, kawai dai ranar ka vata masa rai ne ba wani abu ba, kuma ai kasan halin sa da fushi.
Duk fushin da zaiyi saiya mare ni?, kawai dai yaci albarkacin masu albarkan ne harna bashi hakuri, kuma bakasan wani abu ba?
Eh inajin ka.
Muna komawa gida zan dawo garin nan.
Me zakayi anan kuma ?
Wannan yariyar zan dawo gunta, idan har zata bani hadin kai auren ta zanyi.
Wacce yatiyar kenan.
Wala Habaru, Magaji ya fada Yana murmushi.
Runtse Ido Muftahu yayi, lokaci daya yaji wani zufa na karyo masa kenan Magaji ma sonta yake, Koda yake babu Mamaki domin yariyar daka ka kalleta ko cikin Hijjabi kasan zatayi kyau, duk da ciwa ta taso cikin talacin da yayi mata katutu, amman tafiyarta ma abun kallo ce, gata wani irin kyan sura na musamman, hakama tafukan hannun ta da kafarta kawai abun kallo ne, hakika ba namiji da zai kalleta beji Yana sonta ba, daker Muftahu ya iya fadin, " ai da ita zamuje.
Ina zamu da ita?
Can gida Mana, tuni fa Modibo ya nemo izinin tafiya da ita gurin kanin maaifiyar ta, kuma ambashi daman tafiya da ita, sannan kuma nifa tuni na gsyawa Modibo Ina son yariyar.
Da sauri Magaji ya Mike kenan kuna min zagon kasa Kai da Modibo, akwai abun da kike shirya min, kuma ma tayaya Modibo zai dauki yariya ya tafi da ita batare da izinin kowa ba, nifa abun nan nasa ya fara isata, Yana yanke hukunci kansa tsaye batare da izinin kowa ba daga gida, cikin sauri Magaji ya nufi dakin Modibo yayim da Muftahu ya bi bayan sa, kusan atare suka shiga, Modibo waya yake adaidai wannan lokacin, Dan haka sukayi tsaye bayan ya sauke wayar kallon su yayi yace", Lafiya kuwa?
Ahakali Magaji ya matsa kusa da Modibo ya zauna agefen gadon yayin da Modibo yake tsaye agefen gadon.
Ahankali Magaji ya shiga fadin, ashe ka samu an baka damar tafiya da yariyar nan?
Eh an bani, gobe insha Allahu zamu tafi da ita,
Kansa ya Dan shafa kada daga goshi zuwa keya sannan ya kalli Muftahu yace, " toh meye kuma ka biyo ni, kaje Mana, mgn zamu yi.
Ni ba abun da ya dameni da kai.
Da kallo kawai Modibo ya bisu, gani yayi Magaji na hararan Muftahu dan haka yace wai meye haka?
Modibo wai biyoni yayi Dan nace zan gaya maka Ina son yariyar nan.
Murmushin Modibo yayi har hakoran sa suka bayyana sannan yace, " shine kake koran shi?, abukin cin mushe fa ba'a boye masa wuka, taho ka zauna nan gurin Muftahu, tahowa yayi ya zauna kusa da Magaji, kamar yadda Modibo ya nuna masa sannan Modibo ya kallesu ya sake yin dariya yace, " karkuyi fad'a dan kun hadu ason abu daya, inace da aure kuke son ta, kuma ai matar mutum kabarin sa, sannan akwai wani abo wadda duk ku biyun nan baku sani ba, idan baku manta ba antaba ce mana wani yayi nacin bin yariyar harna tsayon shekara daya amman bata saurare shi ba, toh ba kowa bane wannan mutumin illah Suraj.
Duk su biyon Modibo suka kallah, yayin da ya kara tabbatar masu da lallai Suraj ne, sannan ya kara da cewa, " amman duk da hakan wannan ba wani abu bane, abun da ruwan zafi ya dafa idan akayi hakuri ruwan sanyi ma saiya dafa, domin Inda rabon kura a takobi sai a sayar asai mata akuya, ita mace Kamar allura ce acikin ruwa, me rabo ka dauka.
Cikin sauri Magaji ya tashi ya fice adakin, yayin da Muftahu yai saurin ruba masa baya, harabar gidan Magaji yaje ya tsaya, sintiri kawai yake tare da jujuye zantukan Modibo, kenan Modibo Yana nufin duk mu ukun muje mu taka rawar mu, kalaman Modibon yaita tunawa har tsayon wani lakaci, shima Muftau irin wannan halin ya shiga, yayin da Suraj ko bema san me suke ba.
Modibo ma zurfi yayi atunanin yadda zasuyi bayan sun koma gida, yayin da yake girmama farin jinin da yariyar ta samu agarin su Magaji.
Misalin farfe bakai na safe duk sun gama shiri, Dukkan su manyan kaya ne ajin su, na shadda yar gaske, wadda aka mata ado da aiki na zamani, kowane sanye da malum malum, amman banda Modibo sabo da kafar sa.
Mota uku kawai suka dauka domin yiwa Malam baba Sallama, sannan su dauko yariyar, gidan Malam Baba suka sauka bayan sunyi Sallama suka nufi gidan Unaisa.
Duk da cewa sunjima basuzo ba saida gabanta ya fadi, domin yanzun hankalin ta ya fara kwanciya, tahowa tayi ta bude kofar, Modibo kadai tagani, Ganin ta bude kofar yasa kafar sa ciki.
Jikin kitchen din ta tsaya Kamar yadda ta saba.
Sallama Modibo yayi bayan ta amsa yace, gaishe ni?
Daker ta iya bude baki tace Ina kwana.
Shima cike da takama ya amsa sannan yace, kin dade baki gammu ba amman kikasa tambayan ko lafiya, koda yake nasan murna ma zaki yi.
Kawar da kanta tayi, Dan haka Modibo ya bita da kallo sannan yace, " kina jina na?, Kwanaki naje gidan ku na samu baban ki.....
Da saurin ta ta kalleshi tare ta katse shi da dan karfinta, ni bani da gidan da ya wuce wannan, sannan bani da wani baba da ya wuce Baffah kuma ni Baffana ya rasu.
Kallonta yayi sannan yai ajiyan zuciya tare da fadin, " Allah ya jikan shi, amman bana son ina mgn a katse ni, ki saurareni kawai.
Nan danan yaga idonta ya koma launin ja jawur, duk da haka saiyaci gaba da cewa.
Baban ki Malam Ayuba yabani ke halak malak intafi dake ki zauna karkashin kulawata idan kin samu miji na aurar dake...
Bazani ba, kuma na gaya maka banda wani uba aduniyar nan, karka kara dangantani da wasu.
Ni kikewa mgn haka?, toh Bari kiji dole zan daukeki ko kinaso ko baki so, yanzun yanzun nan kuma ba sai anjima ba, dan haka nake shawartan ki da kifito da kafarki ko insa adauke ki aka.
Zamewa tayi zuwa kasa, ta rushe da matsanancin kuka, bude baki tayi da murya sosai tana fadin, " saidai ka fitar da gawata, wlh bazani ba, da kanka kamin alkawarin kace saida aminceata yanzun kuma kace ko inaso ko banso ba, sabo da angani ahaka?, bani da wata daraja?, ganin yadda take kurma ihu yasa hannu ya riko hannun ta, wani irin rawa yaji jikin ta nayi yayin da tashiga kwalawa Dada Kira tana fadin Dadana kizo kigani, zasu tafi miki da amanar ki, Dada!! Kizo dan Allah ban iya rayuwa ko ina, kenake gani kamar uwar data haife ni, karki bari a rabani dake, Dadda!! Kizo fa idan Kika jinkirta zakiyi kukan bakin cikin rasa inda nake, za'a tafi dani wata duniyar Dada!!
Irin wannan surutan Unaisa keyi cikin ihu ta karaji, tuni Modibo ya fara fadin, ya isa kanwata ki dawo cikin nutsuwar ki, ganin Kamar batajin sa yasashi girgizata, daker ta dan fara nutsuwa lokacin harsu Suraj sun shigo cikin gidan sabo dajin ihumta.
Bayan ta nutsu ne Modibo yace Kanwata wacece Dada?
Hanakali tace Mama tace?
Jimmm yayi sannan yace mamanki?
Kai ta saga masa, Modibo na kallon cikin idonta yace tana Ina yanxun, nan kusa take?
Amsawa tayi da eh dan haka yace tashi ki kaini gurin ta.
Cikin sauri ta mike ta nufi fita, bata tsaya jiransu ba sauri taitayi yayin da suka shiga mota har tai nisa sannan suka biyo bayan ta, ko kafin su karaso ta karya kwana aguje dan haka Koda suka iso babu ita, saidai sun gane gidan dan waccen lokacin da suka biyota Nan tashiga,
Kofar gidan suka faka motar su saidai tunkan sukai ga fitowa Dada tafito hannunta rike da itatuwa biyu.
A hankali Modibo ya bude gilashin motar sa, Sallama yayiwa da Dada Sallama dan haka tamaida masifar ta tare da amsawa tana fadin, " kune kuka biyo min yariya?
Sakowa Modibo yayi daga cikin motar yana fadin, banje da niyar tafiya da itaba saida na nemi izini, dan haka bana kallona a mara gaskiya, kuma banta sanin ki kojin sunanki ba sai yau abakin ta, dan haka nace mata ta kawo ni gurin ki, ni yanzun gunki nazo dake zanyi mgn.
Haka nan taji kalamin yaron sun shige ta, Nan ta bashi dama ya shiga zauren gidan duk kudirin sa ya gaya mata, sanyi jikin ta yayi sosai, sannan kuma ta yaba da dabi,un yaron saidai duk da haka bata iya bada Unaisa ba. dan haka tace, "nafahim ce ka Modibo, amman wannan yariyar tana dangi, na uwa dana uba, ni nan da kake gani mahaifiyar ta ce tasha nono tabarwa mahaifina...
Katseta Modibo yayi da fadin, " Amman meyasa aka barta ahaka bawani kulawa?
Ai nike ciyar da ita kuma nabiya mata kudin makaranta zaman gidan ne kawai me gidan ya hana, sannan dangi kowa yaki ta sabo da wani dalili nasu.
Wanni irin dalili ne wannan Mamma?
Jimmmm, matar tayi, sannan tace, ' a'a wannan dalilin sirri ne da bana iya gayawa kowa face mijin da yazama nata na aure, banajin zan iya bude wannan saiga mijinta.
Jimmm Modibo yayi sannan yace ton Mama har yanzun Ina Kan bakana duk danaji kina tsaye akanta, ina son kibani ita, domin inje in daura daga inda Kika tsaya.
Wallahi yaro bana iya ba bada ta, ni nan da kake gani banga abun da zai rabani da Itaba, na tsallake matsalolin kala kala domin cika alkawari dana dauka, kuma Ina son in cikashi shi.
Lumshe Ido Modibo yayi batare daya bude ba yace Yaya sunan ta to?
Sunanta *RAHMA*
Bude idon sa yayi tare da fadin, _*Rahma* maganin zugi_, mama kibani ita inje da ita kema ki bimu kiga iyayena.
Modibo inajin kunyan sake sanar dakai bazan iya bada Ita ba, idan kaga abun da zai rabani da Unaisa saidai in aure, wannan nasan na sauke amanar dake kaina ne.
Jimmm Modibo yayi sannan yace Mamah kenan idan aure ne zaki yadda?
Me zai hana, aure babu inda bekai Mutum, Suraj Modibo ya kallah sannan yace, Muje mama zamu dawo.
Sallama sukama mama suka fito, saidai duk jikin Modibo yai sanyi, banda bad'uwan gaba babu abun da yake, dan haka ya kasa daukan kafarsa ya daura amotar, tsintan kanshi yayi da kwantar da kansa saman motar cikin wani irin yanayi da baya Ina tantance shi, lokaci daya yaji ya diri dirice.....
[11/20, 11:16 AM] +227 90 16 59 91: BA LABARI
By
Fadila Lamido
EXQUISITE WRITER'S FORUM.
Page 26- 28
Gaba dayan su bin sa sukayi da kallo, Suraj ne yayi karfin halin dafa sa tare da tam bayan Yaya akayi ne Modibo?
Dagowa yayi tare da shiga motar ya zauna, kowa tambayan sa yake amman ya gaza yin mgn, Hanyar gida suka nufa yayin da suka tarar da tarin motocin su suna jiran su, kowa cikin Shirin tafiya duk an gama zuba komai cikin motar, cikin gidan Modibo ya nufa daka kalli fuskarsa kasan Yana da damuwa sosai.
Zama yayi cikin falo, gaba dayan su su tambayan ta suke waishin me yake faruwa ne?
Daker Modibo ya iya fadin, matar takin amincewa, dana dage mata saitace saidai in aure ne zai raba ta da yariyar, Ni ko azahirin gaskiya nafi son intafi da ita babu aure akanta domin ta samu kulawa ta data ammi mu, inason ta zamo wani abu, idan aka mata aure a yanzun Kamar an sata cikin matsala ne....
Me yasa kace haka Modibo?
Kansa tsaye yace saboda Batasan me rayuwa take ciki ayanzun ba, burinta kawai ta zauna ita daya tana ikirarin cewa adakin mahaifiyarta zata rayu harta mutu, nasan ko an mata aure yanzun bazata wani samu farin ciki ba, kaga fa inda take mgn daker Kamar intayi yankata za'ayi, naso na canza mata arayu amman matsawar ta tafi da aure akanta babu wani kulawa da zata samu daga gare ni.
Toh ai Modibo nima zan kula da ita sosai, Ina son yariyar kuma ko yanzun ashirye nake Dana aure ta, Ina da kyakyawan nufi akan yariyar.
Nasan haka Suraj amman duk da hakan dai nafi son tafi da ita ba auren kowa kanta.
Shikenan yanzun dai kana nufin gara mu tafi ba yariyar kenan?
A'a ba nufina kenan ba, Insha Allahu da ita zamu tafi, ko da auren ko babu, amman dai Kai me kake gani?
Nifa Modibo ko yau saina bada sadakin ta, wlh inason ta.
Shikenan, yanzun ina ga fasa tafiyan zamuyi, gobe sai mu koma, idan har zasu iya daura auren agobe zuwa jibi.
Afusace Magaji yace, ni gaskiya mutafi kawai, Abba nacen najira, kowa acikin gidan ya shirya wa zuwan mu, be dace suga bamu dawo ba.
Duk wadda ya tambayi dalili kuce masa Muftahu ne beda lafiya cewar Suraj, saidai tun Kan ya rufe baki Muftahun yace, a dai ce wani dan yawancin lokaci idan nai karyan ciwo toh ciwon yakan same ni da gaske.
Modibo da yasan me yasashi fadin haka yai saurin fadin toh ni ace nine banjin dadin
Magaji ne yai surin fita yayin da Muftaho ya rufa masa baya.
Modibo ko kokari yake kar Suraj ya fahimci su Magaji dan haka yace, " su Kada suje gidam.
Da yamma Suraj ne ya shirya ya fita yayin da Modibo dasu Magaji suka zauna a gida, bayan fita Magaji ya samun Modibo cikin yanayi na tashin hankali yace, yanzun Modibo kana ganin ya dace mu tafi kawai da mata ba sanin iyayen shi?
Magaji ai tunda yace yaji ya gani babu matsala kenan.
Shikenan, yanzun daura auren za'ayi kenan?
Eh insha Allahu.
Tafdi lallai, Amman inda Abba mu ne kawai yaga anje masa da mata kawai ba BA LABARI yana iya tsinewa mutum, hakama ammi da Yadikko.
Ajiyan zuciya Modibo yayi sannan yace hakane Amman ai kasan kowa da ahalin sa.
Shikenan nadai kula kana karfafa masa guiwa.
Eh insha Allahu komai zaizo da sauki.
Shikenan Allah ya tai maka.
*****
Washegari sunje Kamar yadda Moddibo yace, maga ta fahimta sukayi da Dada inda suka yanke shawan gobe zasu kawo Sadakin ta sannan a daura auren nan take.
Bayan sun tashi zasu tafi Suraj ya nemi da Yana son mgn da yariyar, rokon sa Dada tayi akan cewa kwata kwata karya sako mata zancen aure domin Zazzabi na samunta da zaran taji zancen aure.
Modibo cikin mota ya koma ya zauna, Muftahu Magaji duk jikin su a sanyaye.
Sun jima suna jiran fitowan Suraj amman shiru, saida ya kwashe kusan awa biyu sannan ya fito.
Zuwa can ya fito yana share zufa, ya zauna acikin motar Yana sauke ajiyan zuciya.
Babu wadda yaiwa wani mgn har suka isa gida.
*****
Da daddare Suraj ne ya kasa bacci, dan haka ya tashi zaune tare dasa hannun sa ya Dan daki Modibo.
Tashi Modibo yayi zaune tare da fadin lafiya?
Modibo akwai abun dake damuna.
Meye shi?
Yariyar nan jiya naso ta bude min fuskarta ingani amman taki sam, duk zama da nayi gurin dazon ko kala bata ce min ba, gashi kuma ance da safe za'a daura auren.
Kashhh, Suraj kabar zancen ganin fuskarta, inace ahanta ka ganta kaji kana so?
Eh Amman gaskiya Modibo nafara wani tunani, idan ba ansan da wata akasa ba ta bude fuskarta Mana, kilama fuskar tata kesa jama'a ke gudun ta, ai Unguwar tasu cike take da samari kuma yariyar daidai da rana daya baka taba ganin ta babu ni'kabi, Koda ciwo take fuskarta rufe take ruf, kuma Modibo wani dalili ne zaiya dangin uwa dana uba su kitaa alhalin sun tabbatar ita d'in yar halak ce, kuma jinin su, sannan Modibo me zaisa mata da mazan Unguwar, yara da manya su dinga tsron wucewa Koda ta kofar gidan ne?, Dan haka nidai nafi ganin tana da swata siffa ne afuskarta me firgitarwa.
Shiru Modibo yayi cikin yanayi na sanyin jiki sosai, zuwa can yai gysran murya tare da fadin, " Suraj kabar wannan tunanin, sheda ne kawai, kasa ma tana da wata hallita din, idan ka aureta kayi taimakon masulunci kuma zaka samu lada.
Kai ina gaskiya ni ina da ra'ayin auren kyakyawan Mace ne, dan haka inaganin gobe da safen kawai mukama hanyan.
Suraj karkayi haka, ka aureta inyaso saika aure wata inhar kaga Bata maka ba din, kuma ai mutane sun shaida yariyar nada kyau.
Toh ai kowa cewa yake ance, kuma kanajin abun da waccen matar tace, dangi sunkita saboda wani dalili, sannan daka bukaci ta gaya maka dalilin tace saiga mijinta kad'ai, dan haka nina lura wannan rufa rufa ne kawai ake, domin sai adaura auren afito ma mutum da mata tamkar dodonniya atunnin su dole mutum ya hakura, dan haka ni babu ni a wannan tafiyar nacire kaina aciki bazan auri gaibu ba.
Suraj nafi ganin ka tsaya ka nutsu kayi shawara da zuciyar ka dakyau, ada mun ce gobe da safe za'a daura auren mu wuce amman yanzun bari mu barshi sai zuwa jibi da safe lokacin ka kara nutsuwa da kyau.
Nifa Modibo kawai bani aciki, mikewa yayi yana fita daga cikin dakin yana surutai akan cewa shifa kawai ya janye.
Sabo da tunani ranar Modibo kasa bacci yayi, sosai ya kosa su koma gida kuma lallai Yana son su tafi da yariyar.
Washegari har misalin Tara na dare Modibo Suraj bece komai ba, Modibo ma bece masu komai ba har washegari, Magaji da Muftahu ko had'a Kai suka yi wannan lokacin, dan Basu san wani hali ake ciki ba akan mgnr, su dai kawai sunga ba'aje ba Kamar yadda aka ce.
Washegari da Safe misalin 9 Modibo ya fito falon, Suraj Magaji da Muftahu duk suna zaune, kowa da kalan tunanin sa, Tsaye Modibo yayi da sadar sa, sannan yai gyaran Murya tare da fadin, " Suraj me ka yanke akan mgnr yariyar nan??
Batare da Suraj ya juyo ba yace, " aina gaya maka bani awannan tafiyan.
Jimmm yayi na tsayon lokaci Yana nazari, zuwa can yace, Shikenan, Muftahu da Magaji ya kalla sannan yace, " Suraj ya janye akan mgnr yariyar nan, acikin ko waye ya shirya auren ta?
Cikin sauri Magaji yace nine, Muftahu ko kallon yabi Suraj dashi tare da mamakin meye dalilin sa na janyewa.
Shikuwa Modibo ganin Muftahu bece komai ba yace, toh iyayenta mu su ke jira, idan har ka gamsu ba matsala ni zan karba maka auren ta.
Eh Ina so, nawa ne sadakin nata?, Modibo ya tambaya cike da zumudi.
Cikin da kwarin guiwa yace sai munje tukuna.
Shiko Muftahu tsintan kansa yayi da tambayan Suraj yace Meyasa ka fasa Suraj?
Muftahu haka kawai zan aure yariya ne banga fuskarta ba?, Kowa fa nata ya gujeta, kuma sun amasa yariyar jinin su ce, mezaisa su gujeta?, idan ba tana da sifar dodanni ba, kanaji fa wannan Dadar cewa tayi sai mijinta kawai ne zaisan dalilin kinta, Ni wlh ko inda take ban Kara zama.
Kuma fah haka ne Suraj ya fada tare da tsoro kara akan fuskar sa.
Idan hakane me zaisa ta bude fuskar tata kafin a daura auren?, Magaji ya fada cikin yanayi irin na wadda ya firgita.
Cikin sauri Suraj yace, ai taki ne Magaji, duk dad'ewar da nayi agidan shekaran jiya kala batace min ba, kuma duk nacin da nayi ta bude fuskar ta taki, nifa wlh ko rantsuwa nayi bazanyi kaffara ba yariyar Nan tana da matsala afuskarta shiyasa kawai tacire tsammani da aure.
A'a bahaka bane, Ina son kusa zuya daya, acikin ku daya ya aure ta, ku maza ne kuma da daman kara aure.
Modibo wai babu kira me yaci gawayi, nidai bani aciki duk wadda yaga zai iya ga hanya.
Kama kugu magqji yayi sannan ya sauke hannun sa daya ya shara zufa tare da fadin, Modibo mu sama ma kanmu lafiya kawai mu kama gaban mu gobe da safe, dan wlh wani abokina ya taba bani labarin abun da ya faru agidan su, yariya ce yar islamiyya kullum cikin hijjabi, Yana murna yayi amarya sai adaren farko yaga ashe nono daya gare ta....
Dariya Suraj da Muftahu suka saka bayan Muftahu ya gama kyajewa yace, to kila ita duk biyun ne babu.
Modibo ne yai masa wani irin kallo Yana tsaye fuskarsa daure tamau Kamar be taba sariya ba, zuwa can yace, kuyi shawara Dukkan ku, acikin ku ukun dole wani ya aure ta.
Hada baki suka yi wajen fadin wlh bani ajiki.
Jimmm Modibo yayi zuwa can ya sake cewa, nidai nace muku ku kara nutsuwa, daga nan zuwa safe sannan ni Ina baku shawara kubi ahankali domin shi me rawar kai baya d'igirgire.
Da haka ya barsu afalon ya koma ciki, hira sukaci gaba duk akan yariyar, Magaji ne yace, kuna jin Modibo wai dole, shiya aureta Mana.
Washegari tun da sassafe suka haushi shiri, tunanin su Modibo zaice bayau zai tafi ba, amman Yana fitowa suka ganshi cikin shirin sa na tafiya, duk motocin sun sun hallara tare da yan rakiyar su, motoci goma sha daya ne jere, ahankali suka fara fita daga cikin gidan, saidai hanyar Unguwar su unaisa suka nufa kodar gidan Malam Baba suka tsaya, waya Modibo yai masa ya fito ya shiga cikin motar, tafiya kadan sukayi suka isa wani madaidaicin masallaci, cike da Mamaki suka shiga masallacin yayin dasu Magaji suke kuskus din ko sama da kasa zata jade bazasu yadda da auren taba.
Cikin suka samu masallacin bayan kowa ya zauna Modibo ya ciro kudi a aljihun sa ya mika, Malam Baba ne ya kalle shi yace dawa za'a daura ranka ya dad'e?
Suraj ya kalla yayin da Suraj yai saurin girgiza kansa, su kuwa su Magaji cikin sauri suka juyar da kansu, ganin haka Modibo ya kalli Malam Baba yace a daura dani.
Kabbara Malam Baba yayi sannan ya kalli Modibo yace, "wane sunan ka?
Ahankali Modibo yace *Fahat*
Nan take aka daura aure tsakanin Fahat (Modibo ) da Rahma.
Fitowa sukayi jama'a ne suka fara tambayan shi ongon wanene daga Ina yake? ganin babu me iya amasa masu sukabi abun da Ido kawai.
Daga nan gidan Dada suka wuce domin daukan Rahma, suraj Magaji da Muftahu sai kallon Modibo suke tare mamakin sa.
Magaji kuwa fadi yake, lallai, Ammi Afnan, Safna saidai kawai su ganshi da yariya BA LABARI.
Akofar gidan Dada suka jera motocin su, bayan an bashi damar shiga gidan, har cikin dakin Dada ya shiga ya zauna, babu kowa adakin zuwa can Dada ta shigo da Unaisa cikin shigarta kamat yadda ta saba, saidai da alama batasan me ake ciki ba, domin tana ganin Modibo ta fara raba ido, daker Dada ta zaunar da ita saitin kafar Modibo sannan tasa hannun ta ta roko na Modibo tana kokarin had'awa Dana Unaisa take fadin yau zan gaya maka wacece Rahma...
Alhamdulillah
Anan nakawo karshin littafi na daya.