BAKAR FURA

BAKAR FURA CHAPTER 3

by @3135605806678644

*🕳️BA'KAR FURA🕳️*

  _A true life story_

*Na*

_Fadeela Lamido_


  PEN WRITERS ASSOCIATION✍️

          *episode 11- 12*

Zare ido Aysha tayi yayin data koma da baya ta zauna, hawaye ya gani shar yana zobo mata dan haka ya isa bakin gado ya zauna yana binta da kallo, yayin da kunnen sa suke tsakar gida.

    Sosai hawaye ke zubo mata, dan haka abun ya shiga bawa Aliyu mamaki, kasa yayi da murya yace matsoraciya kawai, kinsan kinajin tsoro meya kawoki?

   Ahankali tai mgn dan haka ya ce mene?

       Akaine kace min bakajin tsoro, yanzun Kuma kace Ummi na tsakar gida"

    Kawar da kansa yayi yai murmushi sannan ya juya ya kalleta, kenan nine matsoracin sabo da ban fitar dake ba?

       Tana Satan kallon idon shi tace a'a.

   Toni kibar min kuka.

   An fara kiran Sallah, nasan Mama zane ni zata yi.

     Kawar dakai yayi sannan yace, "kiyi hakuri Ummi ta shiga daki, kinsan yanzun idan ta ganki fada zatayi, zaki zama baki da damar nan wadda kika sameta ayau, idan kin amince kinbar zuwa daga yau to kizo ki wuce, nayi hakane sabo da tsaro badan tsoro ba.

     Ahankali ta fara share hawayen ta saidai duk da haka fuskanta akwai tarin damuwa.

   Mikewa yayi ya sake lekawa har yanzun Ummi na nan zaune bamata da niyar tashi Dan haka ya dawo cikin dakin yana kallon Aysha tare da fadin, " inje inyi sallah in dawo?"

   Cikin sauri ta girgiza kanta alamar a'a

    Kallon ta yayi sannan yace lallai kuwa, kenan yau bazan samu jam'i ba?, sabo dake?, tsaki yaja kadan sannan ya nufa toilet din dake cikin dakin, alwala yayi ya fito yana ware hannun rigarsa, abakin kofar ya hangeta, dan zaro ido yayi sannan ya tsaya yana tunanin hanyar da zai billowa al'amarin.

      Window dake dakin ta baya ya kalla sannan ya fara takawa ahankali ya isa window, labulen ya yaye sannan ya leka, juyowa yayi ya kalleta sosai sannan yace, kwaso takalmin ki mugani ko zaki iya fita tanan.

   Cikin sauri ta kwasa takalmin ta ta isa gareshi, daukanta yayi cak ya tura ta, cikin ikon Allah ta dire tsaf tare da sauke ajiyan zuciya, aguje ta fice agidan, shiko Aliyu murmushi.

    Juyowa yayi ya nufi masallaci yayin da ya wuce Ummi tana sallah a tsakar gidan.

             *****

  Daga ina kike?, Ina kika tsaya har aka Kira sallah?

    Jakar makarantarta ta aje tare da yaye rigar jikinta tana nunawa Mama bayanta, Mama yau duka mukaci, da cewa ma akayi amakaranta zamu kwana, bayana duk ya kunbura.

      Yar dariya Mama tayi, radadine ya rudaki Amman bayanki be kunbura ba, saki rigarki.

   Muryan Umma sukaji tana fadin, ta dawo ne ne gantalallar?

  Eh Umma gata ta dawo.

 Gidan ubanwa ta tsaya?

   Mamace ta sanar da ita duk yadda akayi yayin da Umma tace yayi kyau ai, yanzun haka surutu sukai, gara da aka zane kun ai.

     Mikewa Aysha tayi tana fadin, " su Umma anji gulma"

     Wanni itin kallo Mama taiwa Aysha yayin da Aysha taki kallon ta, Muryan Umma sukaji tace ga magulmaciya nan agaban ki"

     Jimmmm Aysha tayi tsayon lokaci yayin da Mama tace tashi kije kiyi sallah ki dauki abincin ki.

    Mikewa Aisha tayi bayan tayo alwala tana kokarin maida dan kwalin ta taga wucewan Umma kitchen bayan ta tabi da kallo sannan tace, " Umma dazon naga me kama dake a hanya"

   Tukunyan miyar Umma ta dauko sannan ta fito tana fadin, " haba"?

    Allah kuwan, Aysha ta fada sannan ta dauki hijjabinta ta zura tare da sake cewa, " Umma baki tambayen me kama dake din ba"

     Toh inajin ki gaya min waye ne me kama dani din?

    Birii.

   Cikin sauri Umma ta sauke tukunyan miyan tare da kallon Ayaha data kambara sallah, Mama ma kallon Ayaha tayi tare da fadin, lallai baki da mutunci.

    A'a barni da Ita, ai nima ba kanwar lasa bace, kallon Ayaha tayi wanda zuwa yanzun tayi ruku'u tace, mancewa kikai ai biri namiji ne, wannan mutumin na wancen garin shine katon biri, dashi sukafi kama, ficewa tayi adakin ta nufi tsakar gida, inda mama keta dariya tana fadin Aikuwa Umma kinyi maganin rashin kunya.

       Ai kibarni da ita.

   Zuwa can Aysha ta fito hannunta dauke da kofin da fura me sanyi aciki, Mamace ta kalleta sannan tace kizo kidauki abincin ki.

    Banaci, furar nan ta ishe ni.

   Mama batabi ta kanta ba ta jawo abincin dake gabanta, yayin da Aysha ta koma daki, Umma ce ta zauna kusa da Mama domin cin abincin amman sai ganin Mama tayi tana ya mutsa fuska.

   Yaya akayi?, Umma ta tambaya

    Umma miyan nan gishiri yayi yawa.

   Hannu Umma tasa cikin miyar ta dandana tare da kallon mama tace, " wlh miyata lafiya kalau take, Indo ce ta takara min shi.

     Batanan akayi miyan ai Umma, kila dai hannun ki ne ya subuce.

    Saifa kiyi, Aysha ce ta kara shi, aina zagi ubanta, ta zuba min gishirin ne dan karnaci, toh sainaci ko inaci ina rufe ido ne.

    Aikuwa indai hakane sai mata duka wl....

    Kashhh, karkice mata komai, barta kawai, muci abincin mu bamuma san tayi ba kawai.

          ******

   Yau tunda ya tashi dariyar Aysha ta jiya ce ke fado masa, wadda aduk lokacin daya tuno saiya murmusa, sannan yana yawan tuno yadda hasken ta ya dannen dan hasken da yake dashi nesa ba kusa ba, afili yayi dari tare da fadin dole kiyi dariya Aysha kinga dan baki me karfin hali, kallon fatarsa yayi sannan yace kai ina, niba baki bane, kawai dai hasken tane yai yawa har yana kashe ido.

      Irin wannan tunanin baya awa daya batare daya fado masa ba, dan hakan yake yawan murmushi musamman idan ya tuno irin amsan da take bashi wadda yafi kama da aje ahaka din.

       Aliko yau murmushin me kake ne?

   Innawo wanine yabani dariya.

      A lallai kuwa yana da abin dariya, yau bazaka kasuwar bane?

    Zani amman sai 4 yanzun zuwa zanyi in kwanta.

     Mikewa tayi ta nufi daki yayin da Aliyu ma ya mike ya nufi nasa dakin, cikin ransa yake fadin kila yau bazatazo ba, dan naga jiya ta tsorata.

   Kwanciya yayi yana jiran lokacin daya gindaya mata na zuwan, yayi yaji ana kwankwasa window sa ahankali.

   Mikewa yayi ya isa window ahankali ya bude, Aysha ce tsaye cikin kayan islamiyyarta riga da wando da hijjabinta daidai guiwa, jakar makarantar ta rataye agefenta yayin data bude madaidaicin bakinta tace, " ina yini"

   Lumshe ido yayi batare daya amsa ba, juyawa yayi ya bude kofar data shigo jiya ganin haka tai saurin zagayawa ta shigo"

       Rufe kofar yayi sannan ya dawo ya rufo window tare da dawowa wajen zaman shi ya zauna, itama Aysha kujeran jiya ta zauna tana kokarin fito da littafin ta.

     Aliyu kuwa kur yamata da ido yana me kare mata kallo tsayon lokaci.

   Kallon da yake mata yasa duk taji ta tsargu, rasa inda zatayi tayi tayi, tun tana kawar dakai harta fara buga kafarta akasa, tana dan sheshshekar kuka?

   Lumshe idon sa yayi tare da fadin, "Menene"?

    Kai ne.

   

  Idon shi lumshe yace me ya faru?

   Ya Aliyu kallo na fa kake?

  Neman ki nake, hasken ki ke kashe min ido na.

  Kyalkyalewa tayi da dariya, tare da fadin gani nan fah.

   Daidai ina?

   Dariya ta sake sawa, yayin da hakan ke kara sashi nishadi.

     Hannunta ta daga tana yawo dashi saitin fuskarta tana fadin, gani nan fa👐

     Kara ware idon sa yayi nadaiga wasu TAURARI guda 10 suna yawo, tare da wani haske wal wal.

   Dariya ta Kara sawa wadda har shima saida yadan murmusa.

   Sosai yakejin wani nishadi na shigarsa hakama Aysha mantawa tayi da komai zuwa wannan lokacin data kalli fuskar Aliyu take yin dariya domin ba karamin dariya yake sata ba.

     Muryan sa taji yace nidai tunda ba ganin ki nake ba bani littafi kawai karki hanani zuwa kasuwa kamar jiya.

  Littafin tabashi, har suka gama acewarsa be ganinta, haka ya bude bata kofar ta fita shima ya fita.

    Hakace ta cigaba da kansancewa har tsayon wata Uku, aduk ranakun islamiyya saita fara shiga gidan su Innawo sannan ta wuce makaranta, wata rana ta fita ta kofa wata wata rana kuwa saidai ya sakata ta window, tsayon wannan lokacin Babu wadda ya taba sani.

   Zuwa wannan lokacin shakuwa me karfi ta shiga tsanin Aysha da Aliyu har yakai ranar da Babu makarantar suna kewan juna tare da kosawa suka junan su.

     Ayanzun Aysha tasan wasu daga cikin halayen Aliyu, sosai take ganin kirkin sa, haka shima Aliyu ya fahimci Aysha dakyau, akoda yaushe yana yaba kwazonta tare da son karatu nutsuwa da kunya.

             ****

  Yauma kamar kullum Aysha ce zaune ita da Aliyu, littafin ta kan cinyar sa, kokarin fahimtar da ita yake, duk da cewa zuwa yanzun idan an bata aiki amakarantar tana jaraba yi da kanta, Koda za'ayi mata gyara yana zamuwa bame yawa banr, sosai take dauke duk wani abu da zai koya mata, rufe littafin yayi bayan sun gama ya mika mata sannan yace toh bani kudina.

     Wani littafi ta bude cikin Jakarta ta dauko masa kudin ta mika masa.

   Amsawa yayi sannan ya daga katifarsa ya tura, juyo yayi adaidai lokacin da Aysha ke mika masa sweet"

   Murmushi yayi sannan yace, " au har da kari?, to bare min"

  Bare masa tayi ta mika masa, yayin daya tura mata fuskarsa yana fadin saka min.

   Saka masa tayi kamar yadda yace, idon sa lumhe yace, Kai, bantaba shan sweet me dadin wannan ba.

   Cikin yar dariya tace , "Kai, Ya Aliyu duk sweet din da kake Sha?"

  Ummm wannan yafi dadi.

   Yauwa Ya Aliyu wai meyasa kake saka kudin ka kasan katifa?

   Dauke idonsa yayi daga kallonta ina ruwan ki?

  Dan Allah"

 

   Toh tarawa nake in sunyi yawa inje makka"

  Kaiii!! dariya tayi, ya Aliyu har makka ma?🤔, bama katafi Nigeria ba gurin Baffah?

      *Kar me karatu ya manta, duk mgnr da Aliyu yake yi da Aysha sunayin ta ne cikin harcen fullaci, idan karatu ne kuwa da harcen french domin Aysha batajin hausa, yare nan biyu kawai take iyaji, hakama iyayen Aysha, gidan Innawo ne kawai sukejin hausa kadan kadan.* 

   Nace meki kudin zuwa Nigeria nake nema?, wannan kudin aiki nawa zasu baki mamaki, inason nayi wani abu me daraja dashi sabo da sun fito daga hannun 'kanwata, kawata Kuma aminayar sirri na.

      Murmushi Aysha tayi me sanyi har cikin ranta take kallon fuskan Aliyu dake kawace da murmushi, cikin yanayin jin kunya take kallon shi dazaran taga kamar baya kallon inda take"

   Shikuwa Aliyu daya kulla tana kallon sa yake fara wasa da girarsa tare da gashin idon sa, wadda hakan kesa Aysha murmushi, shima Aliyu dayaga tana murmushi yake jin zuciyarsa wasai, suna cikin wannan yanayin suka tsinkayi bugun kofar dakin ta cikin falon, azabure suka kalli kofar gaba dayan su"

    Kai Aliko!!!!

  Muryan Innawo yaji dan haka dan haka ya nunawa Aysha bayan kofar da Innawo ke bugawa.

  Kusan atare suka isa gurin, yayin da Aliyu ke amsawa tare da bude kofar sukayi ido biyu da Innawo"

   Kallon sa tayi sama da kasa sannan tace, " Kai dawa a ciki ?

   Lumshe idon sa yayi, nidawa kuwa Innawo?, ni daya, lafiya?

       A'a daman yariyar nan Indo ce ake nema.

    Wacece haka?

   A'a jeka abun ka, juyawa Innawo tayi batare da ta jira me zaice ba.

   Rufe kofar Aliyu yayi sannan ya dawo dakin yana rike da kugun sa da hannun sa duk biyun yake kallon Ayaha tare da fadin, " wani yaga shigowan ki nan ne?"

    Cikin samyin jiki tace a'a.

     Bakin gadon ya dawo ya zauna yana me tuna irin kallon da Innawo tamai, be dawo daga wannan tunanin ba yaji ana buga kofar dakin ta tsakar gida.

   Da tsananin mamaki ya juya ya kalli kofar, domin babu wadda yasan cewa yana bude kofar a yanzun sai Aysha Kuma gata aciki suna tare.......

   

     

Fadeela Lamido ✍️





*🕳️BA'KAR FURA🕳️*

  _A true life story_

*Na*

_Fadeela Lamido_


  PEN WRITERS ASSOCIATION✍️

       *Episode 13to 14*


 Mikewa Aliyu yayi, mamaki cike da fuskar shi, sai dai ya kasa zuwa gun kofar, yayin da yayi da yai tsaye hannun sa cikin aljihun sa.

    Aysha kuwa tuni ta kara gigicewa tana shirin fara kuka.

  

     Kofar kuwa kara tsananta bugunta ake yi, dan haka yace waye?

   Nice, muryan Innawo yaji cikin daga murya

Dan haka ya saki ajiyan zuciya sannan ya nufi kofar dakin cikin falon ya fice zuwa tsakar gida da innawo ke tsaye.

     Gaban kofar ya sameta cike da kallon tuhuma ta kalle shi ina Indon?

   Kawar dakai yayi can gefe sannan yace wai wace miki tashigo nan din?

   Runtse Ido Innawo tayi, Aliko wannan ba halin ka bane ka bude min kofar nan.

       Ai kinsan ba'a bude wannan kofar muje ta ciki ki duba ki gani.

  Ban zuwa, alamu ya nuna kana amfani da kofar nan Aliko, dan ada ba haka rufuwarta yake ba. sannan yariyar nan sau uku ana shigowa nimanta ni jikina ya bani indo na dakin ka.

    Zuwa yanzun kam bashi da mafita dan haka ya kawar da kanshi tare da fadin karatu tazo.

  Raratu?, toh daman har yanzun ba'abar wannan karatun ba?, Maza ka bude mata kofa ta fita tun kafin uwarka ta dawo.

   Lumshe ido yayi, sannan ya koma ta inda ya fito, Aysha ce ke zaune ta fara hawaye ya cemawa tashi muje"

  Mikewa tayi tana raba ido, yayin data rike wani daga cikin littafin ta ahannu, jakar makarantar ta Aliyu ya dauka sannan suka fito Ayaha na gaba Aliyu na binta abaya, a tsakar gida suka hadu da innawo, kallo kawai ta bisu dashi yayin da Ayaha ta wuce sumi sumi, ganin da Innawo tayi Aliyu nashirin fita har kofar gidan tare da Ayaha tace dawo Aliko.

 Lumshe ido yayi sannan ya mika mata littafinta ya dawo ciki.

   Wanni irin kallo innawo tabishi dashi sannan ta dawo takoma ta zauna tare dasa tagumi.

     Kusa da innawo ya zauna domin ya kula hankalin Innawo ya tashi sosai, dan tafadata yayi, Innawo menene wai?, Naga duk kin damu ne.

   Ba dole in damu ba Aliyu, bamu ankara ba har ka canza hali Aliyu, me zai kaika ka dauki yariya mace budurwa kasata cikin dakin ka ka rufe kofa ka rufe window babu me ganin ku sai Allah.

   Wani irin kallo yai mata, Innawo wannan ce budurwa?, Aysha ai karama ce.

   Himmmm Aliyu ka gyara tunanin ka, mace mace ce, ba iyayenta ba harni bazan amince da haka ba, hakika nashiga tashin hankali, ga manya manyan 'yan mata can awaje me zakayi da Ayaha dahar za'a ce maka ka rabu da ita ka kasa rabuwa da ita. 

    Innawo ki fahimceni, ni kina bani dariya idan kina nuna wai son ta nake, haba Innawo kallini fa, babban yaro ne fa, Aysha fa ko nono bata dashi, me zanso a ita?, wlh karatu take so kuma nasan bazaku bari ta dinga zuwa ba sabo da kakarta, niko ban tsoron kakarta.

   Baka tsoron kakarta?, amman kasan duk wanda yaga wannan al'amarin zai kawo wani tunani daban ko?

    Innawo dan Allah kibar wannan mgnr, toh waini ce miki akayi dan iskane ni?, alkawari na dauka zanbawa Aysha gudunmawata dari bisa dari akan karatun ta, kuma kome wani zaice bazan janye ba daga abun da nai niya, Innawo ai daman mutum baka iya mishi, dan haka kawai mutum yayi abun da yake ganin ya dace karya kula da me mutane zasu ce.

    Zuwa wannan likacin innawo ta kasa mgn damin ta lura lamarin nashirin girmama, daker ta iya fadin, " kenan Aysha zata cigaba da shigowa gidan nan, Kuma acikin dakin ka batare da kowa ya sani ba??

   Zanso ki ki rufe min wannan sirrin Innawo, ki yadda dani, wallahi daidai da rana daya banta bataba ji cikin raina wai zanyi wani abu da ita ba, ina mata kallon kankanuwar yariya ce yayayyiya, ina jinta acikin zuciyata kwatan kwacin yadda nakejin Husna, sai dai nashaku da ita sosai fiye da Husna, ni kaina ina son yi mata karatun innawo.

     Wani irin yawo Innawo ta hadiye sannan tace, Mahaifiyar ka bazata yadda da wannan tsarin ba?

   Karki gaya mata dan Allah"

  Waigowa Innawo tayi ta kalle shi sannan tace shikenan.

           ****

  Karfe 6 Aysha ta taso islamiya tun daga nesa ta hango motar Aliyu akofar gida, dan haka ta labe wani zaure tare da kiran wani yaro, dan Allah kaje can gidan kace ana kiran Aliyu.

   Juyawa yayi yayi Ayaha ta sake kiran sa idan an tambaye ka inji waye kace inji wani ne. 

    Tafiya yaron yayi ba jimawa sai gashi sun fito tare da Aliyu, lekawa tayi ta hango su dan haka ta fito"

  Tun daga nesa Aliyu ke murmushi, Aysha ma cikin jin kunyarsa take murmushin.

   Karasowa yayi gabanta lallai ma yariyar nan kin rainani,towai kece har zaki tsaya kice akira miki ni?

    Dana sani nashigo???

   Kishigo kimin me? ba dazon maka rabu ba?

    Lumshe ido tayi sannan tace na dame ka ko?

  Ni bance ba, amman dai kinsan yanzun gida ya dace ki isa ko?, ogogo ya kalla yazun za'a kira mangariba kije gida.

   Jikinta babu wani karfi ta wuce dan haka yace, nagode da kika leko na ganki.

   Gani yayi ta juyo tayi mgn, tana kifkifta ido tare da jujuya bakinta, sai dai tayi nisa dashi bayajin me take cewa dan haka ya zuba hannun sa cikin aljihu ya bi bayanta, tana gaba yana binta abaya yake fadin.

   Ni kike murgudawa baki?

   Tana gaban sa da tazara tsakanin su sosai tace, ni ban murguda maka baki ba.

    Takawa take cigaba dayi yayin da shima yake cigaba da takawa, yadda suke da tazara ko mutum kusa dasu yake baya iya gane magana suke yace, " nagani ai, kenan kema kin iya murguda baki.

   Ya nifa ban murguda maka baki ba, ka koma kar wani ya ganmu.

     A'a aike kika aika har gidan mu a kirani dan haka duk inda kika shiga saina biki"

   Dariya tasa tare da dan juyowa ta kalleshi, yaya wallahi ka shiko gidan mu zaka hadu da Umma.

    Toh bake bace daga nace yanzun muka rabo kin hau fushi, da bakiyi dariya ba har ciki zan biki.

     Ton naiyi ai kaje kaji.

      Korata kikeyi?

  

     A'a tsoro nake kar wani ya gan mu.

  Ko an gamu ai baza'a gane tare muke ba.

      Eh amman nakusan shigewa gida in barka awaje.

    Ba komai, ana aiken kine da daddare?

    Wata rana dai ana aike na gurin idi sawu maganin sauro ko wanni abun.

    Zaki fito anjima injira ki a wajen ?

        Eh amman kuma ni idan ba'a aikoni ba fah?

   Sai in koma gida inta kuka.

    Dariya ta kuma yi tare da dan juyowa ta kalleshi toh ai bana wajen bare inyi dariya.

    Lallai ma yariyar nan, wato har kukana ma idan inayi dariya zaki min?

   Toh daman babba kamar ka yana kuka ne?

     Yanayi mana, amman ni bazakiga kukana ba insha Allahu, danni bana kuka, amman anjima idan baki fito ba zan kasa bacci.

       Zanzo tafada adaidai lokacin data dafa kofar gidan su dare da fakan idon mutane ta daga masa hannu cikin fara'a.

   Da kansa ya amsa, tare da daga mata gira, tana shigewa gida shiko cigaba da tafiya yayi saida yai nisa da gidan nasu sannan ya dawo ya nufi masallaci.

             ******

  Da daddare kamar yadda Aliyu yace ya Isa gurin idi me shago Ana fitowa sallan Isha,'i saidai har ya karaci zaman sa Aysha bata fito ba, dan haka ya nufi gida, tashi yayi ya nufi gida cikin sanyin jiki sosai domin ba haka ransa yaso ba, Koda ya kwanta gadon sa yata tuna Aysha yana dariya daga can bacci me nauyi ya dauke shi.


        Misalin karfe 03:15pm, Aliyu ne kwance bakin katifar sa, runtse idon sa yayi da karfi ayanzun jiran zuwanta kawai yake yi, zuwa can yaji ana kwankwasa kofar ahankali.

  Sakowa yayi ya Isa ya leka window Aisha ce dawowa yayi ya bude kofar ya leka ya mata nuni da tashigo sannan suka shiga dakin tare da maida kofar ya rufe.

     Ina wuni Yaya Aliyu?

  Lafiya Lau, ya fada tare da mika masa hannu ta bashi litrafinta.

   Littafin ta fito dashi sannan ta mika masa cikin daure fuska ya amasa.

     Satan kallon idon sa take yadda yake daure fuska saita tunashi acan da kafin ya fara sakar mata fuska.

     Karutun yake mata, Amman kwata kwata hankalinta baya gun karatun tunanin ta kawai be wuce tasan me yake damun sa ba dan haka ahankali tace, ' yau baka da lafiya ne?

     Lafiya ta Lau, bacci ne kawai ban samu ba jiya, kaina ciwo yake min.

   Littafin ta mika hannunta ta dauka ta maida cikin jaka adaidai lokacin da yake cewa kawo Mana.

    A'a baka da lafiya gobe sai muyi, 

   Ki kawo nace.

  Yaya ka bari gobe sai muyi.

  Idan gobema na tashi da rashin lafiyar fa, ni haka nake idan banyi bacci ba saina kwana biyu Banda lafiya.

   Lumshe ido tayi sannan tace, jiya bakayi bacin bane?

  Banyi ba ya bata amsa yana me kawar da kansa.

 Yi hakuri, naso fitowa ba'a barni bane, amman yau insha Allahu zan fito.

    Sakin ransa yayi kadan dan kaha Aysha ta sake cewa kayi hakuri kaji?

    Naji, kawo littafin to.

   Kabarshi sai gobe. 

   Komawa yayi ya kwanta saman katifar, yayin da Aysha take zaune kujerar dake gefen gadon tana me karewa sumar kansa ido ahankali ta kira sunan sa, Yaya Aliyu?

   Na'am indo.

   Bakayin aski ne??

  Dago kansa yayi yana kallonta tare da fadin, me kika gani?

   Naga gashin ka yayi tsayo kamar na mace.

  Murmushi yayi, macen da bata da gashi ko?, Inayi kawai yana saurin taruwa ne.

   Sumar ta Kara kallo sannan tace, Yaya Aliyu?

  Na'am indo, ya sake fada akaro na biyu.

  Inma kitso?

  Kitso kuma Ayaha?, Kin iya kitson ne?

   Eh na iya.

   Murmushi yayi bayan ya kalli fuskarta ya tabbatar da gaske take sannan yace yi min to.

    Hannunta ta daura kansa tare da diban gashin kamar yadda makitsa keyi ta fara kitsawa.

    Duk abun da take Sadiq najinta, aciki zuciyar sa yasan babu wani kitson da zata iya dan haka ya barta ta masa din, yanajin yadda take ta cikuikuye masa gashi, ita ko Aysha yi take tana cigaba da surutu yayin da yake amsa mata, saidai zuwa can taita magana tajishi shiru dan haka ta leka fuskarsa, baccin sa yake merai da lafiya dan haka ta fashe da dariya wadda dariyar ta tadashi.

    Ke baki wuce ba.

  Nagama maka kana bacci.

  

   Tashi yayi zaune, tashi ki wuce gida, saukowa yayi ya leka tsakar gidan yana fadin, yi maza insaki ta window Innawo da Ummi suna kitchen.

  Takalmanta ta diba yayin da Aliyu ya dauketa cak ya zurata batare daya lekaba kamar yadda yasaba kowacce rana.

    Gaban sa ya yaji ya fadin adaidai lokacin da yaji muryar wata na fadin, Innalillahi wa inna ilaihir raju'un, toh kuzo ku gani.

   Jin wannan kalamin yayi matukar daga hankalin Aliyu, dan haka ya taho da sauri ya leka.

   Wata mata ce take tafa hannuwa cikin tsabar mamaki da tashin hankali akan fuskar ta, yayin da Ayaha ke rungume da jakar makarantar ta tare da takalmanta a kirjinta.

  Innawo da Ummi ne suka karaso gurin yayin da matar ke fadin kunce bata shigo ba?, Gata adaki. Katon namiji balagagge.

     Ummi ce ta kalli Aliyu dake tsaye ta window, cikin tsananin mamaki ta juya ta kalli matar tana fadin, " Murja daga Ina kikaga Ayaha ta fito?

  Gashi kina gani kuwa ga wadda ya daukata nan cak daga cikin dakin ya dareta anan, akan idona ba wani ne ya gaya min ba, nifa daman jiya da idona naga shigowan Ayaha gidan nan Amman kukace bata shigoba sabo da da hadin bakin ku ake sata adaki.

     Wani irin kallo Ummi taiwa Aliyu na tuhuma sannan tace, Aliyu kaika sako Aysha ta window?

    Fuskarsa daure sosai yace eh.

   Eh?, Aliyu eh fa kace min?

   Lumshe idon sa yayi cikin yanayin dake nuna beji dadi ba, yace Ummi karatu tazo"

      Karatu?, Hannunta ta daga cikin zafin rai ta rafka masa mari wadda har saida yasa hannunsa ya dafe.

      Murja kuwa juyawa tayi ta fice agidan tabar Aysha tsaye agurin"

   Innawo kuwa bata da bakin mgn, rasa abun yi yasa Ummi fashewa da kuka, cikin kukan take zagin Aliyu mgn ta ciki bacin rai babu irin wadda bata fada masa ba.

   Idon sa ne ya kada yai jawur, tare da fadin, Ummi tsaya kiji, amman Ina ta inda take shiga batanan take fita ba, cikin wannan yanayin Umma da Murja suka samu Ummi, nan umma ta shiga surfawa Aliyu zagi tare da fadin, ya lalata mata jika"

    Idan hankalin Ummi da Innawo yakai dubu toh yau duk sun baci, cin mutunci sosai Umma kewa Aliyu yayin da yake kallonta ido cikin ido tana me nuna shi da yatsa, wannan lokacin Innawo hakuri ta shiga bawa Umma yayi da Umma ke ture Innawo tana zagin Aliyu.

   Cikin wata irin murya me cike da karadi da hargowa yake kadawa Umma Hannu tare da fadin karki Kara zagina ya isheki haka

     Eh lallai, ke Murja kiga min dan iska mara mutunci, wadda besan darajan manya ba.

   Juyowa Aliyu yayi afusace ya fito daga dakin, ganin barin sa dakin Innawo da Ummi sukayi cikin gida aguje, ganin sa sukayi da masifar gudu ya fito daga kitchen dauke da bakin wuta ya nufusu, tara tara suka masa daker suka samu suka rike shi yayin da Umma ke fadin, kubarshi ya kawo dan uban shi.

  Zafgegen itace ne ahannun sa, yayi da Ummi da Innawo suke kokarin kwacewa, duk yadda suke son hakan ya gagara kokarin nufar Umma yake yayin da Umma ke tsalle tana surfa masa zagi,

   Daker Ummi da innawu suka tura Aliyu cikin daki suka maida kofar suka rufe.

   Zuwa wannan lokacin jama'ar unguwa sun fara cika gidan, mutane ne tun daga ciki har kofar gida, ganin yadda aketa gutsura mgnr ya dagawa Ummi hankali yasata daukan gyale bashiri tabar gidan.

   Innawo ko da mutanen unguwa daker suka fitar da Umma da iyalenta, har gida Innawo ta bita tana me bata hakuri, hakama kwakota hakurin suke bawa Umma domin dai babu wadda ya taba ganin abokin fadan Aliyu Kuma ba'a sanshi da wani mugun hali ba, asali ma be cika sakin fuska ba, sai dai kowa yasan shi mutum ne meson yara, daker Umma ta lafa sannan suka baro gidan, ganin yadda hankalin Innawo yake atashe mutane sukaita kokarin kwantar mata da hankali, har cikin gida wata makociyarta ta rakata yayin da har wannan lokacin Aliyu na rufe adaki.

    Innawo ce atsakar gida tare da inna talatu makociyar su, inna talatu ce tace toh abudeshi Mana.

  Kofar falon Innawo ta kalla, a'a rabu dashi aciki, fadan karfin hali yake yi, mutumin da bashi da gaskiya wai shi ke tada jijiyoyin wuya.

    Ummi ce ta dawo ita da Alhaji Umar da wani yayanta Alhaji sani, ganin su Inna talatu ta tashi ta fita.

 

    A tsakar gidan suka tsaya suna maida mgnr Ummi kuwa gefe ta koma tasa tagumi, bayan Innawo ta gama musu bayani Alhaji Umar yace, " yanzun Ina Aliyu?"

    Rufeshi mukayi tunda yaki sauraron kowa.

    Mikewa mazan guda biyu sukayi suka bude kofar suna kallon yadda Aliyu ke huci"

  Alhaji Umar ne yace sannu da karfin hali.

   Sunkuyar da kanshi yayi kasa tare da gyara wuyan rigar sa.

     Alhaji Sani ne yace wai toni abun dake daure min kai, karattun dole ne?, itama yariyar yar iskace bata da tarbiya.

   Ummi ce tace ai ni yanzun ma Aliyu shi babba me laifi, kwata kwata indo bata wuce shekara 14 , Ina za'a hada shi"

   Alhaji Sani ne yace, au 14 aini na dauka ma ko budurwa ce.

    Ina fa sa'ar Husna ce fah, nan suka shiga masa fada tare da Haddad masa bashi ba Aysha, sosai suka masa fada tare da daura duk laifin akanshi, sannan suka wuce gidan su Aysha suka Kara bada hakuri, yayin da Innawo da amsa da sharadi. Baruwan Aliyu da Ayaha.

  

   Koda suka dawo gida, Sun Kara zaunar da Aliyu tare da gargadin sa sosai akan Aysha, Ummi ko sabo da nuna tsananin bacin ran da tayi aka sashi ya bata hakuri.

    Tuni unguwa ta dauka ko Ina labarin ake yayin da hakan ke Kara tada hankalin Ummi.

              ***

  Har akayi kwana biyu da faruwan abun fuskar Aliyu bata dawo daidai ba hama fuskar Aysha da kannen uwar ta suka taro suka zane, yau ta fara zuwa isalamiya, koda tazo wuce gidan su Aliyu rage sauri tayi tana me kallon kofar gida.

      Misalin karfe 6 Aliyu ne zaune saman motar sa akofar gidan su, tun daga nesa ya hangota dan haka ya maida hankalin sa gareta, lokacin da tazo saitin shi murmumai daga nesa yayin daya mayar mata, sannan yace.

     An bigeki ranar?

      Batare data tsaya ba tace, eh

      Wace ta bigeki?

     Sakkowa yayi yafara takawa abayanta"

    Gaba dayan su saida suka dakeni.

   Allah ya isa ya fada, sannan ya sake cewa, kwa biyu ban gankiba banajin dadi.

  Nima haka.

   Zaki fito anjima gun idi?

  Kila, ta fada tare da hawa gadan gidan su.

     Zan jira ki awajen ya fada tare da wuce gidan nasu.

            08:00pm

  Umma sauro sun hanani bacci baki da maganin sauro ne.

    Buda cikin kwanon nan ki dauka.

  Bude kwanon Aysha tayi bakomai aciki Umma.

     Babu?, miko min ingani.

  Mika mata tayi, ganin babu ta dauko kudi ta mikawa Aysha amsa maza kije ki sawo.................






*🕳️BA'KAR FURA🕳️*

  _A true life story_

*Na*

_Fadeela Lamido_


  PEN WRITERS ASSOCIATION✍️

           Episode 15- 16



 Agogon dake daure a hannun sa yake kalla tare da waigawa ya kalli kofar gidan su Aysha.

    Har cikin ransa yake son ganin ta, yayi da ya kafe gidan nasu da ido yana daga karkashin wata katuwar fishiya gefen shagon idi cikin duhu.

   Akan idon sa ta fito daga cikin gida, murmushi yayi wadda yasa zuciyarsa yin fari Kar sannan ya zuba mata ido harta karaso gaban shagon idi"

  Hasken fitulun unguwar ne ya haske fuskar Ayaha, itako har ta Isa shagon idi raba idon take yayin da yaita murmushi.

   Ganin harta amsa maganin sauro din tana ta waigen bayanta yasashi tausasa murya tare da mata dan Kira, Indo!!!

  Cikin sauri ta kalli cikin duhun tare da dan karasawa gurin ta dan tsaya nesa dashi,yaya Kaine anan?

   Eh shigo mana Indo"

    Nidai gaskiya ka fito sarari.

   Murmushi yayi kadan, kina nufin nan asako nake?

  A'a kam Yaya, amman duk fadin layin nan mu rasa inda zamu zauna sai a mattarar aljanu"

   Dariya yayi har ya fitar da sauti sannan yace, kice tsoro gareki kenan?

   Nidai banson bishiya.

   Waigawa ya fara yi to Ina zamu tsaya nan yafi sirri ai"

    Nidai ka fito nan gurin.

  Takowa ya farayi hannun sa cikin aljihun sa yana me binta da kallo, Yaya akayi kika fito?

  Wayau nama Umma, cemata nayi sauro ya hanani bacci.

   Ke!!! nine sauro?

  Cikin matsancin murmushi tace, " Kai!! Yaya ta yaya zance maka sauro?

   To danwa kika fito?

  Dan kai.

  Kinga kenan nine sauro.

  A'a Yaya kafi karfin sauro, ni kawai wayau nayi dan in fito.

    Toh naji me wayau, yanzun Ina kudina kodan ban miki karatu kwana biyu ba shikenan bazaki bani ba wannan karon?

   Cikin dariya sosai tace wlh yaya kacika son kudi.

   Kinga laifina?

   Tana dariya tace a'a.

   To gaya min Ina kudina, suna jakata Ina Tara maka ai.

     Toh kin kauta, yanzun ki koma gida sai gobe ko?

   Kaita daga alamar eh.

    

   Hannunsa dake cikin aljihun ya murza sannan ya fito da kudi ya mika mata.

  Yaya daman kana da kudi ne?

   Au kin dauka kasuwan da nake zuwa gantali ne kawai?

   A'a Yaya ni bance ba, amman ni ka barso, yanzun fa ka gama tambayana kudi.

   Eh naki nafiso.

   Toh zan baka nawan wannan ma ka barshi.

   A'a ya fada yana waigen layin tare da fadin kona sawo miki nama ne?

   Itama?, waigawa tayi ta kalli me naman tare da fadin, ni banson Naman mutumin nan dama dai me kuli ne.

   Me kuli?, Hanyar ya kallah Ina zuwa to barin nemo miki me kulin.

     Mikewa yayi yabi saman layin yayin da Aysha ta fara raba idon kar wani ya ganta, Aliyu be wani jima ba ya dawo ya mika mata ledan sannan ta nufi gida.

  Shima fitowa yayi yana me bin bayan ta bayan tahau gadan gidan su ya daga mata Hannu itama ta daga masa.

       Maida hankalin sa yayi kofar gidan su, yayin da ya hangi Innawo zaune kan takalin dake kofar gidan.

   Kallonta yayi sosai sannan ya karasa 

    Yana fadin Innawo me kike nan?

   Karaso ta fada ahankali.

  Karasawa yayi tare da zama gefenta, sai dai ya kula akwai damuwa akan fuskarta dan haka yace Innawo meke damun ki ne.

  Kallon shi tayi sosai sannan tace, Aliyu Kaine, Aliyu me kake nema ne gurin Aysha, yanzun ranar nan yadda aka tara maka jama'a bakaji kunya ba? Abun da ya faro ranar ko yaro na goye da yana da baki saiyace wani abu domin ko yagaji da Jin sunanka bakin uwarshi da ubanshi wajen maida mgnr, kuma duk wadda yaji wannan lbrn dole saiya zarke ka, yanzun wannan besa kai hankali ka rabu da Aysha ba, to yanzun daga Ina kuke??🤔🤔.

    Zancen kauce kauce be taso ba, Aliyu ya fada azuciyar sa, afili kuwa cewa yayi, ni naje wajen idine kawai muka hadu.

    Kuka hadu Aliyyu?, Yanzun Aliyu bazaka guji wani abu ya sake faruwa ba?, karka bari a buga maka tanbari fah.

   Innawo nifa, abun da wasu zasuce baya damuna fah, tunda nina San ba wani mugun abu neke ba, Allah ma yasani, toh Innawo idan duk duniya zata dauka bani da kirki ni dan iskane suje suyi tayi, ai zargi haramun ne, Kuma ni ba dan iska bane, ko Ina iskanci bazan tsaya a jaririyar yariya kamar Aysha ba, taimakonta kawai nake ni.

   Wanni irin kallo Innawo ta masa na tuhuma sannan tace Amman kuwa idan har haka kake da kafiyan tsiya baka dauko abun arziki ba, Kuma matsawar baka rabu da itaba toni nabar bin bayan ka, kuma zan gayawa uwarka domin baxan bari abun yai nisa ba, mikewa tayi ta shige gida yayin daya bita da kallo.

               ****

    Ganin duk suna bacci ta lallaba ta wuce bayan Umma ta kwanta, kusan minti 20 da kwanciyarta sannan ta fara laluban namanta tana turawa abaki, tas ta cinye sannan ta saka agadon tasha ruwa tare da fita tasa ledan abola tare da wanko hannunta ta koma dakin.

     Washegari da Safe Umma ta fito ta nufin shara, gidan tashare tsaf sannan ta kwashe ta nufi bola, ledan datagani saman bolan ne ranta be kwanta dashi ba dan haka ta dauko ta bude.

    Nama me kuli ta hanga aciki guda biyu tare da yankan albasa, cike da mamaki ta juya ta kalli dakin tare da kwalawa mamakira.

   Fitowa mama tayi yayin da Umma tace, waye ne yaci nama da tsohon dare dan munafunci.

     Nama?, Umma.

       Nama kuwa gashi nan dan keta har zubarwa akayi, idan bake bace to yarki ce.

  Jimmmm Mama tayi sannan ta fito tana leka takardan sannan ta kwalawa Aysha Kira"

     Ganin takardan Naman jiya hannun mama gaban Aysha yai mugun faduwa.

   Ina kika samu wannan Mama ta tambayeta.

   Tsintan kanta tayi da fadin, idi me shago ne yabani.

   Ke kiji masharraciyar yariya, ni Zaki rainawa hankali, shi idin me yaci bare yaba wani, duk yadda akayi kin hadu da wannan dan iskan yaron, shine kawai duk nan duniya yake da wannan karfin halin, dauka yake kamar shidin babu wadda yake shayi, kana masa mgn yana wani rurrufe idon sa na rashin d'a'a.

  Kallon tuhuma Mama tabi Aysha dashi sannan tace, fita kikayi da daddare??

    Sunkuyar da kanta tayi Umma ce tace na sawo mata maganin sauro.

    Zaro ido Umma tayi, nace ki sawo min maganin sauro koko ke kikace min sauro ya hanaki bacci?🤔

   Ke kika aikeni, Aysha tafada batare data kalli inda Umma take ba.

     Cikin tsabar mamaki Umma tace, eh lallai Aysha baki da kirki, zuciyarki bata dakyau Sam, Kuma idan ba da gaske aka miki ba mgn Zaki dauko mana akwai alamun hakan.

     

    Mama dakin ta dawo yayin da Aysha ta zauna abakin gado cikin tagumi.

       Itama mama cikin damuwa tace, " Jiya kinje gurin Aliyun ne?"

     Nifa Idi ne fa ya rage daidai naje Sayan maganin sauron ya miko min.

   Shikenan Mama ta fada sannan ta juya ta fita tsakar gida, yanajin tashin hirarsu sai dai bayajin me suke cewa.

    

              *****

Indai nice uwarka dana tsuguna na haifeka toh nagaya maka ka rabo da Aysha, wai wanni irin masifane haka, me kake nema wajenta Aliyu?, aita mgn daya ko kunya bakaji, wlh bantaba maka shedan rashinji ba, Kuma bantaba tunanin haka daga gareka ba, nasanka dai da fushi kamar kuturo amman baka da rashin ji sai wannan karon, ni daga gau bazan sake maka mgn akan Aysha ba, Amman kasani, nafada Kuma zan Kara fada maka ayau, tunda nake a duniya bantabajin natsana wani mutum ba kamar yadda na tsana Aysha, Aysha karamar yariya ce amman tanada naci, tun tana zuwa karatu yanzun gashi wai har Kai kebinta kofar gidan su, duk da irin kashedin da aka maka. Ninayi Innawo tayi, su Yaya ba irin mgnr da basu makaba rana duk akan ka rabu da ita amman Ina, to yau nace maka indai nice uwarka ban amince ko sake kallon Aysha ba bare har kayi mgn da ita.

       Jikin sa amatukar sanyaye yace shikenan naji, kiyi hakuri.

   Dauke idonta tayi yayin daya mike yana ma Innawo wani irin kallo.

               *****

   Misalin 8:30pm Aliyu ne ke juyi kan gadon sa, duk cikin son hana kansa fita, fuskar Aysha yake tunanawa tana wannan dariyar tata dake sashi nishadi.

   Tashi yayi ya zauna, har ga Allah yana son bin umarmin Ummi sai dai wani abun da yakeji yanai masa yawo balakin son ganin Aysha yake yake dan haka ya Mike kawai ya fito hannun sa cikin aljihun sa.

   Yana dafda fita falon Innawo ta fito tana fadin, " Ina zuwa?,

     Gadina kike ne?, Wucewa yayi batare daya jira amsanta ba.

        Kallo ta bishi dashi har ya kule ko tantama batayi gurin Aysha zashi dan ada daya dawo sallah baya sake fita.

     Wani irin yanayi ta shiga na damuwa ko Yaya karshen abun zai kasance oho, tunda Aliyu ya fita har kusan minti 15 da fitansa Innawo ta kasa sukuni tashin hankali ne da damuwa me tsanani cikin zuciyar Innawo.

    Innawo!!!

   Na'am Fatima. 

  Ina Aliyu, Ummi tafada alokacin data fito daga dakin Aliyun.

      Cikin tsananin damuwa tare da takaici tace ya fita.

   Jimmmm Ummi tayi zuwa can ta koma ta zauna tare da fadin, Innawo mun shiga uku, wani irin al'amari ne wannan.

   Waigowa Innawo tayi tana fadin, wlh kuwa tunanin da nake kenan, zance duk ya wade unguwa amman shiko ajikin shi, Kuma ni abun dake daure min Kai ita yariyar ba aure ta Isa ba bare ace sonta yake.

     Innawo kibar wannan mgnr, ni yanzun mafita kawai nake nema, yanzun fa Kila gurinta yaje, ko Ina suke haduwa ma oho🤔 

      Innawo ce ta mike tana fadin, Ina zuwa barin leko shi.

            ******

   Ya akayi kika fito daga gidan?

    Duk bacci suke.

  Lumshe ido yayi tare da fadin, ban zaci zaki fitoba ai, kawai fitowa nayi in kalli kofar gidan ko in koma in kwanta .

  Dariya Aisha tayi irin Wanda kesa Aliyu nishadi cikin ransa sannan tace, " Yaya ka kalli kofar gidan fa kace?

   Eh Mana, da babu ai gara ba dadi ko? Yanzun bani lbrn makarantar Yaya karatun kwana biyu.

  Yau banje makarantar ba gidan kitso naje har sai yamma nadawo.

   Shine baki aiko aka kirani ba?

     Banga motar ka ba ai"

  Ban dawo ba kenan lokacin, kice yau kitso kikasha?

    Eh cewa nayi amin irin wadda namaka ranar nan.

   Cikin sauri ya shafa kansa tare da fadin, aini babu wani kitso akaina kindai har batsamin gashi kawai.

  Wlh na maka kitso ranar. Matsawa tayi daf dashi tana daka tsalle domin ta samu ta taba kansa tace daya yabi tanan dayan Kuma tacen yabi.

   Dariya yayi sannan yace ni banga komai ba akwai dai alamun an cuccure min gashi.

   Toh sai in warewa yayi daman kanka ya cika santsi

    Kedai kice baki iya ba kawai.

  Yaya kasan me?

  Sai kin fada.

  Gashin kanka fari ne shima.

  Fari Kuma Aysha??

   Eh sabo da farin shima da kadan fuskarka tafishi haske.

   Dariya ne ya kamasa yana me kallon fuskanta tare da yanayin girmanta so da yawa idan tayi wani abun mamaki take bashi, tunda tai mgn ta koma can gefe tana rufe bakinta.

  Shikowa Aliyu murmushi yake tare da fadin kizo nan ni ba abun da zan miki, d'anawa kika yi.

   Motar da Aysha ta hango ta faka kofar gidan su yasa Aysha ta saurin waigawa.

    Umma ta iya shaidawa tare da wan mahaifiyarta sai wasu maza guda biyu, cikin tsananin firgici da tashin hankali ta koma bayan Aliyu tana fadin nashiga Uku yaushe Umma ta fita?🙄

   Aliyu kuwa hannunsa duk biyun ya zuba cikin aljihun tare da tsayawa tsaye babu alamar fargaba cikin fuskarsa.

    Gadan gadan suka nifo garin yayin da Umma ke fadin, " gashi nan katon ballagagge yana neman hurewa yariya kunne domin ta bujirewa mgnr iyayenta.

       Shikuwa yayan Mama fadi yake ku tafi dashi, Ina Aishan?

   Police ne guda biyu suka rike Aliyu yayin da Aysha tai saurin ta rike rigar Aliyun ta baya tare da share hawayenta jikin sa.

   Duk yadda suke jansa yaki jawuwa fadi yake ku sakeni intafi da kafata.

    Baza asake kaba, kuja shi Dan iska ne mara mutunci, me kokarin raba yara da iyayen su muje can ofishin su amana iyaka dakai 

   Cikin sauri Aliyu ya fixge kadarsa daga hannun Dan sandan dake rike dashi yafara takowa gaban Umma yana fadin, adai rika Jin tsoron Allah, Kuma na tabbata rana tana nan zuwa.

   Cikin kufula Umma tace haka kaima taka ranar tana nan zuwa, kada ka jinkirta tuba wai dankai saurayi ne, ah'ah, dan amakabarta babu inda aka rubuta tsofi kadai.

     Tafe yake Aysha na rike dashi har yanzu yayin da Aliyu ke sake fadin, inda kika nufa kenan ke?, to kisa azuciyar ki jiya ta wuce bazata taba dawowa ba.

    Oho maka Mara mutunci, kokarin tura Aliyu suke yayin da adaidai wannan lokacin Innawo ta karaso cikin rasa abun yi tasa koka tare da fadin, kagani ko, fadi yake Innawo ki koma gida.

   Sosai gurin ya ciga duk da cewa darene, wani abun da ya daurewa mutane Kai gadai Aliyu acikin motar police Amman Aysha taki sakin rikarsa duk da irin dukan da Innawo ke dirka mata"

  Jawota ake tana sake komawa cikin matsancin kuka yayin da kukan nata ke Kara jawo hankulan mutane.

 Mamaki jama'ar gurin suka fara yayin da wasu ke dariya wasu ko cewa suke wannan lamari. Ko na lafiya ne?🤔🤔

    Ganin an dauke lokaci bacin rai yasa mahaifiyar Aysha Mama cewa itama atafi da ita aci ubanta, tunda bata da mutunci.

   Da yawan mutane agurin wannan shawaran suka bada yayin da wasu ke fadin gara atafi dasu a horasu a samu saukin abun, dan haka aka barta Tashaga motar,

 yayin da aka wuce dasu gaba daya.

      Duk abun da ake Ummi taji, bacin rai ya sata fadin, aje dashi duk abun da za'a mishi amishi tunda shine ya sayawa kanshi.

    Innawo kuwa hawaye yaki tsaya cikin idonta ita kadai tasan me take ji.

    Hakama ma mahaifiyar Aysha tsananin bakin ciki yasa take addu'ar Allah yasa suma Aysha dukan dasai ta kasa tashi ta hakane kawai za'a samu saukin abun........