BAKAR FURA

BAKAR FURA CHAPTER 5

by @3135605806678644

*🕳️BA'KAR FURA🕳️*

  _A true life story_

*Na*

_Fadeela Lamido_









*🕳️BA'KAR FURA🕳️*

  _A true life story_

*Na*

_Fadeela Lamido_


  PEN WRITERS ASSOCIATION✍️

         episode 25- 26

Tafe suke cikin motar tana kallon hanya, tunda take bata taba biyo irin wannan hanyar ba, iya tafiyanta me nisa gidan Daddy yau gata tana keta dajuka.

  Tun tana ganin tafiyar me sauki ce harta fara tunanin kodai duniyar za'a bari, duk kokarinta na kada tai bacci cikin motar saida tai bacci me tsayo ta tashi, wani mutmi dake kusa da ita ta tambaya har yanzun ba'a kawo ba??

   Ke yariya ai ba'ama soma tafiya ba, baki taba zuwa bane halan?

  Eh kam wannan ne zuwana nafarko.

   Toh ki shirya zama, akwai zama agaban mu.

   Ya mutsa fuska tayi sannan tace da driver inajin fitsari.

     Muryan wata mata daga bayanta taji tana fadin ke yariya daure mu Isa masallaci.

   Waigawa tayi ta kalli matar tare da fadin ankusa ne?

    Eh yanzun zamu Isa.

    Bayan kusan tafiyan minti 27 suka Isa masallacin, yayin da Aysha tafice da sauri daman abakin kofar take domin itace takarshen shiga motar.

    Masallaci ne Babba, wadda yake awajen gari, da alama masallacin kusam Dan matafiya akayi shi, waddan aharabar masallaci akwai masu abubuwan siyarwa nama tsire lemo ta sauran abubuwan motsa baki.

     Cikin toilet din da aka samar domin mata ta shiga zuwa can tafito taga wasu har sun fara al'wala, itama wata butar ta dauka tayi alwala sannan ta shiga cikin masallacin, sai yanzun ta tuna bata dauko hijjabin sallanta ba, gyalene kawai ajikinta wadda ya kasance karami ne sosai wadda be wuce adaurasa akai ba, kuma ko cikin kayanta duk irin sune. Dan haka dole tajira wannan matar ta idar da sallar sannan tace , " mama dan Allah aramim hijab inyi sallah.

   Cirewa tayi ta mika mata, sannan ta zauna agefe, Bayan Aysha tayi sallah ta bawa matar hijjabin tare da gyara mayafinta.

      Atare suka fito da matar wadda ya kasance su kadai ne mata acikin motar, hannunta matar ta rike suna tafe take matsa hannun Aysha tana fadin Yaya sunan ki?, Cikin harcen filatanci take mata wannan tambayar.

      Sunana Aysha.

  Ina zakije?, Ina nufin wajenwa zakije Nigeria?

   Jimmm, Aysha tayi zuwa can tace wajen Babana zanje.

  Babanki, Ina mahaifiyar ki fa?

   Mahaifiya ta muna tare da ita anan Cameroon Babana Kuma dan Nigeria ne"

  Cikin gamsuwa matar tace nafahimta, Amman meyasa ba'a hadoki da wani babba ba akabarki ke daya.

   Ni kadaice agidan, kakata Kuma tsohowace mamanace take kula da ita.

    Allah sarki, nagane, amman duk da haka naga gangancin su, kasancewarki yariya budurwa yakamata da wani babba atare dake, Amman insha Allahu Allah zai tsareki.

    Insha Allahu Mama.

  

  Kallon ta Mama ta sakeyi tare da fadin gaki kyakyawa dake, son kowa kin wadda ya rasa, ko in inyiwa dana kamo ne?

  Murmushi Aysha tayi tare da sunkuyar da kanta kasa tana wasa da yatsun ta.

   Matar ce ta sake cewa, ko kina da wadda kike so ne?, Ina da yaro na Babba in Zaki soshi?

   Murmushi Aysha ta kumayiwa Mama kanta akasa.

  Mama ma dariya tayi tare da cewa, Ina baki kunya ko?, Da haka suka Isa gurin motar yayin da matar ta roki mutumin dake kusa da ita ya dawo gurin Aysha domin Aysha ta dawo kusa da ita.

   

    Be musa masu ba ya basu guri suka dawo kusa da juna.

    Hanya aka sake dauka tsayon lokaci suna keta hanya yayin da Aysha ta gaji da zama sosai.

    

  Tun tana ganin abun kamar wasa har taga dare ya raba, sosai hankalinta ya Kara tashi, tun gurin 9:00am tafito, cikin firgice ta kalli Mama tare da fadin Mama ahanya zamu kwana ne?

  Eh Mana Aysha Idan Allah ya taimake mu gobe da rana zamu Isa idan Kuma mun samu tsaiko har jibi muna iya kawai.

   Wayyo Allah na mama kafata duk ta sake.

   Daure diyata. Insha Allahu gobe war haka kina gidan mahaifinki kina hutawa.

    Daren nan Ayaha bata iya runtsawa ba yadda taga rana haka taga dare, washegari

  Misalin 3:30pm Aysha ta sauka a garin Kano, sosai gabanta ya shiga faduwa yayin da wani shashin nazuciyarta ke mata fada anya kuwa hakan ya dace, sosai jikinta yai sanyi hankalin ta ya tashi har mama take tattare kayanta ta kula da hakan kallonta tayi tace, " Aysha ya dai?" 

   Bakomai mama.

  Jimm tayi sannan mama tace motar Ina Zaki hau?

   Akwatinta ta nufa ta bude sannan ta ciro wata farar takarda tace sunan unguwa yana rubuce anan.

   Wani irin kallo Mama taiwa Aysha sannan tace amman dai iyayen ki suna da ganganci. mika Hannu tayi ta amsa takardan ta bude. dagowa tayi ta sake kallon Ayaha cikin yamutsa fuska tace, Inazuwa, driver daya sauke su ta nufa ta nuna masa takardan, sakkowa yayi ya yana rike da takardan yace ta dauko kayanta ga mota can asata.

   Daukan Akwatin Aysha tayi yayin da mama tabita abaya har suka Isa cikin motar, shiga Aysha tayi ta zauna yayin da driver yake ke gaya masa sunan unguwar wannan lokacin bata sanin me mutumin yace dan bata san wani yare bane.

    Takardan ta karba sannan Mama ta juya taiwa Aysha sallama tare da Kara gargadinta cewa takula da kanta.

      Kwallah Aysha ta share domin Jin mama take tamkar mahaifiyarta sabo da yadda ta nuna kulawanta agareta, hawaye ne ya shiga ziraro mata yayin da can kasan zuciyarta takejin kamar batawa iyayenta adalci ba, saidai data tuna yadda take balakin son ganin Aliyu saitaji zuciyarta na dada dakewa.

   Nan ma tafiya akayi da ita sosai sannan mutumin ya juyo yace, "har yanzun ba'a kawo ba?"

    Kai Aysha ta daga masa domin ta fahimci tambaya yayi amman bata iya sanin me yace mata.

       Tafiya yayi me nisa sannan ya tsaya ya bude motar yana fadin sakko Hajiya, nan gurin shine karshe.

  Cikin rashin fahimta ta yamutsa fuska cikin kokarin sakkowa tana me kallon garin tare dayin kwal kwal da idonta, hawaye ke shirin zubo mata.

    Motar ya mayar ya rufe sannan ya zagaya ya shiga motar yana fadin, da Alama yariyar nan batajin Hausa.

     Tausayi tabashi dan haka ya kirata da hannun sa yace Ina Zaki ne?

      Cikin fullacin tai mgnr dan haka ya yamutsa fuska tare da fadin toh fah, sakkowa yayi ya nufi wasu maza dake zaune ya basu hannun suka gaisa sannan yace yariya ce na dauko tundazon da alama batasan garin ba Kuma batajin Hausa ko akwai bafulatani anan?

   Bafulatana ce?

   Amsa masu yayi da eh sannan ya daga Hannu ya Kira Aysha.

   Tahowa tayi ta tsaya gabansu, daya daga cikin sune yace ke ya sunan ki???

     Fulacin dai ta sake masu cikin takaici dayan yace ke bamejin fullanci anan gurin sunan ki akace, Yaya sunan ki??

       Wannan karon tafara tsorata dasu domin ta fahimci cikin fada sukayi mgn.

     Daya daga cikin sune yace, duk yadda akayi irin yaran nan ne masu guduwa daga gidan iyayen su, ke bakijin wani yaren ne sai fulatanci kadai?

   Kaita daga dumin iya fahimtarta tambaya sukayi, fada mutanan sukaci gaba dayi yayin da Aysha ta tsaya idonta jawur.

    Dayan ne ya kula da takardan dake hannunta batare data ankara ba ya amsa takardan ya bude.

      Dagowa yayi ya kalli sauran tare da fadin, Ina tunanin wannan shine adireshin inda zata ke yariya wannan shine adireshin inda Zaki??

  Kaita daga yayin da daya daga cikin mutanen yace ita kome zakace mata ai amsa maka zatayi ai daman fulani ba hankali suka cika ba🤪 inba hakama kya taso bakisan gariba Kuma baki da hausa.

     Daya daga cikin su ne dai ya sake cewa yanxun abun da za'ayi ka taimaka ka kaita Dan kunma baro unguwar abaya, Kuma indai da gaske wannan shine adireshin to takwana gidan sauki, taimakawa zakayi ka kaita har gidan tunda akwai no gidan ajiki.

   Eh to bance bazani ba, amman ni gaskiya sana'a nafito, idan tana da kudin da zata biyani har da bata lokacina toh zan kaita.

    Toh babu laifi, kallon Aysha sukayi kina da kudi??

   Raba ido kawai Aysha keyi dan haka suka shiga mata kurma kurma suna nunawa da hannun su.

  Hannun tasa cikin akwatin ta dauko cajin da aka bata.

  Gaskiya baxani awannan kudin ba.

   Nan dai suka lallabe shi akan idan sunje acika masa kudin sa agidan, haka akayi Aysha ta shiga motar sannan suka dauki hanya.


              *******

  Sai yau ka tuna Dani agarin nan Aliyu?, Shekaran ka nawa yanzun, tunda naje akace min kana nan neke zarya gidan ku, Amman kullum nazo ace kana makarantanta, haba Aliyu?

    Aini ban masan kinsan ina nan ba, Kuma ita Ummin da ta gaya miki ba itace ta koroni ba?

   Ai Kai kajawo komai, idan bata koreka Yaya zatai dakai.

   Eh shine Nima ai nakoma gefe.

        Gara taka koma gefen, yanxun ma dakasani ai bakazo ba, wato sai abarka kayi abun da kaga dama.

       Daure fuska Aliyu yayi sosai yana zaune falon Hajiya Rukayya cikin kakin sojojin sa fuskar nan tasa kirtim, lumshe ido yayi sannan yace, Ina Yaya Fahat?

      Yana wankacan dakin ta numa masa da hannunta.

    Kallon dakin yayi sannan yasake cewa ya jikin sa fah?

   Jiki Alhamdulillah.

  Amman akwai wani cigaba??

   Toh Alhamdulillah yana nan dai a yadda yake.

   Har cikin ransa yaji ba dadi mikewa yayi yana kokarin nufar dakin Aunty Ruqayya tace, " yaushe zaka je gida?"

      Yanzun Yaya Fahat kawai zan gani na wuce"

   Can gida nake nufi gurin Ummi"

   Dan waigowa yayi ya kalleta sannan yace Aunty itafa ta koreni, ni bazani ba sai in ita ta nemeni, haka tace min ita burin ta in zauna gidan ubana.

  Mikewa Anuty tayi tabi bayansa cikin dariya take fadin, dan auta sunyi fada da Ummi, bafa ason ranta bane.

    Nima ai ba ason raina bane, da haka suka Isa dakin fahat, cikin wani irin farin ciki fahat din yake kallon Aliyu domin rabon su da juna sun dade sosai.

    Zama yayi gefen sa yana me kura masa ido ko kiftawa babu, idon Aliyu cike da kwallah ya kama hannun sa yana fadin, Yaya Fahat nine Aliyu, Yaya kake?, Ya jikin ka?

    Bude baki yake cikin kokarin amsawa da irin mgnr sa wadda ba'a ganewa sosai.

     Hawaye ne ya zubowa Aliyu cikin sauri ya kawar da kansa ya share sannan yasa hannun sa cikin aljihu ya ciro kudi yasa a hannun fahat yana fadin, gashi inji Ummi tace na kawo maka.

  Amsa yayi da murna akan fuskarsa, mikewa Aliyu yayi yana fadin barin je ai muna tare zan dawo kaji.

   Amsawa yayi,yayin da Aliyu da aunty Rukayya suka fito har motar sa, BAyan ya shiga ya zauna ta kalleshi tace, " Auta an girma, to yaushe zakayi aure?, gaka yadda kai katoto kuwa, dan Allah kaje Ummi ta ganka.

   Hmmmm, aunty yaushe rabon ki da can?

     Sakera biyu, amman nakusa komawa.

       Tada motar yayi tare da fadin, idan kinje ki gaishe ta, amman Banda innawo.

   Cikin dariya tace ita Kuma Innawo meta maka?

    Itace nan ta zuga Ummi, tada motar yayi batare yajira me aunty zatace ba.

             ******

    Ana Kiran sallan magarib suka iso kofar gidan kallon Ayaha yayi ya mika mata takardan tare da numa mata cewa wannan bayanin nata ya nuna wannan ne gidan dan haka ki shiga ki amso min cikon kudina.

    Ganin kamar bata gane ba yai mata kamar mgnr kurame har saida yaga ta daga Kai sannan ya zauna saman motar tare da fadin ina nan.

 

   Itako Aysha gidan ta nufa duk da cewa girman gidan yabata mamaki cikin dar dar ta shiga bugawa.......



  PEN WRITERS ASSOCIATION✍️

  Comment BA'KAR FURA *Sumayya Magaji*

*Tabdijam gsky yakamata iyaye sudauki darasi anan koba komai wani lokacin iyaye sukan dinga tsanantama yaransu akan abinda baikai yakawoba su aganinsu tarbiyace suke koya musu kuma yaro yanada wani Abu dik abinda yaga ana tsananta mishi akai koda abin baije yadawoba tofa shiyake qoqarin aikatawa aikatawa, Wanda aganina dik abinda zaman lpy baikawo ba to tabbas tashin hankali bazai taba kawoshiba, tin farko inda iyayinsu sunbi abin ahankali dayanxu hkn batafaru ba, yanxu wagari yawaya idan har iyayin Aisha suka sami lbrn tagudo har Nigeria wajan Aliyu?*🤦🏿‍♀️

*Sann ko Yara wani lokacin danasu laifin iyaye fa sunfi qarfin wasa duniya daka rasa iyaye baxaka taba samun wasuba kuma dik abinda mukaga iyayen mu sukeyi mana bawai Dan basu sonmu bane Aa kwe dae sunayi ne dansuga sunkare martabar mu d mutuncin mu sann kuma susauke nauyin da ubangiji yadora musu.*

Kowa ya aikata daidai ba shakka zaiga daidai ammh dae wann yaxama ixina awurin iyaye kai harma damu yaransu💁🏼‍♀️

*Tin ba'aje ko inaba wann lbrn yafara bayyana irin darasin da yake dauki dashi,*

*Ubangiji Allah kabamu ikon yiwa iyayin mu biyayya adukkan wani abu dasuka doramu akai muddin baisaba maka👏🏻

*Ya Allah kasa mugama d iyayin mu lpy👏🏻*

*Wadan da iyayinsu suka rigamu gidan gsky Allah yagafarta musu yayi musu rahama Amin ya rabbi*👏🏻

*Sis @⁨Fadeela Lamido⁩ muna gdy sosai Allah yaqara basira da daukaka yasa kifi hk yashirya miki zuri'arki👏🏻🥰*

   

              episode 27- 29


Kwankwasawa take ahankali cikin sanyin jiki, daga can taji an fara bude gidan.

    Me gadine ya leko ya kalli Aysha tare da fadin Yaya dai?

   Cikin fullacin tayi mgn wadda baya fahimtan koma sai Aliyu da take Kira.

  Cikin tsananin mamaki yace Aliyu?, Iya sanin sa dai Aliyu ko mgn ba cika yinta yayi ba, tsareta da ido yayi, neman sa kike Aliyun?, tunawa da yayi fulacin takeji yasashi yace, Aliyu baya nan.

   Wannan mutumin daya kawo Aysha ne ya matso yana faddin, waishin baka fahimci sunan wadda take Kira bane? Ko banan gidan yake ba?

    Eh toh anan madai Akwai Aliyu amman Ina tunanin ba wadda take nema bane.

        A'a Sam nan ne, gashinan Zane hannun ta, wannan yariyar bakuwa ce ba yar garibace tun da sauran rana nake yawo da ita acikin motar nan, yanzun dai bude mata ta shiga ta amso min kudina.

       Gurin wa?

   Aliyu take Kira Kuma Aliyu baya nan.


   Toh ai saika bude mata kofar ta shiga ta jirashi ko, nadade Ina yawo da yariyar nan ba inda zani da ita kuma.

     Tsaki Me gadin yayi sannan ya juya rufe gidan.

    Cikin wani irin yanayi Aysha ta juyo ta tsuguna akasa saboda yadda kafarta tagaji, ga tarin yunwa a tattare da ita.

     Ganin garin yayi duhu ta fara hawaye gaba daya cikinta ciwo yake mata ga wani masifar fiya yunwa da yake ji.

       Mutumin ko na nan zaune sai masifa yake yayin da Aysha ta tsuguna a gefe tana share hawaye.

      Wata katuwar mota ce ta shigo layin, yayin da duk hankalin su ya karkata kanta ahankali harta karaso gurin su, nan suka fahimci gidan zata shiga dan haka suka kauce.

    Gate din gidan aka bude yayin da motar tasa hancin ta cikin gidan.

    Fitowa Aliyu yayi daga cikin motar da saurin sa domin gani yake kamar Aysha ce awaje, idan kuwa ba Aysha bace lallai suna tsananin kama.

    Yana daf da shiga gidan me gadin ke fadin, " ranka ya dade, akwai wata bafulatana tazo batajin Hausa amman tana Kiran sunan ka.

   Aliyu bebi takansa ba yayi waje cikin tsananin mamaki yake binta da kallo yayin da itama tai saurin mikewa ta da tsareshi da ido.

     Aysha?, Aysha kece anan ba gixo idona yake min ba???

   Kwalkwal tayi da ido har yanzun tana kallon sa, gani take kamar bashi ba, sosai ya canza mata yayi wani irin kato ya tara kasumba ga Kuma kayan sojojin ajikin sa.

    Kara matsawa yayi daf da ita tare da dafa kafadonta yana fadin, kimin mgn Mana inji muryan ki kece haka??

     Fadawa tayi jikinshi cikin fashewa da kuka, yayin dayai saurin rungumeta tsayon lokaci sannan ya fara dan dukan bayanta tare da cewa ya Isa ya Isa cikin harcen fullacin.

    Mutumin dake zaune ne saman motar yace taxo gari ita ba hausa ba tun dazon nake bulaye da ita agarin nan, tasan batajin ko wanni yare mezaisa tazo n........

  Cikin sauri Aliyu ya dago Aysha daga jikinsa sannan ya juya ya kalli mutumin yana fadin, " Kai me kake jira??

      Cikin furgici da tsawan da ya masa yace a'a ni cikon kudina za'a bani.

    Hannun yasa a aljhu ya ciro kudin dabesan ko nawa bane ya mika masa.

    Cikin sauri mutumin yabar unguwar yayin da Aliyu ya tattara hankalin shi gaba daya gun Aysha yana fadin kedawa Aysha?, yaya akayi har kikazo nan?

     Wasa da hannunta take cikin sunkuyar da kanta tsayon lokaci.

  Kallonta yayi sannan yai murmushi tare da cewa, " har yanzun dai ana nan ba'abar wasa da hannun ba?, Juyawa yayi ya kalli akwatin ta sannan ya sake cewa inajin ki kedawa kikaxo nan??

 

    Batare data dago ta kalleshi ba tace ni kadai.

   Cikin sauri ya zaro ido, ke kadai????

     Har yanzun idonta akasa tace eh.

   Shiru yayi tsayon lokaci yana kallonta, tsarguwa tayi da kalon dan haka ta Kara saukar da idonta kasa kafin taji yana fadin.

     Aysha ashe baki da hankali?, ina nan ina yabon halayen ki, yanzun ke kadai kika kamo hanya toh agida ansan kin taho?

   Kanta ta girgi alanar a'a

    Ina kikace masu Zaki?

    Muryanta can kasa tace gidan babana.

     Shiru ya sakeyi tsayon lokaci sannan ya sake cewa, amman dai baki da hankali Ayaha

  ta Yaya zaki baro gida babu izinin kowa kina da hankali kenan?, kina tunanin idan suka lura baki can wani irin tashn hankali zasu shiga?

   Wasa take da hannunta yayin da hawaye ya fara sauka akan kumatun ta.

    Cikin tsareta da ido ya sake cewa Aysha kina son mukara shiga cikin wata matsala ko?

    Girgiza kanta tayi da sauri yayin data share hawaye tare da saurin tsugunawa ta dauki akwatin ta ta juya afusace ta fara tafiya.

 

    Kallo yabita dashi zuwa can yace Ina Zaki???

    Tafiya kawai take dan haka ya sake cewa zonan.

   Ganin tacigaba da tafiya ya sashi daga murya tare da fadin, " Aysha kinaji nace ki dawo ko?

     Ganin har yanzun tafiya take yasashi yabi bayanta, abuka da namiji nan danan yacin mata, akwatin ya karba sannan yace juya muje, Ina miki mgn kina tafiya,, yanzun bada bane saina miki duka, wuce muje.

      Juya tayi kamar yadda yace, yana gaba da akwatin ta ahannun sa yayin da take binsa abaya tana share hawaye.

        Har cikin gidan suka shiga yayin daya doshi wani babban kofa da akwatinta ahannun, duk da cewa ma'aikata nata miko hannu yana girgiza kai.

  Cikin wani katun falo suka bayyana yayin da taji ya ya bude murya yana Kiran Meenat.

             ******

Dirowa Meenat tayi daga gado, tana zare ido tare da kallon Islam tana fadin nashiga Uku, kamar Yaya Haydar ne ke kira na, ko Baffah ne??

   A'a kamar dai Yaya Haydar din ne.

     Cikin zaro ido Meenat tace bantabajin ya Kira sunana ba, kefa Islam yana Kiran sunan ki??

    Kafin tabada amsa suka sakejin wani Kiran wannan karon duk su biyun ya Kira Meenat Islam"

   Kusan atare suka amsa tare da saurin fitowa.

     Akwatin ya mikawa Islam dake gaba sannan ya kauce Aysha ta bayyana yana fadin, ga bakuwa, kuje da ita dakin ku tai wanka taci abinci.

    Amsawa sukayi, yayin da ya kalli Aysha yace ki bisu, kiyi wanka kici abinci.

    Wucewa tayi kawai kamar yadda yace binta yayi da kallo har yanzun fushi take dan haka yadanyi murmushi sannan yace nayi farin ciki da zuwan ki, cikin harcen fullacin.

   Juyowa tayi tadan mai wani irin kallo wadda yasa shi ya sake sakin murmushi.

        *********

Misalin 09:30pm Islam ta shigo tace muje Yaya na Kiran ki.

      Wanni irin kallo taiwa islam cikin rashin fahimta.

 

   Suna ko mgn taita mata ganin dai taki ganewa ta fito zuwa falon Haydar tana fadin, Yaya inata mgn bata kulani.

    Lumshe ido yayi tare da fadin bata jinki ne ki kamo hannunta kawai.

  Ai har kamo hannun nata nayi taki.

   Kawar da kansa yayi yai murmushi sannan ya juya yace, " kin iya french"

   Meenat dai tanayi kadan kadan.

   Kice mata tai mata french zata amsa ta.

  Juyawa Islam tayi zuwa can saika Meenat da Ayaha, Aysha na shigowa Meenat ta fice, kallo yaitabin Aysha dashi tsayon lakaci.

    Itako zama tayi ta juyo masa baya tsayon lakaci yana kallon bayanta, zuwa can ya mike ya dawo kusa da ita yana fadin"

  Har yanzun kina fushi?, Aysha dan namiki fada kike fushi, har yanzun kina nan da halin ki ko?

   Hawaye ta fara sharewa can kasa da murya tace bakayi murna da ganina ba.

    Inji waye ya gaye ya gaya miki?, Nayi farin ciki da ganin ki fiye da yadda kikai farin ciki da ganina Aysha, nafi son ace nine nabiki ba kece kika biyoni ba, sabo da darajarki ta 'ya mace, ni namiji ne dan nabiki ba wani abu bane, yanzun me kike tunani idan Kakarki ta fahimci haka??

     Shiru Aysha tayi kwalla tap idonta.

    Cigaba yayi da cewa nayi farin ciki da ganin ki, kin girma Aysha, amman farincin bashi zai hana nagaya miki gaskiya ba, Ina son kisani cewa meson ka shine yake gaya maka gaskiya, kin rigani kamo hanya ne kawai amman har yanzun kina zuciyata, yanzun mubar wannan mgnr Ina Ummi na?, Kina ganin ta?

   Batare data kalleshi ba tace muna haduwa a hanya.

   Innawo fah?

  Itama haka.

  Har yanzun baki shiga gidan??

   Kaita daga.

  Baki Zaki bude inji muryan ki.

   Ahankali tace ban sake shiga ba.

  Wani irin kallo yake mata na kasan ido, cikn ransa yake yaba hallitan ta, Allah yayi mata sura me kyau, da daukan hankali, tayi wankan ta, ta canja kaya, sai dai suma irin dinkin dazon din ne duk sun kamata, dan karamin gyalene kawai tasa akanta ko dan kwali babu sai bakin sumsrta yake hangowa yana kyalli

       Kallonta da yayi na tsayon lokaci sosai ya saukar mishi da kasala irin wadda be tabajin taba, cikin ransa ya raya inama ace matarsa ce ta aure suke zaune tare adaidai wannan lokacin, idon sa ya sake kaiwa kan kirjinta ganin su cike tam yasashi saurin lasan leben sa batare daya shirya ba, cikin ransa yake Kara tabbatarwa lallai Aysha itace matar daya dace ya aura, duk da cewa abaya ba soyayya sukayi ba, amman yanzun ya tabbatarwa kansa cewa yana son Aysha, haka itama ya tabbatar soyayya ce ta kawota wadda ada suke gani kamar kauna ce.

    Acikin ransa yaci gaba da cewa, yanzun haka take yawo a Cameroon, nonuna luntsum lumtsum, kawar da kansa yayi zuwa can ya juyo idon sa cike da kishi yace"

     Samarin ki nawa?

   Juyowa tayi ta kalleshi, can kasa tace, "da yawa"

  

   Da yawa ko?, har kina saurin fada?, ai daman nasan zasuyi yawa, tunda kina yawo ahaka, kin gim katuwa dake kina yawo Kai ba dan kwali Koda dama can haka kike, baki damu da suturta jikin ki ba, anan bazan yadda da wannan ba.

     Cikin sauri ta sake juyo mishi baya akaro na biyu.

  Mikewa yayi ya dawo gabanta tare da mika hannun sa ya roko nata, yatsunta ya rike yana murzawa, karon farko arayuwar sa daya hakan taro dan haka yai saurin lumshe ido tare da sauke ajiyan zuciya.

   Ahankali yake murza hannun ta wadda zoben sa yake Kai, cikin matsanancin farin ciki yace, " Aysha kin hadu, kin nuna min kauna, bazan taba mantawa dake ba arayuta, kina da kirki Ayaha kina da nutsuwa ga kamon Kai, gakuma tarin ilimi, tunda muka rabo nake tunanin ki, ban iya mgn da kowacce mace ba saike Aysha, nayi zamana ne kawai saboda Ummi ta nuna zamana anan shine farin cikin ta, nasan Ummi tana son in rabo dake kamar yadda yan gidan ku keson ki rabo Dani, Kuma haryau bandenajin abun da nakeji akanki ba kullum karuwama yakeyi, dan haka naki dawowa kawai.

   Hawaye Aysha ta share da hannunta daya cikin kasa da murya tace nima wlh Yaya ban daina ba, Umma nata fada bana kula kuwa nikadai nasan abun da nakeji.

  Hada kansa yayi dana Aysha yace nina fahimta Aysha, yanzun muyi tunani kina ganin zamuyi aure?, iyayen mu zasu bari kuwa?

    Kawar da kanta tayi ta share hawaye tana fadin bansani ba Yaya Aliyu😭😭

      Lumshe idon sa yayi sannan ya bude tare da share mata hawayen yana fadin, kidaina kuka, insha Allahu zamuyi aure, Allah ne ya daura mana kaunar juna batare da yayi shawara damu ba. Da yardan sa zamuyi aure insha Allahu dan ni Ina tunanin indai ban sameki ba bazanyi aure ba, kefa Aysha zakiyi aure ki barni??

    Kukane ya kwacewa Aysha dan haka tai saurin fadawa jikin sa, saurin rungumeta yayi tsam ajikin sa tayon lokaci sannan ya shiga lallashinta daker ya iya yakeceta ajikinsa domin ji yake kamar su dauwama ahaka.

    Kije ki kwanta Aysha dare yayi. hannunta ya riko ya kaita har bakin dakin su Meenat saida yaga shiganta sannan ya juya zuwa dakin sa.

   Gado ya fada, yayin da yakejin tamkar Aysha ta fama masa ciwon dake karkashin zuciyar sa, wani irin masifar sonta yakeji yana bin duk wani sassan jikin sa, wadda yakejin tamkar idan aka hanasa aurenta zai iya mutuwa, gawani irin masifar tausayin Ayshan daya saukar masa, ganin irin yadda ta sadaukar da rayuwarta takamo hanya, jikawai take ayanzun bashi da wani babban buri daya wuce yaga ya mallaketa, tsintan kansa yayi da zubar da hawaye dan yasan akwai babban aiki agaban sa, bayaga haka yau daya da ya hada jikinsa dana Ayaha duk yana jinsa abirkice dan haka ya kwanta kawai yai rufda ciki yana cire kwallar dake taruwa gefen idon sa.

      

          ****



  Washegari da Safe, Aliyu ne zaune gaban Baffah yayin da Momy take gefen Baffah.

     Cikin daure fuska Baffa ke fadin.

   Kasan dai Ina da mutuncina ko?, Mutane suna ganina da daraja, nayi nayi dakai kayi aure kaki, Ina lallabaka dan banson in takura maka, ko na hanaka aure ne??

   Leben na kasa ya lasa sannan yace a'a.

   Toh akan me zaka dinga lebo yaran mutane kana kawo min cikin gida?

   Momy Aliyu ya kalla sannan yace wacce yariya na kawo?

    Baffah ne yace ni zaka kalla ka tambaya yariya da kazo da ita jiya, ina ka samota ko hausa bataji......








*🕳️BA'KAR FURA🕳️*

  _A true life story_

*Na*

_Fadeela Lamido_


  PEN WRITERS ASSOCIATION✍️

          episode 30- 31

  Dagowa yayi cike da kwarin guiwa yace Baffah matar aure ce ita, wannan yariyar tana da aurenta, matar abokinace daga Cameroon suke, ita da Mijinta, tafiya ce takamashi zuwa garin dabesan Ina zai sauka ba, gshi anan din ma batasan kowa ba, asalima bata hausa, shine ya nemi da in kawota gidan mu ta zauna nawani lokaci kafin ya dawo, cikin baccin rai ya sake cewa inda nemanta nake ai bazan kawota gidanmu ba, Kuma cikin kannaina Baffah, nadauka cewar Ina da damar da zankawo wadda naso.

  Ajiyan zuciya Baffah yayi, cike da gamsuwa yace, " nafahimta Haydar, kana da damar shigo da duk wadda kaso kuwa domin gidan mahaifin kane, saidai inaga ba laifi bane dan naga kamar zaka karkace natuhume ka, Kuma bayani yana da dadi, dole ne hankalina ya tashi ace yau na samu labarin ka sauki mace bana miji ba, batare da wani bayani ba, ya dace ace da abokin ka ya kawo matarsa ka kawoshi mugaisa, sannan ka sanar Mana cewa zaibar matarsa anan, kamar yadda kai bayani yanzun, dan haka nan gaba ka gyara wannan kuskure ne.

    Kansa akasa ya amsa da toh yayin da Baffah yace wane sunan yariyar??

   Muryan Aliyu adakushe yace, " Sunanta Humaira"

    Allah sarki, toh Allah ya dawo da mijin nata lafiya.

    Dakai ya amsa sannan ya mike yayi sallama ya wuce Office.

           Ajiyan zuciya yaketa saukewa ajijjere, wani na korar wani, yayin da yake bakin cikin turkeshin da Baffah yayi tabbas yasan Momy ce ta zogoshi dan haka yaji abun nakara bata masa rai, kenan dan iska suka maidani, irin wannan tunanin yaita yi yayin da yakejin ransa na dada baci.

    

            *******


   Aisha zaune kusa da Islam, waige kawai Aysha take yau bataga Aliyu ba, hankalinta ne ya fara tashi sai raba ido take, tun safe take sarai da ganin sa, gashi yanzun har sha daya, cikin ranta ta fara tunanin gida Mama Umma acen bangaren Kuma ga Daddy ta duk tabarosu ta tahonan da kudin data dade tana tarawa gashi yanzun har yanzun bataga Aliyu ba, wata zuciyar ce tace mata yanzun idan be dawo ba fah Yaya zakiyi, ki koma gida?, hawaye taji ya zubo mata sharrr, Hannu tasa ta share sannan tace duk acikin ranta, idan kin samu kudin motar Ina zakibi kihau motar? kinsan hanyar tashan ? Me zakicewa masu mutar?, yin wannan tunanin hawaye ya fara ziraro mata babu kaukautawa, Meenat ce ta kula tabajin kukanta kasa kasa waigawa tayi ta kalleta cikin mamaki tace da Islam kuka take🤔

   Juyowa Islam tayi ta kalleta tare da tafata tana fadin kiyi hakuri baiwar Allah.

  Meenat kuwa fadi take menene?

   Islam ce tace ai kinsan baji take ba French Zaki mata.

      Akace miki wani iyawa nayi?, ni bansan yadda zan lallasheta ba.


    Islam ce ta saki bayan ta koma bakin gado ta zauna tana fadin, mudai mun shiga uku, ya hadamu da aiki ya wuce aiki abun sa, ni wlh abun nan haushi yake bani, ace kaita mgn da mutum besan me kake cewa ba.

     Ayaha ko shashekar kuka take taree da Kiran sunan Aliyu, sunan kawai suke iya fahimta.

  Meenat ce tace niman ya Haydar fa take bakijin tana cewa Aliyu ba, Islam kice mata yaje aiki anjima zai dawo.

    Cike da fada Islam tace ke meya hana kice mata, gaki kusa da ita.

    Ai bajina take ba, Meenat ta bata amsa.

   Mikewa Islam tayi tana fadin, toh ni Jim nawa take ne?, Kofa ta nufa tana fadin wlh ni dakin Momy zanje inyi bacci na.

       Dan Allah karki tafi kibarni da ita, bansan ya zanyi ba, ficewa Islam tayi, yayin da Meenat ta kalli Aysha sannan itama ta fice adakin.

     Gun Momy suka Isa kallon su haka yasa tace Yaya dai?

  Momy kuka fa take, tana fulani ni bangane me take cewa in Banda Kiran ya Haydar.

      Aiki ya sameku, saiku koma ku lallasheta Kar abokin Mijinta ya dawo yaci ubanku, dan nikam karma kununa nasani, gara daku Niko idan ya wullo min wannan idon nasa, ba dai mgn zaiyi ba amman akwai kallon raini.

    Batare da sun fahimci inda tasa gaba Islam tace, " Wlh Momy bazamu iya ba, nidai gaskiya nagaji.

   Cikin sigan lallashi Momy tace kunga kuje ku zauna adakin, ko bakuce mata komai ba yafi dai ace an barta ita kadai.

   Da haka ta lalabesu suka koma.


    Misalin karfe 4:30 Aliyu ya dawo gida, masifar kosawa yayi ya dawo sabo da Aysha kawai, yana tunanin ko Yaya ta kwana, kawai ya iya daurewa ya barta ne dan Kar a fahimci akwai wani abu a tsakanin su.

       Kai tsaye dakin sa ya wuce bayan yama Momy dake falo sannu, cikin sauri sauri ya shiga wanka, fitowa yayi yana tsane ruwan dake kansa, sannan ya shiga shiryawa, kananan kaya yasa tare da fesa turare, kokarin fita yake yaga Aysha idonta a kunbure.

    Murmushi yayi idonsa cikin nata, yana me tsareta da ido sosai yace ya dai naga kamar kinci kuka kin koshi"

     Kawar dakai tayi cikin sunkuyar da kanta kasa.

   Meya faru ne?, nidai nasan Aysha jaruma ce an zanaki ma idon ki be kun bura haka ba, gaya min waye ya bata miki rai.

     Lumshe ido tayi hawaye suka zobo ahankali tace tunani nayi.

    Motsowa yayi daf da ita yana fadin, " tunanin me?

   Ka barni anan bani da kudin komawa gida, Kuma gashi bansan haryar da zanbi in samu hanyar gida ba.

    Dariya sosai Aliyu yayi yana kallon cikin idon ta, hannun sa ya mika ya dafa kafadanta ahankali yake turata da baya har suka Isa kujera ya zaunar da ita sanan ya zauna agaban ta, kinaji Aysha?, ki kwantar da hankalin ki, ni bazan gudu in barki ba, kuma Zaki koma gida cikin kwanciyar hankali inaha Allahu bazaki wahala ba, Ina son muyi hira sosai, sai dai kin San me??

   A'a

  Baffah na dazon yayi min mgn akan ki, kacenwar basu sanki ba bakuma Susan komai daga gareki ba.

    Kallo ta tsare Aliyu dashi tsayon lokaci  sosai ya fahimci tashin hankali a tattare da Aisha.

   Bude baki tayi cikin shirin yin kuka yayin da Aliyu yai saurin daga mata Hannu tare da fadin, " a'a karki tada hankalin ki, nagaya masu ke matar abokina ce, tafiyar gaggawa ta kamashi ya bukacin ki zauna anan, dan haka daga yanzun ke matar abokina ce.

    Sunkuyar dakai Aisha tayi har yanzun fuskarta babu sukuni, ido Aliyu yabita dashi sosai ya gama fahimtar ta sannan ya cire hannun sa daga kafadanta ya ruko habarta yana fadin, " karki damu kinji ko, wannan ba wani abu bane, bason su fahimci komai game dake, har na kaiki gida sannan na neme auren ki.

      Kwallah ta share, har yanzun zuciyarta babu nutsuwa gata ga Aliyu amman kwanciyar hankali babu.

   Tunanin me kike Aysha?

    Hawaye ta sake sharewa akaro na biyu tare da fadin, ya Aliyu na damu sosai, inajin wani iri acan hankalina ba akwance ba anan ma hankalina be kwanta ba.

   Toh meyasa?, Bana son ki koma gida kinajin haka, inason kiji dadi sosai, Ina son ki kasance cikin farin ciki domin hakan ne zaisa ki koma da walwala, Nima in tunaki inyi murmushi, Amman idan kika koma gida kina cikin wannan halin zuciyata zata kasa nutsuwa, yanzun kinsan me nake so dake?

   Kaita girgiza yayin da Aliyu ya mika hannun sa yana kokarin share hawaye yake fadin, " ke mata aure ce Aysha karki yadda wani ya gane cewa baki da aure, nace haka ne badan Ina tsoroba sai gudun Kar abun da ya faru abaya ya sake faruwa, Ina son na maidake gida sanan in Kuma daukoki alokacin da kowa ya shaida nine mamallakin ki.

     Sosai taji zuciyarta tai sanyin har ta sauke ajiyan zuciya.

  Murmushi yayi tare da fadin ko kefa.

  Itama murmushi tayi kadan tare da turi hannun sa daya rike habarta dashi, cikin sauri ya dauke hannun nasa yana fadin, " yi hakuri, na mance kin girma dauka nake dace.

     Wani irin kallo ta masa wadda yasashi ya kumayin murmushi, amman naga kinyi sanyi da yawa bakiyin wannan darigar take dake Dani murmushi.

    Yaya toh ai Kaine baka bani dariyar.

      Shikenan, naji, ki shirya gobe idan na dawo aiki zan fita dake musha hira, kibani lbrn Cameroon.

    Amsawa tayi da toh.

 Juyawa yayi ya dauko ledan dake bayansa ya mika mata, tare da fadin, wannan Hijjab ne Ina son ki rika sasu.

    Godiya tayi sannan ta mike ta tai masa sallama.

            *****

  Ina zashi da ita Kuma?, amman sun matukar dacewa wlh, duk da cewa cikin nikaf take amman abun ya dace.

    Babu ruwana ki, ki daina mgnr sa, kinsan halin sa saikiga kamar ba kallon ki yake ba amman duk yadda bakin ki ya motsa yasan me kike nufi.

   Kara kintse hakora Islam tayi tana fadin, daka nace sun dace, gani nayi tayi kamar matar shi, gashi Kuma yace matar abokin sa ce, Kuma wlh ki waiga ahankali ki kalli wani kallon love da yake mata.

     Kallon so?, matar abokina sa ce fah?

    Nidai Naga ya Aliyu soja ne, Kuma bashi da aure bashi da mata, baya zama gari daya, abokai kala kala, 'yan mata kala kala, karuwai burjik, Kuma wlh daganin ya Haydar ba kanwan lasa bane nan dai gidan ne yake mana mazurai.

  Cikin sauri Meenat ta kalli Islam tace me kike nufi?

   Bance komai ba, nidai fatana Allah yasa kada ranar da abokin nasa zaidawo daukan matar sa ya tarar ya fita masa yawo da mata.

       Lumshe ido Meenat tayi, sannan tace toh Ameen.

          ******

Tunda suka shigo babban gate din sojoji kawai take iya gani maza da mata, wasu na tafiya wasu na zaune wasu ko sintiri suke yi, wannan ya tabbatar mata da cewa waje ne da aka tanada domin sojoji, ahankali ta fara hango gidajen da bishiyoyi suka masu kawanya, wani abun mamaki, duk inda Aliyu ya ratso Sara masa ake, duk da cewa yana cikin motar da aka rufe gilashin ta.

    Gidaje ne irin na sojoji, tafiya sukayi me nisa sannan ya tsaya, bude masa motar akayi ya fita sannan ya zagaya ya budewa Aisha, bayan ta fito rufewa yayi sannan ya shiga gaba tana binsa abaya.

       Awani yalwa tattacen falo suka bayyana wadda yai matukar burge Aysha.

     Ganin ya doshi wani daki ta zauna afalon, juyowa yayi ya kalleta sannan yace Ina zuwa.

    Zaman kusan minti 39 tayi sannan ya fito yana sanye cikin wadon sojoji da farar riga.

Kallo

     Kallon sa tayi sosai, sannan tayi murmushi.

   Ahankali ya iso kusa da ita, yana fadin, ko baki fada ba nasan kina kallo nane sabo da Kinga nakara kyau, fiye da lakacin da Ina Can Cameroon. 

   Bawani, kana nan yadda kake, tsufa kawai ka Kara.

   Tunkarota yayi gadan gadan yana fadin, kice Allah.

   Mikewa tayi da sauri tana toshe bakinta yayin da Aliyun yace, Me kike nufi??

    Dariya ce ta kamata, ganin inda ya hade ransa yana tunkaro ta"

  Ahankali take komawa da baya harta Isa kofar tana fadin babu komai.

    Kina nufin har yanzun Ina nan a baki na ban washe ba???

   Dariya ta sake sawa, ganin yana dada tunkarota ta bude kofar ta tai waje aguje.

  Wani irin dariya yayi har zuciyar sa tare da sauke ajiyan zuciya me karfi sannan ya fito cikin kokarin boye murmushim sa.

    Babu kowa afarfajiyar da bishiyoyi suka zagaye, daga can gefe ana iya hango sajoji nata zirga zirga sai dai babu ruwan wani da wani.

      

   Ahankali yake takawa zuwa inda take tare dajin dadin yanayin sosai cikin ransa.

    Runtse ido tayi tunda ta hango tahowan sa tare da dago hannunta cikin nuna alamar karya taba ta cikin dariya take kare jikinta da hannunta duk biyu.

    Tsaye yayi agabanta sannan yai saurin mamayanta ya cukuikuyi hijjabin ta cak yai sama da ita tare da fadin muje kimin bayani........              Pls kubi wannan link din ku dannan min subscribe tare da alamar kararrawa