BAKAR FURA

BAKAR FURA CHAPTER 7

by @3135605806678644

*🕳️BA'KAR FURA🕳️*

  _A true life story_

*Na*

_Fadeela Lamido_


  PEN WRITERS ASSOCIATION✍️


        ***

 

    Episode 37- 38


Tsayon lokaci Aliyu ya dauka yana abu daya, baji ba gani, cikin tsabar gigicewa da sambatu kala kala, gaba daya ya rasa inda zaisa kansa, bayan kusan minti 30 nutsuwa ta samesa bayan ya samu gamsuwa me tarin yawa.

     Ahankali yake janyewa daga cikin ta, gefenta ya kwanta yana fadin, " ya subuhanallah, astagafurullahi wa atubu ilaika, kashhh, nashiga uku, wayyo Ummi na.

    Kukan Ayaha yakeji yana tashi kasa kasa kara jawota yayi jikinsa sosai yana fadin"

   Yi hakuri Aysha, ki yafe min, na tabka babban kuskure, Aysha, Aysha kinaji na?

      Kuka kawai take yi kasa kasa, yayin da yakejin hawayen ta na jika girjin shi.

    Rasa inda zaisa kansa yayi, saboda tsabar takaici da tashin hankali, dan haka ya shiga rarrashin Aysha dake kwance akan kirjin sa, lamu tayi a jikin sa, saidai fah kukanta Kara yawa yake, ganin ba kulawasa take ba ya sakko gadon ya nufi toilet wanka yayi, yanayi yana zubar da hawaye, kafin ya gama wankan idon shi yayi jawur sannan ya hada ruwan Aysha ya fito, bece mata komai ba ya dauketa cak ya nufi toilet da ita, zuwa wannan lokacin tureshi tafarayi duk da cewa bata da karfi sam.

      Cikin ruwan daya Tara me dumi sosai yake kokarin sakata, yayin da tafara cewa banso nika barni.

    Cikin ido ya kalleta sannan yace, barin saki mana saina barkin.

   Ni banaso😭😭

   Kawar da kansa yayi sannan yace, toh barin fita na baki guri, amman kafin na fita inason naga kin zauna acikin ruwan.

     Cikin matsanancin kuka muyar bata fita sosai tace, bazan shigaba ubanane kai?

    A'a Sam Aysha, amman lallai sai naga kin shiga ruwan nan zan fita.

       Bazan shiga ba toh.

   Toh naji Allah ya baki hakuri, juyawa yayi kamar zai fita sai Kuma ya juyo da saurin sa ya dauketa cak ya dannata cikin ruwan.

     Wani irin ihu ta yanka, yayin da Aliyu yake danne da ita, zuwa can tai shiru yayin da yaga gumi na tsatsafo mata agoshi, idon shi cikin nata, sakinta yayi sannan ya fito yabar mata bayin.

      Aliyu ko Koda ya fito kasa shiryawa yayi saboda tsabar damuwa da tunanin daya shiga, sosai yaji tashin hankali mara missaltuwa, hakika ya aikata babban kuskure.

      Hawaye ne suka shiga zobo masa ahankali ya juya ya kalli zanin kadonsa dayai kaca kaca da jinin Aysha, nan take yaji kanshi na ciwo. Be ankara ba yaga Aysha na kokarin fitowa, Amman tunda ta leko ta ganshi daure da towel har yanxun saitai saurin komawa.

    Ganin haka Aliyu ya mike, Hajjabin ta ya dauka ya Isa bakin toilet din ya tura kofar kadan ya mika mata, sannan ya dawo ya dauki jallabiya yasa, tare da yaye zanin gadon yai nufi falo.

   Tsawon lokaci ya dauka afalon sannan ya dawo lokacin Aysha tana zaune akasa ta hada kanta da guiwa sai kuka ta ke cikin tsananin tashin hankali tare da danasani mara amfani.

     Ahankali ya Isa gefenta, Ayaha nace kiyi hakuri kinji.

   Cikin matsanancin kuka tace, " Nina shiga uku Yaya Aliyu, rayuwata babu dadi, yanzun idan baka aure ni bafah?😭😭.

  

  Yi shiru, ki shiyiru Aysha, nine mijin ki insha Allahu, kibar irin wannan tunanin, kiyi addu'a kawai Allah ya cika Mana burin mu.

     Bawani nan,nasan yanzun barina zakayi tunda bani da abun da kowacce mace ke takama dashi, nashiga uku na lalace.

     Kashhh, nagaya miki kibar wannan mgnr, ni ke kanki nake so bawani abu dake jikin kiba, aure nake son muyi ba lalata ba, wannan abun da daya faru ki daukeshi ama matsayin kaddaramu ce, nayi iya bakin kokarina kawai dan ganin nakauce ma hakan, Aysha meyasa kika dawo????

   Kuka kawai take ganin baxata amsa ba yace toh yanzun ki gi kwanta ki huta.

     Mikewa yayi ya dauko zanin Gado ya shinfida, sannan yace kizo ki kwanta bari nemo miki abun da zakici rana tayi.

    Kin kulasa tayi dan haka ya sake cewa ki kwanta nace,

     Cikin sauri ta juyo masa bayanta, kallonta yayi tsayon lokaci sannan ya kada kansa ya fita.

     Bayan taga fitansa Kara tsananta kukanta tayi, saida tayi me isarta, nan gurin bacci ya dauketa.

      Koda Aliyu ya dawo ya samu tana bacci ledojin hannun sa ya aje sannan ya koma falon ya zauna cikin damuwa sosai, hawaye ne ya fara zubo masa yana sharewa, azaune take baccin wata zuciyar kece masa ka gyara mata kwanciyar yayin da wata zuciyar ke hanasa yin hakan,

   Ayanzun tausayin Aysha yafi ji fiye da tunanin Umma, sosai yakejin tausayinta cikin ransa, yasan yariyace karama, wadannan tashin hankalin sun mata girma, har aka Kira sallah Azahar Aysha bata tashi ba, bayan ya dawo sau uku yana lekata, ganin har da yadawo sallah la'asar bata tashi ba ya shigo dakin yana Kiran Sunanta.

      Aysha, kitashi kiyi sallah.

     Kula yayi tana rawan sanyi, dan haka ya karasa ya taba wuyanta zafi yaji rau, take yaji gaban sa ya fadi.

    Tsaye yayi yana binta da kallo tsayon lakaci idonta abude suke da alama ma ba bacci take ba,  

    Juyawa yayi, cikin rasa abun yi, bayason ma a ganta akwance haka adakin sa, daya Kira likita ya duba ta, mutane na ganin sa da mutunci, baya son ashiga shargin sa dan haka ya yanke shawaran sawo magani kawai, daker yasata tadanci Naman daya sawo mata sannan Tasha maganin ta kwanta.

   Kafin dare ta danji dadin jikinta harta tai sallah

     Kula Aliyu yayi bata dawo da kayanta ba dan haka da daddare ya fita, kaya kala biyu ya sawo ma Aysha sannan ya dawo gida lokacin tayi bacci dan haka ya ajiye kayan sannan ya dauki filo ya koma falo.

    

          Kokaci bayan lokaci yana leka Ayaha sannan ya koma ya kwanta, saidai fa bacci ya gagaresa jiya beyi bacci ba yauma babu sannan tashin hankalin da yake tattare dashi yau yafi na jiya dan haka yaji duk wani iri yake ji.

      Aysha ko baccin ma da take bame dadi bane, cikin mawucin hali take baccin gashi duk jikinta ciwo yake mata, ji take kamar jijiyoyin jikinta ya rake.

          

  

                  ******

Washegari tunda Aliyu ya dawo masallaci yazo ya tashi Ayaha, yana fadin, kiyi wanka muje"

    Mikewa tayi ahankali tanufi toilet, Aliyu kusa juyawa yayi zuwa falon bayan ya ajiye mata kayan daya sawo mata agefen gadon.

    Koda ya koma falon kansa ya sake hadawa da guiwa, mafita kawai yake nema cikin sauki.

      Bayan kusan minti 30 Aysha ta shigo falon cikin sunkuyar da kanta.

      Zama tayi hannun kujera ta kalli can gefe, binta da kallo Aliyu yayi sannan yace, " Ina kwana.

   Kara dauke kanta tayi can gefe yayin da ya sake cewa Ina kwana Aysha?

   

      Wannan karon ma bata tankashi ba.

   Aysha nace Ina kwana, ya jiki?

    Cikin sauri tasa hannun ta tashere hawaye tare da zunboro baki.

   Mikewa yayi cikin sanyin jiki yana kokarin dawowa kusa da ita, ganin haka tai saurin mikewa.

   Lumshe ido yayi sannan ya kalleta yace, " shikenan, komawa yayi ya zauna sannan yace, jiya me ya dawo dake??

   Banza tamai, tare da cuno baki.

  Ina kayan ki?

   Murya can kasa tace, suna can.

    Inajinki meyasa kika dawo???

     Ganin bata da niyar mgn yace shikenan ki tashi muje.

 Mikewa tayi yana gaba tana binsa abaya 

   Cikin motar ma Aysha baya ta juyo ma Aliyu, Sam beson su rabo ahaka, dan haka ya kasa tada motar sai kallonta yake yi ahankali yace, " Aysha mufahimci juna dan Allah kafin ki tafi, kibar fushi nan beda wani amfani, bada gangan nayi ba kema kinsani, idan kika tafi kina fushi Dani kin zalince ni.

   Toni zalincin daka min fa??😭😭 Kara juyo masa baya tayi bayan ta fadi haka.

   Naji nazalinceki Aysha, amman banyi da niya ba, nata gudun kada hakanta faru, inaji azuciyata nafiki damuwa, kwata kwata bansoba Ayaha, amman ki kwantar da hankalin ki aana dawo zanzo.

     Hawaye take sharewa nidai ya Aliyu bansan inda zansa rayuwata ba, nashiga uku.

    Aysha ki nutsu Mana, ni bani da burin cutar ki, gaya jiya bayan nasaki amota meyasa kika dawo??

   Ni Yaya Aliyu kasa tafiya nayi, nafison mutafi tare, shiyasa na dawo ince maka kazo mutafi ne kawai, Kuma ga abun da ya faru😭😭😭, 

    Lumshe idon shi yayi, yayin da hawaye suka zobo masa, hannun sa ya mika ya jawota suka hada kansu waje guda yana fadin, " Nima naso haka Aysha, amman baxai yiyuba bane, wannan tafiyan dole dani acikin ta, kuma bekamata ki zauna har indawo ba, domin agida za'a nemeki, zaman naki anan beda wani amfani idan kinyi tunani Ayaha, kiyi kahuri kije gida, kibani wata uku na miki alkawarin zanzo, zanzo da mgnr auren ki.

     Cikin kuka sosai tace zaka zo da gaske??

   Zanzo ki yadda dani.

    Yaya Aliyu?

  Na'am Aysha

  Meyasa Allah ya jarabceni da son ka har haka?

   Ya jarabce mudai Aysha, Allah ne kadai yasan wannan, Aysha in tambaye ki mana?

    Tam Yaya Ina jinka.

  Ki share wayen ki, ki saki ranki sai muyi mgnr.

  Dagowa tayi daga jikin shi ta koma kujerar tana share hawaye.

   Saidai ta gama share hawayen sannan yace kinajina?

   Eh.

 

   Nawa ga wata kikeyin al'adan ki??

     Cikin sauri ta sunkuyar da kanta sannan tace, " ashirin da hudu"

   Jimmm yayi sannan ya kalleta yace" ashirin da hidu?, to ai yau talatin ga wata fah?

     Eh, jiya nayi wanka kafin mu fito.

   Leben sa nakasa ya cija da hakorin sa sannan ya fita a motar yana fadin Ina zuwa"

      Kusan minti shabiyar ya dauka sannan ya dawo, idon sa jawur ya zauna amotar sannan ya suka tafi, gudu yake dan haka nan danan suka isa

    

      Inda ta bada ijiyan kayanta sukaje suka amsa, sanan yasa mata amotar dake shirin tashi yanzun, Jakarta ya karba ya bude sannan yasa hannun sa ya ciwo kudi me yawa yasa aciki, rufewa yayi kalleta, Aysha ki shiga motar karki ce zakisake sauka, nima yanzun ko gidan baxan koma ba wucewa zanyi daga nan, sannan komenene yake faruwa a Cameroon ko wani hali Zaki shiga karki sake cewa Zaki dawo Nigeria, ko Ina nan bazan so ki sake kamo hanyar nan ba bare bana nan, namiki alkawarin dana dawo zanzo, kema kimin alkawarin baxaki sake kamo hanyar nan ba sai tare dani.

    Cikin sauri tace bazan dawo ba ai daman Yaya, amman kacika alkawari.

     Insha Allahu Aysha 

    Rakata yayi har bakin motar ta shiga sannan aka rufe motar, Hannu yaita daga mata itama take daga masa har suka daina ganin juna, sannan ya koma motar sa ya zauna tare da hada kansa da guiwa, zaman kusan awa daya yayi agurin ya kasa tafiya, tunanin sa ko Aysha zata dawo, Koda ya fito cikin tashar ya dade abakin hanga saida ya tabbar yanzun sun bar Kano sannan ya wuce gidan Aunty rukayya

           ******

  Aunty bani da lafiya.

  Meye haka Aliyu, kuka kuma kake katon ka dakai, meke damun ka haka?

  Bansani ba aunty, haka nan nakejina wani iri narasa inda zansa kaina naji dadi aunty.

  Subuhanallah, kana addu'a kuwa?

  Inayi aunty, komai da ya dace inayi, sannan Ina kokarin hana zuciyata sabon Allah, amman hankalina Kara tashi kawai yake, idan Ina tunanin Ina cikin damuwa sai wani abu yazo ya kifto min wadda yafi na baya, gaba daya na kasa nutsuwa.

    Kana da damuwa ne Aliyu bazaka fada bane dai kawai, toh koma menene kaita addu'a.

   Aunty ni ki rarrasheni, ki kwantar min da hankali kamar yadda Ummi kemin

    Hmmmm, ka fara kewanta kenan, kayi hakuri kabar kukan nan kada Yaya Fahat ya gani, idan yagani hankalin sa tashi zaiyi, lallashin ka Kuma babu wadda zai iya maka kamar nata, waye zai zauna yana rarrashin kato kamar ka ai sai ita Ummin, da kasan danine agarinan shekaranka biyar amman sau daya kazo gidana.

   Kansa ya kwantar kan kafadar aunty Ruqayya yana fadin, kiyi hakuri na bari.

     Tausayi ya bata dan haka ta daura hannunta akan sumar sa tace, " Allah ya yaye maka abun da yake damun ka, ya Kuma kawo maka mafita.

   Har cikin ransa yaji dadi sannan yai masu sallama ya fito, daga nan gida ya wuce yayi wanka tare dayin sallama dasu Baffah, farfe 04:00pm jirgin su ya tashi.

            Cameroon

    Misalin 01:44pm Aysha ce ake sauke mata kayanta atasha, wata motar ta tare tana zuba kayan tare da fada masa inda zata.

  Cikin motar ta zauna duk jikinta asanyaye hanya suka kama yayin da take kallon garin nasu duk ya mata wani iri, inda ta shiga tunanin yau watanta Uku da sati biyu rabonta da Cameroon, gabanta taji yayi mugun faduwa, ko me zataje ta tarar agida?, Me zace masu?, Yanzun Sunan bana gidan Daddy na, idan suna sani Ina zance masu naje?😔🙊

    

***











*🕳️BA'KAR FURA🕳️*

  _A true life story_

*Na*

_Fadeela Lamido_


  PEN WRITERS ASSOCIATION✍️

  

         episode. 30- 40

      

Tsintan kanta tayi da zubar da hawaye, cikin tsananin tashin hakankali take jinta sosai mara misaltuwa, babban abun dake damun ta ada bewuce taje dan taga Aliyu taji dadi ba, amman gashi zuciyarta har yanzun babu dadin

      Hawaye ta fara sharewa ganin motar ta shiga cikin unguwar su gabanta yaci gaba da faduwa,

    Akofar gidan su motar ta tsaya, fuskarta ta share dakayu sannan ta fito cikin motar, yayin da ake sauke mata kayanta, ahakali ta shiga Jan akwatin ta tanufi cikin gidan, gabanta na tsanta faduwa, cikin siririyar muryanta tai sallama.

    Ummace tai saurin fitowa daga cikin dakinta tana fadin, "Aysha idon ki kenan' Kinga kayana nan nadaure Ina shirin zuwa biko, saiki tafi ki share gindi kiyi zaman ki?

   Daker Aysha ta iya daurewa tace, keda ba zaman lafiya muke dake ba Ina ruwanki da zamana.

   A'a, ai da baki wlh duk gidan babu dadi, koma dai yayane nafison dai kina gidan Koda zakita sani surutu ne, juyawa Aysha tayi domin dauko dayan akwatinta, yayin da Umma ta biyowata abaya cikin tsananin farin ciki take cigaba da fadin"

  Wlh ba irin tunanin da banyi ba, nace to ko ubanki ya riki ne, inda ko ya rikeki wlh bazan yadda ba, ko sama da kasa zata hade saina amso ki, haba, naji ki shiru shiru, itama uwarki duk kawaicin ta saida tagaji tai mgn, zuwa wannan lokacin har sun shigo cikin gida.

     Falon Umma ta zauna akasa tana fadin Ina mamana?

   Mamanki yanzun sukaje dubiya ita da Murja.

    Ajiyan zuciya Aysha take saukewa ahankali ganin babu wani alamun dake nuna cewa sunsan bataje gidan Daddyn ta ba.

    Hira sama sama sukayi da Umma yayin da Umma keta nan nan da ita, wanka Aysha tayi tai sallah sannan tahau gado ta kwanta, abun da ya faru tsakaninta da Aliyu jiya taita tunawa yayin da take share hawayen gefen idon ta.

     Wani irin bakin ciki takeji idan ta tuna tarasa budurcin ta, duk da cewa tana son Aliyu amman wani Shashi na zuciyarta ya shiga Jin haushin sa, musamnan idan ta tuna azabar daya gana mata duk da irin ihun da take zubawa be saurara mata ba ko ya tausaya mata ba har saida ya gama abun da yai niyya, wannan dalilin yake sata take danjin zafin sa cikin ranta saidai duk da haka batabar Jin sonsa ba.

     Kuka tayi sosai tana daga kwance taji dawowan su mama ita da Murja, kasa kallon su tayi dan haka tayi lamo kamar me bacci.

      Daga can bacci ya dauketa, bacci tayi sosai domin Daman akwai gajiya ajikin ta, yamma lilis ta tashi, tsakar gida ta samu Mama da Umma, Mamanta ta gaisar cikin tsanin fara'a Mama ta amsa sannan tace ya Baban ki?, ai mun dauka ya rike ki ne"

      A'a mama nice bance zan dawo ba.

  Yayi miki kyau, tunda Umma tana miki zancen aure ke Kuma baki so ko??, Yaya mgnr karatun naki me yace akai??

    Mama yace zaizo da kansa kuyi mgn.

   Yamutsa fuska Mama tayi, ni meye nawa, ai kin girma kema aiba yariya bace, ko dake ai zaiyi mgn.

   Umma ce tace tunda yace haka ai shikenan, yazo din munajira.

    Da daddare kasa bacci Aysha tayi Aliyu kawai ke fado mata, gashi tun da Aliyu ya kusanceta zazzabi ya sameta har yanzun batabar Jin zafin jiki ba, duk kuwa da maganin data sha.

     Washegari Umma ta kula da yawan kwanciya da Aysha keyi dan haka ta mike tana fadin, " barin sa miki ruwan dumi kiyi wanka, na kula ke ragowa ce wannan dan tafiyan da kiya sai wani nan nad'ewa kike yi"

    Cikin kankanin Lokaci Umma ta juyewa Aysha ruwan wanka, sosai taji dadi bayan tafito wankan maganin zazzabi tasha tare dana ciwon jiki sannan ta koma ta kwanta, kusan kwana hudu Aysha tayi akwance sannan ta fara zuwa islamiyya, sai dai ko a islamiyyar hankalin ta rabuwa biyu take yi, wani lokacin har a tashi bata fahimtan me ake yi, babban abun da yafi dama mata lissafi kusantanta da Aliyu yayi ne, gashi wani shashin nazuciyarta yana ce mata anya kuwa Aliyu zai dawo, fakar idon mutane take ta share hawaye ita kadai tasan me zuciyarta yake mata.

      

           Satin Aysha biyu da dawowa suna zaune ita da Umma a tsakar gida wani yaro ya shigo yai sallama, Umma ce ta amsa tare da bin yaron da kallo.

      Wai ana kiran Aysha, yaron ya fada tare da raba ido.

   Cikin sauri Aysha tace babu Aysha anan gidan.

    Umma ce tai saurin kallonta tana fadin, me kike nufi?, Kai jekace gata nan zuwa.

    Juyawa yayi yayin da Aysha ke fadin, wlh saidai in ke kije amman ni bazani ba.

   Mama nadaga daki takwala mata Kira Aysha?

   Na'am.

  Banson iskanci tashi kije.

  Mama nace babu Aysha tace akwai, toh ita basai taje ba.

   Wlh Aysha nasameki gurin nan ranki zai baci, sa'arki ce ita?

  Mikewa tayi cikin kokarin yin kuka take fadin, wlh Umma nan kin cika hada rigima, ko Ina ruwanki dani oho, duk kinbi kinsa min ido.

   Eh naji, Kuma bazan bar saka miki idon ba sai ranar da kika fidda miji kikayi aure.

    Dan karamin hijjabi Aysha ta dauka tana fadin wlh idan wannan satin ya kare Daddy be zoba komawa zanyi yasani makaranta ni bawani auren da zanyi yanzun.

     Ficewa tayi yayin da Umma tabi bayan Aysha da kallo tana fadin, Bilkisu wannan yariyar taki duk yadda akayi aljanu gareta bantaba ganin gandareriyar budurwa kamar Aysha dake kin aure ba har haka.

    Umma rashin kunya ke damun ta, bata da komai tana sani, yanzun haka ita da babanta suka shirya cewa bazatayi auren yanzun ba.

      Cikin gamsuwa Umma tace toh Allah ya zama mana abun da yafi alheri.

         Ranar da Aysha ta cika sati Uku da dawowa ta shirya zuwa gidan Babanta wannan karon bata dauki kaya ko kala daya ba, daya daga cikin hijjabinta da Aliyu ya saya mata tasa wadda yakai mata har kasa.

   Mamace ke fadin, Aysha karki zauna kiyi sauri ki dawo.

   Amsawa tayi, Kai tsaye gidan mahaifin ta nufa, acikin tafiyan da batafi ta awa daya ba ta iso.

   Babban gida ne babu laifi, motarsa ta hanga tayi ajiyan zuciya duk da cewa daman tayi tunanin zata same shi a gidan.

      Tana shiga cikin falon wasu yan mata biyu suka tasu suka rungumeta, itama rungume su tayi yayin da wani dan saurayi da bazai wuce shekara 16 ba ya roko hannun Ayaha yana fadin, har Daddy yace zai kawo mu gidan ku kin dade bakizo.

     Wayyo inataso inxo makaranta ne ya hanani zuwa kuyi hakuri, karasawa cikin falon tayi yayin dataga Daddyn ta yayi saurin mikewa zai fice

  Sakin hannun kannenta tayi tabi bayan Daddy tare da saurin riko hannun sa tana fadin, Daddy yi hakuri.

   Batare daya kalleta ba yace nasan yau ma batan hanya kikayi.

   Wlh Daddy gunka nazo, makaranta ne kawai yake hanani zuwa.

    Wannan yaron ne yace Aunty ai kin gama makaranta fa Daddy ya gaya mana.

   Hararan sa tayi kadan tare da fadin, ai mu kunsan muna zuwa islamiyya Sama'ila

   Cike da gamsu Daddy yace toh kin kawo azuri, hannunta ya rike cikin murmushi yake fadin ya kike, Ina fatan kina lafiya.

   Lafiya Lau Daddy.

   Ina mutanen gidan ku, suma suna lafiya dai ko?

  Lafiya Lau Daddy sunce in gaida ka.

  Nagode, aini da nayi fushi dake nadauka da kika gama secondary zakizo kimana kwana biyu Koda yake kinfi son mamanki akaina ko?

   Daddy ba haka bane, karatu ne kawai itama tana ta cewa inzo.

    Wani irin kallo yake mata me cike da nuna kauna yayin da 'yan uwanta mata biyu suita taba hijjabinta tare da nuna sha'awar su akai.

    Hira sukayi sosai cikin yan uwanta da Daddy ta har yamma tayi sannan tai masu sallama har wannan lokacin mahaifiyar su Sama'ila tana gurin aiki.

      Da Daddy da Sama'ila har kofar gida suka kawo Aysha, kudi Daddy ya bata tare ta tabbatar mata nan bada jimawa ba zata fara zuwa makaranta.

         **********

  Wai ke Aysha yanzun kin baci da bacci, bacin ki yayi yawa, wannan ma zuwa makarantar taki ai babu amfani.

   Dagowa Aysha tayi idonta cike da Bacci, mikewa tayi ta fita ajin, can baya ta zaga ta zubar da yawon da ya taro abakinta sannan ta matsa gurin tsofin dake saida abuwan ci ta saya garin kuka ta bude ta dau kwallo daya tasa a bakinta sannan ta koma ajin ta zauna.

   Ina kikaje?, Wannan kawar tata ce ta tambaye ta.

  Cike da fada, a Aysha tace, " kincika tambaya toh yawo na zubar to.

   Yawu?, to yanzun me kike sha?

  Kwallon kuka nasa a bakina dan idan babu komai cikin bakina yawu tarowa yake.

    Lumshe ido yariyar tayi sannan tace, Aysha saikace me ciki?, Bacci, yawu, yanxun kuma ga garin kuka?

   Wani irin mumunan faduwan gaba Aysha ta shiga, take jikinta ya fara rawa, saidai bataso kawarta Zenat ta fahimta dan haka tace, wani irin mgn ce wannan, me kike nufi"

    A'a cewa nayi saikace me ciki.

   Tsaki Aysha taja, tundaga lokacin ta fara kokarin hana kanta baccin duk da cewa kuwa yana fizganta, ana tashi ta nufi gida cikin tsananin damuwa tare da fargaba, sai a yanzun ta tuna, idan fa mace da namji suka kebe irin ke bewan da sukayi ita da Aliyu ana iya samun ciki duk kuwa da cewa sau daya ne, 

     

    Kafafuwanta ne suka kasa daukan ta dan haka ta nemi wani kofar gida ta zauna, idan tana kirgawa daidai yau kwananta sattin da uku da dawowa daga Nigeria Kuma har wannan lokacin bata sakiyin al'ada ba. bude murya tayi tace kenan Ina da ciki?

    Tabbatarwa da tayi babu me bata amsa yasa ta shiga zubar da hawaye, daman shiyasa nake yawan bacci, shiyasa akoda yaushe bakina yake tara yawu, nashiga uku na, kuka taci sosai sannan ta tashi ta nufi gida.

      Tunda zinat tai mata wannan mgnr ta fargar da ita, damuwa takeji sosai musaman data tuna batayi al'adaba tun wadda tayi wankansa aranar da Aliyu yasata a mota na farko.

     Koda ta shiga gida ko gayan makaranta kasa cirewa tayi gado kawai ta haye yayin data kasa tsaida hawayen ta.

      Ke Aysha meya sameki kika dawo agigice haka?, Umma ta tambaya tana bin Aysha da kallo.

    Kaina ne yake ciwo Umma.

  Allah ya sauwake barin dauko miki magani kisha, maganin Umma ta bata hartasha Takoma ta kwanta bata yadda sun hada ido da Umma ba, wani irin yanayi ta shiga me wuyar misaltawa.

   Daddare tanajin su Umma da Mama sunata hira, itako tsabar damuwa ya hana mata Jin dadi, ayanzun gani take ashe dacan acikin ni'imar Allah take, bata da matsala yanzun ne take da gaggarumim matsala, waye zata gayawa wannan mgnr taji sanyi. Kuka taji tanasonyi sosai dan haka ta mike ta nufi toilet kukanta taci ta koshi ta fito idonta duk a kunbure.

    Washegari kin zuwa makaranta tayi saboda karma asake mata irin zargin jiya, bacci taitayi har misalin 11 shima saida mama ta tasheta tana fadin, " wai Aysha wannan bacci naki na lafiya ne kuwa?🤔

    Innawo ce tace, Nima naso in miki mgn, yariyar nan bata da lafiya tuni, karfin hali ne kawai dason makaranta kesata fita, amman bata da lafiya,inajin shawara ce baki ganin duk ta d'ashe.

  

   Mama ce tace toh aiko dai barin je in nemo mata magani, tun da kikaga Aysha ta kwanta agida lallai ba karamin ciwo bane.

    Aysha kuwa data juyar da kanta can gefe hawaye take sharewa tare dajin kunyan su Umma me tsanani daya shigeta har bata iya hada ido dasu.

       Da yamma Umma ce ta dafawa Aysha maganin da mama ta sawo mata nasha Dana wanka, kwana uku tayi tana amman jikin Aysha Kara rikicewa yake yi.

    Yadda Ayaha takejin damuwa yasa ta rasa abun yi, gashi babu wadda zaa gaya mawa taji sanyi dan haka ta fara tunanin gayawa Mamanta cewa wata biyu kenan batayi al'ada ba, sau uku tana zama gaban mama da nufin ta gaya mata amman saita kasa dan haka take Kara shiga cikin matsananciyan damuwa.

    Yau sati biyu kenan Aysha tana kwance agida har wannan ranar Aysha bata bari su hada ido dasu Umma ba, wata yar kamar roba ta samu tana boyewa ta zuba yawun da yake yawan taruwa mata abaki.

          *******

  Innawo?

 Na'am Fatima

   Kinji wani labari da ake kishin kishin dinsa a unguwar nan kuwa?

  Ai kinsan tsegumin unguwar nan yawa garai menene ya faru?

  Yariyar nan Aysha jikar Umma, ana jita jitan tayi ciki.

  Innalillahi wa inna ilaihir raju'un, Aysha fa kawar Husna mutunkyar Aliko?

  Itafa Innawo, kinsan da Aliyu na kasar nan da yanzun ya shiga zargi.

  Kwarai kuwa Allah ya rufa mana asiri, yana dai can ko wanni hali ake ciki oho,shekara biyar kenan, nasan fushi yayi kin sanshi da bakar zuciya.

    Yaje yaita bakar zuciyar shi acan tunda be dauko mana mgn ba.

             *****

Aysha zonan.

   Ahankali ta tashi zaune tare da kallon fuskar mama, hannun mama ta sake kallo, robar da take zuba yawu tagani ahannun mama dan haka ta sake dagowa ta kalli fuskar mama, wani irin mummunan tashin hankali tagani a fuskar mama yayin da taji maman na fadin.

   Ki sauko nace miki.

   Sakkowa tayi ta tsaya gaban mama yayin da cike da tuhuma Mama tace daman jira nake Umma tafita intabbatar da zargina akanki, meye abakin ki???










*🕳️BA'KAR FURA🕳️*

  _A true life story_

*Na*

_Fadeela Lamido_


  PEN WRITERS ASSOCIATION✍️

  

         episode 41- 42





Cikin sauri Aysha ta sunkuyar da kanta ahankali ta shiga lankwasa yatsunta tare dayin kwalkwal da ido.

   Magana nake maki fah, Ummi ta sake fadi cikin daga murya.

   Kwallon kuka ne, Aysha ta fada cikin kasa dakai.

  Kwallon kuka Aysha?, Yaushe rabon ki da al'ada kuma?😭😭

    Dagowa Aysha tayi ta kalli yadda Ummi ke zubar da hawaye tai saurin sunkuyar da kanta tare da zubar ta hawayen itama.

   Cikin matsanancin kuka Ummi kecewa, Aysha mgn nake miki Kar dai ace zargin da nake kanki ya tabbata Aysha😭😭

    Hawaye kawai Aysha ke zubarwa tana lankwasa hannunta yayin da hawaye ke zubowa wani na kora wani.

   Komawa bakin gado Ummi tayi ta zauna yayin da Aysha ke tsaye agabanta tana kuka sosai, zuwa can Ummi ta dago idon ta jawur tace"

   Aysha wanene yai miki ciki?

    Kuka Aysha tasa yayin da tai saurin zubewa kan guiwowin ta, tana matsancin kuka?

   Kinci mutuncin mu Aysha, kin zubar Mana da mutunci, kin bata mana tarihin gidan nan, tambayan ki nake ki gaya min, wanene yai miki ciki"

   Cikin matsancin kuka Aysha tace Mama kiyi hakuri dan Allah. 😭😭

   Kallon Aysha mama take tana zubar da hawayen takaici, wani irin bakin ciki takeji cikin kokon ranta tare da addu'ar Allah yasa cikin mafarki take ganin wannan abun ba gaske ba.

   Aysha da gaske ciki gareki kenan?, Aysha da gaske kinyi cikin shege gina gida bakiyi aure ba?.

   Mama kiyi hakuri dan Allah, nima bansa ni ba Naga dai kawai banda lafiya ne Kuma banga....

   Kasa karasawa tayi tare da fashewa da kuka.

  Shikenan Ayaha, bakomai, nagode Allah ya saka miki da alheri, bakiga al'adarki ba kenan kin san kina kefewa da wani, kinyi asara Aysha, kin lakata rayuwarki, kin Kuma zubar da kimarki da darajan ki ta 'ya mace, kin cuceni Kuma Aysha kin munafunceni, babu wadda zaice Zaki aikata, ashe kina kula samarin ki na banza ne?, ashe kina zuwa ki mikawa wani kanki sabodake baki da lissafi Ashe....😭😭

   Mama wlh sau daya ne😭😭😭

       Wani irin bakin ciki ne ya cika mama wadda yasata ta dauke bukitin karfen dake kusa da ita ta wurgawa Aysha, cikin tsananin bacin rai Ummi tacigaba da fadin, " fice kibani guri banson ganin ki agaba na.

    Cikin matsanancin kuka Aysha ta durkushe akasa yayin da hawayenta ya dame da majina tace mama kiyi hakuri dan Allah 😭😭😭.

     Idan kika sake bani hakuri saina sa itace namiki dukan mutuwa, dan Ubanki waye yai miki ciki?

      Sheshekar kuka Aysha keya idonta akasa, tabbatarwa da Ummi tayi Aysha bazatayi mgn ba yasata ta mike kawai ta shige daki tare da turo kofar.

      Itako Aysha nan tsakar gidan ta zauna dirshen akasa taci kukanta me matsanancin karfi ta bude murya, saidai harta lafa babu wadda yace mata ci kanki.

      Zuwa can ta fara yunkurin amai, dan haka ta mike aguje ta Isa gefen fanfo, kwarara amai. bayan ya lafa ta shiga wanke jikinta Sam babu kwari ko kadan.

     Can gefen kitchen Aysha ta koma ta kwanta a kasa tare da curewa guri daya, hawaye ke xobo mata tana sharewa.

      A lissafinta saura kwana Ashirin da biyu yau wata ukun da Aliyu ya fada su cika, idan yazo zaiji mummunan lbr, 😭😭, idan yaji Inai yaya zaiyi?,😭😭 Me zaici?, Nasan bazaiji dadi ba, wata zuciyar ce tace toh yanzun idan bezoba fah🤔, shikenan nikuma na shiga uku na.😭😭😭

    Tana cikin wannan kukan Umma ta dawo, kallonta tayi cikin tausayawa tace Aysha jikin ne?, Meyasa Zaki kwanta akasa ko tabarma babu?

     Bata samu amsa ba domin sabo da kukan dake cin ranta ko mgn bata iyawa.

       Dan haka Umma ta shiga kwalawa Ummi Kira, Bilkisu ke Bilkisu haka ake jinya ki shige daki ki rofe kofa?

    Jin Mama bata amsa ba yasa Umma ta nufi dakin cikin fada ta tura kofar.

      Ke Haka ake jinya, Ina mgn kinajina?, Kallon fuskanta yasata hadiye zancenta, sosai ta tsura mata ido cikin tsananin faduwan gaba tace menene?, Lafiya kuwa?

    Ki zauna Umma, murya adashe tai mgna dan haka Ummi ta zauna dambar akasa har yanzun idonta akan Mama.

    Umma Aysha ba shawara bace ke damunta kamar yadda kike tunani, Umma Aysha ciki gareta.

  Dafe kirji Umma tayi tare da fadin, Innalillahi wa inna ilaihir raju'un, ciki?, Cikin haihuwa?

   Kukan da Ummi keyi yasa ta kasa amsawa Umma yayin da Umma tai saurin mikewa tana fadin, munshiga uku acikin unguwar nan amman kuwa Aysha akwai matsiyaciyar yariyar, kitchen Umma ta nufa yayin da ta dauko wani katon itace tayo kan Aysha dake kwnce, ita ko Aysha awannan lokacin bata da karfin tashi dan haka Umma tashiga dukanta da itacen tana fadin wani dan iskan ne yai miki ciki?

    Dukanta Umma ketayi babu me ceton ta, yayin da Aysha ko ihu bata iyawa kare fuskarta kawai take da hannunta hawaye na tsiyaya akan fuskarta.

      Dan kanta tagaji tabari domin Aysha bata gudu ba, Ummako sai haki take cikin tsananin bacin rai tace, aiko saidai ki tattara kayanki kibar gidan nan dan baza'a haifarmin shige acikin gida ba, ke Bilkisu kifito ki tambayeta ta gaya miki wadda yai mata cikin, idan ba hakaba wlh saidai tabar gidan nan, munafukar yariya kawai wadda zuciyarta babu alheri, haba, gaskiya naga makota namin wani irin kallo, aahe kallona kawai suke inata shela a unguwa shawara na damun jikata ba'azo aka duba min ita ba, shikenan tafaru ta kare, Aysha wlh kinyi asara, kinyi asara duniya data lahira kina abu kamar bakisan komai ba ashe duk munafuncine, kije kin bude ma wani takon kawai kafafuwa ya gama dake, tirrrr wlh tirrr baki dauko halin uwarki ba, shegiya fitinanniya, kinsan auren kike so meya hana ki nuna Mana, a'a ke munafunci kika sa gaban ki, Zaki fadamin dan iskan naki koko saina tara miki jama'a?

   Sosai Aysha ke zubar da hawaye ganin da Umma tayi Aysha ba mgn zatayi ba ta mike ta zari gyalen ta tai waje tana cigaba da masifa.

    Aysha kuwa na nan zube, yau wani irin amai take kwarawa wadda ta rasa Kona menene, tunda tafara ciwo bata tabayin amai ba saiyau, da akasan da cikin. wani irin ramewa tayi rana daya.

   Umma kuwa kusan awa daya ta share sannan ta dawo sauran 'yaranta mata har uku suna minta abaya, biyu yayyen mama ne sai Kuma aunty Murja wadda kebin Mama.

   Nunata Umma tayi da hannunta tafadin ga watsartsiyar nan, kuyita dukanta harsai ta fada maku dan iskan dayai mata ciki.

      Tashi Aysha tayi zaune yayin da Yan uwan mama suka zagaye ta saidai yin duniya taki mgn kuka kawai takeyi dan haka suka shiga surfa mata zagi, wasu nakai mata duka.

    Sosai fuskarta tai jawur saboda Marin da suka yanyanka mata, ayanzun radadin fuskar kawai takeji zuwa wannan lokacin hawaye ya kafi a idonta sai sunkuyar dakai kawai take yi.

  Mamace ta fito tana fadin ta fada maku wadda yai mata?

  Inafah?, ai kinsanta da kafiyan tsiya, wlh yariyar nan Sam bata da mutunci, tantiriyar yar iskace, saboda bakin hali tabude baki ma tayi mgn ya gagareta shige barbadadiya.

     Ai maman Sadam kuita dukanta har sai ta sumai.

   Weadda Mama takira da maman Sadam ce tace, " me cikin ?, Idan jini ya balle mata fah"

    Ummace tace duk abun da zai faru ya faru, ni wlh ko mutuwa Aysha tayi yanzun bani da asara.

     Hada baki sukayi wajen fadin, wlh da haihuwar Aysha gara barin ta.

     Tafarfasa kawai zuciyar Aysha kiyi, kuka ya bushe cikin idonta, haka gidan Umma ya zama kamar gidan makoki wasuma acikin su kwana suke, babu irin tambaya da ba'a ma Aysha ba taki fada, duka kuwa da Zaki marasu dadi babu irin wadda bata Shashi ba, har takai gaba daya masa mgn da ita bare ma har akara mata tambaya kowa tirrr da halinta kawai yake, dan haka arakube take acikin gidan, babban wan Mama ma cewa yayi ahada mata kayanta taje duk inda zataje, mama ma haka tace, ta tafi gurin wadda yai mata cikin ita ko ganinta bata son yi.

      Sosai Aysha ta cansa nan danan ta fita cikin hayyacinta, wuya take shan ba kadan ba Koda yaushe yawo cike fal da bakinta, ga yawjun sun abubuwa saidai babu me bata haka take hakuri har aka dauki tsayon sati biyar.

   Har wannan lokacin babu mema Aysha mgn acikin gidan, abincima saidai ta faki idon Umma ta diba, Mama ko ko kallon inda take batayi, dan haka duk ta rame ta lalace, zuro zuro tayi har yanzun laulayi bebarta ba kamar ma karuwa yake.

      Yauma Ayaha ce kwance adakin mama, wadda tun ranar da Akasan tana da ciki takoma kwana cikin sa, Mama dakin Umma ta koma domin tace ita ko son ganin Aysha batai.

      

    Sati Uku kenan Aliyu ya Kara akan lokacin da yace zaizo, amman har yanzun babu alamarsa, tun ranar da yacika wata uku kamar yadda yace yake saka ran ganin sa, kullum zura ido take ganin har andau sati Uku bayan ranar da yace yasa hankalin ta duk ya tashi, kuka taci sosai, yanzun kam tacire rai da zuwansa, harma ta fara ganin rashin hankalin ta data debi kafa tabishi can, ahankali tace gashi yanzun ya barni da ciki Kuma yaki zuwa kamar yadda ya min alkawari.

      Sosai taji ta shiga jin haushin Aliyu me tsanani, gashi cikin sosai yake wahalar da ita, kasa kasa take fadin, shikenan zan haifi shege wadda zai dawwama babu Uba domin yanzun Aliyu yana ma iya cewa banashi bane tunda kowa yasan baya kasar nan, wayyo ni Allah nashiga uku😭😭

  Kuka tayi sosai duk idonta ya kod'e bakinta ya bushe.

   

     Ita kadai azaune a tsakar gida ji tayi tana son ta sha kukar fulani, dan haka ta mike tasa hijjabi ta fita, hanyar gidan su Aliyu ta nufa tun kafin ta karaso take bin gidan da ido, sosai taji ta tsana ko ganin gidan dan haka tai saurin dauke kanta, har ta sawo ta dawo bata sake kallon gidan ba .

          ********"

Ina kikaje?

  Wani irin faduwa gaban Aysha taji tunda taji muryan Umma, Dan ta dade bataji ta mata mgn ba.

   Ledan Hannunta ta nunawa Umma cikin sunkuyar dakai tace wannan na sawo.

     Umma taji tana fadin, " Bilkisu yariyar nan fah batasan zuru ba, idan mukayi wasa saidai muji inya, lokaci yayi daya dace ubanta ya sani, lallai kije ki same ubanta asan abun yi.

    Mama batace komai ba har Aysha ta shige daki.

      Misalin biyar na yamma taji Muryan Daddy ta acikin gidan dan haka jikinta duk ya kama rawa domin tunda tasan Daddyn ta bata taba ganin bacin ransa ba dan haka ma yanzun duk jikinta ya dau rawa.

       Ke! Aisha fito ga Baban ki?

    Fitowa tayi tana sanye da hijjabi Daddy na hango Aysha ya yamutsa fuska yana fadin"

    Lafiya?

   Umma ce tace matso nan ki zauna ki gaya masa.

   Kallo Daddy yake kare mata sama da kasa duk ta rame ta d'ashe idonta duk sun zurma yace Aysha menene ya same ki??

    Wasa Aysha ta fara da yatsunta yayin da wasu hawaye masu zafi suka shiga zubo mata.

    Juyawa yayi ya kalli Umma yace Meya sameta?

   Ciki tayi.

  Cikin sauri ya runtse ido, sannan ya juya ya kalli Aysha yana fadin, " cikin haihuwa ?

      Kuma anyi anyi ta fada wadda yai mata ta ki, duka ba irin Wanda bata sha ba amman takk mgn, amman taki mgn.

   Daddy ne ya sake cema Aysha, Aysha waye yai miki ciki?

      Har yanxun bata dago ba kuma batar wasa da yatsun ba hawayenta kawai yake gani yana diga, dan hska ya mike yaje gabanta cikin tsananin baccin rai ya watsa mata mari.

      Sosai zafin ya rudata tana jinshi acikin kanta taji Daddy ya sake cewa, " 

      Bazaki bude bakimin mgn ba?

  Durkushewa tayi cikin matsanancin kuka take cewa, Daddy kayi hakuri, wallahi Nima bansan kowaye ba, 😭😭 dan Allah kuyi hakuri ku yafe min.

  Wani irin kuka take me shiga rai dan haka Daddy ya Isa gabanta ya dagata, kirjinsa ya sata rungumeta yayin data tsananta kukan ta, ahankali Daddy ke share hawaye yayin da take dafa bayanta cikin sigar lallashi, sosai ya rungumeta zuwa can ya dago ya sunbaceta sannan ya rike hannunta ya kalli Umma yana fadin, " Umma bari muje muyi mgn nida ita kawai.

   Toh kaje, ka tirketa ta fada maka idan ba hakaba kuwa ni bame haifar min d'ana shege agida....