BAKAR FURA CHAPTER 8
*🕳️BA'KAR FURA🕳️*
_A true life story_
*Na*
_Fadeela Lamido_
PEN WRITERS ASSOCIATION✍️
Episode 43- 45
Rike da hannun Aysha suka fito, cikin motar yasata, suka bar unguwan, wani asibiti yakaita bayan an tabbatar masa da Aysha tana dauke da cikin daya kusa cika wata 4.
Baro Asibintin yayi cike da tashin hankali daker ya Isa saita kansa ya juyo ya kalli Aysha dake matsanan cin kuka yace' " ba kuka zakiyi ba Aysha, bude baki zakiyi ki gaya min wadda yai miki, ba zancen rigima bane ko tashin hankali, abun bukata kawai yasan da cikin, Kuma ya amince cikin nashi ne, matsala anriga an sameta, kuskure Kuma an riga anyi, waye ne Uban cikin?
Daddy kayi hakuri dan Allah, wlh basani ba.
Baki sani ba?, Kina nufin baki san waye yai miki cikin ba?
Kaita daga ahankali.
Shiru Daddy yayi tare da tsurawa guri daya ido tsayon lokaci sannan yace, " shikenan, idan cutarki akayi Allah ya saka miki,ya Kuma kawo miki mafita, idan Kuma kece nan kika Kai kanki, toh sai nace miki ki nemi sunan da Zaki Kira 'yarki ko danki, sannan ki neme amsar da Zaki bawa abin da kika haifa aduk ranar daya tambaye ki ubanshi, inason ki sani, idan baki yi mgn yanzun ba bayan kin haihu babu wani mataki dazan iya dauka, baza 'a zubar da cikin nan ba kamar yadda Kakarki ta bukata dole saikin haifi shi.
Kuka Aysha keyi sosai, bayan sunyi tafiya me tsayo ya tsaya yai mata sayayya sannan suka kama hanyar.
Zuwa can yacigaba da cewa, " naso ki zama kamar mamar ki, maman ki yariya ce me nutsuwa, akanta nafara sha'awan musulunci, Kuma har yanzun itace ta gujeni bani ne na gujeta ba, ke ko yanzun waye zaiso dansa ya aureki, har dai yaji abun da kika aikata?, Kin bata wayaun ki, mutanen unguwar ku, zasu dinga yin tirrrr dake, shiru yayi tsayon lokaci sannan ya sake cewa, kina sa hijjab kina Sallah, kince amiki aure ne ba'a miki ba?
Gargiza Kai tayi idonta cike da hawaye.
Koko akwai wannda kike so ne ban sani ba?
Nan ma hawaye ne suke zobo mata tasa hannun ta share tare da girgiza kai.
Daddy ne ya sake fadin, Ina tsananin son ki Aysha, amman ga abun da kika min, duk cikin 'ya'yana nafi son ki, Ina alfahari dake Amman kinje kinyi abun da mutane zasu min dariya dangina sun dade suna min korafin nabarki kina Islam, kinci amanata bantaba zaton haka daga gareki ba.
Daddy kayi hakuri dan girman Allah ka yafe min.
Ya zanyi dake, Allah ya rabaki da cikin lafiya ya Kuma kawo miki mafita.
Daidai wannan lokacin suka Isa kofar gidan, Aysha agaba, Daddy ta nabinta abaya suka shiga gidan, dakinta ta nufa yayin da Daddy ya nufi dakin Umma.
*******
Batasan Kona waye ba???, Aysha fa da kake ganinta munafukar yariya ce, munafunci ne cike da cikinta, nafi ganin a tutsuyeta ta fada, idan ba'ayiwa tufkar hanci ba ko, anrabata da wannan tana iya kwason wani, ba fata nake mata ba, Amman wlh idan ba wani ikon Allah ba zata jima bata auro ba.
Umma wannan yana daya daga cikin dalilin dayasa nace abarta da cikin, idan aka cire cikin kamar an bude mata hanya ne, idan ko aka barta dashi shine zata fahimci illar abun, annan zata gane inda matsalar take, dan haka nake son kuyi hakuri mu rungume wannan kaddaran.
Cikin sauri Mama dake kan gado tace, " aikuwa saidai ka wuce da ita, baza'a haifi wannan kazantar anan gidan ba.
Kashhh, Daddy ya fada, kuyi hakuri Aysha tacigaba da zama anan, jama'ar unguwar ku sun riga sunsa ni, tafiya da ita kamar Kara baza zancen ne, dangine sun dade suna korafin nabarta tana musulunci yanxun suna Jin wannan lamarin dariya zasuyi, nafi ganin muyi hakuri kawai.
Duk ta yadda Umma ta fillo Daddy toshewa yake, har dai suka yadda sannan yai masu sallama tare da jadda masu zai ringa zuwa akai akai.
******
Ai kullum Kara godewa Allah nake da ya daddara Aliyu baya kasanan, da yanzun an jingina mana shege.
Hmmmm, aini nayi farin ciki nagodewa Allah, Kinga yayi zamansa shima yanzun ya samu abun da ransa ke so, sai dai fah yaci ace zuwa yanzun ya waiwaye mu.
Bazai zo ba, ai kin sanshi da bakin rai, yana can yana fushine ne, yasha zamanshi idan zai yi aure naje ni.
Dariya Innawo tayi, aifa yai zaman sa fitina bata da dadi, duk da dai yanxun kam ya girma nasan yayi hankali.
******
Tundaga ranar da Daddy yazo su Umma suka Dan rage zafin su akanta, ayanzun suna bata abinci, saidai ko taci ko kartaci babu abun da ya dame su, sannan yawancin abincin nasu bashi take so ba, tsananin damuwar da take ciki be barin ta taci abincin, haka har cikin ya shiga wata na biyar, har wannan lokacin acikin 'yan uwan mamanta aunty Murja ce kawai take mata mgn, kowa harara ne da zagi tsakanin su.
Sosai rashin zuwan Aliyu har wannan lokacin yake dagula mata lissafi, ashe bazai zoba, amman yace min in bashi wata uku, gashi har yanzun shiru, besan da ciki ba, nasan ko yanzun yazo bazai karba ba, dan haka babu amfanin Kiran sunan shi, shekaran sa biyar baya kasar nan yana cewa karya nake shikenan ta zauna, kowa cewa zaiyi sharri zan masa tun da narasa uban cikina, kuka ta kwana tanayi wadda yai dadlili Kafin safiya ta tashi da matsanancin ciwon mara me tsanani.
Ganin tun safe Aysha bata leko ba Mama ta faki idon Umma ta shiga dakin.
Yau Yaya dai?
Mama cikina ne ke ciwo.
Allah ya sauka ta fada sannan ta fice, ganin har anyi azahar Aysha bata fito ba yasa Mama ta koma dakin.
Kudi mama ta mika mata amshi kije asibiti.
Daker Aysha ta iya mikewa tana tunanin ta Ina zata fara zuwa asibiti ita daya.
Tana fitowa layin aka fara binta da kallo rabon data fito ta manta, dan haka taji sai hardewa takeyi, daker ta karasa gidan.
Da fada aunty Murja ta rufeta dashi, meyasa tazo mata gidanta, acewarta bata son mijinta ya sani.
Irin wannan abubun sunyiwa Aysha yawa Dan haka saita yi da gaske hawaye ke zuwar mata.
Meya kawo ki?, taji muryan aunty Murja bayan ta gama fadan.
Cikinna ke cewa shine na fito inje asibiti.
Ba dole cikin ki yai ciwo ba, kina sane sarai, cikin ki ya girma, ko bakici abinci Dan kanki ba dole kice sabo da abun dake cikin, yunwace kawai take damun cikin.
Cikin sauri Aysha tasa hannunta ta dafa cikin, jinsa tayi ya cure guri daya, sai yanzun ta tabbatar eh lallai me raine acikin ta.
Kunun gyada Murja ta damawa Aysha tashashi da lumishi, yayin da tana gamawa bacci ya dauketa.
Bayan ta tashi ruwan wanka Murja ta bata tai wanka sannan ta kamo hanyar gida tana mejim dadin jikinta ba kama sanda ta fito ba.
********
Sannun ahankali kwanakin suke juyawa zuwa watanni, ayanzun cikin Aysha ya cika wata 9, wani irin girma yayi naban mamaki, tuni tabar saka kayanta domin duk sun mata kadan, Kuma har cikin ya tsufa nan wuya kawai take sha, bama kamar daya girman nan yafi bata wahala, zama daker tashi dake babu wani me taimakonta, komai ita takewa kanta har wannan lokacin da ta tabbatarwa kanta cikinta ya kusa fita.
Babban abun da yafi kona mata rai shine watanta tara da dawowa Nigeria amman har yau wata ukun Aliyu basu cika ba, wani irin zafi sa takeji fiye da misali, sosai ranta yakebaci data tunashi domin kuwa yanxun ta tabbatar ya yaudareta, cikin matsanancin kuka ta shiga rokon Allah ya dauki ranta wajen haihuwar ita da cikin baki daya, saidai tana addu'ar tanajin yadda dan cikin nata ke zillo kamar zai barka cikin.
Cikin matsancin kukan da sai zuwa yanzun hawaye ya fara zubo mata tace, "ya rabbi na rokokeka, ko a lahira karka hadani da Aliyu, Allah kasa nagama ganin shi kenan har rayuta ta kare, Allah ka hanini ganin duk wani abun daya shafe shi barema shi da kansa. Mugu kawai azzalumi wadda besan girman alkawari ba, yasan ya cuceni shiyasa bazaizo ba.
Cikin matsancin kuka take Kiran sunan Allah tare da addu'ar ya dauke ranta ita da dan cikin nata.
Bayan Sati biyu ta tashi da matsanancin ciwon mara.
Murkususu take tun safe har rana tana saman katifar ta, ganin har rana tayi, Mama ta tashi ta leka dakin tana fadin ke lafiya kuwa!
Mama marana ke ciwo.
Lumshe ido Mama tayi tare da fadin, Bismillahir rahamanir rahim, Allah nagode maka daka jarabceni da ganin wannan mummuna al'amari wadda bame dadi ba agareni.
Umma ce tace lafiya?
Aysha nakuda take yi Umma.
Munshiga Uku,, naka takaine Yaya zamu yi?
Umma ko asibiti zakuje?
A'a ai batai awo ba, adai Kira mata unguwar zoma.
Umma, Amman kinsan Innawo ce kadai keyi anan haka, Kuma Innawo nasan bazata zo.
Gyale Umma ta dauka tana fadin kedai Ina zuwa.
**********
Innawo karkije dan Allah, lallai ma matar nan bata da Kunya ko kunya bataji ba ta iya tskowa gidan nan meya hana sukaita asibiti.
Bakomai Fatima barin je, wlh taban tausayi, zanje idan naga da matsala zance suje asibiti, idan ina iyawa Kuma zan amsa, ai da nakowa ne.
Kofar gidan Innawo ta nufa yayin da Ummi ke fadin, kashh, dan Allah Innawo ki dawo karkije.
********
Wani dan karamin littafi ya bude, ya zubawa shafin ido sannan ya mayar ya rufe, mikewa yayi ya dauko a kwatin sa tare da zuba kayansa aciki ahankali ya mayar ya rufe, yana daga tsaye ya zuba hannun sa duk biyun cikin aljihu, guri daya ya tsirawa ido, bakin gilashi sanye a idon sa cike da kwarin guiwa yake sauke ajiyan zuciya.......
***
*🕳️BA'KAR FURA🕳️*
_A true life story_
*Na*
_Fadeela Lamido_
PEN WRITERS ASSOCIATION✍️
episode 46- 47
Da Sallama Innawo ta shiga gidan, yayin data samu Umma rike da Aysha acikin dakin Ayashan, cikin nuna kwarewa Innawo tace, "haihuwa ce , abani leda da reza"
Cikin sauri Umma ta fice adakin tare da daukan gyale tai waje, bata jamaba ta dawo dakin.
Sosai Aysha ke murkususu Innawo na mata sannu su biyu a dakin.
Murkususu take yi tsayon lokaci tare da share hawaye, sosai tagaji iya gajiya, ciwo takeji bana wasa ba.
Innawo kuwa fadi take daure dai Aysha.
Kusan awa uku aka kwashe ana abu daya, ganin mangariba na gabatuwa Shiru babu wani lbr yasa Hankalin Mama ya tashi sosai, wani irin tashin hankali takeji, Daman yadda cikin Aysha ya girma abun tsoro yake bata.
Bayan isha'i ne abun ya tsananta, daga dakin Umma tana jiyo nishin Ayaha, Innawo kuwa tana rike da Ayaha tana mata addu'ar neman sauki tare da sauka lafiya, kokarin yariyar tagani sosai.
Misalin tara da rabi na dare kan dan ya fara turowa, cikin kwarin guiwa Innawo ke fadin, " yauwa Ayaha, kadan ya rage, yi karfi da jikin ki saura kadan ya fita ki huta.
Wannan mgrn ta Innawo ke karawa Aysha karfen guiwa cikin ikon Allah jaririn ya gama fitowa tare da uwar gaba daya.
Ajiyan zuciya Ayaha ta sauke, hakika haihuwa akwai raradi wadda bashi missaltuwa yanzun ji tayi kamar an zare mata ciwon.
Innawo kuwa harta yanke ciben ta nade abin da aka samu cikin zanin Aysha yayin da gidan ya karade da iho, Umma ce ta shigo tana tambayar Innawo ta sauka ne, cike da kwarin guiwa Innawo tace ta sauka ga danta nan kwaton gaske.
Hmmmm, kawai Umma tace sannan ta juya ta fita.
Ganin haka Innawo ta tsaya ta gyara komai tare da wanke kayan da aka b'ata, ganin inda Umma ke shashsharewa Innawo tace abata ruwan zafi tama yaron wanka.
Nan danan ko Umma ta kawo ruwan, bude yaron Innawo tayi tana kokarin saka shi aruwan wankan take fadin, wai, wannan yaron baki ne, beyo farin uwarshi ba, juyawa tayi ta kalli kunnen yaro sannan ta kalli keyarsa, zabura Innawo tayi tare da dan zaro ido.
Mamace ta shigo ta fita da Aysha domin yi mata wanka, dan haka Innawo ta shiga duba yaron dakyau.
Gani take kamar Aliyu ne yayi kaki ya tufar, cikin tashin hankali ta furta Innalillahi wa inna ilaihir raju'un, wannan yaron bashi da banbanci da Aliyu, haka yake sak lokacin da aka haifeshi, katon gaske ga tsandara ihun tsiya, haka wannan yaron tunda yazo duniya be rufe baki ba Kona sakan daya.
Cike da rude Innawo ta shirya yaron cikin wani kayan sanyi da Umma ta kawo.
Gashi an samu karuwa Amman Umma da mama zuciyar su babu dadi, fitowa Innawo tayi adaidai lokacin da Aysha ta fito wanka, godiya Umma tai mata sannan ta fita ta nufa gida.
Har Allah Allah Innawo take ta Isa gida, dumin hankali ta atashe yake, lokacin har Ummi ta kwanta dan haka tasa hannunta tana bugunta tana fadin, Fatima tashi ki zauna.
Innawo sai yanzun kika dawo, tun rana ko lekowa gida ki koma bakiyi ba fa.
Katseta Innawo tayi da fadin, "ke Fatima ba wannan ba, akwai matsala"
Matsala wacce iri Innawo?, bata haihu bane?
Ta haihu, ki zauna dakyau nace miki.
Gyara zama Ummi tayi tana daga bakin gado.
Innawo ce tai kasa da murya tace, "dan da Ayaha ta haifa kamar Aliyu ne yayi kaki ya tofar"
Dirowa Ummi tayi daga gadon, tsintan kanta tayi akasa wanwar, Innawo ban fahimceki ba?
Hmmmm, Fatima yaron kama yake da Aliyu, kama bana wasa ba.
Innalillahi wa inna ilaihir raju'un, Innawo dan Allah ki bari, kin manta shekaran Aliyu biyar baya kasar nan gaba daya?, Innawo karki sake fada, bazamuga shege ba insha Allahu, Aliyu bazai haifamana dan xina insha Allahu.
Ai saidai Kar akuma Fatima, amman duk inda akeje aka dawo wannan yaron namune ko shakka bana yi.
Innawo kiyi shiru dan Allah, kibar jingina mana shege, kamace kawai tai yawa.
Shiru kawai Innawo tayi domin bata son jayayyan nan da Ummi ke yi.
******
Wannan abun bakin ciki dame yai kama, ni dan takaici ma na kasa kallon yaron, ita kanta Aysha yaron kwana yayi yana tsandara ihu taki daukan kasa, danaji najin da jin kukan sa nace mata tashi ta bashi nono sai tasa min kuka, haka muka kwana ita tana kuka danta nayi, ba irin abin da ake gudu kenan ba, yanzun da aure ne ya kawo wannan yaron me shegen kwakwazo haka nan zamuyita ririta shi, amman wlh yanxun danaji muryan yaron sai inji kamar in hadiyi zuciya in mace.
Kawar dakai mama tayi tare da fadin, tana daukan alhakin yaron ne, shi meye nashi nashi? adolenta ta shayar dashi. ni yanzun abun dake cimin rai ace wai Aysha ta rufe ido tace ita Sam batasan uban yaron ba, wlh Umma ban yadda da wannan ba.
Ita ta jiyo, yanxun dai ai ga tukuicin rashin Jin mgn nan Allah ya bata, idan ta yaye shi idan Allah ya bata miji ko wanni iri ne sai a kukuta ta tafi, hankalin mu ya kwanta.
Umma waye zai aureta da yaron?
Indai ta samu mijin saidai tabar Dan nan dan musamu ta zauna agidan mijin cikin kwanciyar rai.
Saidai ubanta ya dauka, wlh ni Umma ko ganin dan bani kauna.
Ai kiyi hakuri kawai, indai ba Koran Aysha zamuyi ta shiga duniya ba toh rayuwa da danta yazamar mana dole, Kinga lokaci na tafiya barinje ingayowa 'yan uwanki, ke Kuma kije ki ma yaron wanka ga ruwa can ya gama dahuwa har gurin babanta zanje.
A'a Umma kibari abawa abawa iro kudin mota yaje duk ya gayo masu, ni bad'an dazama wanka.
Jimmm Umma tayi sannan tace toh shikenan.
Mikewa Umma tayi ta debi ruwan zafin ta koma dakin, itako Mama gyale ta dauka ta nufi waje domin aika iro.
*****
Wai har yanxun kukan kike?, ai wannan kukan beda amfani, kuma d'an ba laifinsa bane ki dauke shi maza kibashi nono, kafin asashi a ruwan wanka.
Karawa kawar dakai Aysha tayi, dan haka Umma ta nufi dan ta dagoshi ta daura cinyan Aysha dake zaune sannan tagama hannun Aysha ta tallabo kan yaron dake ta tsandara uhu, kallon Aysha Umma tayi tace toh fito da nonon kisa masa abaki.
Hawaye kawai Aysha ki zubarwa yayin da kukan yaron ya dami Umma dan haka ta daga rigar Aysha ta ciro nonon tare dasa hannunta ta Kara dago kan yaron dumin nonon yasamu shiga bakin sa, carab kuwa ya rike nonon tare da fara tsotsonsa bada wani bata lokacin.
Jin yaron yayi shiru yasa Umma takai idonta fuskan yaron tana fadin, " kin bani da tsotso ai ku......
Cak ta tsaya tana me karewa yaron kallo, Rabon data tuna Aliyu ta mance, dagowa tayi ta kalli Aysha dake hawaye sannan ta kara maida idonta kan yaro, idonta akan yaron take fadin, " Bilkisu fito ki gani!!, Bikisu kina ina!!
Tunawa tayi Mama ta fita dan haka tamaida hankalin ta ga Ayaha tare da fadin, "wannan yaron uwa Aliyu aka zuke ya zama 'kankani. Duk yadda akayi Aliyu nashigowa garin nan, shiyasa kikace baki san wadda yai miki cikin ba.
Kawar dakai Aysha tayi har yanxun hawaye na zubo mata ga wani irin faduwa dataji gabanta nayi tunda Umma ta Kira sunan Aliyu.
Cikin wani irin yanayi Umma tace, " rike danki, kan yaron Aysha ta kama yayin da Umma ta matsa can gefe tana kallon Ayasha sannan ta juya ta kalli yaron tsayon lokaci ta dauka ahaka sannan Umma tace akwai tashin hankali agarin nan, wlh wlh bazan yi shiru ba, kowa yaci tuwo dani miya yasha, Sam bazan yadda ba.
Mama ce daga waje take fadin, " Umma Yaya aka yi?
Ai tana kwala miki kira, shigo kiga Aliyu a hannun Aysha, wallahi wannan yaron na Aliyu ne, ko kaffara banayi jikan Innawo ne.
Cike da sauri suka shiga dakin gaba dayan su, Maman Sadam da Murja Koda suka kalli yaron salati. Suka fara, Aysha kuwa kawar da fuskanta kawai take babu bakin mgn.
Maman Sadam ce ta fige yaron daga hannun Aysha ta fice adakin yayin da aunty Murja da Umma suka rufa mata baya.
****"
Innawo ki daina damun kanki, Ina kallon ki Innawo bakiyi bacci ba da daddare, ni Ina da tabbacin abun da nake fada miki ko kina ganin Aliyu zaizo garin nan ne ya juya batare dayazo nan ba?
Nima abun da ya tsaya mun arai kenan Amman fa Fatima koma dai ta yaya ne yaron nan na Aliyu ne, domin har kafa, hannun, ido, baki hanji ke har sumar kan yaron irin na Aliyu ne, yadda kikasan Aliyu sanda yazo duniya haka garon yake.
Innawo ki kwantar da hankalin ki, ni Ina da tabbacin banasa ban.....
.
Har gowan mutane yasa suka maida kallon su ka kofar shigowa gidan, inda Maman Sadam tai saurin daura yaron kan cinyar Ummi tana fadin, ki duba kiga abun da danki ya shuka.
Mikewa Ummi tayi rike da yaron tabas taga kamar da Innawo ke fadin, cikin azama ta shilla yaron yayin da Murja tai saurin cabewa tana zare ido, cikin zaro ido Ummi ke fadin nafiku hauka, wato yarku ta haife d'a kun rasa inda zakiyi dashi zaku kakaba Mana, toh duk inda za'aje aje bazan taba yadda ba, shekaran Aliyu biyar kenan kwarara baya kasar nan, kowa cikin unguwar nan yasani tunda Aliyu yasa kafa yabar gidan nan be sake lekowa ba, dan haka bazan taba karban dannan ba, ko sama da kasa ce zata hade, 'karyar bala'i kuke yi.
Ai kuwa kowa ya kalli yaron nan yasan na Aliyu ne, Umma ke fadin haka tana me nuna yaron.
Ummi ce tace, " Inna hujar take?, Kije ki nemo hujja ki kawo, idan ba haka ba wlh zanyi karan ku.
Jiki babu kwari suka fita domin dai basu da wata hujja suna komawa suka tarar Baban Aysha yazo da kaya niki niki, Aysha kuwa har wannan lokacin kuka take yi nan suka shiga gaya masa duk yadda aka yi.
Kawar dakai yayi tare da fadin, "aina gaya mata, ita yakamata ta bude baki tai magana tuni, nayi nayi da ita taki, tunda batai mgn ba kuwa Nima bani da ita, dan haka ku rabu da ita.
Sallama ya masu akan da yamma zai dawo , bayan tafiyan sa yaran Umma duk sun hallara dan haka suka Kara yanke shawaran akara komawa da yaron gidan Innawo.
Lokacin da suka Isa tunkafin su shiga gidan Alhaji Umar ya taresu, domin harda maza cikin su, anan Alhaji Umar ya kara tabbatar masu da bazasu karba ba domin babu wata hujja da ke nuna Aliyu yazo garin nan acewar Alhaji Umar idan akwai hujja suje su kawo.
Haka suka sake komawa da yaron, ayanzun duk uguwar ta dauka, akan wannan tirka tirka da ake tsakanin gidajen guda biyu, yayin da duk jamar unguwar ke goyon bayan Ummi akan cewa karta karba, domin dai kowa yasan Aliyu be Kuma dawowa kasar ba, ko Ina cikin unguwar mgnr da ake kenan.
Gidan Innawo kuwa gaba dayan su tutsiye Aysha sukayi akan ta bude baki tai mgn amman abu ya gagara, zagi babu irin Wanda basu mata ba yayin da wasu suke cewa amata dukan ne, wannan abu ya dauke su tsayon lokaci har misalin karfe biyar na yamma so kawai suke Aysha ta fada masu domin su samu hujjar komawa gidan Innawo.
******
Karfe biyar da kwata ya shiga cikin unguwar, acikin abu biyu yasan tabbas zai tarar da daya, kodai Aysha tagaji da jiran sa tayi aure, ko Kuma tana dauke da tsohon cikin sa, wadda jikin sa yafi bashi na karshen, a zuciyarsa yasan mayuwacin abu ne ace Aysha bata da cikin sa, saidai idan wani ikon Allah, dan haka yanzun bashi da burin daya wuce yaji labarin Aysha tunkafin ya Isa gida.
Adaidai kofar gidan su Innawo motar ta tsaya, yayin da yake ganin komai ya cansa masa, akwatin sa ya sauke sannan ya Kira wani matashi yace dan Allah ka shigar min da kayana nan gidan.
Dauka yaron yayi ya shiga, yayin da Aliyu yai saurin karasawa gurin Idi me shago.
Wa nake gani haka kamar Aliyu?
Cikin murmushi Aliyu yace, " ba kama bace nine"
Aliyu Kaine?, Kallon Aliyu yake sosai yayin da yaga ya zama katon sajo babban mutum.
Nine Idi.
Nayi farin ciki da zuwan ka ta wani bangaren Kuma banyi ba.
Menene yake faruwa?
Hannun idi yasa yaja Aliyu bayan sagon sa yana fadin, " bayan tafiyan ka abubuwa da dama sun faru, kayi hakuri zan gaya maka wata mgn wadda bata da dadi, Aysha tayi ciki....
Tun kafin ya rufe baki Aliyu yace, " nasani"
Au ka sani???🤔
Eh na sani, idi yanzun Aysha tana Ina?, Cikin na nan ko babu shi?
Ai ciki ma an haifeshi jiya da daddare.....
Bebari ya karasa ba yace ita Aysha tana Ina?
Tana nan cikin gidan su ....
Nan ma be bari ya rufe bakiba ya doshi gidan, acikin zauren gidan ya tsaya hannun sa cikin aljihun sa, cikin karkausar murya ya rangada sallama Har sau uku sannan aka amsa.
Innawo ce ta tahowa tare da fadin, " waye nan??
Acikin daga muryar irin na sojoji yace, " nine.....