BAKAR FURA CHAPTER 10
_A true life story_
*Na*
_Fadeela Lamido_
PEN WRITERS ASSOCIATION✍️
Episode 48- 49
Mikewa yayi da takardan a hannun sa ya shiga gidan, tunda ya bude ta be rufeba.
Afalon ya samu Ummi sai faman sheshekar kuka take yi, yayin da yaji muryan Innawo daga cikin dakin maccin ta tana fadin, " tunda bazaki bari ba saikije kita yi, idan wani ciwo ya sameki sai kizo kiyi jinya, ace mutum ya wuni yana kuka, komai yayi zafi maganin sa Allah, ni ko Aliyu bezo yanzun ba na tabbatar koma yaya ne d'an nan nasa ne.
Jikin Aliyu a matukar sanyaye ya zauna afalon nesa da Ummi, yayin da kowanni saukan hawayen ta yakejin takaicin sa cikin ransa, dan haka ya shiga fadin, " Ummi dan Allah kiyi hakuri"
Cike da tsananin zafi tace, "ranka zai baci ka sake ka sake min mgn, babu ruwana dakai, mara mutunci kawai, wadda besan mutunciba, Dan iska kawai wadda ya dauki zina ba abakin komai, gara daka nunana min ka zama tantirin dan iska, kaje ka amsa kazantarka tun wuri ga kaima Ubanka, nan bama rike d'an iska bare mu rike kazantar ka.
Ji Aliyu yayi kamar Ummi na watsa masa wuta, dan haka duk jikin shi ya Kara sanyi, cikin sanyi sosai yace, " Ummi kiyi hakuri dan Allah ki Kuma tsaya kiji Uzurina.
Dallah gafara cen, Kai dan baka da Kunya har kake tunanin ni zan saurara ta tsuniyar ka?, Mara kunya kawai, kama yariya ciki saboda tsabar rashin kunya jiya tana haihuwa har ka iya shigowa garin nan, kowa na kallon ka bakajin kunya Kai?, to idan Kai baka da digon kunya mu muna dashi, nasan ka riga ka zubar Mana da mutunci kowa yasan wannan lbrn acikin unguwan nan, harma da kewayeta, dan haka yau yau dinan kaje ka amsa danka kabar kasar nan, baxaka kwanar Mana agida ba kaji Kuma na gaya maka.
Mikewa Aliyu yayi cikin rasa abun yi, adaidai wannan lokacin Innawo ta fito tana fadin, " ni yanxun ba wannan ba, surutun nan bashi da amfani, ke ki bari yayyan ki suzo kwai anemi mafita.
Innawo idan Ina kaunar ganin Aliyu toh Ina kaunar ganin mutuwata, wlh banson kallon shi idan Ina kallon shi raina namin zafi, zuciya ta nafarfasa, jibeshi kawai, katon banza mazinaci dan isaka fasiki matsiyaci kaw......
Cikin sauri Innawo ta katse Ummi da fadin, " ke!! , Ki dawo cikin nutsuwarki, naga kina da niyar yi masa baki, karki fara, wlh ranki zai baci.
Toh Innawo wadda ya aikata irin wannan abun kuma meya rage mishi?, ai ya riga da ya lalace.
Nace miki kiyi shiru ko, bakama yima yaron mugun baki ba kenan inaga ka mishi?, Kai Aliyu tashi ka shiga ciki.
Ajiyan zuciya Aliyu ya sauke me karfi sannan ya mike muryan shi can kasa yace, " Ummi kiyi hakuri dan Allah, nasan ni me laifine, bacewa nayi akan daidai nake ba, matsala kawai aka samu, kokarin shiga dakin yake ya sake cewa Innawo kema kiyi hakuri ba ason raina bane, tsintan kaina kawai nayi ahaka.
Sosai wannan kalamin nasa ya shiga jikin Innawo, tausayin Aliyu taji ya dan shige ta dan haka ta hada abinci ta nufi Kai masa, sai dai tana dire abincin yace Innawo bazan iyacin komai ba, hankali na ba akwance yake ba.
Murmushi Innawo tayi me kama da yake sannan tace, " duk jarumtar daka taho da ita Aliyu?, ai naga ka taho da jarumta, naji kanace ma Umma d'a naka ne, amman bazaka amsa ba, wai kabata, toh Kai kanka kasan ba abu me iya yuwa kake fada ba, kasan masifa da balaki irin na Umma, da ace ba Umma bace sai mu roki tashayar da yaron bayan tagama shayar dashi tabamu, toh Umma kota amince da haka na tabbatar hankali bazai taba kwanciya ba idan ba dan nan aka amsa ba......
Innawo nifa baxan amsa yaron ba.
Bangane ba Aliyu?, kafa amsa d'an naka ne?
Amman wlh Innawo bazan amsa ba, ko ita ta kirkiro masifa.
Ashe kuwa Umma zatai karan ka.
Ai tamayi, ga takardan yanzun aka kawo min.
Innalillahi wa inna ilaihir raju'un, shikenan zancen ya wade duniya, naso arufe abun.
Ninafi son haka Innawo.
Aliyu bakajin kunya?, Wannan fa babban abun kunya ne, ace acikin zuri'armu muna da shege.
Kashhh,😬 Aliyu ya fada, Innawo shege fa kuke cewa, shige shine wada ba'asan ubanshi ba ai,
Ai ba aure kukayi ba?, Ko auren sirri kukayi?, Idan kuwa har ba aure Aliyu ko kaki ko kaso sunan sa kenan.
Yamutsa fuska Aliyu yayi tare da kawar da kansa yake fadin, " amman Inawo wannan yaron ba sunan sa kenan ba, kuma idan har ana gaya masa haka za'a dinga samun matsala.
Mikewa Innawo tayi tana fadin, Allah ya rabamu da ita, Kuma Ina baka sharawa aje duk wata rashin kunyarka harsai zuciyar Ummin ka yayi sanyi inba haka ba ta iya gaya maka kalma mara dadi, dan tana cikin fushi sosai.
Tana gaba fadin haka ta fice yayin da yabi bayanta da kallo.
*******
Koda rana da Alhaji Umar da Sani sukazo gaba sukasa Aliyu, fada babu irin wadda basu masa ba, sosai ya roki su tsaya su saurari uzurin shi, amman Alhaji Umar yaki bashi wannan damar, acewar sa, bashi da wani uxuri da zaisa su saurareshi, idan har zina ne ba aure ba, basu bukatar uzurin shi, dan haka ya sunkuyar takai kawai, cikin yanayin dake nuna yanajin kunya, daga karshe Ahaji Umar yace, tunda sunkai mgnr kutu babu wani hukunci da zasu iya dauka abari ashiga kotun.
Cike da fada Ummi tace ai shikadai zaije babu wadda zaije kotu acikin gidan nan.
Kara sunkuyar dakai Aliyu yayi yayin da yaji muryan Ahajin yana fadin, " kedai ki zauna agida, amman dole asamu wadda zai rakashi, hannun ka baya rufewa ka yanke ka yar, dan haka yazun mafita ake nema.
Mikewa Ummi tayi tabar dakin, yayin da duk suka shiga yima Aliyu nashiha.
Bayan sun gama da Aliyu gurin Ummi suka nufa, nan ma dai nasiha sukaita mata akan hakuri, aduk halin daka tsinta kanka aciki.
Washegari misali 7: 30 Aliyu ne ya fito cikin kananan kaya, a kitchen ya samu Innawo bayan sun gaisa yace, " ina Ummi na?"
Kallon shi tayi tace, " tana kwance sai bayan sallan Asuba ta samu bacci.
Jimmm yayi, sannan yace, " dan Allah Innawo ki bata hakuri, kinji, wlh tsautayi ne kawai.
Hmmmm, toh naji ai Allah ya kawo Mana mafita.
Ameen, ya fada ahankali, sannan ya juya ya fita.
*******
Wannan Zaki mikawa Aysha Idan da hali ki dauko yaron.
Amsan jibga jifga ledojin guda biyu matar malam Idi tayi a hannun Mijinta sannan ta kalli Aliyu dake gefe ta kada Kai tai waje.
Gurin zama Malam idi yabawa Aliyu sannan ya zauna kusa dashi, kusan minti 10 sannan matar malam Idi ta dawo rugume da jaririn ahannun ta.
Malam idi ne ya mika hannun ya amsa yaron, sannan ya mikawa Aliyu, nan danan murmushi ya bayyana afuskan Aliyu yayin da ya kurawa yaron ido.
Daker ya iya dagowa ya kalli Matar malam idin yace, " aunty Aysha tana lafiya dai ko??
Eh lafiya lau take.
Maida Hankalinsa yayi kan yaron dake kokarin wangale baki sannan ya sake dagowa yace, " bata cikin wata matsala ko?"
Eh toh, gaskiya dai na sameta tana kuka dai, ga yaron ma ba'a masa wanka ba, ita dai naga alamar tayi wanka.
Jimmm Aliyu yayi cikin sanyin jiki sosai zuwa can yace to ta karya kuwa?
Gaskiya bana tunanin ta karya, da alamar dai tana cikin damuwa sosai, dan kayan da nakai yanzun ma cewa tayi indawo maka dasu daker tabar su.
Ajiyan zuciya Aliyu ya sauke, sannnan yace, aunty dan Allah kimin kokari kisata taci abinci, sannan kice mata ta kwantar da hankalin ta, Ina nan bazan tafi ba harsai mun samu mafita, da yardan Allah, ta kwantar da hankalin ta Ina tare da ita.
Daga idi har matarsa cike da tausayawa suke kallon Aliyu, hakika shima cikin damuwa yake, ruwa matar malam Idi tasa taiwa yaron wanka sannan ta nadeshi da nufin idan ta mayar dashi zata canza masa kaya cikin Wanda takai yanzun.
Aliyu bebar gidan ba harsaida ya tabbatar Aysha taci abinci sannan yabawa matar idi kudi yace ta dinga lekata akai akai abun da babu acikin kayan asaya idan ana bukatar wani abu Kuma amasa mgn.
Ranar da Aysha tayi kwana 4 haihuwa ranar ce ta kasance ranar da za'a shiga kotu, misalin 8:00am Aliyu ya gama shiryawa tsaf cikin manyan kaya shadda ce wadda ta amsa sunanta, sosai ta karbesa matuka yayi kyau sannan ya daura hula, baka taba kallon sa kace baida iyali agida sabo da kwarjinin sa, Aliyu kyakyawa ne na gaske hasken fata ne kadai beda ita, dogone me dogon hanci uwa uba iya daukan wanka, Dan koga yasa kaya saika dauka ya shirya yin gayune Koda kuwa cikin damuwa yayi ta.
Afalo yacidda Innawo tana tana fadin, kawun ka yace daga can zai wuce nikuma Ina nan zuwa.
Gyada Kai yayi sannan ya fice agidan.
Cike harabar kotun yake da mutane, Babban kotune da ake shari'a kala kala, ganin ba'a fara shiga kotun ba ya nemi guri ya zauna, bega wani daga cikin yan gidansu Aysha ba, hakama kawun nansa basu zoba, zuwa can ya hango Umma da gayyan yaranta sun sakko daga mota saidai babu Aysha acikin su, balakin kosawa da yayi yaga Aysha yasashi Jin hankalin sa ya fara tashi.
Zuwa can Hankalinsa ya koma gun Innawo ganinta tare da Ummin da abun yai matukar bashi mamaki, zuwa wannan lokaci bakin babban kotun cike yake da dan mutum, saidai har wannan lokacin bega Aysha ba.
Duk inda zai kallah ya kalla Amman babu ita, daga can ya hangi wata mota ta faka, wani mutumi yaka ya fito dattijo ya zagayo ya bude kofar motar, Aysha yaga ta sako kafa tana rungume da yaron a hannunta, saidai bata iya dago kanta harta fara takowa tana boye sukanta da hijjabinta, can gefen su Umma ta koma ta rakube yayin da Daddyn ta ta Isa gurin su Umma.
Tunda ta sako kafarta kasa Ummi take mata kallon tsana tare dabita ita da dan nata da kallon sosai takejin tsanar Ayaha ita da abun da ta haifa har cikin kokon ranta.
Shikuwa Aliyu, tunda Aysha ta zauna kallonta yake yi, yadda ta takure sosai ita daya agefe yaji beson hakan dan haka ya mike ya fara takawo kai tsaye yake ratsa mutane har ya Isa gurinta fuskanta yana daga cikin hijjabi.
Tsaye yayi akanta ya kalleta ya kalli yaron yayin da duk idon mutane ya koma kansu.
Umma kuwa wani irin tafarfasa zuciyarta keyi, hakama maman Ayaha gaba daya jitake ta tsana Aliyu hukunci me nauyin gaske take son amasa wadda zai raina kansa, gaba daya yaran Umma hakalin sune ya tashi yayin da suke ganin yaje ne ya dada hure mata kunne ta basu kunya.
Sukuwa jamar dake gurin waddan suka San abun dake faruwa mamaki sukeyi sabo yadda suka kula kamar Aliyun na nuna kulawan sa akan dan dayaki karba dan ganin ya mika hannun sa ya gyara ma jaririn hular dake kansa.
Da yawa mutanen dake gurin kosawa sukayi ashiga kotun ciki harda iyalan gidajen guda biyu domin duk kusawa sukayi ya tashi daga gaban Aysha.
Shikuwa Aliyu tsaye yake akanta yake fadin, " malama ki bude fuskarki, ke kike karawa kanki damuwa da kanki, kece ma zaki jawo mutane su kalleki, da an ganki anga mara gaskiya, dan Allah ki nutsu sosai karkije kimin shirme, inba kinsan bazaki iya mgn ba kiyi shiru kawai.
Batare data bude idontaba tace, " ai dole kace nayi shiru tunda kanson ka barni da yaron.
Kawar da kansa yayi sannan ya juyo ya kalleta tana kudundune da fuska yace, " eh zan barki da yaron ne amman ai nine ubanshi.
Shikenan naji bakomai jeka.
Bazan tafiba saikin tashi kin goya yaron nan, kina rufe fuka saikin je kin yadda shi?
Wlh bazan goya shi ba, Kai ka amsa ka goya mana.
Kawar da kansa yayi tare da cizon lebensa yace, " badan wani dalili guda daya ba Dana baki mamaki"
Kuka Aysha tafara harda shasheka adaidai lokacin da aka fara shiga cikin kotu, cikin sauri ya bi ta bayanta tare dasa hannun sa akanta yaja hijjabin baya fuskarta ta bayyana sannan ya wuce ya shiga cikin kotun......
*🕳️ BA'KAR FURA🕳️*
_A true life story_
*Na*
_Fadeela Lamido_
PEN WRITERS ASSOCIATION✍️
Episode 50- 51
Ahankali akai ta shigowa har aka cika kotun makil da jama'a.
Bayan kowa ya nutsu kotun yayi tsinta yayin da aka shiga kiran kararrakin.
Shari'a biyar akayi sannan aka karanto Karan su Aliyu.
Sosai gaban Innawo Dana Ummi ya buga Jin yadda aka fadi karan.
Hajiya Umma ke Karan Aliyu Moh'd Bello akan cewa yayiwa jikarta ciki ya Kuma ki amsan d'an.
Kotu ce ta bukaci ganin Aliyu Muh'd agaban ta.
Wani irin mikewa yayi cike da kwarin guiwa ya kamo hanya yana me cire gilashin idonsa ya maida cikin aljihu sannan ya Isa inda ya dace ya tsaya ya tsaya.
Bayan Aliyu ya tsaya agaban kotu sannan aka bukaci ganin Umma, sosai mutane suke mamakin Aliyu domin daka ganin shi babu alamar lalacewa ko rashin gaskiya a tattare dashi, daka ganshi kaga cikakken mutum me mutunci, dan haka dayawan mutane suka shiga mamaki, gashi ance yayima yariya ciki yakuma ki amsan d'an, gashi Kuma cike da kwarin guiwa.
Fitowa Umma, tayi ta tsaya, yayin da aka bukaci ta maimaita abun da take karansa akai.
Tama kallon Aliyu da nuna kwarewa asurutu Umma tace, "toh wannan yaro dai gashi Aliyu ya azabtar Dani arayuwuta, wato tun Ayaha na kankanuwarta ya fara lalatata, tare da hure mata kunne ta guje mu, nayi, nayi, ba yadda banyi ba akan ya rabommun da jika, bayan na dauki duk matakin dazan iya dauka yaki bari, gurin 'yan sanda ne, kofar sarki, har kotu munje daga karshe uwarsa ta dauke shi nan ta maidashi Nigeria, shekara biyar kenan da tafiyarsa, duk na saki jiki bekasar Ashe, Ashe yana lallabowa yana amfani da ita, kawai sai ganin ta mukayi da ciki, dan haka nake rokon kotu data bima jikata Aysha hakkin ta na rayuwarta daya lalata mata.
Da yawan mutane kallon su suka mayar kan Aliyu har yanzun yana tsaye idonsa akan Umma sosai yake Jin haushin Umma cikin ransa.
Alkalin ne yace akwai Aysha acikin kotu??
Eh, ranka ya dade, juyawa Umma tayi tana nuna Aysha, yayin da Aysha ta mike, Aunty Murja ce ta amsa yaron, sannan ta fito cikin sunkuyar dakai har ta Isa gaban kotun bata iya dago fuskanta ba.
Alkalin ne ya kalli ta ya cire gilashin idon sa cikin tare gida sosai alamar babu wasa ya kalli Aliyu, gyaran murya yayi sannan yace, malam Aliyu kaji abun da Hajiya Umma take zargin ka dasu?, Hane ko kuwa kana da abun da zakace?
Ina dashi ranka ya dade, duk abun da ta fada ba haka suke ba.
Uwarka ce take karya mara kunya, kana nufin ni makarya......
Tsawan da Alkalin ya buga mata ya sata Ummata tai saurin rufe bakinta batare data shirya, ido ta zubawa Alkalin Jin irin tsawan da ya buga sannan yaci gaba da cewa karki sake yin mgn batare da an bukaceta daga kareki ba, nan ba filin yaki bane.
Kar me karatu ya manta duk cikin harcen filatanci ne suke mgnr.
Maida hankalin yayi kan Aliyu tare da daukan alkalamin rubutun sa sannan yace Ina sauraron Aliyu.
Awancen lokacin da Aysha take shigowa gidanmu karamar yariya ce da mata wuce shekara 13 zuwa 14 ba, Kuma karatu ke kawuta, dalilin tana samun inawa kanwata karatu take zuwa Ina masu tare, Kuma babu wata alaka da muke da ita nida Aysha bayan ta karatun, banta nementa da wani abun na iskanci ba iyaka dai inmata karatu ta wuce gida, gata Kuma a tambayeta, na taba nemanta da iskanci?
Kowa hankalin sa ya ya mayar kan Aysha dake hawaye yayin da taji an sake jeho mata irin tambayan da Aliyu yayi, kanta ta girgiza tare da fadin a'a.
Rubutu Alkalin yayi sannan ya maida kallon shi ga Aliyu yace, " amaganganun da Hajiya Umma tayi tafada cewa, tata nuna bata son kula jikarta da kake, wadda har tafada cewa anje police station, anje Kofar sarki, harta Kara da cewa anjema kotu, meyasa baka rabu da yariyar ba tunda ka fahimci danginta basa so Kuma Kai kafi Aysha hankali?
Ranka ya dade nashaku da ita sosai, Kuma haka nan Allah yasamin tausayinta acikin Raina, a wacen lokacin idan bangantaba banajin dadi, duk da cewa babu wata alaka da muke da ita bayaga karatu kawai.
Jinjina Kai Alkalin yayi sannan yace muje ga zargin Hajiya Umma na gama, munji Umma tace bayan faruwar duk waddan abubuwan mahaifiyar ka ta turaka Nigeria da zama, amman saika shigowa ciki Sirri, kana kwatsam sai tsintar Aysha sukayi da ciki.
Kawar dakai Aliyu yayi sannan yace, ranka ya dade ba haka bane, tunda mahaifiyarta ta turani Nigeria shekara biyar kenan zan iya rantsuwa da alqur'ani me girma cewa banta dawowa kasar nan ba sai wannan karon.
Sosai cikin Aysha ya luri ruwa, dama cikin hawaye take duk jikinta taji babu karfi, ji take kamar ta zube akasa domin kafa fuwanta rawa suke.
Cike da mamaki Alkalin ya maida idonsa kan Aysha yana kallon inda take zubar da hawaye yace, " Aysha Ina kika samu ciki?, Aliyu yace tun bayan tafiyan shi shekara biyar kenan be dawo ba, ki saki jikin ki kiyi mgn, anan muna kokarin kwato miki hakkin ki ne"
Hawaye kawai Ayaha take zubarwa dataga ma idon mutane yayi cah akanta saita fara shashshrkar kuka.
Sosai hankalin Aliyu ya tashi ganin inda take kuka, dan haka ya daga hannun sa alamar yana da mgn.
Kallonsa Alkalin yayi tare da bashi dama.
Ranka ya dade bayan nakwashe tsayon waddan shekarun na fahimci inason Aysha, kullum bani da tunani sai nata, har nafara kokarin inason indawo in nemi auren ta, saidai Ina tunanin gidan su da gidan mu, akarshe na yanke shawaran dawowa, saidai yanayin aiki na bansamu daman ba, kawai wata rana na dawo gidan mu na samu Aysha akofar gidan....
Wanni gidan??, Alkalin ya tambaya yayin da mutane suka Kara baza ido.
Gidan mahaifina a Kano Nigeria.
Cikin tsananin mamaki kowa ya Kara baza kunnen sa yayin da Umma tabi Aysha da kallon cikin ranta take fadin kaji tsinan ne matsiyaci.
Itako Aysha kuka kawai take.
Taya Ayaha tasan gidan ku a Nigeria bayan kun rabo da Aysha tana da shekara 14 kamar yadda kaima da bakinka ka fada?
Ranka ya dade akwai adireshin Dana bata na gidan mahaifina, Alokacin da zanyi tafiyar nazo nai mata sallama, ganin tana kuka nai mata alkarin idan aurenta ya tashi ta rubuta ta aiko min zanzo, dan haka na bata adireshin da zata aiko sakon, wadda dashi tayi amfani tazo gidan mu.
Mamaki jama'a suka shiga yiyin da alkalin ajuya ya kalli Aysha yace, Aysha kinji abun da Aliyu yace, " da gaske ne kinje Nigeria?
Kara kudundunewa Aysha tayi, sheshekar kukanta kawai take, yayin da Umma ta daga hannunta.
Dama aka bata, Dan haka ta fito tace, " ranka ya dade, karya yake, ni jikata babu inda take zuwa, daga makaranta tana gida bata tabayin kwana daya ma bata gida ba, dan haka babu inda za'ayi Aysha ta tafi har Nigeria batare da sanin mu ba, Kuma Aliyu ya riga ya amsa mana ba sau daya ba cewa dan nasa ne, yanzun Kuma yanata mgn Kashi Kashi, yace zai rantse be taba zuwa ba, yanzun Kuma yace Aysha ce ta bishi.
Kallon Ayaha dake kuka Alkalin yayi sannan ya kalli Aliyu yace, "Malam Aliyu Ayaha acikin rana daya taje Nigeria ta dawo?
A'a tayi kwanakin da suka Kai wata uku da kwana sha biyu, kuma ta gaya min cewa gidan mahaifinta aka turata hutu.
Sosai jama'ar gurin suka zaro ido, ciki harda Umma da tai saurin kallon Daddy Aysha, yayin da Aliyu yacigaba da cewa, " nayi kokarin nayi mata fada wancen lokacin sannan na kaita cikin gidan mu wajen kannaina ta zauna, tafiya tsakanin Cameroon da Nigeria ba karamin tafiya bace dan haka nafara neman ranar da zan iya kawota gida da kaina nakuma nemi aurenta, sabo da Ina sonta, Kuma nasan itama soyayya ce ta kawota da rauni irin na mace, amman yanayin aikina be bani dama ba, ganin lokaci nata tafiya gashi wata tafiya harna tsayon wata Uku ta taso min na yanke shawaran sakata amota ta dawo gida, bayan na fito da ita daga gidan mahaifina ne Kuma awannan ranar garin sallama tsautayi yasani na kusanceta, hawayen gefen ido Aliyu ya cire sannan yai saurin ciro gilashin sa ya maida.
Zuwa wannan lokacin dayawa agurin sunyi kuka, shiru kotun yayi tsayon lokaci yayin da alkalin ya sunkuyar da kansa tsayon lokaci sannan ya fara rubutu akan takardan dake gaban sa, zuwa can ya maida kallon sa kan Aysha yace, " Aysha abun da Aliyu ya fada haka ne ko kina da jah?
Cikin sauri ta girgiza kanta.
Abun da Aliyu ya fada gaskiya ne??
Eh ta fada ahankali.
Alkalin ne yace, " Ina Hajiya Umma"
Mikewa Umma tayi ta fito sarari.
Kin gamsu da da bayanin Aliyu?
Nasan Aysha taje gidan mahaifinta tayi wanan kwanakin kamar yadda yace inaso naji daka bakin mahaifin ta Aysha taje gidansa ko bata je ba?
Bayan mahaifin Aysha ya fitone ya tabbatarwa kotu da cewa, tun wani zuwa da Aysha tayi ta kwana daya bata sake zuwa gidansa ta kwana ba.
Sosai Innawo da ma duk wadda yake cikin kotun yai mamaki.
Cike da tsabar takaici da kunya Umma tace toh shikenan, yanzun ya masa yaron yaje ya rainesa ahannun shi.
Rubuce rubuce Alkalin yayi sannan yace, " Aliyu yanzun ka amsa cewa dan da Aysha ta haifa naka ne?
Ranka ya dade naw ne"
Toh Hajiya Umma ta bukaci daka amsa d'an ka,
Ranka ya dade ni bazan amsa shi ba.
Meye dalilin cewa baza amsa ba bayan ka tabbatarwa kotu dan naka ne?
Nawa ne, amman banaso bazan amsa ba, na bar masu.
A'a toh tsaya,, acikin biyu dole zaka zabi daya, mata ko d'an??
Kai tsaye Aliyu yace mata
Ciki da mamaki Alkalin yayi akbara, sannan yace wadda ya dauki uwa ai ya dau d'anta.
Rubuce rubuce yayi sannan ya dago yace, yaci ace iyayen Aysha dana Aliyu tun ashekarun baya sun ma abun kallo mekyau su masu aure, da ace tunda akaga sunki rabuwa an masu aure da an haifi dan sunnah, amma dake iyaye sun turje gashi abin da ba'aso ya faru, duk da cewa kuna ganin kun raba tsananin su rabuwa me nisa, tsakanin Cameroon da Nigeria, amman dake rabon ya rantse saida Aysha tayi takkakiya tabishi Nigeria aka dawo gida da tsaraba, wannan ya isheku ishara, ku duba tsayon shekarun amman sabo da soyayya nacinta arai bata manta ba, da wannan nake Kira ga iyayen Aysha dana Aliyu da aje a gaggauta daura masu aure.
Cikin sauri Umma tace ranka ya dade, Ina rokon wannan kotu me adalci datamin adalci kamar yadda ta saba, Aliyu ya karbi danshi kawai ya tafi, domin bana fatan hada zuri'armu da tasu.
Kokarin maga Ummi keyi yayin da Innawo ta ke girgiza mata Kai dan haka ta fasa mgn saidai fuskanta na cike da fushi.
Gyaran murya Alkalin yayi sannan yace, Hajiya Umma wannan shine adalcin, be kamata ace zuwa yanzun kuna jayya ba, Kuma Aliyu bashi da da aibun da za'a hana shi aure auren ta, Kinga na farko yana da sana'a, sannan duk mutumin da zaiyi abu laifi ya amsa cewa eh yayi Kai tsaye da karshe ya nemi abashi auren ta, sannan ita kanta Aysha auren shine mutuncinta, Kuma Aliyu yana son Aysha haka itama Aysha alamu sun nuna tanason Aliyu har yanzun dan haka ku ajeye wani son rai naku agefe, am Ina fatan mahaifin Aysha yana cikin wannan kotun?
Amsawa Daddy yayi sannan ya fito gaba,. Yayin da alkalin ya sake cewa mahaifin Aliyu ba?
Innawo ce tace mahaifin sa ba dan nan bane.
Akwai wadda zai wakilce sa?
Alhaji Umar Innawo ta nuna baysn ya fito Alkalin yace, kotu zata daura auren nan take bisaga wasu dalilai.
Aliyu zaka bada Sadakin Aysha"
Cikin sauri yasa hannun sa duk ya tattaba aljihun sa tare da fadin, " ranka ya dade na mance ban fito da kudi ba"
Alkalin ne ya maida kallon sa ga kotun yana fadin, Aliyu bai fito da kudi ba, akwai wadda zai fanshe shi akotun nan??
Daga can baya wani ya daga hannu, mikewa yayi yayin da Aliyu yaga abukin sa wadda sukayi karatun tare anan Cameroon ne ke fadin ranka ya dade Jaka biyar ce a hannu na.
Juyawa Alhakalin yayi ya kalli Aysha yace,
toke Aysha jaka biyar dinan ta Isa amiki Sadaki dashi?
Batare data dago ba tace, eh
Abokin Aliyu aka umarta daya mikawa Aliyu kudin bayan ya bashi shikuma ya Isa ya mikawa Aysha, nan take alkali yadaura masu aure acikin kotun
Haka haka aka fito kotun yayin da jama'a keta mikawa Aliyu hannu, Umma kuwa kamar iska tabar kotun ita da iyalanta, tuni suka mikawa Aysha yaron.
Mahaifin Aysha ne ya dauketa ita da danta domin mayar dasu gida, shiko Aliyu motar Ahaji Umar suka hau gaba daya har Ummi, sai dai tun da Aliyu ya shiga motar farin cikin sa ya yaye domin Jin Ummi tana raira kuka.
*****
Koda su Aysha suka iya gida tun a gaban Daddy ta su Umma suke zagin Aysha tare dayin Allah wadai da halinta, sosai suka Kara nuna mata tsana da hantara, duk da cewa yau Aysha taji sanyi sosai, gannin yadda Aliyu yai mata hallaci Amman yanzun hankalin ta kara tashi yayi, dukan su rantsuwa suke yi cewa basu ba ita har abadah, mamako ko kallon inda Aysha take batayi barema taji wani kalma daga gareta.
Itako Ummi babu laifi tunda suka dawo kotu tana amsa gaisuwar Aliyu, amman bata son aure Kuma ta fada har agaban Aliyu cewa yaje yayi gantalelan aure.
Yayin da danginta ke nunar mata da cewa wannan shine mafita dan haka tai hakuri dashi.
Bayan Sati daya Aliyu ya Sami Innawo adakin ta zama yayi gefenta, tare da mata sannu, zuwa can yace, " Innawo inaganin gobe zamu wuce fah, yaya za'ayi ne??
Batare data kalleshi ba tace, " Kai dawa?"
Aysha mana.
Au daman haka ake yi?, kawai saikaje kace mata fito mu tafi? ko gobe zamu tafi, aika bari iyayenta su shirya ko? Saurin me kake yi?, yariyar da ma jego take yi.
Ni Innawo bawai zancen haka bane, akwai tafiyar da zanyi banason na wuce gobe anan kuma bana son natafi na barsu, sannan ni banason su bata koman su, da ita kadai zan tafi
Toh nidai nace maka ka bari tukuna, yanxun kaje kayi abun dake gaban ka, kasa ranar da zaka dawo ka tafi da ita, ni zan sanar masu ranar kaza zakazo ka dauki matar ka.
Kawar dakai yayi tare da hade fuska sosai yace, Innawo nifa gaskiya nafi son intafi dasu kawai.
Yanzun kai Aliyu saika iya daukan Aysha da yaron nan ka kaima Baffan ka?
Sosai yaji gaban shi ya fadin, batare da ya shirya ba yace, ni karyar da namasa kadai ke damuna, lokacin da Aysha tazo ce mishi nayi matar aboki na ce ita.
Jimmm Innawo tayi, sannan tace toh Ina baka shawara kabari ya samu lbrn kafin kaje masa dasu, yanxun idan kaje ta turo min Ruqayya .
Tununani ya shiga akan mgnr Umma, badan ransa yaso ba ya hakura da haka, dan haka da daddare ya nufi gidan su Aysha domin yi mata sallama dan asubanci zaiyi gobe........
*🕳️ BA'KAR FURA🕳️*
_A true life story_
*Na*
_Fadeela Lamido_
PEN WRITERS ASSOCIATION✍️
Episode 52- 53
Kanan kaya yake sanye dasu yayin yayi sallama zauren gidan su Ayaha.
Daukan murya Maman Sadam tayi dan haka tayi Jim tare da kanne idonta guda daya cike da masifa.
Ji tayi an sake rafka wata dan haka tai saurin zama kan kujerar dake bakin kitchen din tana fadin. " Umma ana mgn"
Umma ce ta fito tana fadin Yaya aka yi?
Nuni maman Sadam tai mata da kofar gidan dan haka ta fara fadin, " waye nan?"
Nine"
Sarai ta dauki murya amman saitace Kai wa?
Aliyu ne, ya fada kansa tsaye.
Himmm lallai, aifa sai Aliyun, Ina kasan inda take, ita jakar dakazo nema, ai sai kazo ka wuce.
Mmn Sadam ce tace, " yazo ya wuce fah kika ce?, ai saidai tafito su tafi, gidan Ubanshi ne da zai shigo?
Magana Umma tai mata kasa kasa adaidai lokacin da Aliyu ya sawo kai cikin gidan.
Kasa yayi da murya yace Ina wunin ku?
Wani irin kallon suka masa tare da kawar dakai batare da sun amsa ba.
Sallama ya sakeyi abakin kofar can kasa yaji ta amsa dan haka ya daga labulen tare dasa kansa ciki.
Kokarin sauke kafarta take yi da alama ta fara bacci, saidai gaba daya fuskarta ta kunbure , zama yayi a kujeran dake gefen gadon yayin da Aysha ta gyara zamanta batare data kalleshi ba tace Ina wuni?
Idon shi akanta yana zuba murmushi yace lafiya Lau ya jiki?
Alhamdulillah"
Lumshe ido yayi sannan yace, " ya khalifa?"
Cikin sauri ta kawar dakanta tare da turo baki ta nunashi da hannun tace gashi nan"
Murmushi sa ya fadada, ganin inda tayi sannan yace idon shi biyu ne?
Bacci yake, tafada har yanxun bakinta azunbure.
Ido ya zuba mata tsayon lokaci sannan yace, Aysha duk kin canza, sannan na kula kinajin haushin yaron nan.
Kuka ta fashe dashi sosai harsu Umma dake tsakar gida suna iya jin sheshekar kukanta, cikin matsanancin kukan tace, banfayi aure ba na haifeshi yaya Aliyu??😭😭
Lumshe ido yayi sannan ya bude su akanta tare da fadin, " aiba lefin yaron bane shi babu ruwansa fah Aysha, kibar yi masa haka kinji.
Juyawa tayi ta dan kalli yaron kadan sannan tace, " wlh banson ganin shi, inajin bakin ciki tare da Dana sani idan na kallesa.
Dana sani ai keya ce, gaba ya gamata mu fuskanta Aysha, sanda abun ya faru naji bakin ciki har nakan kasa bacci tsayon lokacin, ammman daga baya nagane babu yadda zanyi domin dai me aukuwa ta riga data auku, ni abun da nake so dake, ki saki jikin ki kibar takura kanki, wannan kaddaramu ce, Allah yasani Ina iyaka kokarina domin in gujewa zinah, nasani wannan jarabawa ce shiyasa ake son bayan ka tsare kankan ka kara da addu'a mugun gani da mugun ji Allah ya nisanta mu dasu, duk wadda yace shine toh bashi bane, wannan be wuce kan kowa ba, dan abun ba wayaun ka bane ba dibarar ka bace, dan da ace abun dibara ce da danasaki amota bazaki dawo ba.
Cikin sauri ta juyo ta kalleshi cikin idon sannan tace ai da na dawo ba abun da ya dawo dani kenan ba😏 kawai ji nayi kamar narabu dakai kenan har abada.
Murmushi yayi tare da fadin, yauwa Aysha ai nafison bakin ki ya bude, nasani, nasan ba abun da ya dawo dake kenan ba, nine kika dawo kika samu cikin wani yanayi, ai laifin nawa ne, yanzun dai kiyi hakuri abun da ya faru ya riga ya faru shikuma yaron ba laifin sa bane dan haka dan Allah ki kaunace shi.
Shikenan kowa kallon yar iska yake min😭😭😭
A'a Sam, muba Yan iska bane, ki saki jikin ki, kibar takura kanki, mikewa yayi yazo ya durkusa abakin gadon yana kallon Fuskan yaron tare da fadin zo ki gani kama yake dani Sak.
Aina gani.
Eh juyo ki kara gani.
Sunkuyar da kanta tayi tare da nuna bazata yi abun da ya bukata dim ba.
Mikewa yayi ya tura hannun sa cikin aljihun sa duk biyu, kallon ta yayi yana tunanin ta yadda zai gaya mata gobe zai wuce, gaba daya ya rasa da wacce kalma zai fara, agogon hannun sa ya kallah sha daya da kwata yagani dan haka ya maida kallon shi kanta.
Aysha ki fara shiri daga yau, da zaran nadawo kwana daya zanyi sai mu wuce......
Bekai ka rufe baki ba tace, "yaushe zaka tafi??
Gobe da safe.
Cikin sauri ta juya gaba daya ta bashi gadon bayanta tare da wasa da yatsunta.
Sarai yasan me take nufin domin tun bayau ba ya fahimci halinta, ahankali yace, Ayaha?
Kin juyowa tayi yayin da ya farajin sheshekar kukanta.
Kuka kike yi??
Tunda fa muka dawo kotun nan, gidan nan babu memin mgn Ya Aliyu, basa bani abinci yadda suke nuna bakin cikin su har gara kafin aje kotun, yanzun ko ruwan wanka basa bani bare ma suma yaron, Ina rasa inda zansa kaina Yaya Aliyu 😭😭😭
Sosai hankalin Aliyu ya tashi matuka, nan danan launin idon sa ya canza daga fari zuwa jah, cikin wata irin murya me ciki da damuwa yace, ke Kuma har yanzun taurin kanki na nan ko?, baxaki iya basu hakuri ba?
Wlh ya Aliyu Ina basu, daga ranar da sukasan Ina da ciki haryau cikin basu hakuri nake amman abun Kara tsanta yake yi.
Jimmmmm yayi zuwa can yace kicigaba da basu hakuri kinji, naso inje daku Innawo tace im bari tukuna, bazan dade ba zan dawo, Innawo zata dinga leko ku, Husna ma haka.
Ahankali tace toh tare da matso hawaye.
Ganin yana shirin juyawa tace, " Yaya Aliyu?"
Juyowa yayi tare da takowa gabanta yace, Na'am Aysha?
Shekara nawa zakayi kafin ka dawo??
Aysha wanni irin shekara Kuma?
Waccen karon ma haka kace wata uku zakaxo to wannan karon Kuma sai Naga bakama sa lokaci ba.
Murmushi yayi kadan sannan yace, wancen karon Ina sane naki zuwa ai, saboda jikina nabani kina da ciki, insha Allahu bazan wuce sati Uku zuwa hudu ba, ki zama cikin shiri kawai, hannun sa ya mika ya dafa kafanta tare da dagota ta mike tsaye, kokarin hadata da jikinsa yake idon sa alumshe.
Cikin sauri Aysha tasa hannunta duk biyun ta ture sa jikinta na matsanan cin rawa, yadda take danno kirjinsa da matsanancin karfi yasa ya bude idon sa alokacin da take ture hannun sa dake kafadarta da matsanancin karfi.
Sakinta yayi da tarin mamaki a tattare dashi, ba turesan ke bashi mamaki ba, jikin ta daya dauki rawa yai matukar bashi mamaki dan haka yace, " menene haka?"
Tasallake yaron tayi can bayan shi ta zauna tana fadin kaje toh.
Sakko muyi sallama.
Yaya Aliyu dare yayi"
Agogon sa ya kallah sha biyu saura dan haka yayi saurin sauka hannun sa a aljihu ya ciro kudi masu yawa ya aje mata tare da fadin nabarku lafiya.
Bata iya cewa komai ba harya fice.
Shikuwa Aliyu lokacin babu kowa alayin ya fito ya nufi gida.
Washegari da asuba yayi sallama dasu Ummi ya kama hanya.
*******
Ranar da Aliyu yayi kwana biyu da tafiya Aysha ta fito ta debi abinci a kitchen kamar yadda ta saba, tun bayan fitowanta kotu saidai ita ta fita ta diba, ruwan wankama saidai ta daura tayi sannan ta juye na yaron ta masa, tun bata iya ba har tazo ta koya.
Matar idi ce kawai kan taimaka mata wani lokacin tana tafiya dashi ne tai masa sannan ta dawo dashi.
Maman Sadam ce ta shigo ita da Umma ganin Aysha na kokarin shiga dakin Maman Sadam din tace, " Ke Aysha?, Ashe Aliyu ya koma?
Sororo tayi ahankali ta daga kanta.
Caf dijam, lallai baki da hakali Aysha, tunda kika bari ya tafi ya barki sai a lahira keda ki Kuma ganin shi, badai kince ke yar iska bace?, yanzun kika fara gani.
Umma ce tace ai saidai ta Kuma kwasan kafa ta bishi Amman bazai dawo ba.
To meya hana ya daukeki ya kaiki gun uwarsa idan ya cika son ki yake, wlh wuya yanzun kika fara gani, Koda yake kinsan hanyar Nigeria sabo da iskanci nacikin kika kama hanya kasar da ko uwarki bata taba zuwa ba.
Mman Sadam ce tace, ai yanzun ko ta koma baxa ta ganshi ba dan wlh bazai tsaya inda zata kanshi ba, ni wlh badan uwarta ba da koranta akayi Dan wannan yariyar za'a iya hada baki da ita duk a kashe mu.
Umma ce tace, nima ai abun dake bani mamaki kenan, inda ace 'yatace da tuni nakoreta amman Naga kamar uwarta tausayin ta take.
Daga cikin dakin taji Muryan Mama na fadin, Umma ba haka bane, duk hukuncin da kuka yanke akan Aysha daidai ne agurina.
A'a nidai tunda kinbarta ta zauna acikin gidan nan, bayan ta zubar Mana da mutunci ta nunawa duniya muba komai bane, taita zama amman bana Kara bata abincina, dan ba wannan gwansamemen katon bane ya kawo min, karki sake tabamin kayana Aysha kinji na gaya miki, gida dai akwai kason uwarki aciki kita zama, amman wlh ko tukunyata kika taba sainaci uwarki.
Cikin zubar hawaye Aysha tace, " Dan Allah kuyi hakuri ku yafe min, wlh nayi nadama, idan nasake ku dauki kowanni irin mataki akaina....
Ai tunda kika amsa Sadakin Jikan Innawo kin fita daga cikin zuri'armu har abada Ayaha, dani da yarana kisa aranki haduwa ce irin ta titi.
Cike da hawaye Aysha ta shige dakinta wannan lokacin bata iya kwatanta bakin cikin da takeji, wani abun da yake bata mamaki mama bata bari ko su hada ido da ita Kuma yanzun tafi zama adaki.
Kamar yadda Umma da maman Sadam suka fada, tun daga wannan ranar bama abarin abincin a inda zata gani bare ta diba, haka Kuma ko tukunya bata gani bare ta daura ruwan da kanta, kwana biyu tayi batayi wanka ba hakama yaron, dan haka yau tun safe yake kuka, ita kanta jikinta yai mata tsami, misalin karfe daya na rana ta leka dakin Umma lokacin mama tana zaune bisa sallaya, cike sauri Mama ta kawar da kanta yayin da Aysha ta kalli Umma tace, " Umma dan Allah kibani aron tukunya yau kwana na biyu banyi wanka ba"
Inbaki aron tukunya?, Mena gaya miki?
Umma nace kiyi hakuri dan Allah.
Lallai kina wasa dani, da ta wuce Kuma baZata dawo ba Aysha, daidai da garwashin rushi kika tamamin Allah ya Isa.
Zuwa wannan lokacin zuciyar Aysha ta fara tafarfasa take dan haka ta juya tabar gidan batare da tasan inda take saka kafarta ba.
Tunawa tayi da yaron, haka nan taji gabanta ya fadi, bata taba jinsa aranta kamar yau ba, cikin sauri ta shiga gidan iro, halin da take ciki ta gayawa matar iro cikin tsananin tausayawa ta bata ruwan zafi cike da bokiti, cikin sauri ta koma gida saidai tun daga zaure takejin ihun yaron a tsakiyar gidan ta aje bokintin ta shiga dakin, Innalillahi wa inna ilaihir raju'un ta fada lokacin data hangeshi akasa.
Cikin sauri ta daukeshi tana jijjigawa, tsananin tausayin yaron ne ya dirar mata lokaci kuda daker yai shiru sannan tasa masa nono a baki, zuwa can yayi gyatsa dan haka ta masa shin fida akasa sannan tai sauri tayi wanka da dawo, bayan ta shirya a gurguje tai masa wankan ta shirya sa.
Tun daga wannan lokacin saidai taje gidan iro ta roko ruwa ranar da basu dashi kuwa rushi matar iro take bata ta tsuna na tsayon lokaci, sannan ta bata ruwan zafin da zata sha, da Wanda zatama yaron wanka, yaron ko yanayin kwana biyu zuwa uku babu wanka saboda itama matar iro tsoron Umma take ji.
Ahaka har sati hudun da Aliyu ya fada suka cika, gashi komai nata ya kare wadda ya bar mata, ranar da ya cika sati biyar da tafiya Husna da Innawo sukazo da ledoji kayayyakin da suka mata sayayya, awulakanci Umma da Maman Sadam suka amsa gaisuwar su.
Sosai sukaga Ayaha ta fige ta lalace duk alamu ya nuna azabtar da ita sukeyi, yaron ma daganin sa babu wani cikkiyar kulawa a tattare dasu gaba daya, sosai Innawo ta tausaya mata har suka koma gida tanajin damuwan Halin data sameta aciki.
Ranar da Aliyu ya cika sati na shidda Aysha ta tsinta kanta da tsananin haushin sa ganin idan yai alkawari baya cikawa, fushi tayi dashi sosai tare da rasa inda ya dusa, tuni taso ta gudu tabar gidan malam idi da matarsa suka hanata, dan haka yanxun takejin yakai lokacin da zata gudu tabar garin batare da sanin kowa ba barema a hanata.
Cikin dare tai niyayyar barin gidan dan haka tun yamma ta shirya kalifa taimasa wanka bayan kwana uku daya dauka babu wankan, goyesa tayi ram abayanta yayin da zuwa yanzun ya cika bayan nata.
******
Momy gaskiya garin ku da nisa, har yanzun bamu Isa gidan Ummin Uncle Aliyu ba.
Da nisa Sadiya shiyasa kikaga Ina dadewa banzo ba.....
*🕳️ BA'KAR FURA🕳️