Chapter 1
BA LABARI
By
Fadeela Lamido
EXQUISITE WRITER'S FORUM.
PAGE 1 -2
Bismillahir Rahamanir Rahim.
Manyan motocine guda guma zafafa ke shigowa cikin unguwar, banda kyalli babu abun da motocin keyi yayin da suke tafe cikin nutsuwa.
Sannu ahankali take tafiya cikin babban hijjabinta tare nikaf dinta baki yayin da hijabinta ya kasancen kalar sararin samaniya, karan motocin da takeji ne yai masifar gigitata, yayin da yai sanadin gushewar hankalinta, diriricewa ne da dimuwa ya same ta lokaci guda wadda ya haifar mata da rawan jiki tare da gushewan hankali harya kaita da curewa guri guda.
Hayaniya ne ke tashi bisa kanta, cikin yanayin firgici take jin muryan maza saman kanta suna fadin, " sannu ba dai kiji ciwoba ko?"
Wata muryan taji cikin fada ana fadin, aigara taji ciwon ko Yayane, tunda musamman ta shigo da tsuguna saboda tanason tajawa mutane bala'i toh Allah ya fiki, idan mutuwa kike nema dan ubanki kije ki tari tanka, dallah tashi ki bamu waje, cikin tsawa yake mgnr, kokarin tashi take ta hangi wasu karafuna wadda ke zama wa mara lafiya kafa suna tahowa gare ta.
Sandunan karfin tabi da kallo batare da tabi tsawon sadar ba, lumshe ido tayi alokacin data hangi wata kyakyawar kafa fara sol cikin cikin wani tsandanden takalmi, kallonta ta maida Kan daya kafar wadda sai wannan lokacin ta kula da ita, daure take tam da dauri irin na wadda ya samu karaya ko wata mummunan matsala, dan an nade kafar tunda Kan tafinsa har ya wuce kaurin sa.
Yajima tsaye agabanta saidai ta kasa dagowa ta dobe shi, yayin da ta kasa cire idon ta akan daya kafar sa me lafiya, kuma ta kasa mikewa gaba daya.
Ahankali taji yayi gyaran murya kadan, wata irin murya taji me cike da kasaita yana fadi ahankali, " tashi ingani babu wata matsala da ta sameki ko?"
Ko motsi batai ba yayin da idon ta ke iya hangen kafafuwan su, zasu iya kaiwa kimanin mutum ashirin, kuma dukan maza ne cikin kayan alfarma da takalma masu tsada, wani abun Mamaki ada dukkan nin su mgn suke cikin hayaniya, amman wannan me rike da karfin na fitowa gurin yayi tsit.
Kamar daga sama ta sake tsintar irin wannan muryan tana sake fadin, " Ina magana dake ne fah"
Wannan lokacin ma bata tankashi ba yayin da takeji ajikinta kallonta yake saidai ita bazata iya kallon nasa ba.
Ke bakiji ne ana miki magana dan rainin hankali kinyi banza da mutane, tashi ki bamu waje, nasame ki agurin nan takaki zan yi, wani dake can gefe kifadin haka cikin tsawa da hargagi, tsintan muryan mutumin dake tsaye agaban ta tayi Yana cewa, " Magaji bita ahankali"
Bata sakejin muryan wani ba duk suna tsaye yayin da kadan daga cikin su suka koma mota suka zauna.
Kyawawan kafar ta ya zubawa ido sannan ya koma kallon idon ta dake cikin ni'kaf, kasa cire idon nasa yayi har aka dauki tsayon lokaci, sosai idon nata ya burgeshi har baya iya misalta wa, tare da kasa cire idonsa akan nata, acikin ransa yake fadin ban taba ganin idon dayai kyau da ni'kabi kamar wannan idon ba.
Tsayon lokaci suka diba babu me cewa komai, zuwa can taji anbude motar sannan taji ance, Modibo kazo mu tafi dan Allah, muna da abunyi fa, sannan akwai tafiya me tsayo agaban mu.
Ta kanta zamubi ne?, baka ganin ta zauna ahanya?
Tahowa yayi Yana fadi cike da fada ke!! Dallah tashi......
Shiii ka koma ka zauna harsai lokacin data tashi.
Afusace ya juya yayin da gurin ya sakeyin shiru tsayon lakaci.
****
Ahankali ta dafa kasa ta mike batare da ta iya daga ido ta kalli kowa agurin ba ta koma gefen hanya tana karkade hijjabin ta, bayan ta gama ta kara komawa can gefe sosai ta fara tafiya.
Gaba dayan su kallo suka bita dashi sannan suka shiga motar suka fara tafiya.
Koda sukazo saitin ta kallo wadda aka Kira da suna Modibo ya bita dashi, har suka wuce ta yana waigen ta.
Magaji kuwa kallo ya bishi dashi, sosai hakan ya zamar masa bakon al'amari ga Modibo, saida sukai nisa sosai ta yadda ko alamar yariyar basa gani sannan Modibo ya dawo da kansa yana kallon hanyar da suka dosa.
Tafiya me nisa sukayi sannan suka iso wani madaidaicin gida, bayan sun faka motocin su ne suka fara fitowa tare da saurin bude motar da Moddibbo yake.
Cike da kasaita ya sauke kafarsa me lafiya, sannan suka tsayar da sandan karfen bayan ya sako daya kafar, sandar ta shiga tsakanin hakarkarin sa, dakin dake kofar gidan suka nufa mutum biyu ne a bayan sa.
Sallama sukayi bakin kofar yayin da daga cikin dakin aka amsa sallamar tare da fadin, " kun iso kenan, ku shigo sannun ku da zuwa"
Shiga sukayi bayan sun gaisa mutumin dake dakin ya kalli Kafar Modibo yace, " Yaya kafar taka?"
Alhamdulillah ba Kamar daba.
Yauwa haka ake so.
Matsowa mutumin yayi yana kallon kafar Modibo tsayon lokaci sannan yace, " insha Allahu ya kusa zama tarihi, mikewa yayi ya fara hado wasu magunguna tsayon lokaci sannan ya dawo gaban Moddibbo ya zauna, ahankali ya shiga warware nad'in da akama kafar, saidai be gama warewa duk ba ya tsaya ya yana tofa addu'oi tsayon lokaci sannan ya bude wata roba Yana shafawa kafar mgani, bayan ya gama sake nade kafar yayi, yayin da Modibo ke runtse ido.
Sannu yamai yayin da samarin dake gefe suma suke masa sannu, dakai ya amsa, yayin dayai shiru kansa akasa kawai sai zufa ne ke karyo masa.
Tsayon lokaci ya dauka sannan ya dago ya kalli Malamin yace, " Baba maganin Yadikko ya kare, kuma Alhamdulillah tana samun sauki.
Masha Allah, Malamin ya fada sannan ya kara da cewa zan baku wani ku kaimata da yardan Allah zata samu sauki.
Maganin ya hada masu, sannan suka fito cikin girmamawa da mutunta juna.
Yanzun ma d'in rike yake da sandunan karfen dake cikin hakarkarin sa, yayin da mutun biyu ke bayan sa. tun daga ganin fitowan su sauran abokan tafiyar su suka bude motar da Modibo zai shiga, wadda itace ta kasance a tsakiya.
Saidai suna kokarin rabashi da sandunan suka lura hankalinshi baya wajen shiga motar, daya daga ciki ne yabi inda idon Modibo yabi da kallo domin son sanin abun da yaja hankalin sa haka.
Wata yariya yagani tana kokarin bude wani madaidaicin gida da mabudinta a hannun ta, kallon ta yayi sosai, duk da cewa baya ta juya masu, ahankali ya maida idonsa ya kalli Modibo sannan ya sake kallon yariya.
Matukar mamakine ya kamashi, yayin da duk aka gama shiga cikin motar amman Moddibbo tsaye yake.
Modibo muje mana tafiya ce fa me nisa agaban mu.
Lumshe ido yayi sannan ya shigar da kafarsa me lafiya yayin da aka taimaka ya zauna da kyau, adaidai lokacin da yariyar ta gama bude gidan tana kokarin tura kofar Modibo ya kalli wadda ke gefen sa yace, " Magaji ka Kira min yariyar can"
Lumshe ido yayi sannan ya juya cikin azama, beji mamakin jin Modibo yace ai kiranta ba, saidai yadda yake kallon ta abun ya bashi Mamaki.
Kokarin shiga gidan take wadda aka Kira da suna Magaji yace, " ke! kizo ana kiran ki.
Ta cikin nikabi ta juyo kadan ta kalle shi, sannan tasa kai ta nufi dogon zauren nasu.
Ke!! nine nake miki mgn keke tafiya, wanni irin rashin tarbiya ne ke damun ki dahar zan miki mgn ki kalleni ki wuce?
Ko kafin ya rufe baki ta idan shigewa gida, dan haka ransa yai mugun baci sosai zuciyarsa ke masa zafi, afusace ya juya yayin da Modibo cike da kasai ta yace, " metace maka?"
Batace komai ba asali ma kallona tayi ta wuce abun ta.
Juyawa Modibo yayi ya kalli gidan sannan yace, naso inyi mgn da ita kwarai Magaji.
Ba girman ka bane Modibo, bata bata da darajar da zakayi mgn da ita, ni kaina dan dai kawai kai kace inje, har yanzun dai idan taimako zaka bata kabani zan koma nakai mata.
Gidan Modibo ya sake kallo batare da ya cire idon sa agidan ba ya ce muje kawai.
Jin haka Magaji yayiwa driver Umarni batare da wani bata lokaci ba motar ta fara kokarin tashi, hakan ne yabawa Motocin dake gaba damar fara tafiya sannan ta Modibo ta tashi yayin da wasu kebin bayan tasu.
Modibo kuwa babu abun da idonsa da zuciyar sa ke iya hango masa sai idon ta wadda ya hanga cikin ni'kabi tare da farar fatanta dake gefen idon ta sai kuma farar kafar ta me daukan hankali.
******
Zaune take adan madaidaicin tsakar gidan wadda yake share tsaf, kanta ta hada da guiwa tsayon lokaci, akoda yaushe idonta sun kasa daina kallon kafafuwan sa guda biyu daya me lafiya daya mara lafiya, tsayon sati daya kenan ta kasa barin tuno kafar tasa, wannan dalilin ya fara sata hawaye dan takasa fahimtar me hakan ke nufi, daker ta iya yakece tunanin ta mike domin karasa sharar data fara, bayan ta kammala ne tai wanka, shiryawa tayi tsaf kamar kowanne lokaci yadda ta saba fita sannan ta fito ta jawo kofar dakin, gidan ta kallah komai tsaf dan haka taji wani sanyi cikin ranta sannan ta fice tare da sawa gidan kwado.
Tafiya take gefen hanya sannu kan hankali har ta isa wani gida namarasa karfi sosai, sallama tayi cikin siririyar muryar ta tare da saka kanta acikin gidan.
Wata Dattijowa ce ta amsa fuskanta sake.
Jikinta yariyar ta fada, tana fadin, sannu da aiki Dada.
Yauwa sannu dai Unaisa, tun dazon nake ta xoba ido jiran zuwanki harnai tunanin yau bazakizo ba.
Cikin zazzakar muryan ta tace, " zanzo Dada idan banzo ba ai banajin dadi.
Cikin yanayin tunani tsohowar da takirata da Dada tace, " hakane, sannan wani al'amari yafara min yawo cikin kaina.
Da sauri yariyar ta kalli Dada tare da cewa, Dada mene shi?
Jimmmm tayi zuwa can tace, " yanzun matasa duk sun lalace, sa'anan duk unguwar nan kowa yasan da cewa ke daya kike kwana cikin gidan nan, gashi girma nata miki sallama, 'karashe mgnr tayi tana kallon fuskar yariyar da takira da suna Unaisa.
Nan danan idon yariyar ya cika makil da hawaye, yayin da matar ke cigaba da fadin, " aduk sanda nasa hakarkarina akan shinfida ta tun bayan tafiyan ki duk fargaba yaki bari na, Unaisa bakijin tsoro?"
Kwallar da take makalewa ce ta zubo zuwa kan kumatun ta, yayin da tai saurin sa hannunta ta share tare da girgiza kai, banaji Dada, Innawuro tace tabarwa Allah amanata, ki kwantar da hankalin ki, insha Allahu babu abun da zai faru.
Allah yasa Unaisa, tashi maza ki dauki kayan ki wuce, alhamis me zuwa basai kinzo ba zan kawo da kaina, ya makarantar kina zuwa dai ko?
Dakai ta bata amsa sannan ta sauke nikabin ta tare da nufa kayan ta dauka sannan ta mata sallama ta kamo hanya.
Tana saka kafarta akofar gidan wani kyakyawan matashi na sawo kai, ahankali ta kauce ta bashi hanya yayin da ya dan tsaya yana kallon ta, fuskarsa dauke da murmushi yace, "Habaruwala!"
Jimmm yarinyar tayi sannan ta fara takawa ahankali kamar yadda ta saba, shikuwa wannan matashin bebar fada mata wannan kalmar ba har saida tai nisa sosai.
Sosai ta kosa ta isa gida domin tsakanin gidan da gidan Dada akwai tazara, daf take data karasa gida ta hangi wasu jerin gwanon motoci masu kyalli da daukan hankali, motocine manya manya na alfarma jere kofar gidan Malam Baba Kamar yadda ake kiran shi cikin unguwan, shahararrene malamin gyaran karaya da duk wani maganin gargajiya, dan haka duniya tasan dashi kofar gidan sa be rabo da baki akowanni lokaci, saidai tunda take cikin unguwar bata taba ganin zuka zuka motoci har haka akofar gidan ba, sai wancen satin daya wuce, saiyau data take ganin kamar sunfi naranar kyau.
Cire idonta tayi daga kallon kofar gidan Malam Baba sannan ta tsallaka kwatar dake kofar gidan tahau kan dakalin.
Ledan dake hannunta ta sauke tana lalibo mabudin gidan.
****
Magaji jinan, da hannu yai masa nuni da kofar gidan da budurwa ke kokarin bude kofar.
Kallon yariyar yayi sannan ya juya ya kalli Modibo.
Dauke ido Modibo yayi sannan yace, " kamin mgn da ita, kayi kokari ka kawota nan gabana, Ina son in ganta a nan gurin yanzun nan.
[11/20, 11:16 AM] +227 90 16 59 91: BA LABARI
By
Fadeela Lamido
EXQUISITE WRITER'S FORUM.
Page 5- 6
Gaba daya motocin ne suka tashi lokaci guda, bayan ta suke bi a hankali, ita ko Unaisa ko waige batai, gudun ta kawai take tamkar wadda kura ya biyo ta.
Layin nasu nada tsawo sosai, ga hanyar babu kyau dan haka sannu ahankali motar ke tafiya yayin da suke iya hangen yadda yariyar ke falla gudu a gaban su.
Magaji ko ajiyan zuciya yake saukewa, ko ahaka yasan ya fanshe walar da taita bashi dan haka kallon mugunta ya ke ta binta dashi, shikuwa daya matashin ban da dariya babu abun da yake har yanxun, yayin da Modibo ya hade fuska, idon sa akan ta, baya kawarwa zuwa can yaiwa driver Umarni daya tsaya domin wannan lokacin motar suce agaba.
Dan tsayawa sukayi kadan yariyar ta kara nisa sosai dasu sannan yace muje.
Magaji ne yabi Modibo da kallo, cikin nutsuwar sa yaga Yana bin yariyar da kallo dan haka shima ya juya ya kalli yariyar da tayi nisa dasu sai arta gudu take, Modibo ya sake kallo yayin da yaga sai shafa gemon sa yake tare da shafo kansa, sunkuyar da kansa yayi yai murmushi sannan ya dago ya sake kallon Modibo yace, " Modibo!"
Lumshe ido yayi sannan ya juyo ya kalle shi.
Nace kodai mahaukaciya ce?
Lumshe ido ya sake yi akaro na biyu tare da fadi ahankali, " lafiyarta lau"
Ganin tasha kwana suka kara gudun motar, suna saka hancin motar akwanan sukaga ta shige wani gida ta rufo kofar.
****
Matsanancin hakin da take yasa Dada rikecewa, kara shigewa cikin jikinta take tamkar zata shige cikin ta tare da haki babu kaukautawa.
Unaisa menene??, gayamin me yake faruwa?
Shid'ewa tayi gaba daya, yayin da Dada ta kara rudewa, girgizata take tare da Kiran sunanta, ganin babu alamar numfashi yasa ta zame ta, ruwa ta dauko aguje ta dawo ta shafa mata afuska sau uku sannan taji taja dogon numfashi, zama tayi sosai ta kara daurata jikinta tare da rungume ta sosai, tsayon lokaci tana rungume ajikin ta, ajiyan zuciya kawai take saukewa, saida Dada ta tabbatar ta samu nutsuwa sannan tace, " menene yake faruwa Unaisa, gayamin mene ya firgita ki har haka?
Hawaye ta share tana manne ajikin Dada, Hankali tace, wannan ba'kin na Malam Baba ne suka tare min kofar shiga gida.
Jimmm Dada tayi sannan tace, " akan wani dalili?"
Bansani ba Dada, har biyoni suka yi da mota.
Shiru Dada ta sake yi, sannan ta mike ta leka kofar gidan, bata jima ba ta dawo tana fadin, kindai tsorata ne Unaisa, amman babu wani daya biyo ki, mayafinta ta dauka ta sake fita, tsayon lokaci sannan ta dawo tana cewa, naje har layin naku babu kowa inajin sun wuce.
Ajiyan zuciya Unaisa tayi mekyau sannan ta dauki nikaf dinta ta daura, itako Dada gaban murho ta isa tana kokarin daura girkin dare, yayin da hakan yayi daidai da shigowan wanni Dattijo, ganin Unaisa ya sashi yaja ya tsaya tunda nesa yana fadin, " tunda kin ajeta annan ni bari na koma"
A'a Malam shigo mana, firgita tayi ne yau abun da bantaba ganin tayi ba, shiyasa hankalina ya tashi har ka ganta anan.
Eh shiyasa zan baku waje ai, idan ta firgice dake lokacin zaki gane abun da ake gaya miki, nagaya miki batun yau ba bana son ganin Baharuwala acikin gida na, amman muje zuwa duk wadda ya bari sauran tuwo ya Kona shi shiya so.
Malam hakuri zaka yi, abun duk da kaga ya koro bere ya fada wuta to yafi wutar zafi, ka tausayawa yariyar nan Malam, tana tsananin son kulawa.
Tunda kina tausaya mata kin dauke Mana, banda batan basira ta yaya za'a ce yariyar da kowa yaki ta keke daya ki makale mata, duk dangi kowa yaki ta saboda bakin naci kinna nan da ita.
Amanar Innawuro ce Unaisa agareni Malam, ko duk duniya zasuki Unaisa ni bazan kita ba, Unaisa dolena ce.
Shikenan, Allah ya baki sa'a, amman Baharuwala tabarmin gidana, banson nadawo na same ta agidan nan, komai na iya faruwa idan nazo na same ta, afusace ya fita, Dada kuwa bakin aikin ta ta koma ranta bace.
Mikewa Unaisa tayi ta isa gaban Dada, cikin muryar ta kasa kasa tace, " Dada zan tafi.
Batare da Dada ta juyo ba tace, " anan zaki kwana.
Sunkuyar dakai tayi kasa tare da fadin, " bazan iya kwana ako inaba idan ba'a dakin Innawuro ba Dada.
Da sauri Dada ta kalli Unaisa sannan tace, ba inda zaki, idan suka dawo cikin dare suka miki wani abin fa?
Bazasu dawo ba, na kula duk sati suke xuwa tunda sun tafi nasan bazasu dawo ba sai wani alhamis din.
Jimmm Dada tayi sannan tace, Ina zuwa toh bari naxo na raka ki.
Bayan Dada ta gama daura kirkin har gida ta raka Unaisa, acikin ranta take tsananin tausayawa rayuwar ta, fitowa tayi tana tafiya tana hawaye, bakin cikin yadda mutane suke gudun Unaisa ko shege ba'a masa haka.
Unaisa kuwa yau kuka taci tana nade akan gadon Innawuro.
Tun daga wannan ranar duk alhamis gidan Dada take wuni, Dada ke lekowa har saita taga wucewan motocin sannan ta koma gida.
Islamiya kawai ke fitar da ita bata zuwa ko Ina sai gidan Dada wadda daman duk alhamis tana zuwa, sai dai yanzun zama take har yamma sannan ta koma gida.
Akwana atashi asarar me rai, yau sati hudu kenan batasa motocin a idonta ba, dan haka hankalinta ya kwanta, ayanzun batajin fargaba ko tsoro.
Saidai acan cikin zuviyar ta lokaci bayan lokaci tana tuna maza biyu data hanga zaune bayan motar masu kama daya.
Ranar juma'a kuwa ko kofar gida bata zuwa tana cikin gida arufe.
Yau asabar tun misalin goma tafito cikin Shirin makaranta, fararen kaya ne ajikinta tass har hijjabin, sai bakar safa dake kafarta tare da bakin nikabi, sosai kayan suka karbi jikin ta.
Tafiya tafara sannu ahankali harta fita daga cikin unguwar ta isa titi, adaidaita ta tsare tahau tare da fada masa sunan makarantar tasu, bakin makarantar aka sauke ta yayin da ta ciro kudinsa ta Mika masa ta nufi cikin makaran tar.
Sallama tayi sannan ta isa kujerar ta ta zauna, kasancewar mutum daya daya ake zama, saidai har aka tashi batai mgn da kowa ba baya ga daukan karatu.
Misalin hudu ta iso gida cikin saure ta nufi kofar tare da lalibo mabudin ta cikin jakar makarantar ta, jimmm tayi jin karan karfe bayan ta, tamkar dai takowa ake da karfe, dan haka gaban ta yai wani irin bugawa.
Nan danan jikinta ya fara rawa yayin data kasa dago mabudin, banda rawan jiki ba abun da take.
Hannu tasa ta rike hannun kofar, jinda tayi kafar ta nason kada ta, ahankali takejin Karan na dad'a matsowa gare ta, har tazo ta fara hango kafar karfen dake tahowa tare da wata farar kafa cikin kyakyawan takalmi, daya kafar kuwa daure take, anan take ta tuna ta taba ganin wannan kafar.
Tahowa yayi harya ya isa jikin kofar gidan ya jingina bayan sa yana kare mata kallo.
Bata iya dagowa ta kalli fuskarsa ba Kamar wancen karon, sunkuyar da kanta tayi kasa tare da rawan jiki abaiya ne.
Tsayon lokaci suka dauka haka zuwa can yayi gyaran murya cikin wata irin murya yace, "kowa ya hanaka dakin kwana dasafe saiya ganka, dan murmushi yayi kadan sannan yasake cewa yaya sunan ki?"
Kara sunkuyar dakanta tayi tsayon lokaci suna ahaka.
Kara lumshe idon sa yayi sannan ya bude akan kyawawan gashin idonta yace, 'inajin ki aunty na kimin mgn mana, sauke mgnr yayi da ajiyan zuciya me karfi, sannan ya sake cewa, "gudu da waiwaye fa shike kawo mugun zato.
Yadda yake mgn yasata kara lumshe idonta, har cikin ranta taji zakin muryan tasa, saidai babu wata kalma da zata iya furtawa.
Muryar tasa ta sakeji cike da kasaita yana fadin, " meyasa bazaki min mgn ba?, gashi ni ina tsanin son inyi mgn dake.
Lumshe ido ta sake yi yayin da ya zubawa gashin idonta kallo tsayon lokaci sannan yace, "ke kadaice a gidan?"
Wannan karon ma babu amsa, wani irin kallon yake mata wadda kusan shi kadai yasan ma'anar sa sannan yace, " toh ba komai, kowa yaki tsotse hannun beji dadin miya bane, dagoya yayi daga cikin kofar sannan ya gyra sandar sa ya taka gefe hankali.
Tsaye yayi agefe yana kallonta yayin da Magaji yake bayan su yana jin duk yadda suka yi.
Ganin ya tashi kofar gidan tayi kokarin dawo da nutsuwar ta, sannan ta lalubi mabudi ta bude gidan ta shige.
Bayanta yabi da kallo kafin yaji tasawa gidan sakata, lumshe idonsa yayi sannan ya kara kallon kofar gidan, gidane na marasu karfi amman gyare yake tsaf, yaji siminti tare da lafiyayyen kofa.
Modibo muje yamma nayi, Magaji yayi mgnr Yana kallon fuskar Modibo, cikin sauri ya fara takawa yayin da Magaji yai saurin rikeshi Modibo ka manta kafarka babu lafiya ko?
Tafiya yacigaba dayi yayin da Magaji ke binsa abaya har suka isa inda motarsu take, da taimakon Magaji ya shiga motar sannan shima ya zaga ya shiga
Wadda ke zaune mazaunin driver ne yace, "
Kun rutsata ko?
Magaji ne ya bashi amsa, Ina fa, gata dai a tsaye amman bazata yi mgn ba saboda rashin d'a'a, bata amsa kowacce irin mgn koda kuwa sallama ce Muftahu, saidai kaga tana karkad'a kwayar idon ta me kama dana mutanen farko...
Batare da Modibo ya kallesu ba yace, " wacce irin mgn ce kake yi?, ga dukkan alama yariyar kurma ce, tanaji amman bata iya mayarwa.
Kasa Magaji yayi da murya sannan yace, "kada kayi tammanin alheri, a inda bakaga haske ba.
Cikin sauri Moddibbo ya runtse ido tsayon lokacin sannan ya bude ahankali, cikin muryarsa me dadin saurare yace, "Idon da yaga sarki baya tsoron galadima Magaji, lallai Ina son nasan wasu abubuwa game da ita.
Muftahu ne yace, " tayaya zaka san wani abu game da ita alhalin tana kurma ko bebiya?
Kara lumshe ido Modibon yayi akaro na biyu sannan yace, " wannan ba matsalar ku bace.
Basu sake mgnr ba saidai dukkan su ukun kowa da abun da yake sakawa cikin ransa
*****
Unaisa kuwa tsaye tayi jikin kofar harta tabbatar da tafiyan su, ajiyan zuciya ta sauke sannan tai saurin shiga cikin gidan, cikin gudu gudu ta canza kaya sannan ta sake fitowa akaro na biyu, wannan karon gidan Dada ta nufa tana ta tafe tana waiwayen bayan ta.
Kamar daga sama Dada ta ganta, iya sanin ta Unaisa bata zuwa wannan ranar dan haka ta tabbatar lallai akwai wani muhimmin abun da ya kawo ta.
Cikin sauri ta taho gareta ganin inda take waiwayen bayanta yasata kallon kofar sannan ta juyo ta kalli Unaisa tace, " Unaisa meke faruwa?"
Batare data dauke idonta daga kallon kofar ba tace, " Dada! Sun dawo"
Cikin tsananin faduwan gaba tace, " suwaye?"
Dada mutanen nanne dake bibiya ta.
Kofar Dada ta nufa da sauri yayin da Unaisa tai saurin fadin, " sun wuce amma dada nafara tsoron karsu dawo.
Yamutsa fuska sosai Dada tayi, tare da fadin, " me suke nema ne Unaisa, me suke ce miki?, Firgicin da kike shiga idan kin gansu yana daga min hankali, wai daga Ina suke?
Bansani ba Dada, amman Kamar ba 'yan kasan nan bane, nataba ganin fuska guda biyu iri daya acikin su akusa da juna, Basu da banbanci Dada, sannan wani jarababbe ke yawan biyo bayana yanai min mgn, sannan akwai mara lafiya akafarsa guda daya tare da tulin motoci da suke zuwa dasu.
Jimmm Dada tayi, zuwa can tace, " narasa gane me suke nema, Unaisa me suke ce miki.
Dada bana iya tunawa.
Kare mata kallo Dada tayi sannan tace, bazaki koma gidan nan ba Unaisa, maza shiga bandaki ki kama ruwa kiyi alwala kizo ki shige dakina.
Kamar yadda ta fada haka tayi, tanajin dawowan Malam mijin Dada bayan isha'i, misalin goma Dada taiwa Unaisa sallama ta wuce turaka tare da kara jadda mata karta yadda malam yasan tana gidan.
Misalin sha biyu da rabi Dada taji alamar zare sakatar dakin ta, bude Ido tayi da sauri tare da kara baza kunnen ta, tabbas dakinta ne kuma harda alaman tafiya, tashi tayi zaune batare data shirya ba, Malam ta kalla sai bacci yake dan haka tai saurin daukan buta ta zare sakatar dakin, Malam din ne ya motsa cikin fada yake fadin kullum Ina miki gargadi ki dinga shigowa da robar tsuguno.
Cikin sauri ta fice tana fadin, " mancewa nayi Malam.
Gilmawan mutum tagani zauren gidan nasu yayin da ta kalli kofar dakinta dake bude, cikin sauri ta nufi zauren albarkacin farin watan dake sararin samaniya take ganin hanya, ahankali ta furta waye Nan! ?
Cak ta tsaya saboda tsananin kaduwa da rawa da zuviyar ta tayi...
[11/20, 11:16 AM] +227 90 16 59 91: BA LABARI
By
Fadeela Lamido
EXQUISITE WRITER'S FORUM.
PAGE 3- 4
Cikin sauri Magaji ya juya ya nufi kofar gidan adaidai lokacin da ta dauki ledan ta take kokarin shiga gidan, cikin kaukausar muryan sa yace , " ke!!"
Babu alamar ta jisa yaga ta daga kafarta tashi gidan.
Ina miki mgn kina tafiya?, ko kinason ki nunamin baki da tarbiya ne kamar yadda yake azahiri, Ganin da yayi ta kule cikin gidan dole yasa shi yin shiru yayin da bakin ciki ya cika masa zuciya, kasa komawa yayi jin ana sawa gidan sakata.
Daker ya iya juyawa ya koma motar ya shiga ya zauna tare da kauda idon sa daga gefen da Moddibo ke zaune.
Moddibbo ne ya kalle sa yace, " ta maka mgn?"
Batare da Magaji ya kalli Modibo ba yace, " a'a, batace dani kala ba"
Ka mata tsawa ne ko?
Kawar da Ido Magaji ya sakeyin sannan yace a'a
Jimmm Modibo ya sake yi sannan ya sake cewa, " ka koma ka buga gidan lallai ko wanni hali ake ciki yau Ina son in ganta anan.
Batare da Modibo ya gama mgnr ba Magaji ya fita, babban rigar sa ya gyara tare da daidaita zaman hularsa sannan ya koma kofar gidan.
Tun kafin tafara jin bugun kofar turaren sa ya fara mata sallama, zaune take bakin kitchen tana kokarin daura girki, cikin sauri ta mike, acikin ranta take fadin, mutanenan ne na ranar nan, me suke nema gurina, me yasa suke bibiya ta, gaba daya jikinta rawa ya fara tanajin yadda yake buga gidan, zuwa can taji shiru dan haka ta fara takawa ahankali ta isa zauren sannan tasa hannunta akan kofar tare da zura idonta ta kafar kofar.
Wasu maza matasa ta hanga zaune bayan motar su biyu, fararene sosai wadda sukafi kama da larabawa, sai dai shaddace lafiyayya ajikin su babban riga wadda akayiwa ado da aiki irin na zamani, mutun biyu kawai take hanga wadda suke zaune cikin farar shadda, saidai ganin su take tamkar mutum daya ne saboda tsabar kamar da suka yi, mgn suke wadda batajin me suke fadi, shagala tayi da kallon su bata Ankara ba saigani tayi motar ta wuce.
Cikin gidan ta koma ta zauna, gaba daya ji tayi jikin ta ya mutu babu wani karfi jikinta, fuskar mutane nan guda biyu kawai take iya tunawa, cikin ranta take tunani, sudin suwaye?, daga Ina suke haka, kuma me suke son ce mata?
Iri irin wannan tunanin taita yi har ya dauke ta dogon lokaci dan haka ta kasa girkin, tattara kayan tayi ta ajiye sannan tai alwala ta nufi daki.
Gaba daya yau ta rasa sukunin ta, komai ne baya mata dadi, fuska iri daya guda biyu sun tsaya mata axuciya, rasa abun yi yasata fara zubar da hawaye Koda dare yayi daker bacci ya iya daukan ta, cikin ikon Allah washegari ta tashi da sauki, duk aikace aikacen gidan tayi sannan tayi abun karyawa ta kwanta, kasancewar yau juma'a babu islamiya, baccin da bata samu jiya ba shi tayi wannan lokacin.
Misalin daya ta shi, Nan ma sallah tayi sannan ta zauna tsakar gida, yau daya ta farajin zaman gidan ya dame ta, sosai take sha'awar tayi hira kamar yadda takejin mutane nayi, saidai tana tuna gargadin Innawuro.
Washegari ta kama asabar dan haka ta nufi islamiya domin shikadai ke debe mata kewa tun bayan data kammala secondry school bata dawowa sai yamma liss, wannan ya matar da ita tunanin data fara sawa ranta akan samarin guda biyu.
*****
Yauta kama alhamis dan haka tun safe take dakon zuwan Dada amman ba ita tazo ba sai misalin biyu da rabi taji ana buga gidan tare da fadin, Unaisa taho bude min.
Jin Muryan Dada yasata runtumowa da gudu har jikinta na bari ta bude kofar tare da fadawa jikin ta.
Rungumeta Dada tayi cikin nuna so da kauna tace, " nasan kinata zuba Ido ko?
Harna fara tunanin zuwa fa Dada, toh ai gani muje ciki, kayan hannunta ta amsa tana kokarin juyawa ne ta hangi motocin yauma a kofar gidan suka aje wasu motocin.
Ganin inda take kallon motar Dada ta kalleta tace, "Daura aure ake ne a unguwar?"
A'a Kamar dai Bakin Malam Baba ne.
Kallon motocin Dada ta sake yi akaro na biyu sannan tace, " lallai kuwa Malam Baba kullum dada shahara yake, dubi irin wannan zuka zukan motoci haka, nan gaba ai bazai saurara aikin mu na yaku bayi ba tunda irin wanna motoci na masa layi.
Juya sukayi suka nufi gidan yayin da Unaisa ke fadin, " Dada waddan nan fah tare suke zuwa sukuma tafi tare, Ina tunanin mutum daya ne mara lafiyan.
Lallai Kila wani babban mutum ne daya shara, cikin gidan suka shiga yayin da Dada ta cire gyalen aQqta ta rataye kan igiyan shanya sannan ta nufi ta barman da Unaisa ta shinfida masu, abinci data taho dashi ta zuba sannan suka shiga ci tare cikin kwano daya, hira suke sosai suna daf da karasawa Dada tace, Ina son nai wata mgn dake Unaisa.
Da saurinta ta kalli Dada.
Itama Dada tana kallon cikin idonta tace, " mgn ce akan aure...
Batakai ga Rufe bakiba Unaisa ta juya baya tare da hada kanta da guiwa.
Dada ce tacigaba da cewa, bansan me kike nufiba, aduk lokacin da nai miki mgnr aure saiki juya min baya ranar bana sake ganin walwalar ki, da ace Innawuro da kawu basa zaman lafiya da nace Kila wani mugun abun kiga yanai mata, nafiki sanin halin su dan nafiki zama dasu, sosai nake son kiyi aure, abun dake daga min hankali mutanen unguwar nan, duk wadda yazo koron sa suke, basa taba bari zancen yai kwari.
Cikin turo baki Unaisan tace, " ni bakomai Dada taimako na ma suke.
Yadda tayi zancen kasa kasa yasa Dada tace mene kikace?
Nace taimakona suke yi.
Jimmm Dada tayi tsayon lokaci tana nazarin mgnrta sannan tace, " shikenan naji, suna taimakon ki tunda suna kore miki manema, duk wadda yazo yau gobe baya kara zuwa, hakan baya daga miki hankali, har kike iya cewa taimakon ki akayi, shikenan saiki ta zama babu aure daga nan har a busa kaho, ki kare rayuwar babu miji tunda kina ganin hakan daidai ne.
Hawaye Unaisa ke sharewa, kallon ta Dada tayi tace, " in dai dan nayi miki wannan zancen ne kibarmin kuka, ni inason naga kiyin aure ne kafin mutuwa ta kuma tana iya zuwa kowanni lokaci tunda bakiso na bari, inna mutu saiki rayu ke kadai tunda hakan kikafi so
Cikin shashshekar kuka tace, bazaki mutuba Dada tare zamu mutu.
Ai bamuzo tare ba bare mu mutu tare, ni daya nazo, ni daya zan mutu, dan haka nake son ki kaunaci aure.
Toni Dada taya zanyi aure alhalin ban iya zama da wani ba, ban iya mgn da wani ba Dada, bana hira da kowa kwata kwata mutanen da suke min mgn basufi a akirga ba, wlh Dada bazan iya mgn da kowa ba,
Lumshe ido Dada tayi sannan tace bazaki iya mgn da kowa ba ko?, nafahim ceki, bazaki iya mgn da kowa ba bare aje ga batun zama irin na auratayya ko?
Batakai ga rufe bakiba Unaisa ta mike ta nufi adaki, cikin rufda ciki ta fada Kan karamin gado.
Bayan ta Dada tabi da kallo, sannan tasa tagumi, idan tana kirgawa daidai shekaran Innawuro hudu kenan da rasuwa lokacin Unaisa nada shekara sha uku aduniya, jimmm ta sake yi, lallai ya kamata ta sauke nauyin dake kanta ta aurar da ita, wanni irin mummunan faduwa ne ya same ta lokacin da ta tuna sukar da mutanen unguwar ke kaiwa akan Unaisa, cikin ranta ta shiga tunanin mayuyacin abu ne Unaisa ta aure acikin garin nan, indai so ake Unaisa tai aure dole ne ayi nisa da ita, tabbatarwan da tayi tunanin beda wani amfani yasa ta mikewa domin tasan Unaisa bazata taba yadda akaita wani gari ba, mayafinta ta cira akan igiya ta yafa, cikin yanayin dake nuna fushi take tace, nina wuce.
Mikewa Unaisa tayi da saurin ta nikabin ta ta daura sannan tai saurin bin bayan Dada.
Itako Dada tana saka kafar ta kofar gidan ta hada Ido da nawasu maza guda biyu zaune saman motar, ganin sum kalleta tai saurin dauke idonta tare da mayar dasu Kan Unaisa tana fadin koma abun ki banso rakiyar taki.
Bude baki tayi da nufin yiwa Dada mgn itama suka hada Ido dasu, daya daga cikin sune ta hangesu a mota shida wani irin sa sak wani harara taga ya zafga mata me cike da zallah tsana dan haka ta maida idonta ga dayan.
Shikam kallonta yake yana murmushi dan haka tai saurin sakawa gidan kwad'o sannan tai sauri ta zura hannunta cikin na Dada.
Dama baki fitoba Unaisa, domin bana son a dinga fahimtar ke daya ce agidan.
Bakomai Dada insha Allahu.
Allah yasa amman duk da haka ki koma gida na gode.
Sallama sukayi, sannan ta juyo daman ba wani nisa tayi ba, matashin Nan ne ta hango fuskarsa dauke da masifa yana sauka daga samar motan.
Yi tayi Kamar bata ganshi ba ta koma gefen gidan su yayin da daga matashin yayi sauri ya rigata isa kofar ya tsaya.
Daga cikin ni'kabin take kallon shi sama da kasa, acikin ran ta take fadin, " banda abinsa bata jikin sa zaiyi da hau Kan dandamalin gidan mu, kafar sa sheki take hakama takalmin sa tamkar ba kasa ake takawa dashi ba, da dai ace tana da damar yi masa mgn data tambaye shi me yake nima gurinta dahar yake kokarin Bata kata kayan sa.
Daga can nesa taja ta tsaya ta cikin ni'kabi take kallon irin kallon wulakancin da yake mata.
Juyawa tayi ta kalli motocin bata iya hango kowa sai mutun daya da shima ya sauko daga saman motar yanxun.
Cikin wani irin murya taji matashin yace, " ki karaso kina bata mana lokaci, koda yake bayau kika fara ba.
Ganin bata da niyar matsowa ya sashi ya sake fadin, bakijina ne?
Wannan karon ma babu alamun zata amsa shi dan haka yace, idan kika bari na iso gurin daukan ki zanyi cak in direki agaban shi.
Zoro Ido tayi yayin da taga yana kallon cikin idonta sannan Yana tahowa gareta ahankali
Shikuwa matashin yana tahowa ne yana kallon gefen idon ta da yai tsananin nuna hasken fatar ta, tsintan kansa yayi dason ganin fuskar ta dalilin ganin kwayar idonta beyi kama dana hausawa ba, acikin ransa yake fadin, " meyasa take boye fuskarta koda yaushe?, daga idon sa yayi ya hange Modibo yana zaune cikin mota idon sa akansu, meye sa Modibo yanace son mgn da yariyar duk da kasaita irin tasa?, ganin babu me amsa masa ya sauke idon sa akan yariyar yana meji acikin ransa shi ba mgn yake sonyi da yariyar ba Fuskanta kawai yake son gani.
Itako babu abun da ke mata yawo aka Sai cewan da taji yayi zai dire ta agaban shi, shin waye shidin?, me zasu min ko me zai min?, yin wannan tunanin yasa ta fara ja da baya, daga can bayanta taji wani irin murya me sanyin sauti tana fadin, " Magaji rike ta karka barta ta gudu"
Jin haka yasa Unaisa ta kwasa aguje yayin da Magaji ya rufa mata baya, saidai yana tsallaka kwatar ya tsaya yayin da ya hangi yariyar har tayi nisa.
Komawa cikin motar yayi yana ya tsuna fuska, yayin da yasamu wannan matashi da suke zaune tare yanata dariya dariya.
Shikuwa Modibo dake zaune abayan motar tsaki yayi sannan ya duba agogo yana fadin, " muje, bi bayan ta karta bace mana.
Wani irin kallo Magaji yaiwa Modibo ganin inda yake ciccin magani ahankali ya bama driver umarni dan haka suke tashi jerin motocin su cikin kokarin bin bayan ta.....