ZANEN ZABUWA

Chapter 2

by @nanahaleema11

*ZANEN ZABUWA*


        ©️ *Nana Haleema.*




***




*Page 2*




Lokacin da Jannat ta shige a guje Gwaggo ta bita da kallo tare da tab'e baki ta cigaba da aikin gyara zogalen da take yi dan tasan kukan bazai wuce nasaba da laifi ta yiwa Imran ba, sallamar da akayi ya saka ta d'ago kai ta amsa tare da fad'in, "Imran k'araso mana". "Gwaggo sannu da aiki" ya fad'a yana k'arasowa cikin gidan, "Yauwa sannu Imran, ya aikin?". "Alhamdulillah Gwaggo, ina Jannat ne ta barki da aiki ke kad'ai?."

Gwaggo tace, "tana d'aki ban san me yake damun ta ba yanzu naga ta wuce a guje ta shiga d'aki kasan hali kamar mai aljanu haka take." 


Da sauri Imran yace, "Wani abu ya same tane?." "Me zai same ta banda zallar iskanci da shagwa6a, Jannat! Jannat!!" Gwaggo ta fad'a tana kwalla mata kira da k'arfin gaske. Daga ciki suka jiyo ta amsa kafin yace, "zo nan." Imra ya kalli Gwaggo kamar zaiyi magana sai kuma ya fasa.


   Kanta a k'asa ta fito ta samu waje ta zauna har lokacin Gwaggo bata d'ago ba tace, "Uban me kike a d'aki ne wai?". Khamshin turaren Imran dake tashi a tsakar gidan yayi bala'in sake kashe mata jiki ta lumshe ido har bata ji lokacin da Gwaggon tayi mata magana ba, ganin tayi shiru bata bata amsa ba ya fusata ta cikin masifa tace, "Ina yi miki magana kin yi banza?."


Firgigit ta d'ago ido suka had'a ido da Imran da ya zuba mata ido kawai yana kallon ta yana so yaga yanayin da take ciki, d'auke idon ta tayi daga kansa zuciyar ta na sake bada himma wajan gudu tace, "Kaina ne yake min ciwo shine na kwanta kafin magariba tayi" ta fad'a muryar ta a sanyaye matuk'a.


Kafin Gwaggo ta sake magana Imran yayi saurin katse ta da fad'in, "tun yaushe kan yake miki ciwo? Kuma kinsha magani dai ko?" Ya tambaya cikin kulawa da qauna yana kallon ta irin kallon da yake nuna tsantsar kulawa a gare ta.


    Yarrrrr take ji a jikin ta lokacin da kwakwalwar ta ta kawowa kunnen ta sak'on muryar sa sai da ta lumshe ido ta bud'e sannan tace, "nasha." "Shikenan jeki ki huta" ya sake fad'a yana kallon ta dan bai amince ciwon kaine yake damun ta ba domin kuwa damuwa ya hango k'arara a kan fuskar ta ya fad'i hakan ne sabida Gwaggo dake wajan, ba musu ta mik'e ta shiga ciki kanta a k'asa ya bita da kallo har ta b'acewa ganin sa kafin ya dawo da kallon sa ga Gwaggo yace, "Gwaggo kiyi hak'uri har yanzu Jannat yarinya ce k'arama."


  "Yo Imran ai Jannat d'in ce sai da fad'an bata da kuzari samm a jikin kamar kadangaruwa haka zaka ga tana bin bango sabida tsabar lalaci" Gwaggo ta bashi amsa tana cigaba da aikin ta.


"To Gwaggo ai yarinya ce har yanzu, kwata-kwata nawa Jannat d'in take?." Gwaggo ta saki baki tana kallon sa ganin yadda yayi kicin-kicin da fuska tayi dariya kad'an tace, "Imran Jannat d'in kake cewa nawa take? Yarinyar da inda tayi aure da wuri da yanzu tana da yara biyu ko uku ma itace ake cewa nawa take?."


Langwa6ar da kai yayi yace, "Allah Gwaggo yarinya ce dan Allah ki daina yi mata fad'a haka." A yadda yayi maganar kamar k'aramin yaro ba k'aramar dariya ta bawa Gwaggo ba ta dara kad'an tace, "to Imran za'a daina". "Gwaggo bara naje nayi sallah na dawo naci zogalen" ya fad'a yana zira takalman sa ya fita daga gidan. 

Da kallo Gwaggo ta bishi tana tausayin sa sosai.


   Jannat kuwa tana jin fitar sa ta fito tayi alwala ta koma d'akin ta tayar da sallah, lokacin da ta idar ta fito har Gwaggo ta d'ora zogalen yana ta dahuwa akan wuta itama tana sallah hakan ya saka ta k'arasawa ta duba ganin yayi ta sauke ta bud'e shi ta d'auko duk abinda tasan Gwaggon na sakawa ta fara had'awa, koda Gwaggon ta idar batayi magana ba ta cigaba da lazumin ta ita kuma ta had'a zogalen har ta gama ta d'auko ta ajjiye a kusa da Gwaggon ta koma gefe ta zauna, Gwaggo ta kalle ta tace, "Jannat akwai abinda yake damun ki fad'a min ko meye naji." Girgiza kai tayi tace, "Babu komai Gwaggo kawai kaina ne yake min ciwo." Gwaggo bata sake magana ba dan bata son musu ta cigaba da lazimin har Imran ya dawo.


   Zama yayi kafin Gwaggo tace, "Jannat d'auko faranti a zuba masa yaci". Ta yunk'ura zata mik'e Imran ya riga ta yana fad'in, "Zauna ki huta bara na d'auko" ya fad'a yana shiga kitchen d'in Gwaggon ya d'auko ya dawo ya mik'awa Gwaggon, karb'a tayi bata ce komai ba ta zuba masa a faranti d'aya ta mik'a masa, ta zubawa Jannat d'in ma ta mik'a mata ta karb'a ta ajjiye kawai a kusa da ita ba tare da ta fara ci ba. "Gwaggo." Jannat ta kira ta ta d'ago tare da amsawa, "Kin san Yaya ya kwashe kaf kud'in da yake tarawa yaje ya siyi mota sabida kawai ya dinga kai ni makaranta?." Cakk Gwaggo ta dakata daga cin zogalen tace, "ban fahimce ki ba." 


"Gwaggo kud'in sa na kasuwancin ya kwashe kaff ya siyi mota gata can a waje sabida kawai baya son d'auko ni a bayan machine ana ganin na, kuma gaban ki kuma tab'a maganar ta dinga bari na ina hawa adaidai sahu amma yaki."


Kallon Imran tayi da yake cin zogalen sa hankalin kwance tace, "Da gaske ne abinda take fad'a min haka ne anyi?". Kallon Gwaggo yayi yace, "Haka ne Gwaggo." 


   Tafa hannu Gwaggo ta fara tana salati tana fad'in, "Imarana da hankalin ka da tunanin ka zaka yanke wannan d'anyen aikin? Wacece Jannat d'in da baza ka d'auko ta a bayan machine ba,? Kud'in da aka jima ana tarawa ana fatan su taru zaka kwashe kaje ka siyi mota ina laifin ma ka siyi machine d'in ma,? gaskiya banji dad'in wannan hukunci ba samm." 


Girgiza kai Gwaggo tayi kafin yayi magana Gwaggo ta cigaba da cewa, "Imran gobe da safe in Allah ya kaimu ka d'auki motar kaje ka siyar da ita ka karb'o kud'in ka ka cigaba da tarin ka nan gaba Allah zai kawo na siyan motar, ni daman tun farko ba son karatun nan nata nake ba wallahi, babban buri na a yanzu bai wuce Jannat tayi aure ba ba ta dinga wannan yawon makarantar ba".


Lumshe ido yayi yana jin wani irin abu na tsikarar sa a zuciyar sa, indai Gwaggo zata furta zancen aure akan Jannat sai yaji wannan yanayin ya kuma rasa meye shi. 


Dak'yar ya bud'e baki yace, "Kiyi hak'uri Gwaggo in hakan ya b'ata miki rai, amma dan Allah ki bar maganar siyar da motar nan tunda akwai sauran kud'i a hannu na zan cigaba da tarawa kuma zasu taru insha Allah ki cigaba da yi mana addu'a kawai."


Gwaggo tace, "Nifa ban amince da hakan ba ka siyar da motar kawai ka karb'o kud'in ka shine abinda nake so, akan me zaka siyi mota sabida Jannat? Meye amfanin masu adaidaita sahu da suke yawo a garin nan da baza ta shiga ba?."


Zaro ido waje yayi yace, "Kai Gwaggo wad'an nan nasu babur d'in da yawan su barayi ne wallahi shiyasa hankali na bai kwanta da ta hau ba, dan Allah Gwaggo ki bar maganar siyar da motar nan dan Allah badan ni ba."


Shiru Gwaggo tayi bata sake cewa komai ba amma tana jin babu dad'i a zuciyar ta dan gani take mutanen gari da wasu daga cikin y'an uwan sa zasu cigaba da zargin kwace masa kud'i Jannat take yi daman ya aka cika, zare hannun sa yayi daga cin zogalen ya kalli Jannat yace, " Jannat me ya hana ki ci har yanzu?". Kallon sa tayi ta d'auke kai kafin ta zura hannu ta fara ci kad'an-kad'an badan dad'i ba dan kawai ya k'yale ta ya daina mata magana a lokacin da ita kad'ai ta san abinda take ji, mik'ewa tsaye yayi yace, "kafin na dawo ki tabbatar kin cinye, Gwaggo ina zuwa" yana fad'a ya zura takalmin sa ya fita.


   "Yanzu haka zamu bar Imran yana kashe kud'in sa akan ki?" Gwaggo ta fad'a tana kallon Jannat cikin damuwa. "Abinda nake tunani kenan wallahi Gwaggo, nima bai fad'a min sai bayan ya siyo, sabida haka Yaya bata sona sabida gani take nice na hana shi tara kud'i." Jannat ta fad'a muryar ta a sanyaye kamar zatayi kuka. 


Gwaggo tace, "Ai dole ta Fad'a ko nice haka zance balle ita, Imran shine ya fara kawo min riga ta a matsayi kayan barkar haihuwar ki a lokacin yana da shekara goma sha d'aya a duniya haka mahaifiyar sa ta kullo masa leda ya kawo min, tun daga lokacin yake d'awainiya dake har kawo yau, i zuwa yanzu ya kamata ace ya dakata haka gaskiya abin yayi yawa." Shiru Jannat tayi bata ce komai ba dan ita kad'ai tasan abinda yake damun ta. 


  Mik'ewa Gwaggo tayi ta shiga d'aki ta bar Jannat a zaune tana tunani, a baya ta d'auka akwai soyayyar ta a zuciyar Imran amma a d'azu da taji abinda yace da kunnen ta sai ta tabbatarwa kanta itace kawai take haukan banza amma shi ba wannan ne a gaban shi ba, lumshe ido tayi hawaye ya ziraro daga idon ta tak'i bud'e idon sai ji tayi ana share mata hawayen hakan ya saka ta bud'e ido.


hasken doguwar fitila mai amfani da hasken rana kwalli d'aya da ta haska tsakar gida ya saka taga fuskar sa d'auke da damuwa, "ni nasan ba ciwon kaine yake damun ki ba k'anwa ta dan yanayin ki badai mai ciwo yayi kama ba da mai damuwa yayi kama, a duniya babu wanda yayi miki sanin da nayi miki, nasan yanayin ki na farin ciki nasan na akasin sa, nasan yanayin ki na rashin lafiya nasan na akasin hakan, bana son duk abinda zai dame ki har ya saka ki zubar da hawaye fad'a min abinda yake damun ki nayi miki alqawarin zan miki shi ko meye." ya fad'a yana kallon ta itama kuma shi take kallo. 


D'auke idon ta tayi daga cikin nasa kusantuwar su da kasancewar su waje d'aya ya k'ara mata bugun zuciya da kuma fad'uwar gaba, kamar yadda ruwa yake shiga jijiya haka take ji soyayyar sa na sake bin jinin ta a hankali tana zaga ko ina na jikin ta, ji take kamar ta rungume shi a jikin ta ta kwanta a k'irjin sa tana shak'ar khamshin turaren jikin sa mai kwantar mata da hankali amma babu damar hakan.


"Jannaty ki fad'a min dan Allah, kin sani bana so na ganki a cikin damuwa." 


Ajiyar zuciya tayi ta bud'e a hankali tace, "Duk abinda nake so na tambaye ka zaka fad'a min?."

"Kwarai kuwa Jannaty kome kike so zan baki insha Allah."

"Koda kanka nace ka bani?" Kamar an fizge maganar daga bakin ta haka taji futar ta ba tare da ta shirya ba.


dariya yayi kad'an ya lakuce mata hanci yace, "Daman ai Imran naki ne Jannaty oh ready, fad'i abinda kike so sai ayi wasan daga baya." Kallon sa tayi a ranta ta maimaita kalmar wasa, wato shi wasa ma ya d'auki abinda tace, K'asa tayi da kanta sosai kafin tace..........


Free page😁



_Wannan labarin na kud'i ne ki biya naira 300 kacal ki karanta cikin nutsuwa da kwanciyar hankali, domin biya tuntub'i wannan number but only WhatsApp. ***_



Wattpad @Nanahaleema

Arewabooks @nanahaleema11.