Chapter 3
*ZANEN ZABUWA*
©️ *Nana Haleema*
*Page 3*
K'asa tayi da kanta sosai kafin tace, "babu abinda zance maka fa daman." Murmushi yayi kad'an yace, "Wanda bai sanki ba zaki fad'awa haka amma bani ba, kinga ki fad'a min abinda yake damun ki bana son haka fa."
D'ago kai tayi tare da sauke ajiyar zuciya tace, "gobe muna da test ne gashi banyi karatu ba sabida ciwon kan nan kuma malamin bashi da kirki ko kad'an." Zuba mata ido yayi na wasu y'an seconds kafin yace, "Look Jannat, ki fad'a min abinda yake damun ki ba wannan ne asalin abinda yake ranki ba."
Langwa6ar da kai tayi cikin gajiya da kalaman sa tace, "Babu wani abu bayan abinda na fad'a maka" ta fad'a kamar zata yi masa kuka. "test ne ya saka ki kuka kike so kice min?."
D'aga masa kai tayi alamun eh, girgiza kai yayi yace, "har yanzu kan naki yana ciwo?". D'aga masa kai tayi alamun eh, "in akayi sallar i'sha ki kwanta ki huta kan naki zai daina ciwon insha Allah, k'arfe nawa kike da test d'in gobe?".
"K'arfe takwas."
"In akayi sallar asuba sai ki duba abinda zaki karanta zuwa lokacin ciwon ya sauka insha Allah."
D'aga kai tayi ta kalle shi tace, "to zanyi insha Allah." "Ko kefa Jannaty, naga yadda wayar taki ta fashe d'in." "Na barta a d'aki bara na d'auko" ta fad'a tana niyar mik'ewa tsaye, "A'a zauna gobe in zaki shiga makaranta sai ki bani sai a gyara". "Bama sai an gyara ba ashe glass d'in ne ya fashe ba screen d'in wayar ba." "To sai a canja wani". Bata ce komai ba ta mayar da kanta tana wasa da zaren tabarmar da suke kai ita dashi zuciyar ta na k'ara gudu wajan bugawa sabida kusancin da suka samu a lokacin, "Jannaty!" Ya kira sunan in low voice cikin yanayin mai dad'in gaske.
Lumshe ido tayi tsigar jikin ta na mik'ewa yarrrr wani abu na sake nutso cikin tsoka da jinin dake cikin jikin ta, cikin yanayin da ita kad'ai tasan yadda take jin sa tace, "Uhummmm".
"Kin k'i fad'a min abinda yake damun ki ko?".
"Hmmmm" shine abinda ta furta kawai dan babu bakin magana a tare da ita. Kallon ta yake cikin hasken da haske tsakar gidan cikin wani irin yanayi da yake jin jikin sa a cikin a duk lokacin da suke tare, wani abu na fisgar sa yana faman kokawa da zuciyar sa a lokacin da take k'okarin kwacewa.
"Jannaty zanje nayi sallar i'sha zan shiga gida, ki tashi kiyi sallah sai ki kwanta kinji ko?". D'ago kai tayi ta kalle shi bata san lokacin da murmushi ya sub'uce mata ba ganin shima murmushin ne akan kyakykyawar sa tace, "to Yaya na ka kwana lafiya." "Amin k'anwa ta, tare dake" ya fad'a yana mik'ewa tsaye.
kira ne ya shigo wayar sa ya d'auko ta daga aljihun rigar sa ganin number ce ya saka shi bai d'auka ba ya mayar aljihu, kallon ta yayi idon su ya had'u waje d'aya yace, "good night Jannaty" yana gama fad'ar hakan ya juya ya fita daga gidan tabi bayan sa kallo har ya b'acewa ganin ta. Ajiyar zuciya ta sauke ta mik'e jiki babu kwari ta shiga d'aki Gwaggo.
Bayan ta idar da sallah ta had'a komai na gidan ta samu waje ta kwanta kamar yadda yace mata amma tunani ya hana ta bacci, da ta kulle ido shi take gani yana yi mata murmushi fararen haqoran sa sun bayyana suna shek'i da kyalli sabida kyauwun su, da wannan tunane-tunanen bacci ya d'auke ta.
Washe gari kamar yadda yace bayan tayi sallar asuba ta karanta iya abinda zata iya sannan ta fito ta fara aikin ta kamar kullum, kafin k'arfe bakwai da rabi ta kammala komai har wanka tayi duk da jikin ta a sanyaye yake amma haka ta daure tayi komai a nutse, d'akin Gwaggo ta shiga ta same ta zaune da alama farkawar ta kenan tace, "Gwaggo na gama abin karin na kawo miki?."
"A'a Jannat sai anjima zanci, ke kinci naki?."
"A'a Gwaggo sai naje makaranta bana jin yunwa yanzu."
Gwaggo tace, "Sannu da aiki, Allah yayi miki albarka ya baki miji na gari wanda zai kula dake."
"Amin Gwaggo, bara naje na saka kaya kar Yaya yazo yana jira na" tana gama fad'ar hakan ta fita daga d'akin da yake kusa dana Gwaggo.
Y'ar k'aramar wardrobe d'in ta bud'e mai guda d'aya dake tsaye a can gefen k'aramin d'akin nata, babu wasu kaya da yawa a ciki sai wanda baza'a rasa ba amma kayan a wanke a goge tsaf dasu babu kazanta ko kad'an, doguwar riga ta d'auka ta atampa d'inkin A shape ta saka ta d'auki mayafin ta bak'i mai girma ta yafa ta fesa turaren ta dake gefen kayan sannan ta rufe wardrobe d'in. littafin da ta karanta ta d'auka ta saka cikin jaka sannan ta d'auko jakar ta fito, Gwaggo ta samu k'aramin falon nasu a zaune tace, "Gwaggo bara na shiga wajan Umma.mu gaisa daga nan sai mu wuce". "To Allah ya bada sa'a, ki gaishe ta" da to kawai ta amsa ta fita daga gidan ta fad'a wanda yake jikin nasu gidan.
Da sallama ta shiga gidan ta same ta a zaune akan tabarma tana gyara waken kosai, "Sannuu da aiki Umma" ta fad'a tana k'arasawa ciki wajan ta. murmushi Umma tayi tace, "yauwa sannu Khadijah, har an shirya kenan?." "Eh Umma, Ina kwana."
"Lafiya lau Khadija, ya jikin naki? Imran yace min baki ji dad'i ba jiya." "Naji sauk'i sosai Umma daman ciwon kaine, kawo na gyara miki waken" ta fad'a tana ajjiye jakar ta tare da k'okarin karb'ar waken. "haba Khadijah keda zaki tafi makaranta ina ke ina aiki, barshi nagode ai na gama."
Jannat bata yadda ba ta saka hannu ta d'auki waken sannan tace, "ai zan k'arasa gyara miki kafin na tafi d'in". Umma bata kuma tanka mata ba ta bar mata ta fara gyarawa mata waken suna y'ar hira kad'an-kad'an sallamar Imran ta katse musu maganar da suke suka amsa a tare Jannat ta d'ago ido tana kalle shi.
sanye yake da shadda milk colour mai kyau duk da ba mai tsada bace amma yadda take a wanke a kuma goge ba k'aramin d'aukar ido take yi ba ta kuma amshi jikin sa sosai, gaban ta ya fad'i k'irjin ta ya fara yi mata wani irin nauyi a lokaci d'aya yanayin ta ya canja kamar wacce take cikin tsoro ya kuma bayyana akan fuskar ta sosai, ta kasa d'auke idon ta daga nasa duk da tana so tayi hakan amma zuciyar ta tak'i bawa idanun ta umarnin aikata hakan sai ma sake ware idon ta da take a akan kyakykyawar farar fuskar sa wacce kwantatcen gashi bak'i mai tsayi yayi mata k'awanya ya zagaye ta ya kuma kwanta luff.
"Jannat!" Umma ta fad'a tana tab'a ta dan ganin hankalin ta gabad'aya ya bar jikin ta haka nutsuwar ta da kuma tunanin ta, sai da ta firgita sannan ta kalli Umma tace, "Na'am." "Tunanin me kike yi haka har yayan ki nayi miki magana baki ji ba?" Umma ta tambaya da kulawa tana kallon ta.
"Banji bane" ta fad'a muryar ta a sanyaye sosai jikin ta yayi sanyi lokaci d'aya."ta yaya zaki ji bayan kin tafi duniyar tunani Jannat, taso mu tafi kar ki makara" ya fad'a cikin sweet voice d'in sa yana kallon ta cikin wani irin yanayi wanda yake nuna rashin jin dad'in sa akan yanayin da ya riske ta ciki.
mik'ewa tsaye tayi ta ajjiyewa Umma waken ta d'auki jakar ta tace, "Umma sai mun dawo." "To Allah ya kiyaye hanya, Imram kar ka manta in ka tashi daga aiki ka biya gidan kawun ku ka karb'o min sak'on." Da to kawai ya amsa ya fita daga gidan Jannat tayi bayan sa. Umma da ta bisu da kallo tayi murmushi tare da girgiza kanta ta cigaba da aikin ta.
Motar ya bud'e mata ta shiga ta zauna shi kuma ya shiga gidan Gwaggo, bai jima sosai ba ya fito ya shiga mazaunin driver ya kunna motar suka fara tafiya, kanta a k'asa yake ko motsin kirki ta kasa balle tayi magana duk da tana so tace wani abu amma bakin ta yayi mata nauyi sosai ta kasa sarrafa harshen ta balle har ta iya furta wata kalma guda d'aya, shima kuma baiyi magana ba duk da yana so ya tambaye ta abinda yake damun ta amma ganin lokacin shigar ta test d'in ya kusa ya shi yayi shiru baice komai ba. abinda bai tab'a faruwa a tsakanin ba hakan ce ta faru har suka je k'ofar makarantar bata ce komai ba shima baice komai ba sai da ya faka zata fita sannan yace, "ki kula da kanki in kun gama kiyi min waya" ya fad'a ba tare da ya kalle ta ba. kallon sa tayi taga yana kallon titi ba ita yake kallo ba sai tace, "to" daga haka ta bud'e motar ta fita har ta shiga makaranta yana kallon ta sannan ya juya motar ya d'auki hanyar wajan aiki.
Tunda ya shiga company ya tabbatar yau ba qalau ba ganin yadda kowa yake aiki hankalin sa a tashe hakan ya saka shi sake nutsuwa ya ajjiye motar ya fito ya nufi ciki, sama yake hawa inda mazaunin sa yake yaji an kira shi daga bayan sa hakan ya saka shi ya tsaya tare da juyowa yana kallon mai kiran nasa, "A'a Usman barka da safiya" Imran ya furta yana mik'a masa hannu alamun su gaisa, gaisawa sukayi wanda aka kira da Usman yace, "barkan ka, sai kuma naga sabuwar amarya." Murmushi Imran yayi yace, "To gata nan dai."
"To Allah ya sanya albarka ya tsare." "Amin nagode."
"Jiya bayan fitar ka manager tazo ta kuma nemi kowa na company nan, to baka nan ta kuma fahimci hakan aka kuma tabbatar baka bada reason na fitar ka ba shine tace da kazo yau kaje tana neman ka, kayi hak'uri nayi iya bakin k'okari na wajan ganin na dai-dai komai amma kasan halin ta bata ganin k'imar kowa duk ranar da ta raya mata tazo company nan sai ta b'atawa wani."
Imran yace, "babu komai kar ka damu kanka, bara naje na same ta" ya fad'a yana wucewa hanyar da zai kaishi office d'in ta ba tare da fargaba ko tashin hankali ba.
knocking d'in k'ofar yayi aka bashi izinin shiga ya murd'a handle d'in k'ofar ya shiga da sallama. tana zaune akan kujera sanye cikin doguwar riga green colour tayi rolling d'in kanta da mayafin doguwar rigar kasancewar ta farar fata sosai kalar ta amshi jikin ta sai ta k'ara haske sosai, "barka da safiya, nine Imran ance kina nema na."
Bata d'ago kanta ba balle ya saka ran zatayi masa magana sai ma cigaba da aikin danna laptop d'in gaban ta da take yi kamar bata san da wata halitta a wajan ba, "Madam ance kina nema na" ya sake maimaitawa a karo na biyu duk da ransa ya sosu da wulaqancin da tayi masa amma haka ya danne ya sake yi mata magana.
Nan ma tayi masa banza bata kuma kalle shi ba sai ma sake gyara zaman ta da tayi tana cigaba da aikin ta, ran Imran ya b'aci a duniya ya tsani wulaqanci yana jure komai yana kuma kawar dakai akan komai amma banda wulaqanci, bazai wulaqanta ka ba kaima kuma kar ka wulaqanta shi baya so ba kuma ya k'aunar hakan ko kad'an, har fuskar sa sai da ta nuna zallan b'acin ran da yake ciki bai san lokacin da yaja dogon tsaki ba ya juya ya soma tafiya zai bar office d'in sai a lokacin ta d'ago ta kalli bayan sa tace, "in ka sake ka fita daga office d'in nan ka tabbatar ka fita da aikin ka."
Tsayawa yayi cak ya juyo idon sa ya fad'a cikin nata hakan ya haifar mata da fad'uwar gaba mai tsanani tayi saurin runtse idon ta ta bud'e zuciyar ta na wani irin bugawa da sauri abinda bai tab'a faruwa da ita a rayuwar ta ba, maganar sa ta katse ta yace, "zan iya jure barin aiki amma bazan iya jure wulaqanci ba, ki jik'a aikin naki kisha amma ki koma a fad'a miki mahimmacin d'an adam da kuma k'imar da yake da ita a duniya" ya fad'ar hakan ya fita daga office d'in tare da jan k'ofar da k'arfi.
K'arar k'ofar da yaja da k'arfi ya saka ta kulle ido ta bud'e wani irin yanayi yana shiga jikin ta wanda bata tab'a jin sa akan kowa ba sai a kan sa, dafe kanta tayi duk wani kuzarin da tazo dashi ya tafi jikin ta yayi bala'in sanyi ga wani gumi da yanko mata ta ko wacce kafa ta jikin ta duk da sanyin a.c da yake tashi a cikin office d'in, remote ta d'auka ta kunna k'aramar tv dake ajjiye akan table ta fara danne-danne, sai da ta nemo inda Imran d'in yaje tsaye yana amsa waya sannan ta tsaya tana k'are masa kallo a tv d'in har lumshe ido take tana bud'e akan sa har lokacin yana tsaye yana waya, wayar dake kusa da ita ta d'auka ta d'an danna sannan ta kara a kunnen ta tace, "ka turo min wanda yake tsaye kusa da office d'in ka yanzu yana waya" tana fad'ar hakan ta katse kiran tana kallon sa.
Ba jimawa taga Usman ya fito yana yiwa Imran magana tunda ta cire sound d'in ba jin abinda yake cewa take yi ba amma a yanayin da yake magana zaka fahimci kamar yana cewa bazai zo bane ba, gani tayi Usman ya koma office shi kuma ya fita daga wajan ya nufi k'ofar fita daga company d'in.
K'arar wayar ta katse mata tunani ta d'auka ta saka a speaker daga can b'angaren Usma yace, "Ranki ya dad'e yace bazai zo ba wai ai kin kore shi babu yadda banyi dashi ba amma yace bazai zo ba tunda yanzu ba'a k'ark'ashin ki yake ba." Bata ce komai ba kawai ta yanke kiran wayar tana dafe kanta tana jin yanayi mai kama da rashin jin dad'in abinda tayi masa yana kawo mata ziyara lokaci d'aya.
Free page😁
_Wannan labarin na kud'i ne ki biya naira 300 kacal ki karanta cikin nutsuwa da kwanciyar hankali, domin biya tuntub'i wannan number but only WhatsApp. ***_
Wattpad @ Nana_haleema
Arewabooks @nanahaleema11.