CHAPTER 15( THE OTHER SIDE)
by @deejasmah
WANI RABON.........🦋🦋🦋
Elegant Online Writers ( E.O.W)
Khadeejah Bint Ismail ( deejasmah)
In dedication to all single ladies out there........
Arewabooks @ deejasmah
WhatsApp @***
N.B WhatsApp only not call😁
CHAPTER 15 ( The other side)
This chapter is dedicated to Hafsat Hassan and Maimun Abdullah you guys are so sweet your comments and love is what really keeps me going Allah ya saka da khairan enjoy this chapter and be safe❤
Rayuwa tana lulawa banda damuwar komai a office sai Raheenah wacce har yanzu k'iyayya take nuna min bana wasa ba musamman randa Sir ya rage min hanya Moofy ce take min gulmar wai tana son boss ne shiyasa take kishi mai tsanani da duk wacce zata kasance a office d'in secretary d'in dariya ta bani sosai don iska ne yake wahal da mai kayan kara domin na tabbatar mutum kamar Sir A.B ba abinda zaiyi da mace kamar ta saidai ikon Allah kuma
Ta gefen Mukhtar ma kam abin nashi yai yawa don kusan kullum sai ya shigo office d'ina yai ta min soki burutsu bana tanka shi don na lura ba wani kamun kai yake dashi ba nikam ban buk'atar muamala ta had'ani da masu irin halin nashi balle har ta kaiga shak'uwar da yake nema yau ma haka akayi around 10 lokacin aiki ya d'an yi min sauk'i hakan yasa na kirawo number bestie wacce cikinta yai tsufa ainun don yana cikin wata na takwas gashi dama cikin yana mugun bata wuya tun samuwar shi har yanzu bai huta ba har yau k'orafi take ta min irin na masu tsohon ciki ina sake kwantar mata da hankali ina kuma yi mata dariyar sanda tace min wai duk tayi muni hancinta yai girma sosai ni dai dariya nake tayi ganin dariyar tai yawa ne yasa ta kashe wayarta cikeda masifar wai ina mata dariya
Girgiza kai nayi ina sake kiran wayar tata har yanzu da sauran dariyar a fuska ta k'in dauka tayi hakan yasa na ajiye wayar ina cewa " bestie rigima " d'ago idanu nayi ina kallon Mukhtar da tun da na fara wayar idonshi ke kaina har zuwa sanda na ajiye wayar hararar shi nayi ina tsuke fuska ta don na tsani kallon nan nashi
"You have no idea how cute you look when you smile " ya fad'a shamelessly a mamakance na kalleshi saidai ban ko tanka ba ya cigaba da " gaskiya you are the cutest girl I've ever seen everything about you is cute......the eyes,the smile the lips.......kai everything" sake d'aure fuska ta nayi ina cewa " I'm not here for this Mukhtar....kindly respect yourself "
Murmushi yayi yana cewa " I'm also not here for this either but actually fate has its own way......I can't deny the fact that I'm falling for you......bana samun nutsuwa sai in na ganki banda aikin komai sai tunaninki " mik'ewa nayi cikeda jin haushin kalaman nashi wanda yake yinshi cikeda k'warewa da juya harshe alamun ya saba da fad'in su shima tasowa yai ya matso gabana kamar zai shige jikina hakan yasa ni gaggawar matsawa saidai banyi nasarar yin hakan gaba d'aya ba ya rik'o hannuna yana cewa " I love you Faheemah Sadauki I really do "
Kacaniyar fusge hannuna nakeyi bud'e kofar da akayi yayi dai-dai da marin da na sakar masa da d'ayan hannun da bai rik'e ba hakan ya tilasta mai sakin hannuna cikin rawar murya da na jiki na fara magana " this is the first and the last time da zaka sake sa hannunka a jikina be warned......" waigowa nai jin k'amshin turaren Sir wato Chanel bleu de chanel da kuma roger dove auod ina kallon k'ofar had'a ido mukai DA shi m sanye da kayanshi na din-din-din watau suit hawaye ne ya sauko daga idona hakan yasa na sauke idon nawa daga nashi
K'arewa office d'in kallo yai ba tareda yai magana ba kallon sashen Mukhtar da har yanzu yake dafe da kunci yai gyad'a kai yayi alamun "that's good" kafin ya dawo da idanun shi kaina " get yourself ready we have a meeting ........Kai kuma follow me " daga haka ya juya kallona Mukhtar yayi kafin ya rufa mai baya inda na rakashi da kallon tsana ina mai k'wafa a raina ina furta " d'an iska irinsu ne masu taking advantage na mata da sunan soyayya " tsaki nayi tareda nufar toilet
K'ofar office d'inshi nai knocking izinin shiga ya bani bud'e k'ofar nayi cikin sanyin jiki na shiga da sallama amsawa yayi ba tareda ya ko kalleni ba hasalima yana tsaye ne ya zurawa harabar wurin ido watau ya bani baya kenan d'an tsayawa nai ba tareda na zauna ba don nasan sarai yaji shigowa ta jin shiru ne yasa shi waigowa yana cewa " yes......?" da alamun tambaya
" Sir you said we have a meeting ." na furta a hankali " oh yeah but I don't think you are even ready for the meeting" ya fad'a yana mai maida kallonshi inda yake hararar shi nayi wai I'm not ready tareda cewa " Sir I'm ready " girgiza kai yayi tareda juyowa gaba d'ayan shi zama yai tareda nuna min seat zama nima nayi ina mai d'aura wayata a jikina cewa yayi" you are not ready.....since you let your emotions comes before your self compose.......Miss Sadauki wannan ba tarbiyar arewa bane abinda kika aikata macen kirki bata marin namiji....."
Katse shi nayi with bitterness on my tongue " wato tarbiyar arewa ne shi abinda ya aikata......hmmm ko da yake ita arewar ce bata tab'a yiwa mata adalci ba shiyasa tace ' wai duk abinda namiji yai adone!'.......shiyasa kaima ka bani laifi bayan k'iri-k'iri ga mai laifin.....well nima ba wai nayi bane don a bani gaskiya ko rashinshi na aikata abinda nake ganin shine daidai gareshi kuma ko yanzu ya kuma zan yi mai mafiyin hakan " na k'are maganar da murmushin takaici
Kallona yake yi da wani irin yanayi nima irin kallon nake jifarshi da ita cikeda tsanar irin halinshi wato Mukhtar baida laifi sai ni hawaye ne naji yana taruwa a idona hakan yasa na kawar da idona daga kanshi cikin b'acin rai yace " get out!!!" ko kallonshi banyi ba na nufi k'ofa rufo mai abunshi nayi na koma na zauna ina jin fitar shi ban wani maida hankali akan hakan ba tausar kaina nake tayi amma har k'asan raina na k'udurce ba zaa kuma irin hakan ba domin na lura da cewa shima Sir A.Bn bai san darajar mace ba shiyasa yaga laifi na
A cikin kwanakin gaba d'aya na dena sake ma Mukhtar d'in fuska shima na lura da ya kama kanshi a kaina ko wannan rawar kan duk ya rage saidai ko yaya na wuce ya bini da ido nikam ko da can haushi yake bani balle yanzu a b'angaren Sir kuwa babu wata muamala mai kyau tsakaninmu ko naje kaimai schedule saidai ya duba kawai y'ar sakin fuskar da ya fara kwanaki ya daina ta gaba d'aya
Yau dana shigo kawo masa paperwork d'in da ya had'ani dasu ma wulak'anci ya min saida ya gama dubawa kawai ya jefoni dasu dai-dai shigowar Sahal masifa ya fara min kamar zai ari baki wai ba abinda na iya wannan wani irin shirme ne hakan bla bla bla......
Raina ba k'aramin ɓa yayi da hakan ba don zan iya jure komai amma banda wulak'anci especially a abunda nasan cewa ina da gaskiya don mun samu matsala kwanaki bashi bane zai ba shi zai bashi damar wulak'anta ni ba na kasa b'oye b'acin raina tsayawa nai ina kallonshi ban d'auki takardan ba na juya na fita raina yana suya
Ina zama saiga Sahal ya shigo da papern a hannunshi zama yai tareda cewa " dole sai kina hak'uri bestienmu Buddy wani kalar mutum ne wanda ba'a burge shi ko kad'an musamman in yana cikin fushi.... I've went through the work and it's quite amazing don haka ki ajiye in ya sakko sai ki kaimai.....and ba koina ake nuna fushi ba nasan babu dad'i amma sai kin daure " ajiyar zuciya nayi tareda cewa " ni fa bawai abinda ya aikata bane ya b'ata min rai Aa ko d'aya ai ba yau bane ya fara min hakan ba abunda bazan d'auka ba shine wulak'anci akan abunda nasan ina da gaskiya akai don mun samu sab'ani kwanan baya bashi ne zai bashi damar tujara ni ba "
Da iyakar gaskiya ta na fad'i hakan kallona yai cikin mamaki yace " sab'ani kuma? wani irin sab'ani " sai lokacin na tuna cewa ashe bai sani ba shiru nayi ban tanka ba ganin nayi shiru yasa shi komawa office d'in nashi ya barni nan zaune
3rd person's POV
Komawa office d'in yai Arshad dake tsaye fuskar nan a cunkushe shi dariya ma yake bashi don haka ya dafa shi ya na cewa " Buddy wannan d'aure fuskar fa ta mecece?" hararar shi yayi tareda cewa " ban sani ba Malam a gabanka ai yarinyar nan take min rashin kunya " shanye ta shi dariyar yayi yace " aina tai maka rashin kunyar Buddy ina tsaye fa bata ko tanka ka ba fita tayi ma " cikin masifa yace " muguwar rashin kunya ma kuwa......how dare she walk out on me? Kuma this is not the first time da tai hakan last time she cut me off while I was talking daurewa zuciya ta nayi ranar nace ta fita don in da ta tsaya ranta sai yai mugun b'aci " ya k'arashe maganar yana k'wafa
Yasan duk wainnan abunda ya lissafa a wurinshi rashin kunya ne amma ya san shima ba k'aramin abu yaiwa Faheemahn ba har ta aikata hakan cikeda rarrashi yace " toh ka yi hak'uri bazata sake yin hakan ba " k'wafa yayi dukda cewa ba ita ta bashi hak'urin ba amma yaji sanyi a ran shi cewa yai " kaidai ka fad'i hakan amma ita kam ko ajikinta nunawa ma take bata san tayi ba " dafe goshi yayi kafin ya furta " itama zata baka hak'urin amma kaima please ka rage wainnan halayen domin samun irinta sai an sha wuya kai kanka kasan da hakan " hmm kawai yace yana zama shima zama yayi yai mai maganar abinda ya kawoshi wurin bai wani dad'e ba ya fita
Office d'in Faheemahn ya koma tana zaune ta sanya glass a idanunta aikinta takeyi cikeda natsuwa wacce tana cikin abinda yake burge shi da ita zaman da yai yasa ta d'ago cikeda murmushi a fuskarta tace " Yaya Sahal har yanzu baka wuce ba ?" Gyad'a kai yayi tareda cewa " eh fa ammm.....abinda ya dawo dani akan ki shine please ki daure ki bawa A.B hak'uri ......."
Da mamaki ta kalleshi saidai bai bata damar tankawa ba yace " .......and please kar ki sake katse shi in yana magana ko kuma walking out on him cos he hate that kinji " had'iye mamakinta tayi don abun nasu ya wuce mamaki kansu kawai suka sani gani take inda shi akewa irin abinda ake matan bazai tab'a d'auka ba saidai ba hakan bane yana mai mafiyin hakan bai tab'a damuwa ba don ya fahimci mutumin nashi sosai in ma yayi fushin da kanshi zai sauko cikin sanyi tace " okkk"
Jin yanda ta amsa yasa yai murmushi yana cewa " sai anjima" don ya fahimci itama daru ne yake cinta daga yanayin amsar da ta bashi ya san labarin hak'urinta daga bakin matar shi amma ta sanar mai bata son raini ko kad'an girgiza kai yayi yana cewa " Allah ya kawo musu rahama a tsakaninsu" bayan fitar shi da kamar minti 10 ne ta tashi ta nufi office d'in nashi yana zaune saidai ba aiki yakeyi ba a hankali tace " Sir I'm sorry " kallon cikin ido yai mata kafin yace " issokay ya wuce ai....where is the paperwork " cewa tayi " I want to edit it sir " a hankali yace " don't edit it bring it like that......." Ok ta furta tareda fita daga office d'in ajiyar zuciya ya sauke yana mai rakata da idanunshi...............
#vote
#comment
#share
#add
Love y'all😍
Deejasmah🦋🔐❤