Chapter 4
*ZANEN ZABUWA*
©️ *Nana Haleema.*
*Page 4*
Jannat dai kawai ta rubuta abinda tasan zata iya ne ta bayar amma har aka gama test d'in nan hankalin ta da tunanin ta baya jikin ta ga ciwon kai mai zafi da ya kawo mata ziyara a lokacin. bayan sun fito daga hall d'in Nafisa ta biyo ta tana fad'in, "Jannat qalau kike kuwa?." Kama hannu Nafisa tayi tace, "Nafisa kaina zai tsage biyu-biyu nake gani." "Subahanallahi sannu, muje ga inuwa can ki zauna."
A tare suka k'arasa wajan ta zauna tare da dafe kanta, "kodai ki taso muje clinic a baki magani?." Girgiza kai tayi alamun a'a kafin tace, "basai munje ba zai daina yi min ciwon."
Shiru ne ya biyo baya Jannat tana dafe da kanta ga jinyar zuciyar ta da take yi da take mata ciwo itama, "Sannu Jannat." Kai kawai ta d'aga mata bata ce komai ba idon ta a kulle, kira ne ya shigo wayar ta ta d'auka ta duba ganin sunan mai kiran ya saka ta mik'awa Nafisa wayar alamun ta d'auka, d'aukar wayar Nafisa tayi tare da yin sallama daga can b'angaren ya amsa yace, "Nafisa ina Jannat d'in?." Nafisa ta kalli Jannat sannan tace, "Gata nan bata da lafiya." A rud'e a yace, "meya same ta?."
"Kanta ne yake ciwo sosai ko magana ma bata iyawa." D'iff taji an yanke wayar ba tare da ya sake magana ba tabi wayar da kallo sannan tace, "ya kashe wayar." Jannat tace, "da kin sani baki ce masa bani da lafiya ba yanzu sai ya baro wajan aikin sa yazo nan."
Nafisa tace, "ai gwara yazo wata k'ila shi in yazk kya yarda ya kaiki asibitin, amma fa in badan nasan yayan ki ne da sai nace gaskiya akwai wani abu a k'asa tsakanin ki dashi." Jannat ta d'an yi murmushi kawai bata ce komai ba har lokacin hannun ta yana dafe da kanta sabida ciwon da yake mata.
Shiru sukayi a karo na biyu babu mai magana a cikin su kusan mintina ashirin suna a haka kafin suga tsayuwar mutum a kan su Nafisa ta d'ago kasancewar kan Jannat a sunkuye yake kuma ta kulle idon ta, ganin wanda yake tsaye ya saka gaban Nafisa yayi mummunan fad'uwa ta had'd'iye saliva bakin ta har rawa yake wajan fad'in, "Sannu da zuwa." Ko kallon inda take baiyi ba ya kalli Jannat da kanta yake a sunkuye har lokacin bata d'ago ba yace, "Ke!." Bata d'ago ba duk da taji hakan bai saka ta motsa ba.
"Jannat ana yi miki magana" Nafisa ta fad'a a tsorace tana tab'o Jannat hankalin ta a tashe, "ko waye yake yi min magana ki fad'a masa ya koma yaje a koya masa sallama a gidan su sannan kuma ni ba suna na ke ba ya bari in yasan suna na sai yazo yayi min magana" Jannat ta fad'a kanta na k'asa har lokacin bata d'ago ba ga azabar ciwon da take ji.
Ran Muhsin ya b'aci ga wanda ya kwana dashi daman gashi ya sake zuwa ta sake b'ata masa rai, hannu ya saka ya finciko kanta ya d'ago dashi kana ya saki fuskar ta yace, "ke wai y'ar gidan uban waye a Nigeria?." Idon ta kulle har lokacin yadda ya d'ago da kanta da k'arfin gaske ba k'aramin k'ara mata azabar ciwon kan yayi ba hakan ya saka ta sake rintse ido tana so ta tantance a inda take dan sai da hankalin ta ya gushe na wasu sacanni.
"Ba magana nake miki bane wacece ke? Me kike tak'ama dashi a garin nan?" ya fad'a cikin d'aga murya yana saka hannu ya jawo ta ta mik'e tsaye, luuuuuuu tayi zata fad'i sabida yadda kanta ya sara ganin ta ya d'auke duhu ya ziyarci idon ta k'afafuwan ta baza su iya d'aukar ta ba, jikin mutum taji ta fad'a an saka hannu an rik'o k'ugun ta gamm duk da ba'a hankalin ta take ba amma gudun da zuciyar ta ta k'ara da kuma khamshin turaren sa ya tabbatar da jikin wanda ta fad'a, "Jannaty meya same ki?" Ya fad'a a rud'e yana d'ago ta daga jikin sa yana kallon fuskar ta amma idon ta har lokacin a kulle yake.
Nafisa ya kalla yace, "Pls Nafisa taimaka min mu kaita mota." Ba musu Nafisa ta zagayo ta rik'e Jannat duk da har lokacin tana rab'e a jikin sa suka fara tafiya.
Muhsin ganin kamar sun mayar dashi shashasha a wajan hakan sai ya sake fusata tashi yasha gaban su yana k'arewa Imran kallo kafin yace, "wato kaine ka tsaya mata take ganin dai-dai take da kowa ko? To ina so ka fad'a mata ni nafi k'arfin na tsaya ina magana da talakawa kamar kai da ita, ka kuma ja mata kunne wallahi tallahi zan ja mata masifa da bala'in da bata tab'a tunani ba a rayuwar ta, Ni Muhsin nafi k'arfin ku na kuma k'arfin Family d'in ku gabad'aya kuma....."
Imran yayi saurin dakatar dashi ta hanyar fad'in, "enough mr man! Bamu da lokacin sauraron shirmen ka in labarin kanka kake so ka bayar kaje gidan radio ko gidan tv a nan mutane zasu san labarin ka har su shaida ka su kuma bawa wasu labari, bama da buk'atar wannan surutan banza naka understand?" Yana gama fad'a masa haka bai jira mai zaice ba suka zagaye shi suka wuce duk da yaso ya karta masa warning akan Jannat amma rashin lafiyar ta tafi d'auke masa hankali.
Da kallo Muhsin ya bisu ya d'aga k'afa zai bisu daga bayan sa aka rik'e shi ya juya ya kalli wanda ya rik'o hannun sa yace, "Su waye wad'an nan talakawan da zasu dinga fad'a min magana san ransu?."
Wanda ya rik'o shi yace, "Relax Muhsin k'yale su zo muje" ya fad'a yana jan hannun sa. Fincikewa yayi cikin fad'a yace, "A kan me zaka ce na k'yale? Kasan abinda suka fad'a min ne?." Kallon mutanen da suke tsaye a wajan yayi sannan ya dawo da kallon sa ga Muhsin yace, "ba girman ka bane ba kalli yadda mutane suke kallon ka kazo muje zamuyi solving problem d'in a nutse" Jin hakan ya saka ya bishi yana huci suka shiga cikin makarantar.
Imran kuwa yana fita wani private hospital dake kusa da makarantar suka shiga da ita dan gani yake kafin ya k'arasa murtala za'a d'auki lokaci, bayan ya faka motar ya fito ya bud'e mata gaban motar ta fito Nafisa ma ta fito ta rik'e ta shima yana rik'e da hannun ta suka shiga ciki.
kasancewar private ne direct wajan Dr aka nuna musu suka shiga, nurse d'in da take d'akin ta tashi ta rik'o Jannat aka kwantar da ita akan gadon dake d'akin kasancewar sunga yanayin ta emergency condition ne.
Yadda take dafe da kanta hakan ya tabbatarwa da Dr d'in kanta na mata ciwo sosai bai tsaya b'ata lokaci ba ya fara had'a allura ya k'araso inda take yayi mata aka had'a drip aka saka mata kafin ya fara auna dp d'in ta, Imran da Nafisa suna daga baya suna kallon duk abinda ake mata zuwa lokacin bacci ya d'auke ta, Dr ya gama auna bp d'in ta ya zare stethoscope d'in daga kunnen sa nurse d'in da take d'akin taja gadon da Jannat take kai aka nufi da ita d'akin da zata samu hutu.
Likitan ya kalli Imran yace, "bismillah". Ba musu ya k'araso ya zauna akan kujerar da ya nuna masa Nafisa ma ta zauna sannan Dr yace, "meye sunan ta?." Jawad yace, "Khadijah Aminu."
Likitan ya rubuta kafin yace, "shekarun ta nawa?."
"Shekarar ta ashirin da d'aya." Rubutawa likitan yayi sannan ya kuma cewa, "tana da aure?." Girgiza kai Imran yayi alamun a'a.
Sake rubuta wa yayi sannan yace, "Meye alaqar ku da ita?." Imran yace, "k'anwa tace." Girgiza kai Dr yayi ya cigaba da rubutan sa wanda ya d'auki tsahon lokaci kafin yace,
"Waye yafi kusanci da ita?." Kallon Dr Imran yayi kafin yace, "ni ne, ko mahaifiyar ta bata da kusan da ita kamar yadda nake da kusanci da ita."
"Amma meyasa ka bari har damuwa tayi mata yawa ta haifar mata da ciwon kai mai zafi wanda har hakan yasa ruwan jikin ta ya kone jinin ta tayi k'asa sosai?."
Da sauri Imran ya kalle shi yana wara ido waje yace, "Jinin ta yayi k'asa kuma Dr?." D'aga kai Dr yayi yace, "Sosai ma kuwa shine abinda ya haifar mata da ciwon kan da kuma jirin da take ji, a karanci shekarun ta bai kamata a same ta da wannan condition d'in ba dan kasan da a samu jini yayi k'asa sometimes gwara jini ya hau, tayi k'ank'anta sosai da wannan yanayin, gaskiya in ta samu lafiya ya kamata ka tambaye ta abinda yake damun ta kar abin yayi gaba a samu matsalar da tafi wannan."
Imran ya kalli Nafisa da tayi shiru tana jin mai likita yake cewa kafin ya kalli Dr yace, "Insha Allah zanyi k'okarin hakan, amma jikin nata da sauk'i ko?."
"Baccin da ta samu zai saka taji dad'i sosai dan tana tashi zaku iya tafiya ma, sai dai a kula da gaba." D'aga kai Imran yayi baice komai. mik'o masa takarda Dr yayi yace, "ga magani an rubuta kaje pharmacy ka karb'a."
Karb'a yayi suka fito tare da Nafisa maimakon ya tafi sai yaja ya tsaya ya kalli Nafisa yace, "Nafisa akwai wani abu da ta tab'a fad'a miki wanda yake damun ta?."
Girgiza kai Nafisa tayi kafin tace, "Bata fad'a min komai ba amma ni kaina na fuskanci hakan a tare da ita, ta rage walwala sosai magana ma sai ta kama take yi ga yawan tunani sometimes sai kazo kusa da ita bata sani ba, ko a d'azu da muna test bana tunanin ta rubuta wani abun kirki dan gabad'aya hankalin ta baya jikin ta in nayi mata magana sai tace na taya ta da addu'a."
Numfashi ya fesar sannan yace, "Amma meyasa baki sanar dani ba kika barta take zama da damuwa har hakan na k'okarin affecting karatun ta?."
"Daman yau da yamma nayi niyar nazo gidan naku na same ka nayi maka magana a kan hakan dan gaskiya abin nata yayi yawa kasan kuma yanayin karatun mu yadda yake." Girgiza kai yayi yace, "jeki d'akin da suka ce kar ta farka" yana fad'ar hakan ya barta a wajan ya nufi pharmacy jikin a sanyaye matuk'a kamar an masa dukan tsiya haka yake jin sa babu kwari ko kad'an a tare dashi.
yana zuwa pharmacy ya mik'a musu takardar suka karb'a jimm kad'an sai ga bill an mik'o masa ya karb'a tare da dubawa, gaban sa yayi mummunan fad'uwa ganin adadin kud'in da ya kashe a iya mintinan da suka yi a asibitin, "50 thousands!" Ya fad'a a bayyane cikin mamaki da kuma al'ajabi.
Cashier d'in da ya bashi yace, "yes Sir, kud'in ganin likita 15 thousand, kud'in magani 15 thousand sai kud'in gado da d'akin da take ciki 20 thousand."
Girgiza kai Imran yayi ya sake kallon takardar tabbas abinda aka fad'a haka ne gashi nan a rubuce a jikin paper, gefe ya koma ya tsaya ya shafa aljihun sa ya fito da kud'in dake cikin su yana dubawa, gabad'aya dubu goma ne a jikin sa shima kuma dubu takwas kud'in Umma ne da ta aika ya karb'o mata wajan yayan ta dubu biyu ce kawai tashi a ciki.
Wayar sa ya d'auko ya shiga bincike account d'in sa nan ma babu kud'in da zasu iya amma akwqi wanda zai d'an gare kafin yayi waya a ara masa.
Atm card d'in ya d'auko yana fad'in, "sai dai ka cire wani abu a cikin kud'in bani da duka a yanzu gaskiya." Cashier d'in yace, "Sir ai an biya kud'in naka ga receipt d'in" ya fad'a yana mik'o masa takarda.
da mamaki Imran yace, "an biya min? Waye to ya biya bayan nidai nasan ban biya ba?." "Sir wata budurwa ce yanzu ta bar nan wajan, yauwa ka ganta nan ma" ya fad'a yana nuna masa wacce take tawowa wajan.
Juyawa yayi ya kalli wacce ake nuna masa, ta canja kaya zuwa atampa d'inkin fitted gown ta yafa mayafi hannu ta rik'e da iphone 14pro max da mukillin mota kirar honda, a hankali ta tako inda yake bugun zuciyar ta na k'aruwa amma haka ta daure ta cije ta kalle shi tace, "nice na bayar".
Kallon up and down yake mata ya tamke fuska kamar bashi ba yace, "amma bance miki ina da buk'atar hakan ba ko? Beside nan ba company bane balle ki nuna ikon ki." Duk da yadda zuciyar ta take bugawa da k'arfin gaske hakan bai hana ta yin murmushi ba tace, "Nima bance ai zan nuna iko na ba Imran alkhairi ne nayi niya kuma nayi." D'age girar sa sama yayi yace, "in kika yi niyar alkhairi ai ba lallai sai a kaina zakiyi ba akwai mabuk'ata da yawa meyasa sai kika zab'a?."
"A kanka Allah ya nufa."
"Collect your money bana buk'atar alkhairin naki."
"Ba'a mayar da alkhairi Imran, nasan ban kyauta maka ba d'azu amma kayi hak'uri raina ne a b'ace a d'azun shiyasa, ka tambayi ko waye wulaqanci b hali na bane ba." Baice komai ba ya mik'awa cashier d'in Atm d'in sa yace, "Wanda ta bayar ka bawa mai buk'ata ka cire nawa bill d'in."
"Haba Imran hakan bai kamata ba tunda har na baka hak'uri ya kamata ace ka hak'ura" ta fad'a masa kamar zatayi kuka cikin kwantar da murya.
Shiru yayi yana tunani dan shi kam baya son abinda zai jawo masa wulaqanci a rayuwar sa shiyasa ya kwammaci ya kwashe kaf kud'in da yake dashi ya biya shi ya zauna babu ko sisi da dai yaje yace a bashi a wulaqanta shi gwara yace a ara masa shima kuma inda yasan za'a bashi.
maganar ta ta sake katse masa tunani tace, "Ka daure please." D'ago idanun sa yayi ya kalle ta akayi sa'a suka had'a ido tayi saurin d'auke nata idon sabida yadda numfashin ta yayi barazanar kwace mata ta lumshe ido tana sauke ajiyar zuciya. "Nagode" shine abinda ya furta kawai ya juya zai koma tayi saurin tsayar dashi ta hanyar fad'in, "kuma gobe ka dawo aiki dan Allah wallahi ba'a san raina na furta abinda nace ba, ka yafe min ka dawo bakin aikin ka." D'aga mata kai kawai yayi ya wuce ba tare da yace komai ba.
Da mutuk'ar farin ciki da walwala Mufeeda ta juya ta fita daga reception d'in asibitin tana ji kamar an canja ta sabida farin ciki da take ciki wanda bata tab'a tsintar kanta a cikin sa ba.......
Free page😁
_Wannan labarin na kud'i ne ki biya naira 300 kacal ki karanta cikin nutsuwa da kwanciyar hankali, domin biya tuntub'i wannan number but only WhatsApp. ***_
Wattpad @ Nana_haleema
Arewabooks @nanahaleema11.