HATSABIBAN TSIBIRI

10

by @mrsjmoon

HATSABIBIN TSIBIBI

By Mrsjmoon


Adabi Writer's Association (AWA)


https://arewabooks.com/book?id=63a2e3d8821822a8402d8eb1 follow me on Arewabooks 馃枙


*Ayimin Affuwa kwana biyu ina cikin hidima ce shi yasa ku ka jini shiru.*


Page 10.


Part d'in Mamie Fulani ta nufa ta shiga k'aton falon da sallama, Lailah ce ta amsa cikin dishewar murya wacce ke zaune gaban Sadauki bisa alamu laifi tayi masa. Da sauri Maryam tayi nufin juyawa ya daka mata tsawa.


"Ke!"


Tsak ta tsaya batare da ta juyo ba.


"Zo nan dama ina shirin kiranki."


'Nashiga uku Allah yasa dai ba masifa Lailah ta janyomin ba.'


Ta ambata a ranta ya yin da a fili ta juyo jikinta na rawa tare da furta "Ni?"


Shiru shi ne amsar da ta samu sai tasami kanta da 茩are masa kallo sanye yake cikin kayan sarauta wanda yafi ta'amali da su domin kafin ka gansa da 茩ananan kaya aiki ne sai ko suit wanda da an gansa cikin shigar ke nuni da zaiyi tafiya ne sai kuma a filin motsa jiki inda ke shigar sport wear.


"Please Maryam ki zo kiyi masa bayani wallahi ba ruwana da Muhib, shi ne ke takurani ke biyoni gida."


"Keep quiet!"


Ya ambata a fusace.


"Sorry Yaya, dan Allah ka taimakeni ka saurari bayanin bakin Maryam domin ita, Neera, da Zuhra ne shaiduna akan bayanin da nake yi maka, wallahi Allah ba ruwana da Muhib."


Kallo kin rainani ya auna mata sai ta fashe da kuka ta kama k'afarshi janye 茩afar ya yi tare da mik'ewa ya nufo k'ofar fita saboda kukanta ya karya masa zuciya kuma a take ya yarda da gaskiya take sanar da shi.

Maryam na ganin tasowarshi ta runtuma da gudu tamkar zata kifa sai lamarin ya bashi dariya ya murmusa tare da juyowa ya ce da Lailah "Ki fita sabgar mara natsuwar yaron nan idan kuma kina son mu sa k'afar wondo 蓷aya da ke ne to in sake ganin 茩afarsa a cikin Masarautar nan sannan in har kin san kin kamu da son shi to kiyi gaggawan cireshi a ruhinki domin kinfi 茩arfinsa ta ko wani fuskan kuma ke mai tsarki ce dan haka ba zan bari ki auri mai cike da dattin najasa ba, a bisa umurnina ki koreshi koro na har abada."


Ya kai 茩arshen maganar na runtse ido domin yanajin tamkar bayyiwa masoyan adalci ba.


Gyada kai ta yi tana share hawayen da ke zubo mata, ganin na kallonta sai ta motsa baki a hankali ta ce "Nayi maka alk'awarin dakatar da shi daga zuwa Masarauta tare da nesantarshi na har abada duk da dama shi ke haukansa ni bai isheni kallo ba."


"Da kyau."


Murmushi tayi ya maida mata da martani ya juya, har ya fice ya dawo ya ce "Saura ki ha蓷a baki da wancan mara kunyar ku turomin macizai saman gadona kamar yarda kuka saba aikatawa idan anyi maku fa蓷a."


"Allah yaya ba ruwana Neerah ce da aikin kasan bana yin Ofi sai da babban dalili."


"Nadai sanar dake kada inga maciji a muhallina."


Sunkuyar da kai ta yi tana murmushi domin tsayawa zancen nan na nufin ya huce kenan.


"Humm zan gyara maku zama ne musanman ita da ta rainani."


Ya ambata yana barin wurin.


"Ka soma gyara kanka Babana domin kai da su duk kanwar ja ce wani fanninma kafisu tsorata mutane da Macizai wai lamarin har kan Mai Martaba dan ya sanar da kai gaskiya."


Da sauri ya dawo falon ya rik'o hannun Mamie yana k'ifta mata ido, alamun tayi shiru.


"Yes, ka soma gyarawa kanka zama kafin ta zo kan wasu wanda basuyi kwatan-kwacin laifin da kake kan aikatawa ba."


"Wayyo Mamiena me na yi kuma?"


"Babban zunubi na auri saki da kuma tsoratar da Musulmi ta hanyar fito da macizai su razanasu akan laifin da baikai ya kawo ba, kwanaki Mai Martaba har kusan fad'uwa 茩asa ya yi dan tsoro, tabbaas da ba dan ina kusa ba da anji mugun labari sakamakon macizai da suka cika turakanshi marasa kyan gani sannan tamkar almara suka b'ace, ganin anyi binkice ba agano komi ba sai na tabbatar kaine ta turosu, anya Babana hakan ya kamace kuwa?"


"Mamie ya wuce fa."


Ya furta cikin tsare gira ganin Lailah na k'unshe dariya.


"Bai wuce ba, mai jin magana kawai kada a fad'i 蓷ayan."


"Please Mamie ki manta da lamarin, ai natuba da jimawa."


"Anya Babana kai ka蓷ai ne kuwa?"


"Me nayi kuma Mamiena?"


"Watsi da cikar kamala wato aure sunnar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam.


"Ayya Mamie ki bar maganar auri sakin nan domin yana daga cikin zanen 茩addarar shi wanda bawa bai isa kufce masa ba saboda rubutacce ne daga Allah."


Duk kallon bakin falon sukayi a tare, Dr. Muneerah ce tsaye idanu jajur bisa alamu kuka tayi.


"A'a Likita bokon turai, lamarin Babana ko da 茩addara to son zuciya ya soma yi masa jagora domin ba sau 蓷aya ko biyu ya aikata laifin ba har fa sau hu...


"Mamiena ya tuba ai ba zai sake komawa ga zunubin ba ko yaya Yarima?"


Kafeta da idanu ya yi batare da ya amsa ba.


"Yes Neerah yaya ya yi tuba na gaskiya da yardan Allah ba zai sake komawa ga wannan laifin ba, zaiyi aure ya zauna lafiya da iyalinsa wannan a rubuce yake."


Lailah ta amshe da sauri tana kallon idanun Sadauki.


"Au, in na fahimta kuna bayan iya shegen da yarik'a aikatawa kenan?"


"A'a fa Mamie amma dai tunda ya wuce to abar d'aga zancen gudun 蓳acin rai kinsan abu ka蓷an ke sanyashi cikin tunani ya soma wasan b'uya da kowa kuma hakan kan jefashi cikin ka蓷aici sannan hakan bai kamata ba yana Sarkin Gobe na fuskantan matsin rayuwa."


"Muneera wai nawa Babana ya biyaki ne?"


"Na me fa Mamie?"


"Na campaign mana."


Ware ido ta yi Sadauki ya murmusa tare da russunawa gaban Mamie ya yi mata rad'a wanda ita ka蓷ai tajiyo abinda ya ambata aikam ta sauke masa dundu tana furta "Allah ya tsare, ya kare, can ga su gada wai Zomo yaji kid'an farauta, wallahi a kul 蓷in ka da wannan lamarin kadaiji na sanar maka in ba so kake mu koma gidan jiya ba."


"Allah Mamie na zama kurna akan lamarin sam banji me kike cewa ba."


"Amsa naka Sadauki, Allah kada naji ko na gani kuma nan da sati biyu ka kawo mana matar aure ko ranka yafi dare duhu da fatan katuna maganar Mai Martaba."


"Mamiena dan Allah ki ami...


"Nagama magana Babana sannan kada na sake ganin ka tasa k'anninka a gaba da zancen baka son suna zance tunda ba jik'asu zamuyi mu sha ba."


"Mamie da dare zan dawo muyi maganar a gaban Abba domin a wannan gab'an banjin zan ja da baya ba."


"Na zama abokiyar wasarka ko Baba Ali?"


"Tuba na ke Fulanin Mai mar...


"Gidanku na ce Sadauki."


Girgiza kai yayi tare da sumbatar hannunta da ke ri茩e da shi tun dazun kana ya saki ya iso daf da Neerah ya rage murya ya ce "Iyayi kawai to ban gode ba."


"Gobe ma rana ce da Muneerah kake zancen 蓷an Samari."


"Mamie 'yarki ta rainani fa."


Ya ambata cikin kawo mata duka ta gofce.


Banza Mamie ta yi masa sai ya fice yana cije lips gami da nuno Neerah da yatsa cikin salon wasa ya yin da ita kuma keyi masa gwalo. Murmusawa Mamie Fulani tayi domin abinda ke saurin sakata farin ciki shi ne ganin walwala a fuskan Sadauki Aliyu.


"Ke kuma taho naji damuwarki da kika tahomin da idanu kamar jan nama."


"Ciwo sukemin Mamiena."


"Kika sake ambatarmin k'aryan nan sai na sa蓳a miki."


"Affuwan Mamie kaina ke ciwo kuma kin san ban da juriyan ciwo ko ka蓷an, shi ne nayi kuka Ammi ta koroni wai na dameta da jan hanci kada in saka masu mura ita da yaranta."


"Ayya sannu, kyale Nana ai ciwo na kan kowa, taho kisha magani domin na san halinki na gaba da magani wai kina Likita amma kina gudun magani, Allah ya kyauta kam."


Cikin murmushi ta iso ta zauna gefen Mamie tare da manno jikinta da 茩afarta, sai ta dafa kanta cike da kulawa take yi mata sannu kana daga bisani ta bawa Lailah umurnin 蓷auko mata maganin ciwon kai a d'akin barcinta, cikin dibara Neerah ta gudu kafin Lailah ta dawo ta nunawa Mami a biyota da shi dakin Lailah saboda abinda Neerah ta tsani shansa shi ne magani.


***

Hajiya Umma ta ya kika yi wannan waftar na fed'ewa Sardauna biri har wutsiya shin kin manta waye shi akan gaba da bin bokaye? To wallahi tun wuri ki dawo hayyacinki ki sanja dabara domin ina da tabbacin bazamu ta蓳a samun ha蓷in kansa ba tunda kinayi waftar sanar da shi gaskiyan lamarin da muke kai."


"Ki bari kawai Hajiya Kilishi wai a zatona in yaji Aljana na tare da Sadauki zaifi yin farin ciki tare da bamu ha蓷in kai har mu kai ga nasara."


"Kin manta har kwanar gobe suna fita rangadi tare domin ginuwar 茩aunarsu kuma 茩aunar da mai Martaba ya dasa a zukatansu bai ta蓳a gogewa sai dai zan sanar da ke hanyar gaskiya domin kawo nak'asu a 茩aunarsu shi ne sai mun tashi tsaye mun sa an raunatashi yarda zasu zamo basa ga maciji ko ka蓷an shi ne zamuyi nasarar 蓷ora shi akan turban da muke so haka game da son kud'insa sai anyi mana aiki ta yarda kome kika nema ya baki batare da kai ruwa rana ba tunda yana da dukiya kuma ba mai amfana da shi sai makirar matarshi da uwarta ke kuwa sai hange daga nesa to sam hakan ba mai yiwuwa ba ne, yarda kika sha wahalar haihuwar sa gami da rainon sa dole ya zamo ke ce ta farko da zaki mori dukiyarsa tare da sanin duk kan bayanen 茩addarorinsa."


"Tabbas kinyi gaskiya Hajiya Kilishi, zantukanki masu amincewa ne gareni, yanzu zan baki wuk'a da nama ki zamo idanuna na kai da kawo tsakanin lamarin saboda yawan fitana a b'oye nada hatsari dan idan Mai Martaba ya sani kashina ya bushe wata k'ilama aurena ya sami tangarda tunda angama da shi bai kallona da daraja sai muguwar Fulanin can wacce ba zata gama lafiya ba."


"Kibari kawai, gata bata jin Asiri."


"Kin manta waye Uwarta kenan? Ai Hajiya Dada cikakkiyar matsafiya ce domin maganar Malam Sale kenan duk in ya buga 茩asa Uwarta na tsaye kanta shi yasa sai yarda tayi da Mai Martaba."


"Aikam na yarda Hajiya Dada na tsafi domin dubi zafin Chiroma amma a gaban Nana Safiyya sai ya koma fulawa saboda laushi."


"Uhm ai 茩arshen su ba zaiyi kyau ba in sha Allah."


Allah ya amsa."


"Amin Aminiyata."


Murmushi Hajiya Kilishi tayi sannan ta maida hiran kan abinda suka zauna a kai, inda cike da kisisina take cewa "Dama ina shirin yi miki wannan maganar fitar da kanki sai nayi nazarin a wakilta Hud yana amsowa tare da sanya Sardauna amfani shi wanda ba sai ya zo hannunki ba kinsan Hud da iya kalaman makirci na tabbata cikin sauk'i zai sakashi yin amfani da maganin hankali kwance, kinga ko wanda zaici a abinci ne duk Hud zai bashi saboda in muna son ya sami farin jinin jama'a sama da wanda Sadauki ke da shi dole sai mun hada na ci a abinci da sha da wanka har da hayak'i."


"To ba matsala hakan za'a yi, zan turo maki sak'o anjima amma kada a amso na hayak'in nan saboda zai harbo jirjinmu."


"To madallah, bari in koma kada mai gidan ya neme ni."


"Yau ke ce da turakar kenan."


"Eh fa."


"Ok tafi nima ina da ba茩i anjima ka蓷an."


"To na wuce, Allah bamu yinin lafiya."


Motsa kai Ummu tayi cikin lumshe ido dan kanta taji na ciwo, harara Hajiya Kilishi ta zabga mata ta gefen ido tana zund'enta a fakaice sannan ta bu蓷e k'ofar ta fice cike sak'e-sak'en yarda tsarinta zai tafi batare da samun tangarda ba na ganin d'anta Hud ya haye karagar mulkin Mungaye tunda shima Babansa 蓷an Sarki ne yana da sarautar da zai iya Mulki ba sai lallai 'ya'yan Sarkin dake kan karagar mulki ba


"Wallahi bana son Sadauki domin tuni na kamla rabashi da Masarautar baki 蓷aya lokaci nake dakon ya yi a nemeshi a rasa daga ganan Hud ya zamo Sarki mai iko domin bazan bari Sardauna ya zame masa matsala ba a tafiyar ba."


"A'a Mamma ina mutuwar son Yaya Sadauki kuma shi nake burin gabatarwa Abba a matsayin zab'ina kamar yarda kuke dakon jin gwanina sannan ina tare da ke kan zamowar yaya Hud Sarki saboda lokaci ya yi da za a kawo sauyi ba lallai sai 'ya'yan Sarkin dake mulki ne zasuyi ta gadon sarautan ba, duk da a gefe 蓷aya ina jin kamar ba zai iya ba dan ban ta蓳a jin mashayi ya hau karagar mulkin Mungaye ba."


A razane Hajiya kilishi ta dubi inda mafi soyuwar 'yar nata 蓷aya tilo mace cikin 'ya'yanta maza hu蓷u. Gyara tsayuwa ta yi tare da jinjinawa mahaifiyar nata kai alamun bata tabbacin furucinta tare da cigaba da cewa "Yes Mamma ina yin Yaya Sadauki kuma shi ne mijina da yardan Allah dan na k'udiri aniyar d'aura d'amarar jure zama da shi a duk yarda ya ke, ni ce zan kawo 茩arshen auri sakinsa insha Allah"


'Wata sabuwa inji 'yan ca-ca, hak'ik'a aiki ya sameni ni jikan Magaji.'


"Momma muje nasan baki rasa shawarar da zaki bani akan auren sannan kada ki kushemin zab'i a kan abinda ya ke zanen 茩addararshi ne wato auri saki."


Dafe kai Hajiya Kilishi ta yi tana jin wani mak'ak'in d'aci na sauka saman harshenta.


'Tirk'a haka zakiyimin Zuhra? To wallahi ko zaki mutu ne ba ki isa hanani kora Sadauki duniyar da bazai kuma waiwayen Masarauta ba.'


Ta sake ambata cikin ranta tana dallawa bayan Zuhra harara wacce take shirin shiga d'akin barcinta.


***

"Hey Doctor Neerah, me ke faru ne har ya sakaki kuka?"


Motsa yatsunta Neerah ta yi tamkar zata furta kalma sai kuma ta tsuke bakinta tare da hayewa saman gado ta juyawa Lailah baya.


"Dan Allah Muneera sanar dani damuwarki ko in had'a ki da Mamie nasan ita zaki sanar da ita."


"A'a Lailah kada kiyimin haka, yanzu taso muje ki rakani gidan Hajiya Dada."


"Asibitin da kikace zaki shiga fa?"


"Na fasa."


"No ki muje na rakaki domin ba kyau sa蓳a al茩awari."


"Na tura masu Dr. Hassana harma ta isa kinga sak'on da ta turomin yanzu."


"Ok amma gaskiya kada ki sake irin haka tunda kin san ke suka fi bu茩ata."


"In sha Allah."


Suka fito bayan Neerah ta gyara fuskanta ya yi kyau suka sami Mamie zaune hadimai kewaye da ita suna yi mata hira cike da sakewa zamowarta mara girman kai irin na mafi akasarin matar sarakuna. Bayan sun amsa gaisuwar hadimai sai suka sanar da ita inda suka nufa ta tsare gira kafin tayi maga Neera ta rigata da cewa "Please Mamina gidanmu na biyu zan kai ziyara fa Allah daga nan ba inda zamu wuce kinsan halinmu.."


"Muneera bana son yawo ne alhalin kuna 'yan manyan gida musanman yanzu da ake maganar aurenmu"


"Mamie dubo fa sanyin idaniyarki zamuyi ba yawo ba sannan baza mu wuce awa biyu ba zamu dawo in sha Allah."


"Ok to shiga kitchen ki wuce mata sak'onta dama Junaid yanzu zai kai mata kun hutash-sheshi kam."


"A'a Mamie suyi tafiyarsu inyi tawa da Maryam dama na ce ta shirya zamuje gidan tsohuwar Mamie ziyara.


"Mun huta kam."


Lailah ta ambata cikin murgud'awa Junaid baki, ya kawo mata duka ta koma bayan Mamie tana dariya.


"Affuwa dai Yarima Junaid."


Kuyangi suka ambata cikin girmamawa kansu sunkuye.


Hannu Mamie ta d'awa su Neerah suka fice sunayi mata godiya yayin da Junaid ya dubi wata kunyanga ya bata umurnin da ta d'auko masa sak'on a kitchen, ta wuce da sauri tamkar zata kifa.


"Bi a hankali Dudu."


Mamie Fulani ta furta cikin kulawa saboda yarda ta ke daraja d'an Adam, ko zaman kuyangi a sashinta na dole ne dan zamowarta matar sarki amma tafi son ta kasance daga ita sai 'ya'yan dana al'umma sosai take tausayawa bayi shi yasa wad'anda ke sashinta suke jin da蓷i fiye da wanda ke sashin Umma da sauran matan masarautar kuma hakan ya 茩ara mata k'ima a idanunsu da zuri'arta dama duk wanda ya ziyarci sashin to zaka samu kuyangin na karrama duk bukatun sa.


Momyn Haske ne 馃グ


*Muna saida ingantaccen man ayu wanda ya zo daga Chad. Yana maganin Infection, asma, limoniya, mura, ciwon basira ciwon kai, ciwon baya, ciwon 茩afa, ciwon mara, kaikayin jiki dana matse-matsi, yalwatuwar ni'ima tare da samun gamsuwa a turaka da sauransu, muna saida 蓷aya ko sari mai so zai iya tuntubar number nan ta WhatsApp ko kira. ***. Yarda ake amfani da shi za a jik'a Lipton sai a d'iga man ayu a ciki a shanye da d'umi-d'umi za a iya zuba zuma ko siga a ruwan Lipton d'in dan gudun d'aci haka za a iya zubawa a ruwan Tea a sha. Masu asma da limoniya kuma zasu jajjaga tafarnuwa su matse ruwan su zuba ruwan d'umi da man ayu su shanye. Masu Infection duk in suka wanke wurin da ruwan zafi sai su saka man ayu haka masu kaikayin jiki idan sun fito wanka sai su shafa amma zasu sha da ruwan Lipton, Allah ya 茩ara mana lafiya Amin.*