37
🧟♀️ *WATA SOYAYYAR!* 🧟♀️
*_Labari/Rubutawa_*
*AMINA ABUBAKAR YANDOMA*
( _Meenat A Yandoma_ )
tare da
*ZAINAB MUHAMMAD*
( _Indian Girl_ )
*NOTE*
_Labarin nan zamu rubuta shi ne a yadda yazo, duk abinda kuka gani mun rubuta a haka aka tsara labarin._
*GARGAƊI!*
_A guji yi mana amfani da labari ta ko wace hanya sai tare da izinin mu_
*PROMO! PROMO!! PROMO!!!*
🥳🥳🥳
*Zumar ƙiba da ta Hips wadda kuka sani a 3500 yanzu ta dawo 3000🤩, ga kuma garin ƙiba 3in1 muna sai da ƙwara ɗaya 3500 bokiti kuma 4500 a cikin sauƙi promo muke💃🏻, ga kuma maganin infection me aiki sadidan wanda ake sha da lipton akan 1000, Hanzar ta ki mallaki naki yar uwa domin neman ƙarin bayani ku tuntube mu akan wannan number ***, Siyan na gari meda kuɗi gida.*
*PAGE 6️⃣7️⃣&6️⃣8️⃣*
...A gigice na juyo dan gane ma idona me yi mani wannan kiran; sanye yake cikin kayan fulani ga sanda a hannun shi kanshi rufe da hular saƙi.
Ganin asirina na gaf da tonuwa ya saka na gigice na kasa furta koda kalma ɗaya ce sai faman binshi da ido nike.
"Baiwar Allah me kike yi cikin wannan jejin me matuƙar haɗari kin ko san a inda kike ga kuma yaririya na gani a hannun ki."
Jin abinda ya faɗa ya saka ni fashewa da kukan ƙarya ina me shassheka.
"Wannan yarinyar bata da uba dan haka bawan Allah ka gyale ni kasheta kowama ya huta."
"Ba zani barki ki kasheta ba baiwar Allah domin ɗa da kike gani kyauta ce daga Allah ba zani barki ki kashe ta ba idan baki son ta ni ki bani ita domin munyi shekaru sama da takwas amma Allah bai bamu haihuwa ba."
Shuru nayi ina tunanin akan maganar shi domin ni kai na nasan in na bashi ita sunyi bankwana da iyayenta har abada.
"Gata na baka ni sunana Ƙwadaga kai fa"?.
"Jauro ina zaune nida mamata a wata rugar Fulani."
"Jauro ga yarinya na baka ina so kayi nesa da ita kada ka bari ko a mafarki in sake haduwa da ita."
"Na aminshe zan riƙeta tamkar ɗiyar dana haifa ba zata yi kukan maraici ba."
Jin abinda Jauro ya faɗa ba ƙaramin tayar mani da hankali yayi ba domin naso ace na kashe jinjirar nan dan har abada bani ƙaunar inga Ta rayu amma babu yadda zanyi dole ne in barta da wannan ɗan ƙauyen."
Juyowa tayi ta fuskanci mahaifiyar Fatima
"Tun daga lokacin ban sake tunanin asirina zai iya tonuwa ba ashe talala ce Allah yayi mani akwai ranar tonon asirina, ina me sake gama ku da girman Allah ku yafe mani domin na cutar da ku ba kaɗan ba alhakin ku kaɗai bazai barni in zauna lafiya ba, magana ta ƙarshe da zan faɗa ita ce na shiga ƙungiyar asiri domin nice sanadin mutuwar Fatima kwaɗayin abin duniya ya kai ni ya baro ni."
"Innalillahi wa'inna ailaihurrajiun."
Ita ce kalmar da tafito dafa bakunan mutanen Falon musamman mahaifan Fatima da suka daskare tsabar tashin hankali.
Alkhamis kuwa kuka yake tamkar ƙaramin yaro jin arin abubuwan da mahaifiyar shi ta aikata.
Umar kuwa miƙewa yayi yana neman mabigi domin ji yake babu abinda zai hana shi karya ƙafar Ƙwadaga, da ƙyar mahaifin Fatima yayi nasarar haka ni yana dannar shi.
"Amma Ƙwadaga kin cuce mu kinyi mana abinda har mu koma ga mahaliccin mu ba zamu taba mantawa dake, kin ɗauke mana farin ciki kin rana mu da ɗiyar mu tun kafin ta buɗe ido ta ga mahaifiyar ta Allah mabazai taba barin ki ba."
Inna Habiba ta faɗa hawaye nabin fuskarta.
Mahaifiyar Fatima kuwa ta ma kasa magana sai hawaye dake kai koma a kan fuskarta.
Jauro kuwa tsabar mamaki ne ya lullubeshi;
"Ashe ba ɗiyar ta bace ta ba shi ita ma sato ta tayi; innalillahi wa'inna ilaihirrajiun."
"Ƙwadaga kin cuce ni kin faɗa mani ƙarya alhalin kinsan ɗiyar nan sato ta kika yi ashe ba ɗiyar ki bace."
"Shikenan Fatima zaki koma wurin iyayenki mu kuma kin bar mu har abada, Allah ya isa tsakanin mu dake kwadaga."
Mahaifiyar Fatima ta faɗa.
"Fatima ba zata taba barin ku ba domin kun riƙi Fatima riƙo na tsakani da Allah baku da laifi ko alama a cikin wannan al'amari har yanzu Fatima a matsayin ɗiyar ku take."
Inna Habiba ta faɗa.
Alkhamis kuwa hawayen Fuskar shi ya share tare da kallon mahaifiyar shi.
"Babu yadda na iya kece mahaifita ta domin komi kika zama bazan gujeki ba amma baki kyauta mani ba, kin tarwatsa rayuwata kin bar mani abun faɗa kin kasa bani tarbiyyar da ta dace bansan komi ba sai neman mata da shaye-shaye Baki kyauta mani ba."
Kukan daya ci ƙarfin shine ya tilasta ma shi kasa ƙarasa maganar.
Duk wanda ke wurin sai da tausayin Alkhamis ya kama shi domin harga Allah sun san Ƙwadaga ita ce wadda ta lalata shi, shiyasa akace ka nemar ma yaran ka uwa ta gari tun kafin suzo duniya.
"Alhamdulillah komi ya dai-dai ta a yau ne kuma zani bar jikin ƴar uwata Fatima iyayena da ƴan uwana sai wata rana."
Fatima na gama maganar suka ga tayi wata atishawa barci ya ɗauke ta.
Da ido suka bita cike da mamaki
"Malam dama nasan fatalwar marigayiya Fatima ce a jikin ta tun lokacin da tazo gidan mu."
Inna Habiba ta faɗa.
Murmushi Mahaifin Fatima yayi tare da kallon Inna Habiba
"A musulumce babu Fatalwa duk canfi ne na malam bahaushe, domin abinda Muslumci ya koya mana shine in mutum ya mutu to aljanin dake jikin shi ne zai riƙa yin suffar shi yana zoma mutane yana ce masu shine wance daya mutu, shi yasa ake so ko ruwan wankan gawa kada a bari ba tare da an zubar dashi ba an kwanke wurin domin ana amfani dashi wurin aikata ba dai-dai ba."
Sun aminta da zancen malam nan Umar ya dubi Alkhamis.
"Ka bamu takardar ƴar uwar mu domin zamanka da ita ya zo ƙarshe."
Alkhamis kuwa ji yayi tamkar an watsa ma shi ruwan tafasshiyar darma a zuciya, bazan iya rabuwa da Fatima ba koda za'a datse numfashin shi daga gangar jikin shi.
Ihu Ƙwadaga ta fara kurmawa tana faɗar gasu nan zasu kasheta ta tona masu asiri, ganin tana ƙoƙarin barin gidan a guje ya saka Alkhamis kama ta ya saka ɗaki ya kulle.
"Alhaji ga Fatima nan ta dawo hannunku dan Allah ku kula da rayuwar ta, mu zamu koma Rugar mu sai wata rana Fatima."
Jauro ya faɗa tamkar zai zubar da hawaye.
"Kunyi mana halacci domin kun riƙi Fatima da zuciya ɗaya dan haka ba zamu barku ku tafi ba tashi zaku yi muje gida in ku ka kwana biyu sai ku wuce."
Haka suka miƙe suka bar Alkhamis nan yana zubar da hawaye, har sun kai bakin ƙofa Inna Habiba ta juyo ta kalli Alkhamis.
"Ka biyo mu da takardar Fatima."
Tana gama maganar suka fice daga gidan...
***
...Jidda kuwa share hawayen fuskar ta tayi tare da cigaba da basu labarin.
"Abinda na haifa ba komi bane face Ɗiya mace amma gurguwa ce wadda gurguntar ta ta tsananta ko tafiya ba zata iya yi ba, murna ce ta koma ciki domin harga Allah ba zani yadda in reni gurguwa a matsayin ɗiya ta ba, da farko Yazid bai nuna mani ya damu ba sai da na zaunar dashi nike ce mashi mu samu mafita kada mu bari ɗiyar nan ta girma, da farko bai fahimci abinda nike nufi ba sai da na zauna nayi ma shi dalla-dalla, a firgjce ya dubeni Jidda ɗiyar tamu zamu kashe saboda Allah ya yo ta a gurguwa; ƙwarai ma kuwa ko so kake ta girma a riƙa kiranmu da uwayen gurguwa duk inda muka fita a riƙa nuna mu?, Jidda ba zani iya kashe ɗiya ta ba kima bar wannan maganar ni duk yadda take ina son ta, yana gama maganar ficewa yayi ya barni a ɗakin, a lokacin ban damu ba domin ko suna ba'a yi ba haka iya tazo taga jinjira tana ta murna Mahaifiya ta kuwa da taga Gurguwa ce ko ɗaukar ta bata yi ba, wannan abu shi ya ƙara tunzura ni akan in kashe ta tunda har na kusa dani zai iya kyamatar ta to ina ga na waje kuma; huɗuba Yazid ya yima yarinyar da sunan Iya wato Lubabatu muna kiranta Baby, ana gama hidimar suna naci gaba da takurama Yazid game da maganar Baby domin yanxu tana da watanni biyar bani so ace tana ƙara girma ba tare da mun aika da ita inda ba'a dawowa ba, zuciya bata da ƙashi lokaci ɗaya Yazid ya aminta da magana ta domin a tunannin mu koda ta mutu zamu haifi wasu yaran dan haka guba muka zuba mata a cikin madarar jarirai muka bata tasha, a gabanmu ta rika harbe-harbe tana kuka ta rirrike ni har rai yayi halinshi."
Kukan da yaci ƙarfin Jidda ne ya saka ta dakatawa da labarin.
"Yanzu Malam idan muka ce zamu ɗauki fansar mu akan mutanen nan munyi laifi"?
Baby da kuma Hafsa suka faɗa a tare.
"Tabbas anyi maku zalumci mafi muni, ashe lalacewar al'ummar mu har takai iyaye su iya kashe ɗiyar su domin gudun kada ace sun haifa Gurguwa; mutum nawa ke neman haihuwar ido rufe Allah bai basu ba wasu ko Gurguwar aka basu murna suke, sai ku da aka azurta da ita kuka kashe ta, innalillahi wa'inna ilaihirrajiun."
"Jidda mi yasa kika yi man haka, dama kece kika kashe Hafsa Jidda kun cuce ni kin jefa ni a cikin bala'i kin kai ni kin baro ni."
Yazid ya faɗa yana kuka tamkar ƙaramin yaro.
"Kai ka cuci kanka Yazid da ka tsaya ka biye ma mace gashi nan ta jefa ku cikin musiba wadda in kuka yi wasa baku tuba ba kuka mutu zaku gamu da Allah, yaku waɗan nan halittu ku sani mu da ku duk Allah ne ya halicce mu kuyi haƙuri domin muma Allah yana haƙuri damu, ku bar waɗan da suka mutu su samu salama a cikin kaburruran su domin ku ba komi bane face jinnu."
Girgiza kai suka yi tare da furta
"Mun haƙura amma akwai wani albishir da zamu yi ma Yazid da kuma Jidda shine ba zaku sake haihuwa ba har abada domin mun ɗauke Mahaifar Jidda Yazid kuma mun lalata kwayayen haihuwar shi, yanzu zaku rayune ba tare da samun ko gurguwar da kuka rena ba.
"Na shiga ukku na cuci kai na innalillahi wa'inna ilaihirrajiun Umma kin cuce ni kin saka ni a hanyar banza kin cuci rayuwa ta."
Yazid kuwa daskarewa yayi ya kasa koda ɗaga ɗan yatsan shi ne.
Nan halittun suka bace ya rage daga malam sai mahaifan Jidda da kuma Yazid.
"Kin gani ko Jidda Yanzu wa gari ya waya kin biye mahaifiyarki gashi nan ta kai ki ta baro ki, Tun baya abinda nike guje maki kenan amma kika riƙa fatali da magana ta ita duniyar nan dama duk abinda ka shuka shi zaka girba."
"Wannan ya zama darasi a gareku ku sani kun tabka babban kuskure amma lokacin tuba bai ƙure maku ba zaku iya tuba kuji tsoron Allah ku dakatar da duk wani shirme, ke kuma Mahaifiyar Jidda kiji tsoron Allah ki daina abinda kike tun kafin ƙasa ta rufe maki ido."
Nan yayi masu nasiha me ratsa jiki kafin ya tafi.
Miƙewa Yazid yayi tare da duban Jidda.
"Jidda bani da abinda zan iya ce maki domin laifi ne nima da nawa sakacin dan haka kije na sake ki saki ɗaya."
Ficewa yayi daga gida zuciyar shi na wata irin suya.
Jidda Kuwa mikewa tayi tare da ƙwala kururuwa ta yanke jiki ta faɗi...
*MEENART..........✍🏻*