Chapter 5
*ZANEN ZABUWA*
©️ *Nana Haleema.*
*Page 5*
A b'angaren Muhsin kuwa tunda suka bar harabar makaranta suka shiga mota yake mita tare da jan tsaki yana kwafa kana ganin sa kasan cikin b'acin rai yake, wanda yake jan motar ya kalle shi yace, "Calm down mana wannan ba abinda zai saka ka b'ata ranka bane bafa."
Kallon abokin nasa yayi yace, "abinda zai saka ni dariya ne kenan ko?." Y'ar dariya yayi kad'an yace, "ba haka nake nufi ba, a gani na wannan ba wata matsala bace babba da zata b'ata ranka, su waye iyayen su balle su da har zaka dinga fushi a kan su."
"Ni yarinyar nan zata kallah ta cewa stupid man shi kuma wanda yake goya mata bayan har da cewa wai basu da lokaci na, sun san waye Muhsin kuwa?". "Rashin sanin ne ya saka suke maka haka ai, amma in ka nuna musu ikon ka ko wani suka ji zai aikata hakan a gare ka zasu yi saurin dakatar dashi balle su." Bai sake cewa komai ba Samir ya cigaba da tuk'in sa shi kuma yana aikin kwafa har suka isa gida.
Koda yayi parking bai sake yiwa Samir magana ba ya fito ya shiga ransa a b'ace sosai har zai wuce sama Mummy dake zaune a falon tace, "Mushin zo nan". Ba musu ya dawo ya zauna kusa da ita akan kujera ta kalle shi cike da kulawa tace, "Lafiya naga ranka a b'ace haka?." Sai da ya girgiza kai sannan yace, "Mummy wasu banzaye ne a school d'in da Daddy ya saka ni zuwan ta dole suke neman su dinga saka min ciwon kai, Mum ni wata yarinya zata kalla ta cewa stupid man?." Zaro ido waje Mamy tayi tace, "kai ta cewa stupid? Waye uban ta a Nigeria?."
"Ba y'ar kowa bace Mummy kawai irin yaran talakawan nan ne masu shegen rawar kai amma zan gyara musu zama daga ita har wani banza da yake tare mata."
"Kar ka k'yale su in ta kama ka saka a kore ta a makarantar, kar ka k'yale ta kayi mata hukunci dai-dai da ita sabida ta fahimci ruwa ba sa'an kwando bane ba." Baice komai ba ya mik'e da sauri ya hau sama ko waiwaye baiyi ba.
Mufeeda kuwa tuk'i take cikin walwala da nishad'i tana ta aikin murmushi har ta k'araso gida tayi parking ta shiga falo da sallama, Mummy ta d'ago ta kalle ta tace, "Yau har kin baro office d'in?."
Murmushi Mufeeda tayi tace, "na tashi Mum." Kallon ta Mummy tayi tace, "ke kin shigo kina farin ciki shi kuma yayan ki ya shigo ransa a b'ace, ke kuma me ya saka ki nishad'i haka?."
Sai da ta zauna kusa da Mummy sannan tace, "Mum daga 2 hours later zuwa yanzu i think I'm filled in love with someone, because ban tab'a jin abinda nake ji akan wani ba kamar yadda nake ji a kansa Mum, ko magana yake bana iya d'auke ido a kansa fa daman gashi very handsome guy."
Mummy da ta saki baki tana kallon ta tayi murmushi tace, "wowww waye wannan mai sa'ar haka da ya sace zuciyar auta na in less than five hours haka? D'an wanne governor ne?".
Murmushi tayi mai kyau sannan tace, "zan baki labarin sa Mum dan nima yanzu na saka ayi min binkice a kansa, ban d'auka daga kallo d'aya ana fad'awa soyayya sai yau" tana fad'ar hakan ta mik'e itama ta shige ciki tana dariyar farin ciki.
*☆☆☆*
Imran kuwa koda ya koma d'akin da Jannat take zama yayi a kan kujerar da take kusa da gadon yana kallon fuskar ta da rame lokaci d'aya, kallon Nafisa yayi yace, "Nafisa ya kamata ki koma gida kar a neme ki."
Murmushi tayi tace, "na fad'awa Mama ina tare da ita asibiti anjima kad'an zan tafi na fiso naga ta farka." Murmushi yayi tare da girgiza kai k'imar ta ta k'aru a idon sa ganin tana son abinda yake so.
Kiran sallar azahar ya saka shi ya mik'e ya kalle ta yace, "zanje nayi sallah na dawo". D'aga kai kawai tayi ya fita itama ta shiga band'akin dake d'akin tayi alwala ta fito ta tayar da sallah akan carpet d'in dake d'akin.
Bata jima da idarwa ba ya dawo da sallama hannun sa d'auke da leda ya mik'awa Nafisa yace, "ga abinci kici". Karb'a tayi tace, "Nagode." Baice komai ba ya zauna tare da cigaba da kallon Jannat ko kifta idon bayayi.
Baifi mintina goma da shigowar sa ba Jannat ta bud'e ido tana kallon d'akin tana so ta tantance a inda tane. "Jannatyyy" ya furta a hankali yana kallon ta hakan yaja hankalin ta ta juyo da idon ta inda yake, k'okarin mik'ewa zaune take yayi saurin mayar da ita ta kwanta yace, "bari ki gama dawowa normal sai ki tashi, pls Nafisa help me ki kira nurse" ya fad'a yana kallon Nafisa.
Ba musu ta mik'e ta fita shi kuma ya dawo da kallon sa gare ta suka had'a ido ta janye idon ta kafin tace, "Zan iya tashi". "Babu ciwon kan?." "Eh sai kad'an."
Shigowar Nurse da Nafisa ya hana ta mik'ewa Nurse d'in ta zare ruwan da ya k'are sannan tace, "ya jikin naki?."
"Da sauk'i sosai."
"To yayi kyau, zaki iya tashi tsaye?."
Jannat ta mik'ewa zaune ta diro da k'afar ta k'asa ta tashi tsaye tayi kamar zata fad'i yayi saurin mik'ewa ya rik'o ta, "nurse har yanzu jikin ta babu k'arfi" ya fad'a yana rik'e da ita. "Noo zata dawo dai-dai yanzu sake ta ka gani."
"Kar na sake ta ta fad'i fa."
"A'a baza ta fad'i ba."
Shi dai Imran bai yadda ba hakan ya saka shi k'in sakin ta yana rik'e da ita har lokacin, dariya Nurse d'in tayi tace, "lallai wannan angon kana ji da wannan amaryar taka" ta fad'a cikin raha dan ita har ga Allah ta d'auka ma'aurata ne.
Kallon Jannat Imran yayi itama kuma ta kalle shi sai ya samu kansa da yin murmushi baice komai ba ya sake ta ta tsaya cak nurse d'in tace, "To baga shi ta tsaya ba cak ba, kuje Dr nason ganin ta" tana fad'ar hakan ta fita Nafisa da take kallon su ta bata mayafin ta ta yafa ya rik'e hannun ta suka fita.
A hankali yake takawa ganin kamar tana jiri ya saka shi matsawa kusa da ita sosai ya zagaya da hannun sa kafad'ar ta ya rik'e ta suka cigaba da tafiya, Jannat kuwa fad'uwar gaba da k'aruwar bugun zuciyar tane suke k'aruwa lokaci d'aya taji jikin ta ya soma rawa a lokacin suka shiga office d'in Dr ya zaunar da ita akan kujera shi kuma da Nafisa suka tsaya a bayan ta, Dr yace, "Khadijah ya jikin naki?."
"Da sauk'i."
Dr ya kuma cewa, "babu abinda yake damun ki yanzu?." Girgiza kai tayi alamun eh kafin yace, "amma Khadijah na tambaye ki wani abu zaki bani amsa?." D'aga masa kai nan ma tayi alamun eh tana kallon sa, "a wacce makaranta kike?."
"B.u.k".
"Which course?."
"Bsc nursing."
"Ma sha Allah, amma kina wannan course d'in babba kuma mai kyau ya kika bari damuwa zatayi tasiri a zuciyar ki haka? Kina so ki fad'i exmas ne a kore ki gabad'aya?."
Kanta ta sunkuyar k'asa hawaye ya taru a idon ta tayi saurin mayar da hawayen tace, "A'a." Dr yace, "Khadijah kina yarinyar ki bai kamata ki bar damuwa tayi tasiri a zuciyar ki ba haka, ki kula kodan karatun ki in ba haka ba zata kawo miki nak'asu babba a karatun ki kin gane ko?." D'aga kai tayi alamun eh kafin yace, "good, zaku iya tafiya Allah ya k'ara lafiya."
D'ago idon da zatayi suka had'a ido da Imran yana jifan ta da wani irin kallo dole ta d'auke kai gaban ta na fad'uwa dan tasan ba makawa sai ya turke ta ta fad'a masa abinda yake damun ta.
Mik'ewa tayi ya rik'e ta suka fita a hankali suka k'arasa har inda motar sa take, Nafisa ce ta shige baya Jannat ta zauna a gaba suka tafi. kasancewar yasan gidan su Nafisa yafi kusa ita ya fara saukewa yayi mata godiya sosai haka ma Jannat d'in sannan suka wuce gida.
Har suka je baice mata kanzil ba itama kuma bata ce komai ba ya faka motar ya fito ya zagayo ya bud'e mata ta fito suka shiga gidan Gwaggon tare.
Gwaggo na zaune ta amsa sallamar da sukayi tana fad'in, "sannun ku da zuwa". Zama yayi yace, "yauwa Gwaggo, mun same ki lafiya?."
"Lafiya lau, har ka baro wajan aikin?." D'aga kai yayi tare da fad'in, "eh Gwaggo da yake Jannat d'in ce bata jin dad'i yanzu ma haka daga asibiti muke."
Kallon Jannat d'in tayi kafin tace, "meya same ta?." Kallon ta yayi kad'an kafin ya d'auke kai ya dawo da kallon sa ga Gwaggo yace, "ciwon kan nan ne dai na jiya shine ya haifar mata da jiri sai da muka je asibiti aka saka mata ruwa."
Gwaggo tace, "Subahanallahi abin har ya kai haka, sannu Jannat Allah ya k'ara sauk'i." Imran ya amsa da amin kafin ya mik'awa Gwaggo maganin ta yace, "ga maganin ta, akwai abinci a ciki na kawo mata taci?." Gwaggo tace, "eh akwai, daman kuma bata karya ba ta fita ko yunwa ai ta saka mata juya."
Baice komai ba ya mik'e ya shiga kitchen d'in Gwaggon ba jimawa ya dawo da faranti a hannun sa mai d'auke da tuwon shinkafa miyar zogale, kusa da ita ya zauna ya mik'a mata yace, "maza ki cinye yanzu ki bani farantin."
Fuskar sa a d'aure yake magana babu alamun walwala a tare dashi hakan ya saka taji shakkar sa ba musu ta karb'a ta ajjiye tana niyar mik'ewa yace, "ina zaki je?." "Zan wanke hannu na ne da baki na" ta fad'a tana kallon sa, "koma ki zauna bara na kawo miki" ya fad'a yana mik'ewa shima.
A roba mai dan girma ya debo mata ruwan ya bata ta fara wanke hannun ta sannan ta kuskure bakin ta, a hankali ta fara kai lomar tuwon bakin ta tana taunawa badan dad'i ba sai dai idanun sa da suke kanta, Gwaggo dai kallon ta take tana cin abincin kana gani kasan ba dad'in sa take ji ba hakan ya saka tace, "ko kunun tsamiya za'a dama miki?." Da sauri ta d'aga kai alamun eh tare da ajjiye farantin tuwon tana satar kallon sa, "yau alhamis zuwa anjima Umma zata dama sai a kawo mata, ki cinye abincin nan fa" ya fad'a yana nuna mata farantin tuwon dole ta d'auka ta cigaba da turawa badan tana so ba.
Sai da yaga ta kusa cinyewa sannan ya jawo ledar maganin ya 'ballo mata ya mik'a mata had'e da ruwa, karb'a tayi tasha maganin ya mik'e tsaye ya d'auke plate d'in da taci tuwon ya kai kitchen ya dawo ya d'ebo ruwa a robar d'azu ya bata ta wanke hannun ta sannan yace, "Kije ki kwanta ki huta." Ba musu ta mik'e ta shiga d'aki ba tare da ta sake kallon sa ba.
Gwaggo ta kalle shi tace, "sannu Imran da k'okari Allah ya biya ka ya saka maka da alkhairi ya baka mace ta gari ya sa aljanna ce makoma."
Murmushi yayi sosai har haqoran sa suka bayyana yace, "Amin Gwaggo, bara na shiga wajan Umma inda wani abun sai ki aika a kirawo ni." "Toh Imran ka gaida Umman taka". Da to ya amsa ya fita ya shiga gida.
Da sallama ya shiga tsakar gidan kasancewar da rana baiga Umma a tsakar gida ba hakan ya saka shi shiga falon da sallama, daga ciki aka amsa wanda yake zaune a kusa da Umma yace, "Wato Imran ganin ka sai dai da asubayi." Murmushi yayi sosai ya k'arasa ciki ya zauna tare da fad'in, "barka da rana Baba." Shima murmushi yayi yana kallon d'an y'ar uwar tasa da farin ciki yace, "barkan ka dai Imran, ya aikin naka?."
"Alhamdulillah komai yana tafiya dai-dai."
"To masha Allah, ina ka baro Jannat?." Kafin yayi magana Umma tayi dariya tace, "gwara dai da ka tambaya daman in kaga wata ai zaka ga zara."
Murmushi yayi kad'an yace, "Bata da lafiya ma yanzu ma daga asibiti kuma dawo dan har ruwa sai da aka k'ara mata." A tare suka had'a baki wajan fad'in, "me ya same ta?."
Imran yace, "Ciwon kaine ya saka mata jiri."
"Allah ya kara sauk'i, amma dai yanzu jikin nata da sauk'i ko?" Umma ta fad'a tana kallon sa.
"eh da sauk'i sosai dan yanzu ma ta gama cin abinci ta kwanta." Baba yace, "Allah ya bata lafiya". Ya amsa da amin tare da mik'ewa yace, "Umma in an dama kunun nan anjima zan mik'a mata". "A'a na mik'a mata ma da kaina nima sai naga jikin nata". "To shikenan bara naje na huta" ya fad'a yana fita daga falon.
Da kallo Baba ya bishi yana murmushi kafin ya dawo da kallon sa ga Umma yace, "ina jin dad'in yadda Imran yake nunawa yarinyar nan kulawa sosai wallahi, yarinyar nada hankali da nutsuwa gashi kuma bata da wa ko k'ani sai shi."
Umma tayi murmushi itama tace, "nima haka wallahi yarinyar akwai shiga rai sabida bata da wani hali mara kyau, nifa badan Imran yana cewa shifa ba soyayya ce a tsakanin su ba da zan fi kowa farin ciki in aka ce yau Imran ya zama mijin Khadijah." Baba yace, "kamar kin shiga raina kinga abinda nake sakawa wallahi, amma nifa sai nake ganin kamar akwai soyayya a tsakanin su kawai yana b'oyewa ne."
"Nima da dai nayi tunanin hakan amma da yace ba haka bane sai na kawar da tunanin tunda shi kallon k'anwa yake mata." Baba ya gyara zama yace, "eh to haka ne, amma dai ni ina jin zan ari bakin sa na ci masa albasa zan nema masa auren ta wajan mahaifin ta in ya dawo daga ziyarar qauyen da yaje."
Umma tayi y'ar dariya tace, "Da Imran ya samu mace ta gari da muke masa addu'ar samu kullum." Cikin jin dad'i Baba yace, "Insha Allahu hakan zata kasance bara mu ga mai Allah zaiyi nan gaba." Daga nan suka cigaba da hira sama-sama kafin Baba yayi mata sallama ya tafi gidan sa kasancewar basu da nisa.
Imran bai sake shiga gidan su Jannat ba sai bayan magariba a lokacin har Umma ta shiga ta fito ya shiga tsakar gidan da sallama kamar koda yaushe, amsawa Gwaggo da ke kan k'aramar kujera tayi tana masa sannu da zuwa, waje ya zamu akan tabarmar da take zaune ya zauna kafin yace, "Gwaggo sannu da gida." "Yauwa Imran, kasha ruwa lafiya."
"Lafiya lau Gwaggo, ya mai jikin?."
"Mai jiki da sauk'i sai dai rashin walwala da take fama dashi ko zaman nan batayi da ta gama abinda zatayi zata koma d'aki."
D'an jimm yayi kafin yace, "Shikenan Gwaggo a barta ta huta daman gobe bata da lecture tafi samun kwari sosai."
"Ga mutumin naka dambun shinkafa nayi maka" Umma ta fad'a tana mik'o masa plate mai d'an girma wanda aka rife da wani plate d'in irin sa, d'auka yayi duk da baya cikin yanayin cin abinci sabida halin da Jannat take ciki amma ya daure yayi murmushi yace, "Ai kam nagode sosai Gwaggo, kamar kin san shi nake sha'awar ci gashi Umma ta cika min ciki da kunu da kosai." ya fad'a yana bud'e plate d'in ya fara ci a hankali.
Shiru ne ya biyo baya yana cin dabun a hankali kafin ya katse shirun da fad'in, "Gwaggo yaushe Abba zai dawo ne?." Gwaggo tace, "kasan qauyen babu wani network d'in kirki ba'a cika samun sa a waya ba amma d'azu dai munyi magana yace sai zuwa jibi insha Allah."
Girgiza kai yayi yace, "Allah ya kaimu lafiya, naga alama dai Abba yana jin dad'in qauyen nan". Bata ce komai ba tayi murmushi kawai.
Ya k'oshi da abincin so yake ya fita amma kuma baya tunanin zai iya barin gidan ba tare da yaga Jannat ba hakan ya saka shi kasa mik'ewa duk da yana son hakan, kamar Gwaggo ta fahimce shi tace, "Jannat zo ki d'auki dambun!" Ta fad'a cikin d'an d'aga murya.
Motsin ta da ya jiyo ya saka shi saurin juyawa yana kallon ta har ta k'araso wajan, kanta na k'asa ta kalle shi kad'an tace, "Yaya ina wuni." Maimakon ya amsa sai yace, "ya jikin naki?." K'arasawa kusa da Gwaggo tayi ta karb'i dambun kafin tace, "Da sauk'i sosai."
"Kinsha maganin ki?".
Girgiza kai tayi alamun a'a kafin tace, "yanzu in naci abinci zan sha."
"Zo ki zauna ki ci in kin gama kisha maganin." Baza ta iya masa musu ba dole ta zagayo ta zauna ta fara tura dambun badan tana jin dad'in sa ba.
Bata ci wani da yawa ba ta jawo maganin dake gefe tasha, yana kallon ta duk abinda take yi sai da tasha maganin sannan ya mik'e tsaye yace, "Gwaggo sai da safe." "To Imran Allah ya tashe mu lafiya" ya amsa da amin yana ficewa daga gidan. da kallon ta bishi tana jin kamar taje ta jawo shi ya dawo ya zauna taita kallon sa amma ina babu damar hakan, lumshe idon ta tayi hawaye suka taru a idon ta tayi saurin mik'ewa ta shige ciki ko maganin bata d'auka ba.
Free page😁
_Wannan labarin na kud'i ne ki biya naira 300 kacal ki karanta cikin nutsuwa da kwanciyar hankali, domin biya tuntub'i wannan number but only WhatsApp. ***_
Wattpad @ Nana_haleema
Arewabooks @nanahaleema11.