MIJIN MACE ƊAYA PART ONE

Chapter 24

by @ummindaddy77

 Ya kalli Hajiya yana dariya, "Ban san me Daddynta da Mummynta kuke ɗura mata ba yaushe muka yi budurin sunanta amma wai yanzu har ta kammala Secondary ana ƙoƙarin shiga Jami'a."


  Adnan ɗa ga Alhaji Saminu babban aminin mahaifin Hafsy tun yana da 5yrs yake wurin Abdulmajeed wan mahaifinsa da ke da zama a Cairo babban birnin Egypt, ba don mutuwa da ta ɗauke shi ba ma da kuma rashin jituwa da suka samu da iyalan Baffansa yaushe zai dawo wurin su.


  


Alhaji Saminu da Alhaji Abdullahi Malkohi, aminan juna ne sosai, shaƙuwar da suka yi da junansu da yadda suke amintaka idan ba faɗa maka a ka yi ba, za ka yi tsammanin su cikin umma ne don alaƙarsu ta yi nisa.


 Alhaji Saminu yana da wa da yake da zama Egypt, a hannunsa Adnan ya girma, tun yana da shekara 5 ya ɗauke shi a hannunsa ya yi karatu yanzu haka ya kammala Masters nasa, tun da yake wurin shi zuwansa ƙasa Nigeria bai fi a kirga ba kuma duk sa'ilin da ya zo mahaifinsa kan tura shi wurin amininsa don ya gaishe shi amma ba su taɓa haɗuwa da Hafsat ba.


 A shekarar da ya gama Masters nasa a Allah ya yi wa Alhaji Abdulmajeed rasuwa sanadin hatsarin mota, zama ya ki daɗi a tsakaninsu sai ya koma wajen iyayensa da zama.

Hafsy haka kawai ta ji tsikar jikinta na ta shi ɗago ido da za ta yi sai ta ga Adnan na kallon ta ko kiftawa ba ya yi da ta fakaici ba a kallon ta ta dalla masa muguwar harara.


   "Ina za ki kuma Hafsat?"

 Mahaifiyarta ce ta jefe ta da wannan tambayar sa'ilin da ta ganta tana ƙoƙarin miƙewa.

  "Mummy zan yi picking call ne ƙira na a ke." Ta amsa da "Okay."



 Tana fita bayan ta yi nisa ta ƙira number da aka ƙira ta har ta katse tana cewa:

  "Allah ya ja zamanin my bugun numfashina, ka fin na ci gaba da magana kaina a ƙasa a yi mini afuwa ka yi ta jira na shiru ko.?"


 Ya ja gwauron numfashi, "Wallahi dear ina ta trying number ki not available. Hope dai lafiya."


 Ta kanne ido, "Network problems ne, dear lafiya lau kawai wani ɗan uzuri ne ya riƙe ni shi ne aka samu jinkiri, amma gani nan zuwa gare ka yanzun nan."



 Ba tare da ta sanar da iyayenta ba, ta fice bayan ta hau adaidaita sahu ne ta kira Mummynta ta shaida mata ai ita ta koma gida. Alhali wurin habibinta ta nufa a Zoo domin su gana.


 Bayan sun gama waya ta dubi mijinta, "Alhaji ka san yarinyar nan me take faɗa min a waya?"

  "Sai kin faɗa, wai ta hau adaidaita sahu ta nufi gida."


  "My daughter akwai miskilanci, da ma yau tun safe na fahimci miskilancin sun motsa."

"Babu wani miskilanci raini ne ya yi mata yawa ni da ma na gane take-takenta ba son zuwan take ba. Za mu koma gida sai na nuna mata abin da ta yi ba ɗabi'a ce mai kyau ba."

   

  Hajiya Maimuna uwargidan Alhaji Ali ce ta yi magana, "Haba Hajiya, rabu da ita yarinta ke ɗibarta."

   

   

   

   Adnan yana daga kwance ya faɗa a fili , "Ba ta da laifi, ni ne mai laifi, saboda na dame ta da kallo kuma ni ma ba laifi na ba ne, laifin zuciyata ce."

   

   Maganar da ya yi ya sanya dukkaninsu kallon juna, kuma suka yi murmushi.

   

   Alhaji Ali ya dubi ɗan nasa, "Lallai ko ka ka yi babban laifi, ka korar mu da 'ya za ka fuskanci hukunci mai tsauri kuwa."

   

   Alhaji Abdullahi Malkohi, ya ce, "To ai shi ma ya faɗa muku ba laifinsa ba ne, laifin zuciyarsa ce, in har za ka hukunta mini ɗana, to kai ma za a hukunta ka saboda na san ka yi wa Mariya wannan kallon a farkon haɗuwa ko ba ka yi ba?

   

   Hajiya Saratu ta cafke, "Alhaji ya yi wallahi har sai da ya sa ni na yi tuntuɓe na faɗi a bainar jama'a bakina ya fashe saboda tsabar kallonsa."

  Dukkaninsu a wurin sai da suka tuntsire da dariyar maganarta.

  "Alhaji kin ga ko shi abin da ya yi ya fi na ɗana."

   Alhaji ya dubi matarsa, "Wannan kuma sharri kika yi mini, ke da wanke ki a ka yi kawai a ka kawo mini a matsayin amarya ban taɓa kallonki ba, ke ma ba ki ganni ba."

   

   "A bar dai tuna baya idan a ka ce za a yi tone-tone sai na bayyana sirrin."

   

   Ta dubi Alhaji Abdullahi, "Daddyn Hafsy amininka har durƙusa mini ya yi yana roƙon na amshi soyayyarsa amma ka ji cika bakin da yake yi."

   

   Ya tuntsure da dariya, "Na san za a yi hakan ai idan kin ce har kuka ma ya yi a kanki ba zan musa ba."

   

   "Kamar kana wurin kuka wiwi har da su majina kamar ƙaramin yaro haka ya dinga yi mini haɗe da magiya."


 "Za mu koma gida duk sharrin da kika yi mini zan rama."

   

   "Ba wani sharri batun gaskiya ne."

 Ya ce, "Shi kenan ka yarda da abin da ta ce kenan, ai idan a ka zurfafa bincike naka soyayyar da Maryam ka yi fiye abin da na yi.

   

   "Ga Maryam ɗin ai tambaye ta."

Tana dariya ta ce, "Ni ai mijin nawa gwarzo ne, mata ke bibiyansa ba shi ke bibiyansu ba, saboda farin jini irin nasa da kuma kwarjini."


 Duk suka fashe da dariya ya ce wa matarsa, "Kujerar Hajji uku na ba ki my wife ki kai wanda kike so."

 "Ba wani kina dai yi wa mijinki rufa-rufa ne dai kawai. To idan ma na yarda ke ma ashe ke kika bibiye shi, ke kika durƙusa rokon soyayya."


 "Don na yi abin da ka ce ma ai ba laifi ba ne, koyi na yi da Nana Khadija, saboda ita ta nemi soyayyar Manzon Allah. Ka ga kuwa ba kaina farau ba, kuma ba a kaina za a daina ba."


 "Shike nan kin gama magana ai tunda har da hujja, Maryama ta Audu."

 Tana dariya ta ce, "Faɗi kanka tsaye mutukaraba ba kuma."

 Yana dariya ya ce, "Uku dai suna kan hanya."

 "Allah ya kawo su da alheri su zo ba a kaina za su zauna ba."


  Ya sauke ajiyar zuciya, "Hira ba za ta ƙare ba, Hajjaju mu tafi gida hankalima fa yana kan Daddy’s girl."


 Ta miƙe ta yafa liffayanta tare da cewa:


 "To mu mun barku lafiya, Adnan Allah ya ƙara lafiya."


 Ya amsa da, "Amin Mummy, a gaishe mini da ƙanwata, kafin na zo gare ta.


  Hajiya Sara ce ta yi magana, "Yaran zamani Allah dai ya shiryeku ba alkunya."

 Ya kudunduna kansa bisa pillow yana dariya.

Hajiya Maryam na dariya ta ce, "Kuma iyayen zamani ba ku ji kunya ba kun faɗi son ranku shi ya ji kunya.'

 Hajiya Sara ta yi musu rakiya ta nuna godiyarta suka yi wa juna sallama.


Tafiya suke a mota ya dubi matarsa, "Hajiya, yarinyar nan tabbas akwai abin da ke damunta, kuma yana neman yin tasiri a zuciyarta ya kamata idan muka isa gida ki yi ƙoƙarin jan ta jiki ki bugi cikinta ko za a samu a shawo kan lamarin."


 "Ita ta sani da damuwarta rabu da ita idan ya yi wari za mu ji."

"Ni ba zan bari har ya kai ga yin warin ba domin idan ya kai ga wannan matakin zai iya lahanta mini 'ya, tun da ke ba za ki yi ba ni zan yi."



 Zaune suke a sanyayyir wuri mai ɗauke da ni'ima mai sanya walwala da farin ciki da nutsuwa ga duk zukatan da suka ziyarci wurin. Domin duk yawan damuwar da ke tattare da kai muddin ka ziyarci wajen za ka mance su ballantana kuma a ce babu damuwar.


 Ga duk wanda ya kalli fuskokinsu zai fahimci wannan fuskokin da cike suke fal da farin ciki.


  Ta lumshe ido tare da cewa, "Ba zan taɓa gajiyawa ba da kallon wannan beautiful face ɗin ba, kunnuwana ba za su taɓa gajiyawa da sauraron zazzakar muryarka ba wacce ta fi sarewa daɗi my love you are my soulmate."


 My angel, i don't know much, but i know i love You and only you."


 Kayataccen murmushi ta yi saboda abin da ya fito a bakinsa yayi mata daɗi.

 Ya ci gaba da cewa, "My dear ko da za mu shekara dubu ba za mu kosa da juna ba saboda mun zama hanta da jini." Ya duba agogon da ke wayarsa, "Amma saboda mu gyara gaba gawara ki koma gida kar su Mummy su riga ki zuwa, su fahimci ashe ba gidan kika je ba, kamar yadda kika ba ni labarin yadda kuka yi. Kar su fara zargin wani abu."

 Ta dube shi ta wutsiyar ido, "Don’t mind your self, in sun fara zargi sai me ye a ciki? Ka san ko ba daɗe ko ba ji ma dole su sani." 


 Ya miƙe ya zura hannayensa cikin aljihun yana cewa, "Duk da haka, ki yi haƙuri haɗuwa ya ai yanzu aka fara."


 Cike da shagwaɓa ta ce, "So ma kake mu rabu ko? Ka gaji da kallona da saurarona na gode."


 Ta haɗa rai alamar fushi ta yi gaba sauri ya yi ya shawo gabanta ya dinga rarrashinta da yi mata lafuza masu daɗi har ta sauko, sun fito bakin kwalbati musu ya kaure a tsakaninsu ita Hafsy ta ce sai ta ga tafiyarsa tukun ita ma ta tafi shi ma kuma ya ce sai ita ta fara.


 Ta tura baki cikin shagwaɓa ta ce, "Wallahi Allah sai dai mu kwana a nan in har ni zan fara tafiya kafin kai."

 Murmushi ya yi, "Su Hafsatu ikon Allah? Shike nan mu tsallake titi ki sani, don naga alama idan na biye miki su Mummy za su riga ki zuwa gida."


 Ta lumshe ido, "Ko kai fa, Mus'ab ina son ka kalli cikin kwayan idona, don maganar da zan yi na da muhimmanci."

 Haka suka zurawa juna ido ba ko kiftawa ta sauke ajiyar zuciya, "Mijina Mus'ab ina son ka, ina kishinka bisa dalilin haka, idan na sanya ka a adaidata zan shaidawa driver kar ya kuskura ya ɗauki wani ko wata har sai ya sauke ka, kuma a duk lokacin da ka ga mata ka runtse idonka, kallo ɗaya na halatta maka a tsakanin ku wanda ka yi shi ba tare da ka sani ba ka ji shalelena one in a million."

 


 Dariya ya yi ya ce, "Lokacin da ban same ki ba ma mata ba sa gabana ballantana a yanzu da na same ki, kin rufe kofa ke ce mace ɗaya da idona ke gani a matsayin mace masoyiya, dukkanin sauran mata ina musu kallon ba su da bambanci da maza.

 Ki sa a ranki a idonki ko a bayan idonki ba mace da zanyi alaka da ita na soyayya bayan ke ki cire kokonto game da ni ki yarda da ni."


 Fari ta yi da ido, "Na yarda da kai my one and only kawai dai ka san halin kishinmu na mata especially a kan abin da muke so."


 Adaidaita sahu ne empty ya zo ta tsayar da shi, "Shehuri north za ka kai shi, kuma drop."

 Ya amsa da, "To Hajiya." Bayan ya shiga ya zauna ta ajeye bandir na kuɗi a cinyarsa ta gudu mai adaidaita sahu ya tafi da shi.


 Ita ma ta tsallako ta hau adaidaita sahu ta ce GRA za a kai ta.


  Zaune suke a falo da sun ji motsi sai su kai duba ga kofa ko Hafsat ce.

 "Alhaji mun kai fa 15 mins da dawo kaga yarinyar nan har yanzu shiru." Cewar Hajiya bayan ta duba agogon da ke jikin bango.


 

Yana ƙoƙarin cewa wani abu sallamarta ta datse shi.


  "Assalamu alaikum." Ta shigo fuskarta ɗauke da fara'a mahaifinta ne ya amsa mata tare da tambayarta, fara’a, "My daughter a ina ki ka tsaya ne, har muka riga ki zuwa gida?"


 Ta sunƙuyar da kai tana sosa keya.


 "Daddy’s girl ina jin ki."


 Cikin sanyin murya ta ce, "Daddy, a waya kawai na faɗawa Mummy gida zan tafi ne, amma na ga hirar taku ce ba mai karewa sai isa na faɗa hakan, sai na samu damar kiran classmate na da na faɗa maka anyi admitting nata, sai ta sanar da ni ai an sallame ta, to gidansu da na je ne fa wasu kawayenmu ma su uku sun zo duba ta a ka haɗu a na hira, ba dan na dage ba ma da ban dawo ba, don sauran ma na bar su a can ce min suke mu zauna bayan isha’i mu fita tare na ce ina, ban nemi iznin haka a gida ba."

  "Allah sarki, ai ni da ma na san tarbiyyar my daughter ba za ta yi duk abin da zai sosa ran iyayenta ba."

 Suka ci gaba da hira, kiraye-kirayen sallar magariba a ka fara ne ya sanya dukkaninsu suka miƙe don gabatar da Sallah.



  BAYAN WASU KWANAKI


Hafsy suna hira da Mus’ab, ta shaida masa yau tana buƙatar su haɗu 11:00am ya nuna mata ba damuwa zai kasance a inda suka saba haɗuwar a kuma lokacin.



 "Ni Hafsat yau kuma wacce ƙarya zan yi a ba ni damar fita, wani lokaci ma Daddy ya fi Mummy saukin kai, yau ga shi baya nan, ya fita aiki, Mummy kuma tun jiya, tana shan ƙamshi dama ita idan ta sauyawa mutum kallo ɗaya idan ka yi mata za ka gane, tun dubo Adnan Mummy ta sauya mini tsoron tunkararta ma nake da maganar fita."



 Bayan ta je wajen mahaifiyarta ta durƙusa gabanta ta fara sosa keya ce, "Mummy da ma ina so ki amince min na je saloon"


 Ta kalle ta sama da ƙasa, "Yaushe kika yi saloon da har za ki kuma yi ba inda zaki je, na fuskanci kina son ki fara yawan yawace-yawace irin na ''ya'yan wasu to ba a gidan nan ba."


  cikin karyayyiyar murya kamar za ta yi kuka, "Don Allah Mummy....."

 Kafin ta kai ga ƙarasawa mahaifiyarta ta ce "Ban son jin wata maganar ba inda za ki fita yau tashi ki ba ni wuri."


 Hafsy jikinta ya yi sanyi, haka ta miƙe, tafiya take kamar an cire mata laka ta nufi ɗakinta ta faɗa gado ta fara gunjin kuka. Cikin sheshshekar kuka ta ce, "Mummy me take nufi, tana nufin yau idanuna ba za su yi arba da Mus’ab ba? Kwana nawa ban gan shi ba sai dai na ji muryarsa a waya. Muna gari ɗaya kuma muna numfashi da lafiyar junanmu a ce ba za mu ga juna ba, ina ba zai yiwu ba!"



 Ta duba agogo 10:30am ta kira Mus’ab, "Dear don Allah ka yi hakuri an samu akasi, haɗuwar mu sai 2:00pm."

  "Ba damuwa ni ma da ma ina so na ƙira ki na faɗa miki a kan zan yi late Ummata za ta aike ni, zan kuma jima a inda zani."


  "To ai shike nan, amma dai zuwa 2:00pm za ka gama duk abin da kake?"

 "In sha Allah."  "To sai mun haɗu my heart desire." Ta katse wayar.


Hafsy ta nufi parlour tana wayar ƙarya, Mummynta na kallon television, da ta ji Hafsy na ce wa Innalillahi wa Innalillahirraji’un, ta rage volume, tana kallonta, sai ta ji tana cewa, "Yaushe ne haka? Rai baƙon duniya, Allah ya gafarta masa, karfe nawa ne jana’izar? Okay, to in sha Allah za ki gan ni, sorry for the lost may Allah give you patience." Ta katse wayar.



Mahaifiyarta da hankalinta ya karkata ga ɗiyarta tana gama wayar ta ce, "Wa a ka yi wa mutuwa kuma?


 "Mummy Fa’iza Yusuf ne, mahaifinta ya rasu ɗazu, jana’iza karfe 2:00pm."



 "Innalillahi wa Innalillahirraji’un! Amma kuma ban wayi yarinyar ba."

 Ta sosa keya, "Umma, ba za ki waye ta ba gaskiya don tana da karancin mutunci duk ƙawayenmu na kuka da ita, ni ma abin da zai kai ni kawai don mutuwa ne da wani abu ne daban idan na jajanta mata a iya waya ya isa."

 Ta numfasa, "Haka ne mutuwa ya wuce abar wasa ballantana na rashin iyaye. Kai Allah ya kyautata ƙarshenmu. Shi kuma Allah ya gafarta masa. Wacce unguwar suke?"

 

 Bayan ta zauna a kujera ta ce, "Abuja Sharaton."

 "Wannan sai mu tafi tare, unguwar su Hajiya Lubabatu ne, da ma yau na ƙudurta a zuciyata bayan azahar zan je mata mun kwana biyu ba a haɗu ba, idan muka je muka yi gaisuwar sai mu je gidanta har da ke don tana complain na rashin zumuncinki."


 Ido ta zaro tare da rikicewa saboda maganar mahaifiyar tata.

  

 Hafsy shiru ta yi a zuciyarta ta ce "Na shiga uku! Ya zan yi da idan muka tafi da Mummy."

 "Me ya faru na ga kin zaro ido tare da rikicewa lokaci guda?"