YARDA CE SILA

GOMA ƊAYA GOMA

by @sanahsmatazu

YARDA CE SILA.

Sanah S Matazu.


GOMA ƊAYA GOMA

🔟


Faɗuwa ya yi tare da sakin ƙara mai ƙarfi yana dafe da wurin, ƙararsa ta ja hankalin wasu jami'an tsaro da su ke zagaye a wurin su ka tsaya cak! Ya miƙe ya sa ke cakumota cikin hanzari ta janyo wata gora da ta ga ni kusa da shi ta ɗaga za ta maka masa ya tare ya tankaɗata hannunta ya faɗa kan wani almakashin ta yi lamo ga Nawaf na tsanyara kuka har muryarsa ta fara dashewa cikin shammata ta sake caka masa almakashin ta yi sa a ta sami gabansa ya faɗi rikica sai ta yi gefe ta suri makulin ta buɗe ƙofar da sauri tare da sunkutar Nawaf dake shassheƙar kuka tana kaiwa bakin ƙofa su ka yi kiciɓus da 'yan sanda su ka tsareta da tambaya maimakon ta ba su amsa sai ta sa kuka ganin kamar mara gaskiya ya sa ɗaya cikinsu ya kutsa kai ciki da sauri ya fito yana faɗin,

"Karku ba ta ta tafi!"

Ƙara fashewa ta yi da kuka mai zafi ita kam ta ga rayuwa, nan da nan su ka kira office ɗin su masu bincike su ka zo aka yi hotuna a daran aka wuce asibiti da shi ƙasancewarsa sannan likita a cikin jihar har mahaifinsa ya zo tare aka tafi asibitin da shi ita kuma babu wani bincike aka wuce da ita police kai tsaye. Ba ƙaramin tashi hankalin mahaifinsa ya yi ba, ya san duk a gama ɗansa ne mai laifi hakan ya sa tun a daran ya gama da 'yan sanda ta hanyar toshe masu baki da makudan kuɗaɗe.

***

Kwanakin nan tana yawan mafarki da shi, mafarki mai muni tun tana kauda abin a ranta harta kai Major ya fahimci matsalarta, yau ƙasa jura ya yi ya turketa,

"Hauwa u na gaji da ganin yanayinki fa yana sossamun rai, wai me na rage ki da shi ne duk kin tarwatsa farin cikinmu hata yara na lura ba su da walwala a kwanakin nan saboda sauyawarki."

"Ka yi haƙuri Major na ƙasa cires hi a zuciyata kamar yadda ka buƙata, yau fa sheƙara uku rabansa da gida ta yaya zan jura? Yaushe zan ji daɗi? Ina son Saif fiye da sauran yaran nan..."

Kuka ya sarƙeta,

"Kin gani ko kukanki kaɗai masifa ne a rayuwarsa, ki daina zubar masa hawaye hakan matsalace sosai a gare shi. Ki yi masa addu'a ni yanzu na daina ɗaga kaina akan Saif wallahi addu'a kawai ya ke buƙata."

"shi ke nan Allah ya kaɗo mana da hankalinsa gida."

"Amin".

***

LONDON

Kwalabe ne a gabansa ɗaya bayan ɗaya, ya ke dubansu idanunsa ya tsaya tar kan ƙaramin kofin gilashi da ke gabansa _glass cup_ wanda aka zuba giya ciki da fasassun ƙanƙara ƙanana tana tururi ya ɗauka tare da kaiwa bakinsa ya saki murmushi yana direwa ya miƙe yana taku ɗai-ɗai cike da ƙasaita ya wuce tuni matasan 'yan matan turawa su ka soma miƙewa suna binsa duk yarinyar da ta raɓe shi sai ya tureta ya wuce hakan ya haifar da shewa da tafi a wurin kai tsaye ya nufi kusa da ita ya zauna ta saki murmushi mai sauti. 

 Tina ke nan yarinyar _Prince_ Saif mai ji da kanta domin ba kowa ce yarinya ya ke kulawa ba. Cak! Ya ɗauketa su ka bar harabar. Yana tunanin yadda ta dame shi su yi aure ko karan hauka ya cije shi ba zai aureta ba ya tabbatar Daddy zai fushi da shi fiye da baya zai cigaba da lalaɓata kawai. 

***

Da safe haka Shukuriyya ta ƙaraci zamanta ga yunwa da ke ƙwaƙularta ɗan abincinta Nawaf ta ba wa. Har yamma ta ƙasa sanin dalilin rufeta ita ba sata ba ita ba maita ba, ita ba fashi ba an kargameta cikin sell kawai saboda son zuciya daga ƙwatar kai ba tare da binciken dalilinta ba. Ranar yini ta yi kuka kanta ya dinga ciwo, ɗakin da take kansa kuntatta ce ne su uku ne ciki da wasu mata gasu mugaye in muguntarsu ta motsa haɗuwa suke su zaneta.

 Tun tana lisafin kwanakinta harta haƙura ta rungumi ƙaddara kusan tafi ma jin daɗin rayuwar sell ɗin babu rashin abinci bale rashin gaba tar da ibada bare kuma akai ga farautar mutuncinta. Abin har mamaki ya dinga ba ta ashe za ka iya kwana a sell kama yi rayuwa cikinsa? Ta ɗauka duk ma'aikata macutane ashe akwai masu mutunci da tausayi? Lalai ta amince duk waje ba'a rasa na kirki dana banza. 

Cikin wurin akwai wani ɗan sanda guda ɗaya, ta gane shi yana ɗaya daga ma'aikatan da su ka yi maƙotaka dasu ya yi mamakin ganinta sosai. Mutum ne mai tausayi da kawaici shi ya dinga kulawa da ita yana siya mata abinci baya bari kwata-kwata ta ci na cikin sell da dama a wurin kanwar Ahmad suke kiranta. 

  Haka Nawaf yana kulawa tun ba ta sakin jiki da shi tana tunanin mugunta irin ta sauran da su ka raɓeta harta soma sakin jiki da shi a haka ya dinga bugun cikinta harta bayyana masa asalin abin da ya kawota wurin, hankalinsa ya tashi ya san waye Dr Faisal ciki da bai ya kuma san mahaifinsa ba su da imani ko tausayi kan na ƙasa da su don haka ya soma ƙoƙarin ganin ya fitar da ita ta kowace hanya kai tsaye ba tare da shawarar kowa ba ya doka ƙara kotu da ke ƙanin mahaifinsa Alkaline cikin kwanakin aka ba shi takardar sammaci ko kaɗan bai ji damuwa ba hasalima ya fi tunanin kawai tanan zai fitar da Shukuriyya.

 Saboda maƙudan kuɗin da mahaifin Faisal ya zuba a rashin imanin wasu cikin ma aikatansu za su iya kauda ita gaba ɗaya ma a doran ƙasa ko kuma su asassa mata dawwama a gidan yari har mutuwarta. Ya hakikance ji daga bakinta kaɗai ne hanyar fitar da ita to amma ta yaya? ya sani sarai Alƙali ne kaɗai zai iya ba ta wannan damar.

 Sammaci ya isa ga mahaifin Faisal ba ƙaramin kaɗuwa ya yi ba, a kuma ranar ne sakammakon gwajin da akai wa Faisal ya fito wato sakammakon buguwa da jijjiyoyin gabansa sun yi sanyi. Abu goma da ashirin ya haɗu ya cakuɗe masa ya dinga zufa yana juyi a ranar ya sa aka nemo masa _inspecter_ da kuma lauyarsa _Barrister_ Rakiya bayan ya bayyana musu komai su ka yi masa sallama tare da alkawarin zasu ziyarci Shukuriyya.


***

Shukuriyya tun tana sa ran ganin an buɗeta amma abu ya ci tura ta haƙura ta durfafi ubangiji tana kai masa kukanta abinci dai ba ta rasawa sai dai cimar babu daɗi. A wani yammaci tana zaune aka buɗeta tare da buƙatar ganinta. Farin ciki ta ke sosai ta fito tana rike da hannun Nawaf, bayan an mata izinnin zama ta sauke idanunta kan wata kakkaurarrar mace mai ƙirar samudawa wadda a take ta kirata da sunan lauya saboda kayan jikinta. Ɗauke idanunta ta yi tana karema office ɗin kallo madaidaici da ashi ta samu guri ta zauna Nawaf na maƙale da ita. Wani kututturi ne cikin su mai sanye da _black suit_ ya dubeta,

"Sunana inspecter Madu ni jami in tsaro ne, wanna kuma sunanta Barrister Rakiya mun zo ne muna son jin gaskiyar lamari abisa abinda ya faru tsakaninki da _Dr_ Faisal."

Tunda ya fara batun take raka shi da idanu,

"Dr Faisal?"

Ta furta da alamun tambaya,

"Gaskiya ban san shi ba"

"Ke!"

Wani tsamurmurin ɗan sanda ya furta yana huci,

"Wanda muka kama ki a chemist ɗinsa"

Tuni ta fahimta murmushi ta yi ta kwashe komai ta bayyana musu. Bayan sun ji komai su ka yi jim,

"Daina kukan Shukuriyya, shin waya ɗaukaka miki ƙarar da kika kai Dr Faisal?"

Shiru ta yi babu amsa,

"Dake ake."

"Ban san shi ba!"

Kallon Barrister ya yi su ka yi murmushi,

"Mene ne cikakken sunanki?"

"Shukuriyya Goni Muhammad Chadi."

Ya yi jim yana ƙare mata kallo,

"Ina mahaifanki kuma ina ne unguwarku?"

"Sun rasu, ni ba 'yar nan bace 'yar gudun hijira ce daga Maiduguri."

Cikin sallo su ka sake kallon juna shi da Barrister Rakiya, ya jinjina kai,

"Shukuriyya muna so wannan bayani da kika yi mana karki ƙara yi wa wani shi ko akwai wanda kika faɗawa?"

"A'a."

Ta faɗa ɗa sauri ya yi jim kamar mai tuna wani abu,

"To karki faɗawa kowa abu na gaba kai ku shigo."

Ɗaya bayan ɗaya wasu ƙati su ka shigo ɗauke da bindiga,

"Kinga waɗanan wallahi za mu sa su ɓatar da ke adoran duniya mudun ki ka bayyana wannan sirri ga duniya, ko mai za ayi miki ki ce ke bakisan batun bama."

Gaba ɗaya ta tsorata ko ina jikinta rawa ya ke yi, su ka miƙe su ka barta a nan ɗan sanda daya fito da ita ya tankaɗa keyarta hadda duka. Ahmad yana zaune yana rubuce-rubuce ko kallon su bai yi ba sai da ya tabbatar sahu ya ɗauke ya shiga ya sameta tana kuka cikin kicin kulawa ya furta,

"Shukuriyya lafiya?"

Cikin kuka ta bayyana masa komai ta ɗora da faɗin,

"Wallahi ban san wanda ya kai ƙara ba don Allah ka je kace ya janye".

Idanunsa jajjur ya furta,

"Ba za a janye ba Shukuriyya sai an bi miki haƙƙinki kada barazanar su ta ɗaga miki hankali ni na kai ƙara kuma da izinin Allah sai kna yi nasara.."

"Dan Allah ka janye wallahi gara ka buɗe ni na fice daka yankamin kazar wahala ba zan iya figewa ba..."

"Allah yana tare damu Shukuriyya kiyi haƙuri bazan iya janyewa ba..ta wannan hanyar kaɗai zan iya fitar da ke daga wannan sarƙaƙƙiyar..."

 Ficewa ya yi ya barta shanye da baki haihan a buɗe. Kwanaki biyu ke nan kullum cikin yi mata barazana ake yi yayin da Ahmad ke ƙarfaffa mata guiwa.

 Ranar Lahdi aka sa ke tunasar da ita tare da gargaɗinta sabida ranar Littinin za su shiga kotu har zuwa lokacin Ahmad bai sami tsayayyan lauya ba wanda zai tsayawa Shukuriyya saboda rashin wadatatun kuɗi. Ahmad maraya ne mahaifinsa ya rasu mahaifiyarsa da kannansa maza uku duk karkashinsa suke kuma dangin mahaifinsa ba wani kulawa suke da su ba. Da aikinsa ya dogara dashi ya kewa rayuwarsu duk wata hidimar da ta dace.

 Ranar da aka yi zaman kotun farko Shukuriyya ƙasa cewa komai ta yi ban da kuka babu abin da take hakan ya sa Alƙalin ɗaga shari'a zuwa satin sama. Ahmad ya ji babu daɗi ƙwarai hakan ya ba wa shari'ar tasu bayyana a kafaffen sadarwa da yaɗa labarai harma da jaridu mane da hotan Shukuriyya. Jaridu da dama sun buga rahotan wanda yaba wa shari'ar damar zagayawa ta zamo abar tattaunawa a bakunan mutane. 

 Wasu na hango wautar Shukuriyya na yin ƙara saboda rashin sanin waye Dr. Faisal wasu kuma kawai suna hango ƙoƙarinta ne. A haka su ka durfafi cinye satin ana jibi ne Ahmad ya samu gayyatar wani Lauya daya amince zai tsayawa Shukuriyya ba ƙaramin daɗi ya ji ba, kwanaki ukun da su ka rage sunyi su ne tare da shi suna zaryar zuwa wurinta dan samun cikakkun bayanai a ranar da su ka gama ne da daddare ana gobe shiga kotu sako ya shigo wayar Ahmad ba ƙaramar kaɗuwa ya yi ba. 

 Wato Lauyan da su ka sha zarya da shi ya samu labarin a rabuwarsu an bi shi an kashe shi tare da kwashe duk wasu muhimman bayanai na wurinsa. Ahmad saboda kaɗuwa kawai kuka ya saka tausayin rayuwar Shukuriyya ya yi masa katutu. Mahaifiyarsa ita ta dinga kwantar masa da hankali da safe ma kamar ba zai je wurin shari'ar ba ita ta dinga ƙarfafa masa guiwa har su ka fita tana rike da Nawaf.


KOTU.

Kotun maƙare take da ɗan adam, kowa a muhalinsa ko kyakkyawan tari babu mai yi. Kamar yadda dokar koto ta tanadar na zuwa da wuri, musamman ga lauyan dake kare wani ɓangare da ke ƙara da kuma wanda ake tuhuma. Hakan ne ta ƙasance Barrister Rakiya ta hallata tun karfe takwas da rabi ta isa koton, karfe tara tawagarsu Dr da Mahaifinsa da su Inspecter su ka zo. n ɗa mahaifiyar Ahmad da kanwarsa su ka iso a motar Ahmad .

 Kotun tsit can _orderly_ ɗin _(Judge)_ mai shari'a ya yi _(banging)_ kofar da _(judge)_ ke shigowa sau uku, take kowa ya miƙe _(Judge)_ ya shigo daga bisani ya yi _(taking bow)_, kowa ya yi _(taking bow)_. Sannan ya zauna kowa ya zauna. Ya jawo takardu ya yi yan rubuce-rubuce aka soma gaba tar da shari a ta farko kan wata mace da mijinta aka gama yanke hukunci sannan aka yankewa wani tsoho hukuncin shekaru ashirin kan aikata fyaɗe ga wata ƙaramar yarinya. Shari a ta gaba ita ce tasu Shukuriyya mai gaba tarwa ƴya miƙe ya gaba tar,

"Shari'a ta gaba ita ce ƙarar da Shukuriyya 'yar gudun hijira take na Dr Faisal yunkurinsa na keta mata hadi."

Alƙali ya nemi ganin lauyan mai ƙara da mai ƙara babu lauya sai mai ƙarar daga bisani ya nemi ganin lauyan mai kare wanda ake ƙara. Brr. Rakiya ta miƙe ta na duban kowa ɗai-ɗai cike da ƙasaita ta gyara rigarta ta soma magana cikin izza,

"Sunana barrister Rakiya M Aliyu ni ce na ke kare ɓangaran wanda ake ƙara".

Ta risina ga Alkalin alamun girmamawa ta koma ya zauna. Alkali ya yi yan rubuce-rubuce sannan ya ba su damar magana.

_(Clerk)_ Mai gaba tarwa ya miƙe ya soma magana,

"Kotu na san ganin Dr wanda da ake tuhuma."

Take kotun ta yi tsit, cikin ɗingishi ya fito babu ko ɗar a tare da shi ya nufi _(dock)_ in da aka tanadarwa masu magana ya tsaya yana kallon kowa ɗai-ɗai. Nan da nan wajen ya yi tsit ido ya yi mata chaaaa suna kallonsa.

Mai gabatarwa ya koma ya zauna, Alkali ya ya dubeshi

"Ka ji kan abin da ake tuhumarka?"

"Na ji ya maigirma mai shari a."

"Shin abin da ake tuhumarka haka ne?"

"A'a ya maigirma mai shari a."

Ya yi tsai yana ƙaremasa kallo ya yi 'yan rubuce-rubuce ya ɗago,

"Me ƙara ko kina da abin cewa?"

Cikin inda-inda ta ce,

"A'a ya mai girma mai shari'a".

su ka haɗa idanu da Ahmad ta ɗauke kai da sauri, sai da ya yi rubutu ya ɗago,

"Lauyan dake kare wanda ake ƙara ko kina da abin cewa?"

"Akwai ya mai shari a."

Cewar Barrister Rakiya ta miƙe tana fitowa.

"Malama zamu so ki bayyana wa masu saurare sunanki."

"Sunana Shukuriyya Goni Muhammad Chadi."

"Shekaru fa?"

"Sha tara."

"Me ce ce hujjarki ta cewa Dr shi ne ya yi yunkurin yi miki fyaɗe?"

Shiru ba amsa, ta sake maimaitawa ba amsa murmushin nasara ta yi, sannan ta cigaba.

Ko za ki iya bayyanawa kotu ɗan da ke tare da ke ɗan waye ko ɗanki ne? Idan ɗanki ne waye ubansa?"

"Ba ɗana bane, ƙanina ne shi ma ibtila i ne ya faɗa masa kamar yadda ya faɗa mini na rasa iyayyena shi ma ya rasa nasa da ɗan uwansa abokin haihuwarsa mahaifiyarsa ce ta ba ni amanarsa a sansaninmu kafin ajali ya risketa".

Jinjina kai ta yi ta furta,

"Ya mai shari a zan so kotu taba ni damar ganin Lado ba nijare mai shayi don amsa wasu tambayoyi."

"An baki."

Mai gabatarwa ne ya miƙe,

"Kotu nasan gamin Lado maishayi."

Shuɗewar mintina uku ya bayyana yana washe baki ba Shukuriyya ba hata Ahmad ya yi mamakin ganin Lado sun kaɗu matuƙa. Ya shiga ya tsaya, ta dube shi,

"Malam Lado meka sa ni akan Shukuriyya?"

Tuni ya soma matsar hawaye sannan ya soma magana,

"Ai Shukuriyya da kuke ganinta taƙadiriyya ce, muguwar 'yar bariki ce ni nan shadai ne duk tsufana zuwa take ta ce wai in taimaka mata...."

Sai ya fashe da kuka, Brr. Rakiya ta juya,

"ko kina da abin cewa?"

Kuka Shukuriyya ta ke mai sauti babu amsa, ta risina,

"Ya mai shari a wannan kaɗai ya isa nuna ƙazafi ta yi wa Dr wanda ahalin da ake ciki ma yana asibiti ne yana karɓar magani sakammakon haɗari da ya yi zan so wannan kotu ta dubi adalci ta hukunta ta bisa ƙazafin da ta yi masa."

Koma wa ta yi ta zauna Alƙali ya yi rubuce-rubuce ya ɗago,

"Bisa rashin ƙwaƙwarar hujja mun ɗaga wannan ƙara zuwa sati biyu masu zuwa."

"Kotu!"

Ɗaya bayan ɗaya aka dinga watsewa Shukuriyya banda kuka babu abin da take. Ta ke yan jarida su ka soma ɗaukar rahoto anji ta baki Lado amma fir Shukuriyya ta ƙi magana sai kuka.

***

Bacci ya ke lakadan a hankali ya riski kansa a wani daji mai duhuwa, idanunsa su ka sauka kanta kusa da ƙaramar bishiya mai kala biyu jikinta rabi koriya rabi baƙiƙƙirin da shi, kuka ta ke sosai ɗaɗɗaure jikin bishiyar,

"Na faɗa maka da kun zo lokacin daya da ce da ba a kashemana iyaye ba, karka matso inda na ke bana son taimakonka, na tsani duk wani jami in tsaro..."

Firgiggit ya farka duk ya haɗa gumi sharkaf da shi a hankali ya dinga tuna kalamanta.

 "Da...lla... ka ...ƙyale....ni ai duk kuka ja, da kun zo kun ba mu agaji da ba ayi asarar al'ummah har haka ba. Mene ne amfanin kayan jikinku in ba kare lafiyar al'ummah ba kaico kunci amanar ƙasarku......Karka matso in da na ke bana son taimakonka...

miƙewa ya yi jiki a sanyayye ya yo alwala ya haye kan abin sallah.