Chapter 7
*ZANEN ZABUWA*
©️ *Nana Haleema.*
*Page 7*
*TUSHE.*
Alhaji AbdulKhabir Isma'il Uba haifaffan garin Kano ne mazaunin unguwar shard'a, yana da mata guda d'aya tal mai suna Hadiza wacce ake kira da Umma itace matar sa ta farko tun auren saurayi da budurwa daga ita bai k'ara ba, basu da wani k'arfi sosai sai dai akwai rufin asirin Allah dan ci da sha da wajan kwanciya baya gagarar su sai dai abinda ba'a rasa ba.
Yaran sa uku kacal Fatima Binta itace babba a cikin su sai Surayya sannan Imran shine.na k'arshe.
Malam Aminu Yakub haifaffan garin Kano ne shima dangin mahaifin sa da kowa nasa suna garin Kano, Malam Aminu yana da mata shima guda d'aya tal mai suna Habiba wacce ake yiwa laqabi da Gwaggo.
Malam Aminu d'an kasuwa ne mai k'aramin k'arfi wanda yake buk'atar taimako, tun auren sa da Gwaggo suka tare a unguwar sharad'a inda suke makotaka da gidan AbdulKhabir.
Umma ta kasance babba a layin da suke dan lokacin da aka kawo Gwaggo matsayin amarya Umma ta haifi Surayya har ta girma hakan ya saka Gwaggo ta d'auke ta kamar uwa kasancewar tata mahaifiyar ta rasu, koda sab'ani suka samu da mijin ta wajan Umma take shiga ta kai mata k'ara tunda katangar gidan su d'aya.
Sosai suke zaman lafiya a tsakanin su babu fad'a babu munafunci sai ganin girma da arzuk'i da taimako dan AbdulKhabir yafi Aminu samu nesa ba kusa ba hakan ya saka shi ya d'auke shi tankar d'an uwa yake kuma taimaka masa. Aminu Malami wacce ya gaje ta a wajan mahaifin sa kuma yana zuwa wata islamiyya da take kusa dasu jifa-jifa yana koyarwa, yasan laittafai na addini a dama da yawa samari sukan zo wajan sa d'aukar karatu. rayuwa na tafiya zaman lafiyar su na d'orewa in kaga Surayya da Binta a wajan Gwaggo baza kace ba itace ta haife su ba sune suka saka mata suna Gwaggo a lokacin suna yara.
Cikin wannan yanayin ne Allah ya azurta Umma da cikin Imran a lokacin sai yazo mata da laulayi sosai ko aikin gida bata iyawa wannan dalilin ya saka Gwaggo komai itace take yi mata hatta wanki Gwaggo ce zata wanke kayan ta dana yaran ta shanya, wannan abin alkhairi ya sake k'arfafa alaqar su har ya zama ko wacce a cikin su babu wacce d'an uwan ta ko y'an uwan ta basu san da zaman d'aya daga cikin su ba.
Zumuncin su yana ta gaba har lokaci Gwaggo bata tab'a yin koda b'atan wata ba da yake lokacin mutanen dah ne ba'a wani damu an tayar da hankali akan rashin samun cikin ba sai magani da Malam Aminu yake bata tana sha.
A cikin wannan yanayin ne aka haifi Imran in Gwaggo ta shiga gidan tun safe bata fitowa sai dare abinci ma sai dai ta aikowa da Malam shi. Imran na girma cikin k'oshin lafiya da kulawar da yake samu daga wajan iyayen nasa biyu sai ya zama in ba Umman sa ba baya yadda da kowa sai Gwaggo da ka d'auke shi zai fara kuka. lokacin da aka tashi yaye Imran Gwaggo aka bawa shi tana bashi kulawa sosai duk da ba wani abin kirki ne dasu a gidan ba amma tana k'okari wajan ganin ta bashi cima mai kyau, Imran ya zama d'an Gwaggo da Abba in sukayi bak'uwa ma d'auka ake Imran d'an Gwaggo ne kasancewar ta farar fata in ta d'auke shi sai a d'auka shine.
Yana da shekara goma a duniya a lokacin yana ajin k'arshen a primary ranar wata asabar Gwaggo ta tashi da wani zazza6i da ciwon kai Umma ta shigo aka tafi asibiti gwajin farko ya nuna tana d'auke da ciki na sati biyu.
Murna a wajan dangi da abokan arzuk'i ba'a cewa komai Gwaggo ta fara samun kulawa daga b'angarori da yawa kowa yana bakin k'okarin sa wajan bata kula.
Cikin ta nada wata bakwai a lokacin har ya fito wata ranar talata Imran ya dawo yana kuka daga makaranta yaje wajan Umma yana cewa ko wanne abokin sa yana k'ani da k'anwa shima ta siyo masa k'ani sai Umma ta ce masa Gwaggo ta kusa siyo masa, tunda yaji haka shikenan kullum yana wajan Gwaggo yana jiran ta siyo k'ani ta bashi har lokacin da Allah ya sauke ta lafiya ta haifi d'iyar ta mace.
K'anwar Gwaggo da auren ta ya rasu itace tazo ta zauna da ita tana kula da ita haka Umma ma ba'a barta a wajan ba dan ta taka rawar gani sosai a haihuwar, labarin haihuwar da yaje kunnen Imran farin ciki da murna ba'a cewa komai yazo gidan a ranar sai wanda yaga dama zai bari ya d'auki jaririyar sabida k'aunar ta da yake yi.
A ranar da daddare Umma sa ta 'kullo masa kayan barka a leda ya kawowa Gwaggo ai kuwa tayi murna sosai dan a lokacin kaya kwalli biyu kacal take dashi wanda zata sawa yarinyar sai wanda ya kawo mata.
Ranar suna yarinya taci sunan Umma wato Khadijah kuma ya kasance sunan Mahaifiyar Gwaggon ne itama Yaya Binta ta zab'a mata suna Jannat.
Yanayin rayuwa da kuma yanayin abin hannun Abba dak'yar aka samu aka yanka tinkiya matashiya shima kuma sai da y'an uwa akayi karo-karo amma kasancewar su masu wadatar zuci baza ka gane hakan ba.
A ranar Imran sai da yayi walima ya gayyato abokai y'an islamiyya da y'an boko yaci kwalliya akayi walima aka raba alawa da biscuit.
Tun daga wannan haihuwar Gwgago bata sake samun wani ciki ba haka ta b'angaren Umma daga kan Imran haihuwa ta tsaya mata cak suka cigaba da rainon wanda Allah ya basu ba tare da damuwa ba.
To tun daga wannan lokaci Imran ya bar kwana a gidan su sai a wajan Gwaggo ga shinfid'ar sa gata Jannat tun kowa yana yiwa abin dariya har aka fahinci har zuciyar sa yake yin komai.
A cikin wannan yanayin ne su Gwaggo suka kuma shiga rayuwar matsi wacce har ta kai ta kawo abinci na gagarar su hakan ya jawo Jannat ta fara ramewa kasancewar bata samun isasshen abinci, dake matar rufin asiri ce hatta Umma bata san da halin da suke ciki ba sai da ta fahimci hakan da kanta duk da itama ba wani k'arfin gare su ba amma gwara su ta samu d'an abinda baza'a rasa ba na yatsi ta aikowa da Gwaggon.
A wannan lokacin Abba ya fara shiga kauyuka yana neman kud'i a kasuwannin su cikin ikon Allah ya fara samun rufin asiri har suka fi k'arfin ci da sha.
Jannat tana girma da yawo tana sake bud'e tana ganin Imran a tare da ita wannan ya saka babu wanda ta sani in ba shi ba tunda kullum suna tare suka shaqu sosai da sosai, Imran nada shekara goma sha biyar ya kammala makarantar secondary a lokacin Jannat nada shekara biyar a duniya, indai Imran yana kusa Jannat bata kuka, bata fushi, bata b'ata rai, a lokacin tana kiran sa da Yaya Iman bata iya cewa Imran d'in har sunan yaso ya bishi nan a lokacin yayyen sa guda biyu duka sunyi aure daga mai yara biyu sai mai uku.
Yau laraba yana rik'e da hannun ta suka tafi islamiyya tare a hannun wata yarinya taga y'ar tsana tana wasa da ita tun daga lokacin take kuka sai an siya mata, hankalin sa ya tashi sosai ganin tana kuka dak'yar ya lallab'a aka tashi suka dawo gida yazo ya saka Umma a gaba sai da ta bashi kud'i yaje ya siyo mata y'ar tsana hankalin sa ya kwanta.
Tun daga wannan ranar yace shifa sai ya nemi kud'i kodan ya siyawa Jannat abinda take so kafin jarabawar sa ta fito ta gama makaranta ya fara bin Baba kasuwa yana bud'e ido da kasuwanci, duk abinda ya samo a kasuwar in abokan Baba suka bashi ko Baban ya bashi wani abun kashewa ranar Jannat zai kashewa su ko nawa ne.
Rayuwa na tafiya a haka kulawa da shaquwa na sake shiga a tsakanin Jannat da Imran wacce shaquwar su ta kai ga islamiyya ma tare suke zuwa, baya so ko kad'an ya ganta tana kuka yanzu sai hankalin sa ya tashi ya rasa abinda yake masa dad'i, gabad'aya unguwa babu wanda bai shaida wannan shaquwar tasu ba har wasu sukan ce mata Imran d'in Jannat. A lokacin ne Allah yayiwa Baba rasuwa, an shiga tashin hankali a wannan lokacin anyi kukan rashi sosai kafin a share makoki.
Bayan wasu kwanaki ne aka zo za'a raba gado da yake zuciyar mutane babu Allah a ciki duk da ba wani abu Baba ya tara ba amma sai da aka samu wanda suka yi sama da fad'i da d'an abinda yake dashi wanda aka bar musu d'an kad'an ne, abinda aka bar musu sai bai kai Imran ya fara neman na kansa dasu ba dan ya taimaki mahaifiyar sa da kuma k'anwar sa Jannat hakan ya saka shi shiga kasuwa ya fara sana'ar dako ana biyan sa yana tara kud'in.
Lokaci d'aya ya rame yayi baqi sabida wahala, Umma kullum cikin tausaya masa take tana yi masa addu'ar nasara da kuma dacewa a wannan lokacin ne jarabawar sa ta fito ta secondary inda ya samu sakamako mai kyau.
Umma tayi aure a wannan lokacin ta auri wani Malam Garba yana da mata biyu itace ta uku, sai wahalar tazo musu da sauk'i domin ya d'auki d'awainiyar Imran kamar shine ya haife shi tunda a gidan su suke a zaune shine yake zuwa duk ranar girkin ta. Basu wani jima sosai ba shima Allah ya amshi tasa rayuwar kasancewae yana da yara da dama ga mata gashi ba wani k'arfi ne dashi ba shima bata samu gadon sa mai yawa ba.
A wannan lokacin ne mutane suke yiwa Malam Aminu magana akan ya auri Umma kodan a tallafi rayuwar Imran kasancewar sa shi kad'ai a wajan ta, da Gwaggo sukayi shawara ta amince har zuciyar ta amma da aka samu Umma da maganar tace sam bata amince ba kar kuma a sake yi mata maganar koda wasa. Ganin ta nuna b'acin ranta akan hakan sai aka bar zancen tun daga lokacin bata kuma aure ba.
Rayuwa na tafiya Jannat na sake girma a lokacin tana da shekara bakwai tana aji biyu a primary har lokacin bata san ba Gwaggo ce ta haifi Imram ba sabida kullum yana tare da ita in ta tashi daga bacci zata ganshi a gidan haka in zatayi bacci yana kusa da ita.
Rayuwa nata tafiya rana na komawa sati, sati na komawa wata, wata na komawa shekara, shekara na zama shekaru, zuwa lokacin Imran ya d'an samu abinda ya samu amma duk da haka bai tab'a kud'in ba ya fara aiki a k'ark'ashin wani kanti da suke siyar da atampa da shadda da laces.
A lokacin yayi tunanin komawa makaranta amma da yaje yaji kud'in reg d'in sai yaji bazai iya ba sai ya hak'ura ya cigaba da neman kud'in sa.
Lokacin da Jannat ta zana jarabawar fita daga primary bayan ta fito sai aka kaita wata makarantar secondary dake da nisa sosai da gida kud'in motar da za'a bata sai yake neman gagarar iyayen ta sai dai ta tafi a k'asa gashi kafin taje ta makara sai an zane ta, ganin irin dukan da aka yi mata har jikin ta ya fashe ya saka Imran kullum sai ya aro machine ya kaita in an tashi ko me yake a kasuwa sai yaje ya d'auko ta sai su hayo d'an aca6a su dawo gida, yau da gobe sai Allah inji hausawa wata rana in Imran yaje aron machine d'in da zai kai Jannat makaranta sai a hana kai tsaye ace bazan bayar ba dole zai dawo gida da y'an kud'in da suke jikin sa su hau na haya ya kaita in kuma babu kud'in suje a k'asa ya nemi alfarmar kar a dake ta.
A lokacin da mai shagon su yayi wata sallama yazo da kud'i ma su yawa ya kawowa Umma yana neman shawarar abinda za'ayi, sharawa ta bashi akan ya koma makaranta kawai dasu tunda ya samu dama, hakan ce ta kasance bayan ya siyo musu kayan abinci ya ajjiye ya siyi na Gwaggo ma ya kai mata ya yiwa Jannat siyayyar kayan sawa ya bawa abokin sa Nura da suka taso tare ya d'inka mata har kala goma ragowar kud'in kuma ya shiga makarantar polytechnic.
Jannat ta zama y'ar gata baza ka ganta ko shigar ta ka d'auka yar talakawa bace sabida yadda yayan ta yake k'okari matuk'a a kanta tun iyayen ta na magana akan kashe mata kud'in da yake har suka zubawa sarautar Allah ido.
Jannat nada shekara goma sha uku ta shiga senior school a lokacin burin zama ma'aikaciyar jinya ya shiga ranta ya zauna daram bata da zance sai in ta zama nursing kaza zatayi, babu wanda bai san burin nan na Jannat ba inda iyayen ta sai dai su jita kawai dan sun san burin nata ba cika zaiyi ba dan inda sune suke biya mata kud'in makaranta da yanzu ta daina zuwa sabida yanayin rayuwa, Imran ne kawai yake k'arfafa mata guiwa akan burin ta dan tunda yaga tana so yayi alqawarin koda zai kwana ya tashi a cikin ruwan sama rana ta fito ya bushe sai ya cika mata burin ta.
Imran shine ya fara siyowa Jannat brezia a lokacin tana SS1 yaga yadda kirjin ta yake fitowa a uniform har ana ganin shatin k'irjin ta sai ransa ya b'aci kishin hakan ya kama shi da ya shiga kasuwa da kansa ya siyo ya kawo mata, ranar kunya kamar ta nutsar da Jannat dan zuwa lokacin ta fara girma sosai tana kuma karatu a islamiyya ta kuma san shi d'in ba ciki d'aya suke ba.
Tana gab da fita daga aji hud'u na secondary wata rana aka dawo da ita daga makaranta tana fama da ciwon ciki mai tsanani gashi lokacin Imran baya nan yana kasuwa, haka aka lallab'a aka kaita asibiti nan ake sanar da su al'ada zata fara, bayan an bata magungunan ta warke rasss suka dawo gida, lokacin da ya dawo yake jin labarin rashin lafiyar a wajan Umma ko abinci bai ci ba ya mik'e ya fita ya shiga gidan nasu, tambayar duniya yayi mata amma tak'i fad'a masa abinda yake damun ta ganin ya shiga damuwa akan hakan ya saka Gwaggo take fad'a masa dalilin ciwon nata, tun daga ranar ya ninka kulawar da yake mata ya kuma rike lokacin da take preiod duk wata kafin ranar zai siyo pad ya kawo mata tun tana kunyar ta d'an rage tunda ta saba wani lokacin ma sai taga pad d'in da ya kawo mata take tunawa lokacin period d'in ta ya kusa.
Cikin wannan lokacin ya kammala diplomar sa b'angaren computer science result ya fito yayi kyau sosai Jannat ma a lokacin ta zana jarabawar fita daga secondary ta dawo gida da zama sai islamiyya da take zuwa.
Lokacin da jarabawar tata ta fito ganin taci duk abinda ake so d'an science ya kawo ya dinga murna shi kuma Imra. a lokaci yana ciku-cikun neman University ya cigaba da karatun sa, abinda ya dakatar dashi kenan shine fitowar jarabawar ta nan da nan yaji nasa karantun ya fita daga ransa ya bazama neman form na jamb, ranar wata lahadi da daddare Abba yake mata nasiha akan baza ta cigaba da makaranta ba sabida yanayin rayuwa bazai iya d'aukar nauyin ta ba kuma baza'a d'orawa Imrsan nauyi ba dan shima d'an makaranta ne kuma ba kud'i gare shi ba ga nauyin mahaifiyar sa da yake kansa ga jikokin da suke wajan Umman in anyi hutun makaranta.
Hankalin Jannat ya tashi ta dinga kuka amma hakan ta hak'ura dan tasan abinda iyayen ta suka fad'a mata shine gaskiya, a wannan lokacin Imran ya shigo gidan yake shaida musu gobe zasu je thumb print na jamb da Jannat, fad'a sosai Abba ya din gayi yace baza tayi makarantar ba ya adana kud'in sa, aka kad'a aka raya amma Abba yace sam bazai lamunta ba Umma ta shiga maganar yak'i amincewa har sai da Imran yaje gidan Yayan Umma wanda ake kira Baba da k'anin ta Kawu ya kai musu k'ara suka zo suka samu Abba suma dak'yar ya amince.
Wannan rashin cigaba da karatun da Imran yak'i yi sabida na Jannat ya fara tunzura Yaya Binta Ta fara jin haushin Jannat dan a ganin ta itace ta hana shi ya k'arasa karatun sa da ya d'auko.
Bayan an kammala komai akayi jarabawar Jamb ta fito Jannat ta samu makin da ake so, wannan nasara da ta samu sai ya saka Imran bazama shiga b.u.k yana nema mata admission sabida yanayin k'asar tamu yana yi yana d'an bawa mutane kud'i dan a saka ta a cikin wanda zasu samu.
Ya sha wahala matuk'a a wajan nema mata gurbin karatun har hakan ya jawo ya kwana biyu baije kasuwa ba wannan rashin zuwan nasa ya ja aka fara masa barazana da rasa aikin, bai wani damu sosai ba koda ya koma kasuwar da zarar an kira shi akan maganar gurbin baya neman izinin kowa zai d'auki k'afa ya tafi. Kusan sati biyu ya jera yana haka sanadiyar hakan yaja aka kore shi daga kantin da yake dan mutumin bashi da kirki, yaji babu dad'i sosai kasancewar yana samun kud'i a shagon amma haka ya daure ya dawo gida yake shaidawa Umma tayi fatan Allah yasa hakan shine mafi alkhairi.
Da wannan labari yaje kunnen Yaya Binta sai ya sake tunzura ta haushin Jannat ya sake ninkuwa a zuciyar ta tazo tana ta maganganu a gidan sai da Umma ta taka mata burki a kan hakan sannan tayi shiru.
Wahalar da yake sha akan neman gurbi a jami'a ya saka Jannat d'in tace masa ita ta hak'ura da karatun kawai tunda yana shan wahala amma hakan bai saka shi ya dakata ba.
Akayi jarabawar utme nan ma ta samu nasara amma duk da haka dak'yar da sidin goshi aka samu gurbin akayi sa'a aka bata course d'in nata da take so sai kuma aka afka cikin neman kud'in reg.
Kud'i suka gaggara tunda ba aiki yake ba yanzu wanda yake d'an tarawar basu wani taka kara sun karya ba hankalin sa yayi bala'in tashi burin sa bai wuce ya samu koda bsahi bane, Abba da Gwaggo suka kira shi suka ce a bar karatun ba sai tayi ba amma yace tunda har an samu a barta tayi d'in za'a amfana dashi nan gaba dole suka hak'ura, abinda Abba ya mallaka na dadbobi ya umarci Imrn akan a kwance a siyar amma yace sam bai amince ba shine yace zai d'auki nauyin karatun ta dan haka bazai karb'i komai ba a barshi ya biya da kansa, dak'yar aka samu Abba ya saka shi ya d'auki wani abun aka siyar.
Abba da Gwaggo kullum cikin yi masa addu'a suke domin basu da masoyin da ya wuce shi da iyayen sa, shi kad'ai ne namijin da ya lamuncewa Jannat ta saurara bayan shi babu wani.
A cikin kwanakin ya zage ya koma aikin da ya bari a baya wato dako in ya dawo kuma yana karb'ar wankin y'an unguwa masu hannu da shuni yana yi, ganin wahalar da yake sha da kuka Jannat taje tana yi masa akan ita ta hak'ura kawai basai tayi ba amma baima kula ta ba balle yace komai sai Umma ce ta rarrashe ta tayi shiru domin babu wanda bai san halin sa ba in yana son abu baya hanuwa. cikin sati aka had'a rabin kud'in ya samu rancen rabin wajan abokin sa Nura aka had'a akayi reg sai a lokacin hankalin sa ya kwanta.
A cikin kwanakin ya fara nemawa kansa aiki da takardar diploma d'in da yake da ita an sha wahala a nan ma sosai kafin ya samu aiki a wani cafe dake tsallaken su. Lokacin da ya fara cikin lokacin su Jannat zasu fara lecture, tasha nasiha sosai a wajan iyayen ta da kuma Umma dashi kansa akan kar ta biyewa y'an matan jami'a ta lalata tarbiyyar ta, sosai akayi mata nasiha ranar fara lecture tayi Gwaggo ta bata kud'in mota a kud'in sana'ar da ta fara na siyar da kayan gida, irin su maggi, daddawa, kuka, da sauran su.
A haka aka fara karatu sai ya zama tana makara sabida rashin samun abin hawa da wuri kasancewar sai goma ake bud'e cafe d'in sai ya aro machine ya kaita in lecture safe ce da ita.
Bayan gama duka wannan wahalar sai aka shiga ta kud'in handout da buk'atun yau da kullum na makaranta wannan dalilin ya saka Gwaggo ta umarci Jannat da ta fara sana'a itama a ragewa Imrwn d'in nauyi, tayi Na'am da shawarar mahaifiyar tata sabida wahalar da yake sha ita kanta tausaya masa take amma shi baya tausayin kansa Gwaggo da kanta taje mak'onta su ta rok'i alfarma akan Jannat zata fara zuwa koyan kwalliya a wajan y'ar ta matar ta amince cikin girma da mutunci, a cikin kwanakin in Jannat bata da makaranta zata je gidan yarinyar ta koya mata a haka har ta fara koya zuwa lokacin daman tayi sauka a islamiyya.
Cikin lokaci kad'an ta iya kwalliya mai kyau sai dai rashin kayan kwalliyar da bata dasu a hannun ta, Gwaggo taje wajan Yayar ta ta ranto kud'i ta bawa Jannat taje kasuwa ta siyo kayan kwalliyar aka fara zuwa jifa-jifa tana yi.
Shi dai Imran yasan tana koyar kwalliya amma bai san wai dan ta d'auki nauyin wani abu na makaranta take yi ba, da hakan yaje kunnen sa yayi ta fad'a yayi fushi da Jannat d'in har gidan Gwaggon ya daina dak'yar suka shirya shima kuma sai da tayi masa alqawarin baza ta siyi komai da kud'in ta ba sai dai ta fad'a masa.
A wannan lokacin shaquwa, girmama juna, abota, da kuma soyayya ta sake yin k'arfi sosai a tsakanin Jannat da Imran, ko fita yayi in basu had'u ba sai ya kira ta a waya dan ya siya mata waya android mara tsada da kansa kuma ya d'auke ta suka je akayi mata rigistar layi.
Tun tana secondary ya hana ta kula samari ita kuma ta hanu har ta shiga jami'a bata yada abinda ya fad'a mata bata kula kowa indai magana ta shafi soyayya sai dai karatu, ranar da wani ya biyo ta har gida yace yana son ta ranar ansha fad'a a wajan Imran yana ta mita akan me zata bawa wani dama yazo gidan su sai ya d'auke mata hankali akan karatun ta, wannan fad'an da fushin da ya nuna akan hakan ya saka kowa ya sake gasgata zargin sa akan cewa Imran na son Jannat ne har ita kanta Jannat d'in.
Umma ta same shi da maganar amma yace shi sam ba haka yake nufi ba kawai baya so soyayya ta d'auke mata hankali ne ta kasa karatu amma shi bawai yana son ta da aure bane matsayin k'anwa kuma kawar sa ya d'auke ta.
Jannat da bata san nufin sa ta cigaba da d'auka cewa son ta yake ta d'auki soyayyar sa mai zafi ta saka a ranta bata ji bata gani indai a kan k'aunar sa ne ta b'angaren sa kuma ba haka abin yake ba. Daman dashi ta saba, bata da aboki ko k'awa in bashi ba, dashi suke shawara, dashi suke hira, ko karatun ne shine yake koya mata musamman abindw ya shafi lissafi. Wannan kusancin nasu ya saka son sa bai sha wata wahalar yiwa zuciyar Jannat dirar mikiya ba.
Jannat sukayi jarabawa suka fita daga ajin farko suka shiga na biyu jarabawar ta tayi kyau sosai babu carry over ko d'aya hakan ya k'arfafa masa guiwar cigaba da biya mata komai na makarantar.
A lokacin ne cafe d'in da yake aiki suka tashi mai cafe d'in duk ya basu hak'uri bayan yayi musu kyauta mai d'an nauyi ya kuma yi musu hanyar wani company akan suje su nemi aiki, Imran baiyi k'asa a guiwa ba yaje company neman aiki akayi sa'a ya samu tunda company ne na sarrafa y'ay'an itatuwa a mayar dasu lemon kwali. Kasancewar masani ne a computer shi aka bawa abinds ya shafe ta.
Ya fara aikin ciki sa'a gashi kuma ana basu albashi mai d'an yawa hakan ya saka shi sake zagewa yana aikin sosai.
Albashin sa na farko kayan abinci ya siya a gidan su ya siyawa su Gwaggo ma y'an uwan sa ya basu wani abu daga ciki ragowar kuma ya siyo shadda da yadi mara tsada ya bawa Nura abokin sa ya d'inka masa Jannat ma ya siya mata Atamfofi masu kyau ya bayar aka dinka ya kai mata.
Duk da samuwar wannan aikin shine yake kaita makaranta kuma yake d'auko ta a machine d'in aro, abinda ya fara sakawa d'auko ta a machine ya fita a ransa shine tanka d'in da mutane suke yi in suna tafiya kasancewar ta mace mai diri in ta hau bashin d'in koda hijjabi ta saka sai bayan ta ya bud'e yayi fad'i.
Tun yana daurewa har ya zama abin ya fara damun sa sai ya daina kaita ya samu napep suna shiga tare a sauke ta in zata dawo ma haka, kud'in da yake kashewa a napep d'in kuma sai ya fara yawa haka ya kuma daurewa yana aron machine d'in Nura yana kaita amma a zuciyar sa baya k'aunar hakan sam. Rayuwar nata tafiya Imran yana aikin sa yana kuma tara kud'i da kad'an-kad'an inda yake burin in sun taru zai bud'e shagon kayan masarufi a unguwar ya saka yaro ya dinga siyarwa.
Shiga yajin aikin da akayi ya saka karatun Jannat ya tsaya cak sai ta cigaba da kwalliyar ta ba laifi tana samu tunda duk fuska d'aya tana karb'ar dubu d'aya a ranar da ta kasance ta biki kuma takanyiwa mutum biyu zuwa uku, duk watan duniya da anyi albashi sai ga siya mata kayan sawa an d'inka hakan ya saka ta ko a jami'a baza ka ganta kaca-kaca ba kullum tsaf take duk da kayan ba masu tsada bane ba.
Imran namiji ne dogo fari ne tasss kasancewar iyayen sa duka farare ne bashi da jiki sosai haka kuma ba siriri bane ba yana da hanci dogo da kuma madaidaitan idanuwa masu kyau da d'aukar hankali, in yayi murmushi kyakykyawar wushiryar sa tana bayyana sai ta k'ara masa kyau sosai, yana da yalwar gashi a fuskar sa da jikin sa wanda suke k'ara masa kima da kwarjini a idanun duniya domin baza ka ganshi kace d'an talaka bane ba sabida yanayin halittar sa.
Yana da hak'uri sosai baya son fad'a ko kad'an in kaga kayi masa abu ya nuna ransa ya b'aci to ka tab'a Jannat ko kuma mahaifiyar sa, baya fushi amma in ya tashi fushi da b'acin rai bai iya ba, ya tsani wulaqanci a duniya yana jure komai amma banda wulaqanci duk k'imar mutum da yake gani da zarar ya wulaqanta shi girman sa zai zube a idon sa hakan ya saka shi baya zuwa koda gidan y'an uwan mahaifiyar sa ko mahaifin sa akan su taimaka masa da wani abun sabida gudun wulaqanci ya yadda yaje ya nema yayi da kansa.
Imran na kula da Jannat fiye da tunani mai tunani yana kuma ji da ita sosai har cikin zuciyar sa, baya so yaga wani abu ya rabe ta wanda zai saka ta a damuwa ko kuka yanzu hankalin sa zai tashi yaji komai ya fice masa a rai har sai tayi dariya. Yana kula da lamarin ta sosai ta b'angaren makaranta ma kawai sai dai ta ganshi unexpected yazo duba yanayin ta amma bai tab'a samun ta da wani abu mara kyau ba.
Duk da shaquwar da suka samu hakan bai hana ta shakkar sa ba da ya d'aure fuska ya fara fad'a zata shiga hankalin ta.
B'angaren Jannat kuma mace ce mara hak'uri da tsiwa bata bari indai ka tab'o ta sai ta mayar maka shiyasa bada kowa take alaqa ba dan gudun raini.
Lokacin da zuciyar ta tayi nisa a soyayyar yayan nata bata farga ba sai da soyayyar sa ta zamo ZANEN ZABUWA a ranta sannan ta fahimci hakan koda ta gane kuma batayi yunk'urin hana kanta ba dan a karancin tunanin ta shima yana son ta ne kamar yadda take son sa, yadda yake nuna kulawa a kanta yake kuna nuna zallar kishin ta ya sake k'arfafa mata guiwa nak'i kula kowa a ganin ta tana da mijin aure a hannu wanda take so yake son ta.
A hankali Imran cigaba da tara kud'in sa tunda yanzu Jannat na gida kashe kud'in nasa ya ragu sosai yana kuma cigaba da aikin sa, indai kai abokin Imran ne ko d'an unguwa kasan Jannat ko baka santa a fuska ba kasan labarin ta sabida yawan maganar ta da yake ko ya kira ta waya yaji ko tana son wani abun, da yawa a company sun d'auka matar sace sai daga baya yake shaida musu k'anwar sace ba matar sa ba.
Zuwan lokacin ya iya mota sabida motar company da za'a baka ka ja dole ya koyi mota sabida gudun b'acin rana dan yana ji ana fad'ar rashin mutuncin manager ta compny shi kuma har lokacin basu tab'a had'uwa ba.
Lokacin da suka koma yajin aiki kud'in sa sun taru sosai aka fara shirye-shiryen bud'e shago sai kuma ya canja tunani yaje ya samu mahaifiyar sa akan yana so ya siyi mota sabida zirga-zirgar wajan aikin sa da kuma kai Jannat makaranta, da Umma taso ta hana shi tace sai dai machine amma ya dage akan mota zai siya sabida baya son d'aukar Jannat a machine dak'yar Umma ta yadda sabida a ganin ta yayi d'age ya kai kansa inda Allah bai kai shi ba, a cikin kashi uku na kud'in ya d'auki kashi biyu yaje ya samo motar second hand wacce ta sha jiki ya siya ragowar kud'in kuma ya ajjiye su dan ya cigaba da tarin sa.
*Wannan kenan.*
Free page😁
_Wannan labarin na kud'i ne ki biya naira 300 kacal ki karanta cikin nutsuwa da kwanciyar hankali, domin biya tuntub'i wannan number but only WhatsApp. ***_
Wattpad @ Nana_haleema
Arewabooks @nanahaleema11.