Chapter 8
*ZANEN ZABUWA*
©️ *Nana Haleema.*
*Page 8*
Mufeedah kuwa tunda ya yanke wayar take jin wani irin nishad'i a ranta duk da yanke mata kiran yayi amma hakan bai hana ta jin dad'i ba musamman in ta tuna taji maganar sai farin ciki ya kuma kama ta, murmushi take ita kad'ai tana juya wayar ta tana fari da ido ita kad'ai, "ke kuma lafiyar ki?" Muhsin ya fad'a yana sakkowa daga sama yana kallon ta tare da zama a kusa da ita.
Sai da tayi murmushi sannan tace, "Yaya Muhsin I'm in love." Zaro ido waje yayi tare da jinjina kai yace, "really?."
"Of course."
"Wow waye wannan mai sa'a haka?."
Farrr tayi da idanun ta zatayi magana Mummy ta fito tana fad'in, "yau naga nishad'i kuke ji dashi yara na." Ta fad'a da murmushi tana zama kusa dasu tana kallon su cikin qauna.
"Mummy Mufeey in love shine nake so naji waye wannan mai sa'ar haka?." Mummy tace, "nima ta fad'a min ina so nima naji waye wannan."
"Okay duk zaku ji ai yanzu".
"Muna jin ki."
"Sunan shi Imran yana aiki a company Daddy."
Fuska Muhsin ya d'an d'aure kafin yace, "what do u mean?." Kallon sa tayi ta tab'e baki tace, "i mean a k'ark'ashi na yake aiki kuma i love him." Zaro ido waje yayi cikin mamaki yace, "Mufeey are you in your sense? Wanda yake aiki a k'ark'ashin ki kike so?." B'ata fuska tayi tace, "Yeah shi nake so."
Muhsin ya kalli Mummy da take kallon ta da alama mamaki ne ya hana ta magana yace, "Mummy kinji me tace kuwa? Wai fa wanda yake aiki a k'ark'ashin ta take so?."
Mummy tace, "Muhsin I'm very surprised about what she said that's why na kasa magana, Mufeeda wai da gaske kike wanda mahaifin ki yake biya salaryn da bai wuce fifty thousands per month ba kike so?."
D'aure fuskar ta ta kuma yi tace, "yeah Mummy da gaske nake i love him kuma auren shi zanyi ni." Rik'e hab'a Muhsin yayi yace, "oh god, Mummy anya yarinyar nan lafiya take kuwa? Ki duba wanda suke cewa suna son ta tana cewa A'a amma tazo tana cewa wai wanda take so a company Daddy yake aiki."
Mummy ma tace, "abinda ya bani mamaki kenan nima Muhsin, last month ya akayi da ita akan Abraham tace ita sam bata so amma yanzu ki rasa wanda zaki so sai talaka Mufeey?."
"Mummy, Yaya Muhsin, i want to tell you something, i love him so ban damu da yana aiki a k'ark'ashi na ba ni shi nake so ba kud'in shi ba, shi nake so ba wani abu na duniya ba, dashi nake ao na rayu daba kud'i ba in ma kud'in ne ai ni ina dashi sai na taimaka masa, wanda kuke magana a kai sam ba son su shi nake so kuma shi zan aura by god grace". Tana gama fad'ar hakan ta mik'e ta bar wajan ranta a b'ace.
Muhsin ya kalli Mummy yace, "Mummy kalli fa abinda yake k'okarin d'auko mana." Mummy kasa magana tayi sai tallafe hab'a da tayi kawai. Kwafa Muhsin yayi ya mik'e ya fita domin indai yana da raii kuma yana rayuwa a gidan bata isa ta auri talaka ba.
*******
A hankali Jannat take bud'e idon ta har ta bud'e su tarrr a tana k'arewa d'akin kallo tana so ta tuna a inda take, rufe ido tayi ta sake bud'ewa nan abinda ya faru ya fad'o mata a rai ta sake k'arewa d'akin kallo ta tabbatar a asibiti take dan ga gadon marasa lafiya nan burgik a gefen ta da kuma masu jinyar su a zaune a gefen su. motsi taji daga bayan ta kafin ta juya har an k'araso inda take ko bata kalli wanda yazo wajan ba khamshin turaren sa ya tabbatar masa da wanda yake wajan, "Jannat kin farka? Bara na kira likita" ya fad'a muryar sa a sanyaye yana kallon ta da tauyasawa ya juya ya koma inda ya fito.
Da kallo ta bishi har ya b'ace ta lumshe ido ta bud'e tana kallon marasa lafiyar da suke kwance wasu ko numfashin kirki basa yi masu jinyar su suna ta kuka, kanta ta d'aga ta kalli wani k'aramin agogo da yake manne a bangon d'akin nan idon ta ya ganar mata k'arfe sha biyu har da mintina goma, d'auke kanta tayi daga kan agogon ta daure ta mik'e zaune tana kallon hannun ta da aka manna mata cannula duk da babu drip d'in a jiki hakan ya nuna mata kenan an saka mata ya k'are, hango Imran tayi da wata nurse a bayan sa suna tunkaro inda take ta d'auke kanta tana sauke numfashi.
Lokacin da suka k'araso ta kalli inda suke nurse d'in tace, "Sannu ya jikin?." Jannat ta bud'e baki cikin rashin k'arfin jiki tace, "da sauk'i." "Ko me yake damun ki yanzu?." Jannat tace, "kaina ne yake ciwo kad'an sai k'irji na da yake min nauyi."
Bata ce komai ba ta fita bata jima ba ta dawo hannun ta d'auke da abinda auna bp ta d'aura mata a hannu ta fara auna bp ta, sai da ta gama sannan ta d'auka paper a aljihun ta ta rubuta abu a takardar ta mik'awa Imran tace, "a samo wannan allurar da kuma ruwan nan yanzu."
K'arba yayi baice komai ba ya juya ya fita da sassarfa tabi bayan sa da kallo, Wani irin abu take ji mai kama da tausayin sa yana ratsa ta ganin yadda yake ta zirga-zirga duk dan sabida ita sai jikin ta kuma yin sanyi in ta tuna itama sabida shi take a wannan yanayin.
Bai wani jima sosai ba ya dawo da leda a hannun sa yaje nurses room d'in ya kaiwa wacce ta bashi ta taso suka tawo tare ta d'aura mata ruwan bayan tayi mata allurar jijiya, gefe ya koma ya zauna yana kallon ta ta jinjina da bango idon ta a rufe, shima lumshe idon yayi yana jin wani irin d'aci a cikin zuciyar sa in ya kalle ta ya kuma tuna shekarun ta ya kuma yi tunanin dalilin kwanciyar ta a asibitin sai yaji damuwa tayi masa yawa kamar yayi hauka haka yake jin sa, "Yaya." Yaji ta furta hakan ya saka shi ya bud'e ido tare da tasowa ya dawo kusa da ita yace, "Ya akayi Jannat?." D'an runtse ido tayi ta bud'e tace, "Fitsari nake ji sosai."
Kallon hannun ta yayi yaga ruwa na shiga gashi kuma ya santa tun tana k'arama bata jurewa fitsari yanzu sai ta fara kuka in batayi shi ba, "ina zuwa." Ya furta tare da barin wajan, jimm kad'an sai gashi ya dawo shida wata nurse fuskar ta a d'aure da alama ba'a son ranta ta taso ba, "wannan garjejiyar budurwa ace baza ta iya rik'e fitsari ba zuwa ruwa ya k'are? Ni da kace min yarinya ce bata iya jurewa na d'auka wata small girl ce y'ar shekara shida zuwa goma, mtswwww haka kawai ka taso ni ina hutawa" ta fad'a tana kallon sa cikin fad'a tana binsa da harara tare da niyar komawa inda ta fito. "Dan Allah ki cire mata in ta dawo sai a mayar." Ya fad'a a sanyaye cikin sigar magiya yana kallon nurse d'in. "Mtsww sai kuma kayi malam nikam bazan iya ba in baza ta jure ba tayi shi a wajan." Tana gama fad'ar hakan ta fita ta barshi a tsaye jikin sa a sanyaye sosai.
Mai jinyar mara lafiyar dake kusa dasu tace, "kayi hak'uri bawan Allah wannan nurse d'in bata da mutunci ko kad'an baza tayi ba tunda ta fad'a, y'a ta ki daure ki jure ko zaki iya rik'e shi."
Ta fad'a tana kallon Jannat da take runtse idon ta alamun fitsarin take ji sosai. Imran ya kalle ta ba tare da yace komai ba ya k'araso yace, "zaki iya cirewa da kanki?." D'aga masa kai tayi alamun eh kafin yace, "cire muje na raka ki." Batayi musu ba ta saka hannun da babu komai ta kashe giving set d'in sannan ta zare shi a daga jikin cannula ta mayar da murfin ta ta kulle ta ziro k'afar ta k'asa ta sakko, kanta ta dafe tana layi kamar zata fad'i yayi saurin rik'e kafad'un ta yana jera mata sannu ya rik'e ta sukayi ciki inda yaga an saka female toilet.
Yana rik'e da ita yana kuma kalle-kalle ko zaiga wata macen da zata shiga ta taimaka masa ta rik'e ta, kallon sa tayi tace, "Yaya zan iya zuwa da kaina bana jin jirin yanzu."
Girgiza kai yayi kafin yace, "A'a in kika shiga kika fad'i fa?." Kafin tace wani abu matar nan ta kusa dasu tazo shiga Imran yayi sauri yace, "dan Allah baiwar Allah taimaka ki rik'e min ita ku shiga ciki jiri take yi". "Lahh babu komai" ta fad'a tana rik'e Jannat suka shiga ciki shi kuma ya koma da baya yayi nesa da band'akin yana kallon k'ofar.
Basu wani jima sosai ba suka fito tana rik'e da ita har lokacin har suka zo inda yake yace, "Nagode sosai." Murmushi tayi tace, "babu komai nima na taya ka kula da amaryar tamu dan ana ganin ku anga sabon aure, Allah ya baku zaman lafiya ya kuma inganta abinda aka samu." Tana fad'ar hakan tayi gaba shi kuma ya maye gurbin hannun matar da nasa hannun a kafad'ar ta baice komai ba.
Kallon sa Jannat d'in tayi ko zata ga wata alamar jin dad'in abinda matar tace a tare dashi amma bata gani ba sai ma fuskar sa da take a d'aure bai kuma yi magana ba, tunda suka doshi inda gadon Jannat d'in yake suke jiyo amon muryar nurse d'in da ta hana Jannat d'in tashi tana ta masifa har suka fara hango ta ita da wata mace mai sanye da atapma d'inki riga da siket ta juya baya tana kallon nurse d'in, har suka k'arasa gadon bata gansu ba sai da Jannat ta zauna sannan ta juyo ta kalle su a fusace ta k'araso tace, "wato da na hana ku tashi sai da kuka tashi ko? Ita ga y'ar gwal da baza ta iya rik'e fitsari ba shine ta cire ruwan da kanta kai kuma ka kaita band'aki wai ku tsuntsaye iyayen qauna ko,? To tunda haka ne sai ku tattara ku koma gida tunda har ta iya cire ruwa sai ta cigaba da kula da kanta." Ta fad'a cikin fad'a sosai tana aikin hararar Imran.
Kallon Imran Jannat tayi taga babu alamun zai kula tama sai ma k'okarin gyara mata zaman ta da yake son yayi ta hanyar d'auke pillown bayan ta yana gyarawa.
Hakan da yayi ba k'aramin tunzura ta yayi ba ta bud'e baki zatace wani abu wacce suke tare ta k'araso tana fad'in, "haba Nanah wannan fad'a haka kamar ba patients d'inki ba?." Juyowa tayi ta kalli wacce take mata magana kafin tace, "abin ne da takaici wallahi Antynah, ki duba wannan zabgegegiyar yarinyar amma ace wai baza ta iya rik'e fitsari na wasu mintina ba, dana k'i cire ruwan shine ta saka hannu ta cire da kanta shi kuma da yake ya zama mijin tace bita zaizai ya biye mata."
"Dallah malama ya ishe ki an tashin kiyi abinda zakiyi d'in, banza wacce bata san aikin ta ba tazo ta tsaya akan marasa lafiya tana yi musu ihu sabida rashin sanin aiki." Jannat ta fad'a cikin muryar ta da bata fita sosai amma kana ji kasan cikin fad'a tayi maganar duba da yadda take bin matar da harara.
Zatayi magana kenan wacce tayi mata magana d'azu tace, "Imran kaine?." Jin an ambaci sunan sa ya saka shi ya juya ya kalli wacce take maganar idon su ya had'u waje d'aya yace, "Madam sannu." Kallon ta nurse d'in tayi tace, "kin san shi ne?."
Mufeedah bata iya kula ta ba ta k'arasa inda Imran d'in yake ta kalli Jannat tace, "Sannu Jannat ya jiki?." Kallon ta tayi ta d'aga ido ta kalli Imran da yake kallon ta shima sannan tace, "Da sauk'i." Murmushi tayi kad'an tace, "nasan baki sanni ba, suna na Mufeedah a ina aiki a company da Yayan ki yake aiki." Sai a lokacin Jannat ta d'an saki fuska tace, "Allah Sarki, nagode."
Kallon Imran tayi tace, "Imran yame jiki?." Sai da ya sauke numfashi sannan yace, "Da sauk'i madam, mun gode da kulawa."
Y'ar dariya tayi tana bin sa da wani irin kallo mai cike da ma'anoni da dama tana jifan sa da wani irin murmushi tace, "babu komai ai an zama d'aya, amm Nana wannan da kike gani k'anwa tace a bata duk wata kulawa kafin a sallame su kar a bari wani ya sake mata fad'a balle ke da kanki kinji ko?."
Jikin Nana yayi sanyi tace, "Insha Allah za'a kiyaye, zo muje na baki sak'on Mummyn" ta fad'a tana juyawa ta bar wajan. Mufeedah tace, "Ammm Imran ko zan iya ganin ka na minti d'aya dan Allah?."
Kallon Jannat yayi yaga idon ta a kasan k'irjin ta na wani bugawa ya dawo da kallon sa ga Mufeedah yace, "babu kowa a wajan ta bana so na barta ita kad'ai in ba damuwa zamu iya bari sai wani lokacin?." Murmushin yak'e tayi tace, "babu komai Allah ya kaimu." Ta fad'a tana saka hannu a jakar ta ta d'auko rafar y'an dubu guda d'aya ta ajjiye kusa da Jannat tace, "Allah ya k'ara lafiya."
Zaiyi magana Umma tazo wajan hakan ya saka shi yin shiru Mufeedah ta duk'a ta gaida Umma tana yi mata ya mai jiki, Umma ta amsa da fara'a tana kallon Imran alamun k'arin bayani hakan ya saka shi yace, "company da nake aiki nata ne." Kafin Umma tayi magana tace, "na mahaifi na dai ni y'ar rik'on k'warya ce." Umma ta fad'ad'a fara'ar ta tayi mata godiya dan taga abinda ta ajjiye a wajan sukayi sallama ta fita daga wajan.
Kallon Umma Imran yayi bayan fitar Mufeedah yace, "Umma bara naje nayi sallar azahar na dawo." Umma ta amsa shi kuma ya fita.
"Azahar." Jannat ta maimaita tana sake kallon agogon d'akin dan ita a tunanin ta fa k'arfesha biyu na daren ranar da ta kwanta a gida ne ashe sha biyu na rana ne, "Sannu Khadijatu ya jikin?." Umma ta katse ta tana kallon ta, "Da sauk'i Umma, yau yaushe ne?." Umma tace, "yau asabar kwanan ki d'aya kenan a nan." Girgiza kai tayi bata ce komai ba wani Dr ya shigo yace, "Hajiya ga takardar sallama an sallame ku amma kafin ku tafi in Yayan nata ya dawo a turo min shi ina so na ganshi sai ku tafi" Umma ta karb'i takardar shi kuma ya fita.
Ba jimawa sosai Imran ya shigo shida Abba Jannat na ganin Abban ta tayi murmushi tace, "Abba yaushe ka dawo?."
"D'azu na dawo Janant, ya jikin naki?." "Da sauk'i Abba."
Umma tace, "Imran kaje likita na neman ka yanzu ya fita an ma sallame mu." Imran baice komai ba ya juya ya fita Umma kuma ta had'a kayan abincin da aka kawo da safe akaci.
Umma ta taimaka mata suka mik'e kafin su fita waje zuwa inda k'aramar motar Imran take su shiga baya ita da Umma Abba kuma ya shiga gaba, basu wani jima da zama sosai ba ya fito hannun sa d'auke da leda da alama magani ya siyo ya shiga ya kunna motar suka tafi.
Tunda suka shiga baice komai ba haka babu wanda yace wani abu kowa da abinda yake sakawa har suka isa gida Jannat da Umma suka shiga gidan Gwaggo suka same ta tana aikin hura wuta, "ina ta sauri na kammala abinci na kawo ashe da munyi sab'ani, sannun ku da zuwa." Gwaggo ta fad'a tana mik'ewa daga kan y'ar k'aramar kujerar da take zaune tana isowa inda suke, kan tabarmar da take inuwa a shinfid'e suka zauna a lokacin Imran da Abba suka shigo.
Imran ya kalli Jannat da ta jingina da bango yace, "Umma tana buk'atar abinci." Umma tace, "ruwan zafi zata fara sha sabida cikin ta ya warware sai taci abincin, kawo mata shayin."
Gwaggo ta mik'e tana fad'in, "haba zo ka huta kaima tun jiya kake a tsaye ko baccin kirki baka samu kayi ba, bara na kawo mata." Imran yayi saurin cewa, "A'a Gwaggo ki zauna bara na d'auko." Bai jira ta ba ya fad'a kitchen d'in dole ta koma ta zauna.
Bai jima ba ya dawo ya mik'a mata ta karb'a ta ajiiye sannan yace, "ina so na wanke baki na nayi wanka sai nasha." "A'a ki fara wanke bakin dai sai kisha daga baya sai kiyi wankan." Imran ya katse ta sauri bai jira ba ya juya zuwa inda yasan ana ajjiye abin wanke baki ya d'auko ya matsa mata man wanke bakin yace, "gashi na d'auko."
Umma ta mik'e ta kama ta suka k'arasa bakin rariya ta taimaka mata ta wanke bakin nata ta dawo tasha shayin zuwa lokacin Abba ya fita.
Tana gama sha ya kawo mata shinkafa da miyar da Gwaggo ta dafa taci kad'an ya bata magani tasha sannan ya kuma Mik'ewa zuwa inda Gwaggo ta hura huta, hannun riga ya tattare ya sauke tukunyar da take kai ya d'ora wata ya zuba ruwan zafi ya rufe dan yayi sauri.
Gwaggo da Umma kawai kallon sa suke duk da ba wannan ne na farko da suka ga hakan ba amma na wannan lokacin yafi komai basu mamaki da kuma burge su sai kallon sa kawai suke suna murmushi.
Ba jimawa ruwan yayi ya sauke ya zuba a bokiti ya sirka ya kai mata band'aki yace, "Gwaggo tazo tayi wankan." Gwaggo tace, "to Imran kaima ka wuce kaje kaci abinci ka huta." Zaiyi magana Gwaggo tayi saurin katse shi da fad'in, "kaje kawai bana son wata magana." Bashi da tacewa dole ya fita, Jannat ta mik'e ta shiga wankan Gwaggo suka cigaba da hira da Umma.
Kwana biyu Jannat tayi kafin ta warware babu laifi, ranar monday bata je makaranta ba sabida yanayin jikin nata tana zaune da maraice Gwaggo ta fita Imran ya shigo da sallama ta amsa masa tare da sunkuyar da kanta, zama yayi d'an nesa da ita yana kallon ta sannan yace, "Jannat ya jikin naki?." Jannat ta sake yin k'asa da kanta tace, "Da sauk'i sosai."
"Kin tabbata?."
"Eh, da zanje ma makaranta sabida bana jin komai yanzu."
"Ina Gwaggo?."
"Ta fita."
"Magani da abinci fa." D'ago kai tayi ta kalle shi sannan tace, "Duka naci na kuma sha."
"Jannat ina so ki bani hankalin ki zamuyi magana." Kallon sa tayi sosai kafin tace, "to Yaya ina jinka."
"Mun rabu da daddare kince min babu abinda yake damun ki daga baya kuma kince min wai aure akace kiyi ke kuma bakya so haka akayi ko?."
D'aga masa kai tayi alamun eh ya cigaba da fad'in, "da yake ban kai nasan abinda yake ranki ba sai kika barshi a zuciyar ki rabuwar mu k'adan kika suma, Jannat jinin ki ya hau sosai sabida damuwar da kika sanyawa zuciyar ki wacce babu wanda ya santa tunda kin k'i ki fad'a, ina so ki fad'a min meye yake damun ki har haka ya sa jinin ki hau kina yarinya k'arama,? Kar kiyi min k'arya Jannat ki fad'a min gaskiya." Shiru tayi ta sunkuyar da kanta k'asa tana jin sa har ya kai k'arshe amma ta kasa cewa komai.
Girgiza kai yayi kafin yace, "Yanayin ki da kuma damuwar da kike ciki yana nuni ne da kamar wacce ta fad'a soyayyar wani haka ne?." Ya tambaya yana kafe ta da idanun sa da suke sake saka ta a rudani.
Hankalin Jannat ya tashi ta d'ago ta kalle shi suka had'a ido tayi saurin sunkuyar da kanta tana sauke numfashi da sauri razani da rud'ani ya bayyana k'arara a tare da ita.
Jin tayi shiru sai jikin ta da yake rawa hakan ya bashi tabbacin hasashen shi gaskiya ne hakan ya saka shi ya sake cewa, "In akwai wanda kike so har soyayyar sa ta kaiki ga wannan yanayin dan Allah dan annabi Jannat ki fad'a min nayi miki alqawarin zan san yadda zanyi ganin ya soki ba tare da yasan ke d'in kina son sa ba." Cikin rauni da kuma taushi yake mata magana hakan ya sake saukar mata da kasala da kuma karyewar zuciya sai kawai ta fashe da kuka mai sauti.
Free page😁
_Wannan labarin na kud'i ne ki biya naira 300 kacal ki karanta cikin nutsuwa da kwanciyar hankali, domin biya tuntub'i wannan number but only WhatsApp. ***_
Wattpad @ Nana_haleema
Arewabooks @nanahaleema11.