KADDARATA CE page 11/12
___________________
Hafiz ya ce "ni ai bana daga cikin ƴan alfarma shekara goma aka ɗiba min" saurayin mai suna Yushe'u ya ce "Allah sarki ai ko shekara nawa ne indai laifin ba na kisa ba ne ai ka iya fita" Hafiz ya ce "an kamani ne da laifin yin fyaɗen da ba ni ne nayi ba" cike da mamaki Yushe'u ya ce "kamar ya ba kaine kayi ba, bayan ka ce anyanke maka hukunci kaga ai anyi shari'a kenan"
Hafiz ya ce "eh anyi shari'a amma ba bisa gaskiya ba kuma anyanke min hukunci shima bi sa zalunci" hawaye ne ya zubu masa .
Yushe'u ya ce " ni dai an kamani ne da motar giya, wacce muka ɗauko tun daga Lagos bansan giya ce a cikiba, ƴan Hisba suka kamani, kuma masu gidana sun gudu, shine aka kawo ni nan ajiya, amma nasan da zarar an danƙosu zan fita , dafa kafaɗar Hafiz yayi ya ce "nayi alƙawarin zan taimake ka, akwai wani lawyer Barrister Sadeeq Hussain Magwan, expert lawyer ne idan ka amince zamu taimaka maka, insha Allah za'a fitar da kai indai kana da gaskiya" wani ganduroba ne ya daka musu tsawa "ba za kuyi mana shiru anan ba, ana magana kuna surutun banza" kallon banza yayi wa Hafiz ya ce " ɗan iska mai hakkewa ƴaƴan mutane kalleka kamar mutumin kirki amma ka kasa riƙe sha'awarka mtswww" sunkuyar da kai Hafiz yayi yana mai jin ciwon kalaman da ake jifansa da su,
shiru suka yi, Yushe'u ya so sanin tarihin Hafiz, aka katse musu hira.
Shugaban gidan yarin ya ƙara yi musu nasiha akan su zauna lafiya da junansu.
Sallamarsu akayi kowa ya koma harkarsa.
Hafiz ya miƙe hanyar ɗakinsu jin ana kiransa da "malam, malam!" da sauri Yushe'u ya biyo shi dan jin labarin Hafiz ko zai iya taimaka masa ya fita daga gidan, ganin saurayin ɗazu ne yasa Hafiz tsayawa, cikin sakin fuska Yushe'u ya ce "ɗazu muna magana ba mu ƙarasa ba shine na biyo ka dan mu ƙarasa" take Hafiz ya sauya fuska ya ce "nagode da kulawarka amma ba na buƙatar taimakon kowa" ya wuce ya bar shi tsaye, Yushe'u ya kuma binsa dan ƙara jarraba sa'arsa, ganin ya nufi hanyar da ake ajiye manyan criminals Yushe'u ya ce " ko baka amince da ni ba inaso ka sanar da ni address ɗin ka" kallon baka da hankali Hafiz yayi masa a zuciyarsa ya na zargin ko dai wani planing ɗin ake shirya wa su Baffa aka turo wannan saurayin?
Hannuwansa ya haɗe alamar roƙo ya ce" dan Allah bawan Allah ka rabu da ni kaje kawai ina godiya da nuna damuwanka akaina Allah ya saka da alkhairi" daga nan ya ƙara sauri ya wuce, cikin sanyin jiki Yushe'u ya koma.
Bayan kwana biyu da faruwar hakan Hafiz ya saba da gidan yarin hakama maganganun da ake yaɓa masa tun suna masa ciwo a rai har ya saba da su.
Hafiz ne tsaye yana ta bugo ruwa daga borhole ɗin gidan, jiniyar motocin governor suka ji, alamar mai girma His Excellency Muhammad Bature ya kawo ziyara.
Ihu prisoners ɗin suka farayi na ganin tawagar governor sun iso, duk da akwai tazara tsakanin office ɗin shugaban gidan da inda masu laifi suke.
Cikin rawar jiki aka sauki mai girma gwamna da muƙarrabansa ciki har da Honorable Murtala G.G, daga nesa aka tara masu laifukan tun daga nesa Hafiz ya gano Hon.Murtala G.G ji yayi tsanar mutumin ta dawo sabuwa a ransa, dan shine yayi ruwa da tsaki ganin an yankewa Hafiz hukunci, duk wata shaida da hujjoji lawyernsa ne yake kawowa,kuɗi kuwa kamar banza yake ajiyewa ƴan sanda, shi ya ce dole akai kotu dan ya zama izina ga samarin da suke da al'adar yin fyaɗe.
Ana ganin shi ne ya tsaya dan kare haƙƙin Jawahir a hukunta Hafiz, daga gwamnan har Hon.G.G duk Hafiz ya tsane su.
Sulalewa yayi ya koma gefe ya dinga kuka yana Allah ya saka masa, masu ƙananan laifuka aka yafewa duk an sallame su, ciki har da Yushe'u wanda yanzu an gano ba shi da laifi, sallamarsu akayi.
Hon.G.G ya manta da wani Hafiz a gidan dan shi ya saba irin haka duk inda yaga anga wani wanda ake zargi indai yaji labari to fa baya bari ayi wani binciken kirki zai shiga gaba domin a yanke hukunci dan so yake ya zama gwamna nan gaba, shiyasa yake ta tara masoya ta hanyar farantawa wasu ya ke kuma ɓata wasu daga cikin talakawa.
Sallama Yushe'u ya je yiwa Hafiz haɗi da ƙara sanar da shi, zai dinga zuwa masa visiting in lokaci yayi, kuma a shirye yake da ya taimaka masa.
Ganin Hafiz cikin damuwa ya ce " Ustazu naso sanin labarinka tun kafin na bar gidan nan ko zan samu hanyar da zan taimake ka amma kaƙi yanzu ga shi ni zan tafi amma a shirye nake duk lokacin da ka shirya ka yarda da ni ina marhaban"
Hafiz yayi murmushi mai ciwo ya ce "to nagode Yushe'u a gaida gida Allah ya kiyaye gaba,sannan ina yi maka nasiha da ka guji harkar da kakeyi na shigo da barasa cikin al'umma kasan dai duk wanda ya ba da gudunmawa a harkar kayan maye yana da nasa kason tun daga masu sarrafata har zuwa masu siyar da ita da masu safararta ko" Yushe'u ya ce "tabbas hakane Ustazu amma wallahi tallahi bansan giya nake ɗaukowa ba kasancewata mai harkar tuƙin mota, ubangidana ne yake aike na a duk lokacin da buƙatar hakan ta taso, amma daga yau insha Allah ba ni ba shi"
Hafiz ya ji daɗi sosai kuma ya amince da shi, sallama suka yi cikin kewar juna.
Gidan yarin ya ragu dan irinsu masu satar Akuya da takalmin masallaci da sauran ƙananan laifuka da masu ƙananun bashi duk an fitar da su dan su samu su biya.Cikin dare Hafiz ya na kwance ya na tunanin abubuwan da suka faru da shi, babu abinda yake so a yanzu sai ganin su Baffa da ƴan'uwansa damuwar da suke ciki ita tafi ɗaga masa hankali "inshanAllahu sai na koyawa Murtala G.G hankali indai na bar gidan nan komai daren daɗewa" karaf a wannan maganar ta sauka a kunnen killer da Sarki.......
HON.G.G HOUSE
"Welcome to our house friends" Rahma ta faɗa tana rungume Farrah, wacce ta ci uban ado Yarinya ce age-mate ɗinsu sai dai gata da buɗewar idonta sun fi ƙarfin shekarunta, cikin jindaɗi ta taro su su shida Farrah, Zulaihat, Minal, Ikram, Firdausi da kuma Mufida, su na murnar ganin juna ne sai ga motar su Sameer kiɗan da ke tashi ne a motar ya sanarwa da Ihsan gwarzonta ya iso, gaba ɗayansu suka nufi motar dan tarar sauran ƴan ajin nasu.
Kamar yanda suka sani Sameer ne da su Aminu da Rashid tamkar wasu manyan samari hutu ya sa sun zama manyan yara kamar ƴan 23/24 years ɗin nan nan kuwa duk eighteen ne, wannan year za su kammala secondary ɗinsu.
Ihsan ce ta buɗe masa motar inda yake driving ta ce " welcome my love" hannusa ya buɗe alamar ta tawo aikuwa yana fitowa suka yi hugging juna, ihu sauran suka sa dan kowa ya san masoya ne har a class ba sa ɓoye son da sukewa juna.
A tare suka nufi parlour'n gidan,Mommy da su Yusuf zaune kamar inda su ka barsu, da sallama suka shigo Mommy ta amsa tare da yi musu welcome.
Farrah na ganin Yusuf physically gani tayi yafi a hoto kyau, tsaf suka nutsu suka gaishe da su Yusuf, Musty kuwa da yaga ƴanmata take ya fara lashe baki, mayen mata ne kamar yanda abokinsa Yusuf yake.
Ganin Farrah sai satar kallon Yusuf take ya sa shima ya gano, a ransa yana yaba yanda surarta take yana faɗin balaifi, Ihsan ta kalli mommy cikin shagwaɓa ta ce " Mommy ga Sameer wanda nake faɗamiki duk cikin class ɗinmu shine yake mana 1st position kuma ko Mommy....sai ta kasa ƙatasa maganar ta saki murmushi, Sameer ya hau sosa kai da car key ɗinsa, Rahma ta ce "bro ga Farrah best friend ɗi na" ba tare da kunya ko shayin Mommy ba Yusuf ya ce " wow hi beauty" Farrah ta saki murmushi ta na faɗin "hi bro, tnx" Mommy ta ce " kun barsu haka sai surutu kuke ba ku basu komai ba" Rahma ce ta tashi ta na kamo Farrah "ta so mu je ku ci abinci" Musty ya tashi ya ce "watukun kinga friends ɗinku kin manta da mu ko to sai mun ci" dariya sauran suka sa, banda Yusuf dan shi akwai shariya musamman a gaban ƙannensa bayason raini bare yanzu da suke tare da abokansu.
Ihsan ta ce " dear zo muje" Sameer ya ce "no barni anan ruwa kawai zaki bani is okay" me Rahma take banda dariya "hahhh Allah ya ƙara wai ke mai saurayi ko gashi nan ya gwasale ki" idanunta ne ya ciko da hawaye ganin dariyar da Rahma ta ke mata, Yusuf ya ce " babu wanda zai bar gidan nan ba tare da kowa ya ci wani abu ba"
Take Ihsan ta ji daɗi ta na yiwa Rahma kallon banza.
Samaeer ya tashi ya ce "ta wo muje dear maƙiya sai suji kunya" Rahma ta ce "oho dai naganku a rana" abun sai ya burge su Yusuf Mommy sai daɗi take ji yanda yaranta suke rayuwar ƴanci.
Sai anan ta ce " ki ce nayi sikiri bansaniba" sai anan su Ihsan suka nuna jin kunya, Sameer da wata tsinanniyar armless ɗinsa da p-cap ya saki murmushi ya yi masifar jindaɗi ganin Family'n su Ihsan wayayyu ne kamar nasu Family.
Farrah ta ce 'Yayanmu mungode da wannan karɓa da kukayi mana" Yusuf ya ce "don't mine baby duk abinda su little suke so muna sonsa ko da kuwa ba mai kyau ba ne, bare kuma ku " Musty ya ce "exactly bro yanzu dai ku zo muje ayi damu" ba kunya a dinning Ihsan ke nuna kulawarta ga Sameer su suka fara tashi, su ka nufi garden a kan plastic chairs suka zauna su na ta abinda suka saba a duk lokacin da suka keɓe, wato taɓa jikin juna, Sameer ya yi ta faman lallatse jikin Ihsan, wanda suka ɗauka ba komai ba ne sai wayewa, da soyayya.
Sameer ya ce "my tunda munzo naku gidan mu yaushe zaki zo namu?" Ihsan ta saki murmushi ta na faɗin " kar ka damu my love very soon i should go" Sameer ya ce "kinyi kyau sosai my Ihsan" abinda take so kenan tayi abu a yabeta.
Ta ce "thank you sweetheart ta na ɗora kanta gefen kafaɗansa.
Wani abu yake saƙawa aransa game da Ihsan wanda yake so ya gudanar a ranar graduation ɗinsu a matsayin gift ɗin da zai bawa Ihsan.
Kafin su Farrah su bar gidan har sun saba da Yusuf da Musty Ikram da Musty sun ɗinke dan ganin ita ce ƴar duma-duma duk tafi sauran girma.
Har takwas na dare suna gidan,Mommy ce ta ce Yusuf ya mai da Farrah ba sai ta kira anzo an mai da ita ba, Sameer ya kwashi sauran su ka tafi cike da jindaɗin karɓar da akayi musu.
Mommy ta ba su kuɗi da su biscuits amma babu wanda suka karɓa, dan duk ƴaƴan manya ne
Ihsan ce ta ba wa Sameer turaren da ya ce masa yanason ƙamshin a duk lokacin da ya ji a jikinta, shi ne dan murnar zuwansa gidan ta ba shi.
Farrah ta zage ta hau yi wa Yusuf surutu, ita ce take sanar da shi mahaifinta abokin Daddy ne, jin ta ce ita kaɗai ce ƴa ga Alhaji Tajuddeen mai Akwai. Sun taɓa haɗuwa da shi a wani hotel da suke zuwa, bai san lokacin da ya ce mata " ai dole ki yi rawar kai" Farrah ta hau dariya ansan waye Daddy'nta.
Murmushi Yusuf ya sakar mata har cikin gidan ya kaita, zai tafi ta ce bata san zance ba, sai yaga Mommy'nta sanin Daddy'nta baya ƙasar.
Shammatarsa tayi ta zare key ɗin motar ta ruga a guje ciki tana dariya. Dole ya sa Yusuf fitowa ya nufi inda ta yi.
Jikin wata farar mata fuskarta ta sha bleaching da tsagun uku-uku a gefen bakinta Farrah ta faɗa ta na dariya, da ganin matar irin ƴan duniyar nan ne, ta ce "kai baby kin girma fa ki ke wannan abun"
"Shittt!!!" ta ɗora hannunta kan lips ɗin Mommyn nata, ta ce " ki yi shiru Yayansu Ihsan ne ya kawo ni, yanzu zai shig.." Kafin ta ƙarasa Yusuf ya shigo, take idanun Hajiya Kursum ya sauka kan irin saurayin da take son yin mu'amalla da su......
Turƙashe!!!!!
Ya zata kaya tsakanin Farrah da Mommynta waye zai barwa wani??????
Shin da gaske Hafiz ne yayi fyaɗen ko kuwa wani ne da ban?