Chapter 9
*ZANEN ZABUWA*
©️ *Nana Haleema.*
*Page 9*
Zuba mata ido kawai yayi ya saka hannayen sa ya tallafi hab'ar sa yana kallon yadda take da zubar da hawaye cikin kuka mai sauti.
Baice mata komai ba sai sauraron kukan ta da yake yi yana jin saukar sa har cikin zuciyar sa amma bai hana ta ba dan yasan wata k'ila shine kad'ai zatayi taji dad'i kuma bai san abinda take ji ba.
A hankali sautin kukan nata ya ragu ya koma na kurame kafin tayi shiru sai ajiyar zuciya da take saukewa. Har lokacin baice mata komai ba ya mik'e ya kawo mata ruwa mai sanyi a kofi ya mik'a mata, ba musu ta karb'a tasha ta ajjiye kofin tana cigaba da sauke numfashi.
Sai da yaga ta d'an nutsu kad'an kafin yace, "Wannan yanayin naki ya kuma tabbatar min da hasashe na gaskiya ne soyayya ce ta jefa ki a cikin wannan yanayin da kike ciki, waye shi? A ina yake.? Ki fad'a min komai game dashi ni kuma nayi miki alqawari zanyi iya bakin k'okari na wajan ganin na samar miki da farin ciki a kan hakan."
D'uf tayi kamar ruwa ya cinye ta tana jin haushin kanta da ta fallasa sirrin zuciyar ta har yake k'okarin gano raunin ta, alqawari ta d'aukarwa zuciyar ta baza ta tab'a furta masa tana son sa koda soyayyar sa zata kai ta ga barin duniya dalilin da ya saka ta kawar da kanta gefe dan bata so tayi wani abun da zai harbo jirgin ta.
"Yaya ni babu soyayyar kowa a raina yanayi ne kawai da Allah ya saukar min amma ba abinda kake tunani bane ba." Ta fad'a a hankali kanta na k'asa ba tare da ta kalle shi ba sab'anin shi da yake kallon ta.
Murmushi yayi kad'an mai kama da murmushin takaici yace, "Jannat kenan, meyasa kike so ki dinga yi min k'arya? Meyasa baza ki fad'a min gaskiyar abinda yake ranki ba, ko tantama bana yi zuciyar ki na cikin soyayyar wani amma waye? A ina yake,? Shine abinda na tambaye ki kawai amma kice min ba haka ba,? Wallahi k'arya kika yi min kinji ma nace wallahi, ki fad'a min abinda yake ranki in kuma ba hakan ba zan fad'awa Abba likita yace jinin ki ya hau in aka cigaba da tafiya a haka kuma kina gab da kamuwa da ciwo mai tsanani, shi nasan in ya tambaye ki zaki fad'a masa ni tunda ban isa dake ba gashi kina min k'arya." Ya fad'a cikin nuna zallar b'acin rai kama jin yadda maganar sa take fita kasan ransa a b'ace yake sosai.
Girgiza masa kai tayi alamun a'a kafin tace, "ka isa dani wallahi Yaya babu wani abu da ya shafe ni da baka isa dashi ba, kayi hak'uri dan Allah."
"To meyasa kike yi min k'arya?."
Shiru tayi bata amsa ba hakan ya saka shi ya sake cewa, "naji na isa dake in kina so na tabbatar da hakan ki bani amsar tambayoyin da nayi miki kawai."
Nan ma shiru tayi tana tattaro dukkan k'arfin guiwa da take tare da ita a lokacin tace, "Wani ne Yaya, Allah ya saka min qaunar sa tun ban san menene so ba, na rayu da qaunar sa a cikin zuciya ta har kawo yanzu, bai san ina yi ba hasalima bai tab'a yi min kallon wacce zai so ba k'arshe yaje yayi auren sa ya barni da tunani da kuma dakon soyayyar sa da ta riga da ta zama ZANEN ZABUWA a zuciya ta, wannan dalilin shine yake saka ni a damuwar da take kaini kwanciya a asibiti, ban saba ba ban kuma san menene so ba sai a kansa, na kasa cire shi a raina kullum addu'a nake a kan hakan amma abin yaci tura." Ta k'arasa fad'a tana sakin kuka mai sauti.
Tunda ta fara maganar ya lumshe idon sa ya jingina kansa da bango yana jin yadda kalaman ta suke sauka a zuciyar sa suna fashewa kamar kwai ruwan cikin su yana bin jijiyoyi da tsokar da Allah ya halitta a ciki.
Jikin sa yayi bala'in sanyi cikin rashin sanin dalilin da ya haifar da hakan idon sa a kulle yana jin duk abinda take cewa yana shiga jikin sa sosai. Jin ta kai k'arshe lokacin da ta fashe da kuka ya saka shi sauke numfashi kad'an ya gyara zaman sa ya mik'e zaune sosai ya bud'e idon sa da suke a lumshe ya kalle ta yace, "A ina yake a yanzu haka?." Duk da kukan da take yi jin yanayin maganar sa ta canja ya saka ta d'ago ta kalle shi ta girgiza kai tace, "Ya mutu Yaya." Ta fad'a cikin karyar da murya sosai hawaye na sake zubowa daga idon ta har lokacin kallon sa take yi.
"Hasbunallahu wani'imal wakil." Abinda Imran ya furta kenan bayan ya kulle fuskar sa da hannayen sa kafin ya bud'e ya sake sauke numfashi kana ya zuba mata ido yana kallon yadda take kuka kana ganin yadda take hawaye zaka fahimci daga zuciyar ta take kukan. "Jannattt!." Ya furta cikin muryar sa mai sanyi yana kallon ta, d'ago idon ta da suka koma jajaye tayi ta kalle shi ba tare da ta amsa ba yace, "Baki yi imani da k'addara bane?."
Girgiza masa kai tayi alamun a'a kafin tace, "nayi Yaya, kawai na kasa jurewa ne ina iya bakin k'okari na wajan ganin na cire komai a raina amma abin yafi k'arfi na." Numfashi ya sake fesarwa kafin yace, "Allah kad'ai yasan abinda kike ji a zuciyar ki ban san me kike ji ba kamar yadda kema baki san me nake ji ba in na ganki a irin wannan yanayin, indai har kinyi imani da k'addara kiyi hak'uri ki cire komai a ranki ki mik'awa Allah lamarin ki cigaba da addu'a komai zai wuce da izinin Allah, wannan damuwar da kike ba komai zata jawo miki ba sai ciwo kinga anyi biyu kenan ga ciwo ga kuma damuwa, damuwa bata magani kamar yadda kuka baya magani daurewa zakiyi ki mik'awa Allah lamarin ki a hannun sa yafi kowa sanin abinda yake ranki shine kuma zaiyi miki maganin duk abinda kike ji."
Goge idon ta tayi ta d'aga kai alamun gamsuwa tace, "In sha Allah Yaya zanyi kaima ka taya ni da addu'a Allah ya cire min abinda nake ji a raina."
Maimakon yayi magana sai kawai ya zuba mata ido yana kallon ta tare da karantar yanayin ta dan shi sam bai yadda da labarin da ta bashi ba kawai ya jita ne ya kuma tabbatar akwai abinda take b'oyewa wanda bata so ya sani shiyasa tayi creating labari ta bashi a tunanin ta zai amince da shi.
Jin yayi shiru sai yawon da take ji idon sa nayi a kanta ya saka ta kalle shi sai kuwa suka had'a ido yace, "shi wanda kike so din har ya bar duniya ya akayi ban san shi ba? Tunda gashi kusancin ku dashi ya jefa ki a soyayya ai ya kamata ace nasan shi." Saurin d'auke idon ta tayi ta mayar dashi k'asa tana raba ido tana tunanin k'aryar da zatayi masa, ganin yanayin da ta shiga tana so ta had'a abinda zata ce masa ya saka yayi murmushi ya girgiza kai yace, "Jannaty kenan, kar ki sake yin k'arya a kan k'arya kar zunubin yayi miki yawa, abinda kika manta shine babu wani wanda zakiyi alaqa dashi a unguwar nan ko a waje ko a makaranta ba tare da Imran ya san shi ba, koda a b'oye kike yi kina tunanin ban sani ba na sani sai dai nayi miki shiru, ban amince da labarin ki ba amma tabbas akwai kwatankwacin sa a ranki ma'ana akwai wanda kike so d'in a ranki bakya so na sani ne kawai shiyasa, is okay Jannat tunda bakya so nasan damuwar ki, ban sani ba ko ban kai naji d'in bane yasa kike min k'arya kedai kika sani, zan kuma maimaita miki ki mik'a lamarin ki ga Allah kuka da damuwa ba shine magani ba nima kuma nayi miki alqawarin zan taya ki da addu'a akan hakan kodan lafiyar ki da karatun ki, basai kin fad'a min abinda yake damun ki ba tunda bakya so na sani shikenan zanyi addu'ar kamar yadda kika ce amma ina so ki sani, matuk'ar kika bari wani abun ya sake samun ki ta dalilin damuwar da kika saka a ranki wallahi sai na fad'awa su Abba da Gwaggo gaskiyar abinda yake damun ki wata k'ila su in sun tambaye ki baza ki k'i fad'a musu ba."
Jin yadda ya k'arashe maganar sa ta k'arshe cikin fad'a ya saka ta d'ago ido ta kalle shi yace, "basu san cewa hawan jini ne ya kai ki ga kwanciyar asibiti ba na sanar dasu malaria ce ta ja hakan, hankalin su bazai tab'a kwanciya ba in har suka ji kamar ki kin kwanta a asibiti ta dalilin hawan jini, tunda abin naki yazo da haka in hakan ta sake faruwa wallahi sai na fad'a musu kinji ma kuma na rantse, ki tashi ki wanke fuskar kar Gwaggo ta dawo ta gane kinyi kuka." Yana fad'ar hakan ya mik'e yana niyar barin wajan.
Gefen rigar sa tayi saurin rik'ewa ta kalle shi tace, "Yaya na!" Ta fad'a cikin sanyin murya tana kallon sa dan tasan fushi yayi da ita. Juyowa yayi ya kalle ta yace, "me kuma zaki cemin Jannat? Kin nuna min matsayi na akan lamarin ki me kuma zaki ce min?." Girgiza masa kai tayi tace, "ka wuce wallahi ka wuce wannan matsayin Yaya dan Allah ka daina fad'ar hakan."
Gyara tsayuwar sa yayi ya hard'e hannayen sa a k'irji yace, "To in bance hakan ba me kike so nace? Bakya b'oye min komai amma wannan kink'i fad'a min ban san dalilin hakan ba." Sakin gefen rigar sa tayi tace, "Kayi hak'uri." D'an murmushi yayi na gefen baki baice komai ba ya fita daga gidan ya barta a wajan tana kallon sa har ya fice.
Had'a kai tayi da guiwa ta cigaba da kukan ta son ranta hankalin ta yayi bala'in tashi dan babban tashin hankalin ta da fargabar ta bai wuce ace yau Imran na fushi da ita ba yanzu zata kasa nutsuwa sai taga sun shirya hankalin ta yake kwanciya.
Cikin muryar kuka take furta, "bazan iya furta maka kai nake so ba Yaya, bazan iya ba koda hakan zai yi silar bari na duba, zan bar hakan a raina har sai lokacin da ka gano da kanka, kayi hak'uri yaya na, wannan sirrin zuciya tane." Ta k'arashe fad'a tana sake fashewa da kuka babu mai rarrashin ta.
Abba da tun daga soro yake jin kukan ta ya shigo da sauri har yazo kusa da ita yana yi mata magana amma bata ji ba sai da ya d'aga murya yace, "ke Khadija!." A firgice ta d'ago ta kalle shi tace, "Na'am Abba." Ta fad'a muryar ta har rawa take idon ta yayi ja hawaye na kan fuskar ta. "Lafiya kike ina ta miki magana baki ji ba? Me yake damun ki kike kuka?." A firgice tace, "Abba kaina ne yake min ciwo sosai."
"To dan kanki yana ciwo sai ki zauna kina kuka? Ina maganin ki?."
"Yana d'aki?."
"Tashi kije ki d'auka kisha, Gwaggon naki bata dawo bane?."
"Eh bata dawo ba." Daga haka ta shiga cikin d'aki Abba kuma ya shiga wani k'aramin d'akin da littafan sa suke a soron gidan.
Har dare bata sake jin motsin Imran ba ko waya bai mata ba hankalin ta ya tashi sosai sai kiran sa take amma tak'i shiga, ta shiga tashin hankalin sosai hankalin yak'i kwanciya ko abinci tak'i ci koda da Gwaggo ta dawo ta bata abinci cewa tayi ta k'oshi kanta na ciwo.
Ta b'angaren Imran d'in ma haka gabad'aya ya kasa nutsuwa so yake ya kira ta amma yana daurewa dan sosai yaji haushin b'oye masa damuwar ta da tayi hakan ya saka ya share ta kodan ya nuna mata b'acin ransa a kan hakan duk da wahalar da yake sha a zuciyar sa akan share ta d'in da yayi.
Duk yadda ya kai da juriyar kasawa yayi da daddare ya shiga gidan da sallama a lokacin Gwaggo da Abba suna zaune a tsakar gidan suna hira sama-sama.
"Abba sannu da hutawa." Ya fad'a yana zama a gefen tabarmar da take shinfid'e, Abba yace, "yauwa Imran ya aikin?."
"Lafiya lau Abba."
"To ma sha Allah, a cigaba da addu'a kar ayi sake domin duk matsayin da kake kai a rayuwa kai kana ganin ba komai bane balle ya tsonewa wani ido to wani da kai yake kwana yake tashi a ransa, yana tunanin ta wacce hanya zai bi yaga ya ture ka daga matsayin da kake kai, dan haka a rik'e addu'a kar ayi sake kaji ko?."
D'aga kai yayi alamun gamsuwa kafin yace, "in sha Allah Abba, Allah ya saka da alkhairi." Gwaggo ya kalla yace, "Gwaggo ina Jannat?." Gwaggo tace, "tana ciki ko abinci bata ci ba wai tace ta k'oshi."
"Me taci da ta k'oshi?." Ya tambaya cikin yanayin damuwa yana kallon Gwaggo. "To ina zan sani Imran? Haka tace ta k'oshi shiyasa na k'yale ta.
Abba yace, "ai bai kamata a barta bata ci komai ba, dubo ta ki kira ta." Ya fad'a yana kallon Gwaggon, ba musu ta mik'e ta shiga ciki ba jimawa suka fito tare da ita tana gaba Jannat na binta a baya.
Abba ya kalle ta bayan ta zauna yace, "Jannat me ya hana ki cin abinci?."
"Babu komai Abba bana jin yunwar ne."
"To maza ki ci abinci yanzu kisha maganin ki kinga ba lafiya ce dake ba." Da toh ta amsa ta yunk'ura zata mike Imran ya riga ta tare da fad'in, "Gwaggo ina abincin yake na d'auko mata?." Gwaggo tayi murmushi kad'an tace, "yana d'akin girkin." Baice komai ba ya shiga ciki ya zubo mata a faranti ya had'o da ruwa ya dawo ya ajjiye a gaban ta, d'an d'ago kai tayi ta kalle shi taga ya d'aure fuska babu alamun dariya a tare dashi hakan ya sake jefa ta cikin sabon yanayi mara dad'i.
Bai bar gidan ba sai da yaga ta ci tasha magani sannan ya yiwa su Gwaggo sallama tare da yi musu sai da safe ya fita ba tare da yace mata komai ba, barin sa wajan duk sai ta takura hakan ya saka ya ta mik'e ta shiga band'aki ba jimawa ta fitowa tayi alwala tayiwa iyayen nata sai da safe ta shige ciki.
Gwaggo ta kalli Abba tace, "Nikam Malam mai ka karanta game da yanayin Jannat da Imran?." Juyo da kallon sa yayi gare ta yace, "kamar yaya kenan?." Gwaggo tace, "ni sai nake ganin kamar shaquwar su tun ta yarinta ta koma soyayya mai k'arfin gaske ma kuwa." D'an murmushi Abba yayi yace, "inda hakan zata kasance ai da munfi kowa farin ciki, amma kar ki manta Imran yasha fad'ar shifa soyayyar y'an uwantaka yake yiwa Jannat ba soyayyar aure ba." Cikin gamsuwa Gwaggo tace, "haka ne, amma sai nake ganin kamar komai ya canja musamman daga b'angaren ita Jannat d'in."
Abba yayi d'an jimm kana yace, "to bama ce ba kin san yaran yanzu ba kasafai ake fahimtar abinda yake zuciyar su ba, abinda na kudure a raina shine indai Imran ya furta yana son Jannat koda an saka ranar auren ta da wani sai an warware, babu wanda ya cancani ya aure ta in bashi ba duba da yadda suka taso tun yarinta, wannan shine kudiri na a zuciya ta." Girgiza kai Gwaggi tayi cikin gamsuwa tace, "Allah ya sa mu dace." Malam ya amsa da amin suka cigaba da tattauwa sama-sama.
Washe gari Jannat ta tashi da niyar zuwa makaranta hakan ya saka ta tashi da wuri ta d'an ragewa Gwaggo ayyuka kafin ta shirya, lokacin da Gwaggo ta fito ma har ta gama saka kaya Gwaggo tace, "Jannat zaki iya zuwa makarantar?." Kallon Gwaggo tayi kafin tace, "Sannu da fitowa Gwaggo."
"Yauwa."
"Waya mukayi da Nafisa tace min ana ta abubuwa masu mahimmaci yana wuce ni shiyasa zanje tunda naji sauk'i."
"To abinci fa kinci?."
"Nasha tea kawai in naje can naci."
"Kije wajan Abban ki ki karb'i kud'in abinci to." Ta amsa da to tayi mata Allah ya kiyaye ta fita.
Bayan ta karb'i kud'in wajan Abba ta shiga gidan su Imran ta samu Umma ta d'an aikace-aikace a tsakar gida, "Umma sannu da aiki." Kallon ta tayi tace, "A'a Jannat, ya jikin naki?."
"Umma ai naji sauk'i, ina kwana?." Ta fad'a tare da d'urkusawa har k'asa. "Lafiya lau Jannat, ya k'arfin jikin naki?." "Naji sauk'i sosai ai Umma."
"Ma sha Allah, Allah ya k'ara lafiya, gashi kuma yau yayan naki har ya fice ina jin bai san zaki je makaranta ba."
Jimm tayi jin ya fita duk sai jikin ta yayi sanyi ta tabbatar fushin da yake da ita ba k'arami bane da har ya fita bai shiga yaga yanayin jikin ta ba, cikin sanyi jiki tace, "lallai yau sauri yake kenan bara nayi sauri na tafi kar na makara." Umma tace, "To Allah ya kiyaye hanya." Ta amsa da amin ta fita daga gidan idon ta ya ciko da kwallah.
Haka taje makarantar bata da kuzari ko d'aya lecture farko ma kawai ta zauna ne amma bawai dan ta fahimta ba dan sosai k'irjin ta yayi mata nauyi ko numfashi taja sai taji zafi, bayan fitowar su daga lecture ta farko suna jiran lokacin ta biyun suna zaune da Nafisa tana nuna mata abubuwan da akayi bata nan ba zato ba tsammani Jannat taji saukar mari mai zafin gaske a kuncin ta.
A firgice jakar hannun ta da littafan dake cinyar ta da wayar ta suka zube a wajan ta d'ago da sauri tana kallon wanda ya aikata hakan, Muhsin ne tsaye a kanta fuskar sa a mutuk'ar tamke yana hararar ta kamar idon sa zai fad'o.
A fusace ta mik'e zata rama yayi saurin rik'e hannun ta tare da murd'a shi baya yace, "kee har kin isa ki kawo wannan kazamin hannun naki inda fuska na yake?." Duk da azabar da take ji hakan bai hana ta tace, "Kaine k'azami, shashasha mai fad'a da mata bani ba, kuma wallahi in badan ka rik'e hannu na ba da babu abinda zai hana ban rama marin da kayi min ba in kuma kana ganin bazan iya ba ka saki hannun nawa ka gani." Ta fad'a cikin amo tana hararar sa.
Ransa ya sake b'aci ganin yadda y'an school suka taru gashi ta kira shi da shashasha kuma banza a gaban su, sake murd'a hannun ta yayi tayi k'ara shi kuma yace, "Warning nake miki akan sake zagi na ko fad'a min wata kalma mara dad'i in ba haka ba wallahi zakiyi dana sanin da baki fad'a yi ba a rayuwar ki, zakiyi kukan da baki tab'a yi ba a rayuwar ki, haka zaki tsani kanki tsana mai muni dan shiga gonar Muhsin ba abu bane mai sauk'i."
Yawu ta tattaro na bakin ta ta tofa masa a fuska tace, "In ka tashi ka kashe ni kar ka barni da rai, an fad'a banza, shashasha, mahaukaci, wawa, mai fad'a da mata wanda kuma bai san darajar matan ba, an fad'a maka ni irin ko wacce mace ce da zanji tsoron ka? Mtswwww dana ji tsoron ka gwara naji tsorom komai na duniyar nan ciki harda dabbobi dan sun fika mahimmaci a waje na."
Wani irin numfashi ya futar ya d'aga hannu zai sake marin ta aka rik'e hannun nasa daga baya.
"Kar ka kuskura wannan ba irin matan da ka saba duka bane." Imran ya fad'a bayan ya saki hannun sa ya kuma fincike Jannat daga rik'on da yayi mata.
Jikin Muhsin har rawa yake sabida b'acin rai ya dafe kai da hannayen sa duka biyu bakin sa na rawa amma ya rasa abinda zai ce sabida tsabar takaici da bak'in cikin da yake nuk'urk'usar zuciyar sa.
Wani irin tiriri yake ji tun daga zuciyar sa har na tasowa yana bin jijiyoyin jikin sa yana shiga jini, har duhu yake gani sabida b'acin rai dalilin da ya saka ya bud'e idon sa ya neme su ya rasa a wajan sai mutane da suke kallon sa, Waje ya samu ya zauna yana dukan bishiyar da take wajan yana gyad'a kai kamar kadangare.
Jannat da Imran da Nafisa kuwa direct security division suka nufa dan sosai ran Imran ya b'aci da abinda Mushin yake yiwa Jannat hakan ya saka shi kai report dan a d'auki mataki.
Bayan ya gama yiwa shuganan su d'in bayanin komai Jannat ma ta d'ora nata ga Nafisa da take shaida ko yaushe a gaban ta ake yin komai yace, "Shikenan malam Imran insha Allah zamuyi maganin abun, mun gode da kazo ka sanar damu baka d'auki doka a hannun ka ba."
Na kusa dashi yace, "yaron sam baya ji ko kad'an ya raina kowa abinda yaga dama shi yake yi dan yana ganin babban sa shine kano central senator shiyasa yake abinda yaga dama, kaga Bashir jeka ka kira mana Muhsin yanzu yazo ayi masa warning."
Assist d'in shi ya fad'a ba tare da ya kalli ogan nasa ba dan yasan ba wani hukunci da zai d'auka ya fad'a ne kawai amma yana daga cikin masu tsoron Muhsin a makarantar.
Ba jimawa wanda aka tura ya dawo yace, "yace ace bazai zo ba in an isa azo a d'auke shi, yaron nan bashi da kirki baka ga yadda ya hayayyaqo min ba kamar zai dake ni." Assi yace, "shi waye da za'a tura yazo yace bazai zo ba? Yafi k'arfin dokar makaranta ne?."
"Makarantar ma nafi k'arfin ta balle wata banzar dokar ku." Ya fad'a yana daga laluben office d'in yana shigowa cikin gadara da isa.
Kafin Ogan yayi magana Assistant ya riga shi da fad'in, "K'arya kake wallahi, ai tunda kana cikin makarantar sunan d'alibi to baka fi k'arfin doka ba dole doka tayi aiki a kanka."
Tsaki yaja kafin yace, "Fad'i matsalar ka wacce ta saka kuka ce nazo." Nuna masa Jannat yayi da suke zaune a gefe guda yace, "Yayan Khadijah Aminu ya kawo k'ara a kan takurawa k'anwar sa da kake dan haka babu kai babu ita an muku katanga da ita daga rana irin ta yau."
Juyawa yayi yaga wacece Khadijah d'in ganin wacce take zaune ya saka shi zaro ido yace, "Ohh daman wai sune suka kawo k'ara ta?."
"Sune, dan haka babu ruwan ka da ita ko harara kar ta sake had'a ku." Girgiza kai yayi yana cize bakin sa ya naushi hannun sa tare da furta, "Damn it." Abinda yace kenan ya saka kai ya fita daga office d'in bai sake kallon kowa ba.
Tsaki Assistant yayi kafin ya kalli Imran yace, "Kar ka damu Imran in sha Allah komai yazo k'arshe, ke kuma kar ki dinga shiga lamarin sa kin ji ko?." Kai ta d'aga kawai sukayi musu sallama suka fito.
Sai da suka yi tafiya kad'an kafin ya kalle ta har lokacin fuskar nan tasa a d'aure take yace, "kun gama lecture d'in ne?." Tafiya suka cigaba da yi kafin tace, "A'a akwai sauran guda biyu sai bayan azahar zan dawo."
"Okay inda wani abun kiyi min waya." Ta amsa da toh suna tafiya har suka zo inda ya ajjiye motar sa.
Kallon fuskar ta yayi yaga gefen fuskar ta ya tashi sosai ga kuma shaidar yatsu a kwance a wajan yace, "Before nazo wajan ya mare ki ne?." D'aga kasa kai tayi alamun eh kamar zatayi kuka, zaiyi magana kenan yaga tawowar Muhsin wajan a fusace yana zuwa ya nuna Imran yace, "waye kai? Me kake dashi? Waye uban ka a Nigeria har zaka kai k'ara ta wajan k'ask'antun makaranta security division?."
"Sa'a ma kayi da ban kai k'arar ka police station ba na tsaya iya makarantar, ina yi maka warning akan Jannat babu ruwan ka da ita kar ka sake d'aga hannu ka dake ta in ba haka ba wallahi zakayi dana sani" Imran ya fad'a cikin b'acin rai yana kallon sa.
"In naki fa? Me zakayi min?." Muhsin shima ya fad'a cikin nasa b'acin ran.
"Sai kayi ai sannan zaka ga abinda zan maka d'in yanzu gargad'i nake maka in kunne yaji jiki ya tsira."
"Kai har ka isa kayi min gargad'i? Me kake dashi a duniyar nan? Baka isa ba kuma baza ka isa ba, kuma wallahi sai na d'auki mataki a kanka sai kayi dana sanin kai k'ara ta da kayi ka dawo kuma kana fad'a min maganar banza, badai k'anwar taka gata ba kuma a school din nan take ko? Ka jira kaga abinda zanyi wallahi sai na saka kayi kuka da idon ka a lokacin da baka shirya masa ba."
Tab'e baki Imran yayi cikin rashin damuwa yace, "in ka tashi yimin hukuncin ka kashe ni kar ka barni da rai in raina a hannun ka yake, amma wallahi kaji na rantse ka sake ko hararar Jannat ka sake yi wallahi nima sai na d'auki mataki a kanka, na wuce duk inda kake tunani indai a kan Jannat ne."
Ya fad'a yana matsowa sosai kusa dashi ba tare da niya ba kawai yaji ya d'auke Mushin da mari wanda shi kansa sai bayan ya aikata hakan ya farga da abinda yayi amma bai nuna ba yace, "Baka mare ta a banza ba in ka tashi sai kayi min hukunci har na marin nakan da nayi maka yanzu, in kaso sai ka saka a cire min fuska ni, Jannaty ku wuce ku tafi class." Ya fad'a yana kallon ta, mamaki da al'ajabin yayan nata ya saka ta kasa koda motsin kirki har sai da taji maganar sa sannan ta iya motsawa suka bar wajan tana waiwayen sa.
Muhsin kuwa kamar wanda aka hana ya kasa koda motsi sai kallon Imran da yake yi shi kuma bai sake bi ta kansa ba ya bud'e motar sa ya shiga ya bar shi a tsaye a wajan yana kallon sa.
Salim ne ya k'araso wajan da saurin yana fad'in, "Haba Muhsin me ya kaika fad'a da wad'an nan? Ina shigowa yanzu abinda aka fara fad'a min kenan wannan ai ba girman ka bane." Jikin sa har rawa yake yace, "sai na d'auki mummunan mataki a kansa, bazan barshi ba wallahi sai na saka shi kukan zuciya da idanu, sai na tarwatsa masa farin cikin sa, sai yayi dana sanin sani na da yayi a rayuwar sa, k'anwar tasa da yake taqama da ita sai na raba su rabuwa ta har abadah." Kamar wanda ya zauce haka yake zuba dak'yar Salim ya ja shi suka shiga mota suka bar school din.
Free page😁
_Wannan labarin na kud'i ne ki biya naira 300 kacal ki karanta cikin nutsuwa da kwanciyar hankali, domin biya tuntub'i wannan number but only WhatsApp. ***_
Wattpad @ Nana_haleema
Arewabooks @nanahaleema11.