KADDARATA CE

KADDARATA CE Page 17/18

by @zinariya0102



Wani yarrr ta ji ganin handsome ya shigo tare da sallama wacce lips ɗinsa kaɗai ne ya motsa alamar sallama yayi, Farrah ta kuma kwantar da kanta a jikin kafaɗar mahaifiyarta tana jin wani irin shauƙi da soyayyar Yusuf na ratsa jini da tsokan da ke sassan jikinta "bar.....kah.. d..da...zuwa" Hajiya Kursum ta faɗa cikin shacking voice, Yusuf ya zauna yayi balanced akan ɗaya daga cikin royal chairs ɗin dake cikin parlour'n ya ce "barka dai Hajiya kuna lafiya" 

Hajiya ta amsa tana sakin fara'a "Alhamdulillah ya su Maman naka, ya kuka sha fama da Farrah" 

Yusuf ya sosa ɗan guntun gemunsa brown colour ya yi murmushi ba tare da ya amsa ba.


Hajiya Kursum ta ce " kar dai kaima ɗan Honorble ne?" Yusuf ya ce "yes i'm first child of my parent Yusuf Murtala G.G by name" 

Mayaudarin murmushi Hajiya Kursum ta saki ta ce "masha Allah, nagode ƙwarai da gaske ai nima inan zuwa mu gaisa da Mommy dan Farrah ba tada magana sai ta Rahma da Ihsan"

Surutun ne ya ishi Yusuf ya miƙe yana yatsina fuska, a tare Farrah da Hajiya suka miƙe, "kai Yaya ba dai tafiya zakayi ba tun yanzu" Farrrah ta faɗa kamar zatayi kuka, Yusuf da yarinyar ta fara hargitsa shi, ya ce "akwai waɗanda suke jiransa ne amma zan dawo wani lokacin" 

Hajiya ta ce " humm ko dai budurwarka na jiranka ba, dan da gani zance zaka je" Yusuf ya kuma yatsina fuska ya ce "no Mom ba zance zanje ba, club zamuje so inason in ɗanyi refreshing kaina ne" Hajiya taji daɗi jin da alama Yaron tantiri ne, ba zai yi wahalar shawo kai ba.


Da sauri ta ɗauki wayarta ta ce " kayi gaskiya kam, amma sai ka ba ni contact ɗinka, dan idan ka koma in san ka isa lafiya" Farrah ce ta karɓi wayan tana washe baki ta miƙa masa, cikin ƙosawa ya karɓa ya sa number yana fita.

Wani fari Hajiya Kursum tayi tana raya cewar " kifi daga sama gasasshe, irin types ɗin da nake so kenan" Farrah ta ce "Mommy nagaji da yawa"  

Da sauri Hajiya Kursum ta ce"ayyah sorry my baby je ki samu rest kinji" Farrah ta nufi sama dan watsa ruwa, bata tare da yunwa dan sunyu dinner a gidansu Rahma.



Hajiya Kursum ta hau neman wata number a wayanta, tana sakin murmushi can taji an amsa, ta ce" Hajiya Badi'a albishirinki?" 

Wacce ake kira da Hajiya Badi'a ta amsa daga can, nan Hajiya Kursum ta ce "nima na samu wani yaro ɗanyen jini sharaf ingayamiki, sai dai bansaniba ko zai amince"

 Hajiya Badi'a da ke cikin parlour'nta tare da wani babban ɗan siyasa mai suna Alhaji Kaita (abokin mijinta,vice ɗin sa) ta sheƙe da dariya ta ce " au yanzu kin yar da makaman wa'azin da ƙalallahu ƙala rasulun kenan?" 

Hajiya Kursum ta ce " wallahi Hajiya abun ne na Alhaji ya ishe ni, yau shine waccen ƙasa gobe wancen gari babu abinda yake tsinana mana, ga wannan Yaron yau ɗin nan na fara ganinsa amma duk ya rikitamin lissafi" 

Hajiya Badi'a ta ce " ai kawai ki sakar masa masu gidan rana, kinsan naira mai sa ayi dole kiyi ƙoƙarin jan ra'ayinsa da kuɗ.. "ke kinsan irin Yaron kuwa shima iyayensa sun taka leda fa, nasan ba shi da matsalar kuɗi" 

Hajiya Badi'a ta ce " haba Hajiya Kursum sai ka ce ba mace ba, ki nuna masa so da kulawa ba Namiji ba ne nan da nan zakiyi ram da shi a tafin hannunki yayi miki yanda kike so, ke yaran nan fa akwai daɗin harka ni babu ruwana da Alhaji ko ya zauna ko kar ya zauna uwarsu ɗaya ubansu ɗaya"

Sun daɗe suna tattaunawa daga ƙarshe sukayi sallama.



Farrah da ta gama komai ta hau online, Yusuf tayi wa magana ganin baya kai ya sa ta sauka dan zuwa ga Mommy. Ta fito kenan daga toilet tana shirin bacci ta ji Farrah ta shigo, kallon ƴarta ta tayi cikin riga wacce take iya cibi da wando iya cinya na bacci, masu taushi.

Ta ce " Farrah ba ki yi bacci ba?" Yeah mommy na zo yi miki good night ne" Hajiya Kursum tayi murmushi da shafa kwantaccen gashin ƴarta ta, ta ce " okay bari in shirya in rakaki har bed sweetheart" Farrah ta zauna ta na kallon yanda Maman nata take ta shafe-shafe, kasa shiru tayi ta ce"oh mommy wannan gayu haka, ko dai daddy zai dawo ne cikin daren nan ne?" 

Hajiya Kursum ta ɓata rai ta ce " wana daddy'n, kenan ba zan ji yarda kaina ƙamshi ba sai daddy"Farrah da ke dariya ta ce "sorry my mommy kinyi kyau" 

Kai kawai Hajiya Kursum ta girgiza ta ce "ta shi muje sarkin magana" 

Sai da ta ga Farrah ta kwanta sannan ta ja mata bargo tayi mata good night kiss in her forehead ta ja mata ƙofa ta fita.



Ɗakinta ta dawo ta ɗauki wayarta dan kiran Yusuf.

Ya na tare da su Musty da wasu ƴanmata a club sai rawa sukeyi wasu na shan shisha wasu wine wasu sigari, duk ringing ɗin da wayar Yusuf take bai jiba.


Hajiya Kursum ta kira shi har tagaji da kira ba'ayi picking ba haƙura tayi har bacci ya ɗauketa, cikin bacci taji ringing janyo wayan tayi dan ganin waye, ware ido tayi ganin number.........




G.G HOUSE


Bayan su Sameer sun tafi Mommy da Ihsan da Rahma sai hirar su sukeyi, Rahma ta ce " Alhamdulillahi yau burina ya cika Farrah taga big bro" Mommy ta kalleta ta ce " daman tasan yayanku ne?" Rahma ta ce "a'a kawai tunda taga pics ɗinsa a phone ɗina kullum sai ta ce min ya yake, in gaishe shi, yauwa dan Allah Mommy wai yaya yafi mu kyau?" Mommy ta ce " yaro kenan maybe jininsu ne ya haɗu dan naga da suka zo ma tafi hira da shi, bai fiki kyau ba ina wani kyau ga Namiji kema kinsan kawai faɗa tayi" cikin murna Rahma ta ce "yeeeh shiyasa nake sonki mommy"

Ihsan da sai nishaɗi take taga abin ƙaunarta Sameer a gidansu,Mommy ta ce "to lover girl idan kingama shirman soyayyar taki sai ki tashi ku wuce sama dan yau Muhsin a gida zai kwana" 

Ihsan ta dafe ƙirji " are you serious mommy?" 

Rahma ta ce " gara da Allah ya sa bayanan friends ɗin mu suka zo, da mun shiga uku"

Mommy ta ja tsaki " wai ace ƙannenka ma ba sa son zuwanka, tsabar jaraba ni kam wana irin yaro ne Muhsin, ɗa kamar ba ni na haifa ba, komai nasa daban kai wannan rayuwa" 

Ihsan ta ce " ashe ba sakewa wallahi gidan uncle Bashir zan tafi gobe acan zanyi weekend sunday na dawo da daddare, Rahma ta ce " babu inda zanje nima ai na iya ɗaure fuskan" dariya suka sa har Mommy dan sun san halin Muhsin da wuya yayi fara'a.



Sai kusan tara na dare Muhsin ya dawo gida, da sallama ya shiga babu kowa a parlour'n hakan yasa ya nufi ɗakin Mommy, ta na zaune suna waya da Daddy, da sallama ya shiga.


"Ga shi nan ya shigo ma" Jin akansa suke wayar ya sa ya ce " Daddy na dawo" wayar ta miƙa masa ta na faɗin "gashi nan" Muhsin ya ce "Assalamu alaikum Daddy nafa zo gidan sai Monday da safe ma zan koma" 

Dariya Honorable yayi ya ce " ikon Allah wai kai meyasa baka son fita abroad ne, kaga dai yayanka har ya kammala nasa a U.K ya dawo shekara biyu ya gama, kai kuwa sai kayi four years indan ma ba'ayi streak ba haba son" Muhsin ya ce "ni dai banaso Daddy ina nan"

Mommy kallonsa kawai take, tanason Muhsin sai dai halinsa na naci da kafiya ne bataso.



Sosai ya sa Hon.Murtala Garba Gabasaww dariya sannan sukayi ban kwana, "Mommy na nayi kewarki sosai" Muhsin ya faɗa yana ɗora kansa kafadarta, ba ƙaramin so yake mata ba, shiyasa ko murya baya ɗagawa a gabanta yana matuƙar girmama ta sosai. Ƙansa ta shafa ta ce "kai ka so ai my son, bansan me kake ji a kwana a cikin wannan jejin ba, idan driving kullum ne ba zaka iya ba, a dinga kaika, amma kaƙi why my son, we need u in our side" Muhsin ya saki murmushi ya ce " nima inaso amma Mommy karatu cikin mutane ya fi daɗi, kinga har discuss muke a junan mu da daddare, a kwai lokaci, saboda na dinga ganinki na ƙi fita karatu waje fa mommy" 

Dungure masa kai tayi cikin farinciki ta ce " maƙaryaci rayuwar talakawa ce take baka sha'awa dai" 

Rahma da Ihsan ne suka shigo dan sun san indai suka bari safiya tayi aka haɗu a dinning yi zaiyi bai san da su ba, kuma ba zai amsa gaisuwarsu ba.



"welcome bro" Rahma ta faɗa ta na yaƙe hakama Ihsan, gaishe shi suka yi gami da tambayar ya karatu nan suma suka hau faɗin sunyi kewarsa, duk da yasan ƙarya suke, amma yaji daɗi, ya ce "ina bro?" Mommy ta ce " ya fita shi da su Musty" Muhsin ya ɓata rai ya ce " Allah ya kyauta ba daman faɗar wani abu yanzu Mommy ta hau shi da faɗa dan ta ce babu wanda ya takura shi, shima ya bar kowa yayi rayuwarsa.


Tun Muhsin na jiran ganin Yusuf har ya gaji ya shige ɗakinsa dan ya samu yayi bacci da wuri saboda tashi cikin dare yayi ibada da kuma karatun bokonsa.



 1:32am Yusuf ya dawo gida, ba wani buguwa yayi sosai ba, yana shiga ya zube wayoyinsa a kan bed ya nufi toilet ya yi wanka dan da ƴanmata biyu yayi sex a cikin club ɗin.

Sama-sama ya shirya ya kwanta yana kashe lamp ɗin dake room ɗin sai na jikin bed ɗin ya kunna mai duhu ya duba wayarsa dan ya kashe kira ya gani sama twenty missed call.........




BAFFA HOUSE


"Inna mun shirya" Walida da ke tsaye a tsakar gida da goyan Noor da alama fita zatayi, Khadija na riƙe da jaka ita ma tayi tsaf da ita. Inna ta fito ta na faɗin "Allah ya sa ba kuyi latti ba, ga shi ku hau adaidaita sahu Allah ya kiyaye" 

Isma'il shima ya fito sanye da uniform farare na makaranta, ya ce "Allah sarki Noor zai sha allura, bari mu tafi tare kekena yayi faci, idan na dawo zan kai shi gyara"

Inna ta ce " to kuyi sauri" 

Isma'il ya ce " Inna dan Allah ƙara min hamsin" 

Walida ce ta ce "muje na baka" a tare suka tafi suna hira, kamar babu abinda ke damunsu.




Malam Lawan ne zaune jikin bishiya gefen hanya, mutum ne munafuki mai sa idon masifa ganin su Walida da sassafe, tun kafin su gaishe shi ya ce " a'a Walida komawa zakiyi ne, ai kam dai yakamata ki koma ɗakinki daga zuwa wankan gida sai ki zauniyarki ai ba tsari" 

Babu wanda bai san aurenta ya mutu akan laifin da aka kama Hafiz ba ansan ta zama Bazawara sakin wawa a yanzu, amma dan gulma Malam Lawan ya zo ji da kunnensa.

Isma'il ya ce " aunty kar ki magana share shi kawai" banza sukayi masa su ka wuce. Walida ta ce " babu komai in ma da izgili yayi min yaje dan kansa" Adaidaita suka hau Isma'il ya sauka a makarantarsu su kuma suka wuce asibitin Murtala.




Haɗuwa tayi da maƙociyarta Sumayya daman lokaci ɗaya suke zuwa awo,tare suke komawa gida kafin Ahmad ya saketa, nan suka zauna tare Khadija na kusa da su suna hira aka zo aka karɓi card ɗinsu, nan aka fara yi wa yaran allura Immunization, ta fito daga asibitin kenan ta hango Amadu ya na sai da gwanjonsa, da sauri ya tawo ya na barin yaransa ganin ya nufo inda take ya sa ta kama hannun Khadija dan ko kallonsa bata son yi.

Ganin tafiya za tayi ya sa Amadu ce wa" ki tsaya inga ɗana, ba wai wajen ki nazo ba da kike wani sauri ɗana zan gani" 

Cak Walida ta tsaya tana mai kwance goyon Noor ta juyo, Amadu ya karɓi ɗansa ya na faɗin "meyasa me shi?" 


Walida ta karɓi jakar hannun Khadija ta ciro card ɗinsa ta ce " ga shi nan allura na kawo shi, sai ka kai shi gurin Baba Haule ta ci gaba da shayar da shi, kaga ya huta da shan nonon masu ci da addini" ta wulla masa card ɗin ta ja hannun Khadija suka tafi.



Cike da ɗumbin mamaki Amadu ya tsaya yana riƙe da Noor yana kallon Walida, sai kallonsa ake da jariri a hannu.

Sai yanzu Walida taji sanyi a ranta dan duk abinda Amadu yake mata Inna da Baffa take tsoro shiyasa ba ta mayar masa, amma yau ko ba komai zai san masu ci da addini suna da rana.

Kuka ne ya kufce mata, tana son ɗanta amma hakan da tayi shine zai sa Amadu ya kiyaye harshensa.




Khadija ta ce "aunty meyasa kika ba shi Noor, Baffa zai yi faɗa" take tsoro ya ziyarci zuciyar Walida sai yanzu ta tuna da hakan.

"Innalillahi wa'inna ilaihirrajiun.........


Zinariya ce