WANI RABON........

CHAPTER 19 (MY GREATEST FEAR)

by @deejasmah

WANI RABON.........🦋🦋🦋



Elegant Online Writers ( E.O.W)



Khadeejah Bint Ismail ( deejasmah)



In dedication to all single ladies out there........

 


Arewabooks @ deejasmah


WhatsApp @***

N.B WhatsApp only not call😁



CHAPTER 19 ( MY GREATEST FEAR)



Sadik Abubakar is a nice and caring guy he's not just a friend but, a brother from another mom He's been my number one source of inspiration. Duk wuya duk tsanani yana tare da ni bai kuma taba gazawa da kasancewa a tare dani ba. Ya rabb ka kula da wannan bawa naka a koina a kowani yanayi da zai tsinci kanshi a rayuwar shi.....this chapter is dedicated to this guy Allah ya cigaba da kare mana kai a kowani hali ya cika maka burikan ka mafi alkhairi ya kawar da idanuwan mak'iya a kanka.....Always remember that Deejah loves you 😍❤


Grill 🌹❤


When it feels scary to jump, that's exactly when you jump.Otherwise you end up staying in the same place your whole life.




__ A daburce ta fara magana tana kallonshi kafin tace " Uhmmm,Yaya we are just passing by,armmm dama munzo mu gaisa ne" shigowa yai da kyau yana kallonta " and when you do come to check on me sai kuma ku ka tsaya zubar min da mutunci,huh?!" Girgiza kai suka fara yayinda wacce ya kira da Zeezah d'in ta rik'e hannun d'ayar alamun neman taimako ai ko cike da karairaya ta fara matsawa kusa da shi




" No,babe it was your secretary that denied us entrance " cikin lank'wasa murya da karya harshe ta furta hakan sai dai kamar bai ji abunda tace d'in ba don wurga wa Zeezahr mugun kallo yayi hakan yasa tace " yes yaya,wallahi ita ce ta hanamu shiga " tana k'ifta ido cike da tsoro da rashin gaskiya gyad'a kai yayi kafin yace 




"So you can lie like this,well thats very good of you but this should be the last time da zaki sake kawo min tarkace office d'ina,don't let me repeat myself again ke kanki ma let this be the last time da zaki zo office d'ina kiyi wannan haukan if not I'll ban you from entering it again " cikin sauri tace " yaya ba wasu na kawo ba Raudah ce fa " 




Kallon kin raina ni yai mata kafin yace " Whosoever is it,now ku bata hak'uri ku wuce maza " cike da bak'in cikin wulak'ancin da yai musu suka tsaya gaba na murya can ciki suka ce " sorry " issokay na furta nima ba tare da na kallesu ba k'ofa ya nuna musu " now,find your way out !!" A zabure suka fice daga office d'in yayinda Raudahr ta juyo ta kalle shi da hawaye kafin ta buga k'ofar da k'arfi I can hear him murmuring something under his breath sai kuma yace min 



" Ke kuma da bansan ta inda zan ajiye ki ba ...how could you let them raining insults on you ba tare da kin d'auki mataki ba what's wrong with you?" Tab'e baki nayi kafin nace " what should i do then sir?, fight them or insult them back? well, ba haka aka koya min ba " Dafe goshi yayi don last statement d'ina yayi masa zafi kam amma ya daure yace " you should have called the securities su fitar miki da su " amsa na bashi da cewa " that's what I'm trying to do when you got in though I'm not sure if they might help tunda na lura masu gidan ne " 




"Ko su waye basu da damar cin mutuncinki a workplace d'inki you have more right here than them,never let that ever happened again" ya fad'a in coarsely " sorry sir it won't happen again " na furta cikin sanyin murya bai tanka ba shima ya nufi k'ofar girgiza kai nayi ina mamakin halayyar shi " sometimes cold another time cool another time arrogant yet another time sweet and caring ko ba komai he respect us as staffs duk da cewa bai son a shiga harkan shi kuma bai yarda da kuskure ba ko yaya ne yanzu kam na yarda cewa mutane da yawa basu san waye Arshad Bello ba hakan yasa suke kallon shi a bai-bai a cikin mutanen kuwa harda ni " 

 



Aikina na cigaba ba tare da na k'ara sa damuwar shi ko ta yaran d'azu a raina ba haka nan naji ban son fita in nemi abinci duk da cewa ban zo da komai ba waya ta na ciro da niyar kiran mufeey akan in ta fita ta siyo dani wayar tata bai shiga ba hakan yasa na tura mata message kawai bayan kamar 30 minutes sai ga tanan da lunch package har biyu a nan office d'Ina muka ci tare da ita muka tab'a fira kafin ta wuce 




Na idar da sallahr Asr ne ina lazumi wani kira ya sake shigowa waya ta tunda na fara sallahr ake kira na duk da bansan waye ba amma na jinjina kiran yayi yawa tunda har mai kiran ya ga ba'ai picking ba ai yasan baa kusa ne saida na kammala nai addua na shafa kafin na cire hijab d'in ninke su nayi da pray mat d'in na ajiye su a inda na saba ajiyewa sannan na nufi table d'in waya ta na d'auka na nufi sofa 



Miss calls d'in na fara dubawa 2 daga bestie 1 daga Sahal sai kuma na Mamie guda 5 da sauri na fara dialing numbern bestie ina cewa " da Alamu bestie ta sauka " sai dai ba ai picking ba hakan yasa na maida kiran kan Sahal shi kuma yai picking amma kuma bana jin mai yake cewa murmushi nayi ina cewa " lallai Sahal is super excited shiyasa ba'a jinshi " Mamie na kira ringing biyu ta d'aga 




"Mamie kin riga ni kenan ba dai har kinje hospital d'in ba?" Cike da d'auki da nishad'i na furta hakan " tun d'azu ai muke hospital d'in but yanzu jikin da sauk'i Alhamdulillah " Mamie tace cikin muryan damuwa " what's wrong Maa?" Na tambaya don muryar Mamie says that something is wrong " Munzo hospital ne da Noosrah jikin nata yak'i dad'i anyi admitting d'inta " 



Cike da tsoro nace " ba haihuwa ba ce?" A hankali Mamien tace " No Bpn ta ne ya haura sosai yanzu dai sun rik'eta till she deliver " a kid'ime nace " toh Maa gani nan zuwa " tashi nai a razane don jikina ya bani ba lafiya ba rufe office d'in nayi ba tare da na sanarwa Sir A.B ba don kwata-kwata na manta cewa lokacin tashi bai yi ba burina kawai in ganni gaban bestie 




Ina keke ina kuka gani nake kamar zanje a ce babu Noosrah kud'i na bawa mai keken ban ko amshi canji ba na nufi ciki a reception naga Mamie da 'yan gidan su sai kuma Sahal d'in da yake gefe yana amsa waya fuskar nan cike da damuwa rungume Mamie nayi ina sauke ajiyar zuciya 




Munyi zaune tsumu sai ga wata nurse tazo wurin Sahal wai zamu iya ganinta amma kar mutane suyi yawa nan hajiya Mama tace " toh mu da Sahal bari mu shiga tunda ba'a son hayaniya " babu ko karar ganin Mamie a gurin ba tayi ba tashi tayi ta shige d'akin da aka kwantar da Noosrah Sahal dai bai San dawar garin ba don ba a wurin yake zaune ba nurse d'in dai ta gaya mai cewa ta tashi 




Wurin mu ya k'araso yana cewa " Bestie ku tashi mu shiga ance ta tashi " Nana ce autar su Noosrah tace " ai wai ance kar ayi yawa ne a ciki shiyasa Mama ce kad'ai ta shiga " kallon wurin yayi kafin yace " Mamie da Bestie muje tohm " ya shige gaba muka bi shi a baya 




A kwance muka tarda ta duk ta fita a hayyacin ta da kuma kamanninta hawaye ne ya cika min ido Sahal ma hakan a tare muka gaishe ta da jiki a hankali ta amsa Sahal ne ya samu wuri ya zauna a bakin gadon bayan ya bawa Mamie plastic chair d'in da Mama ta ajiye domin shi zama tayi nikuma na jingina yayinda tausayin bestie bamu jima a ciki ba doctor yazo fita mukayi dubata yai da kyau kafin ya fito binshi a baya nayi don ban san matsalar ba 




"Uhmm zata samu sauk'i saboda mata da yawa suna fuskantar hakan during pregnancy but zamu rik'eta a nan saita haihu in sha Allah saboda gudun matsalar da zai iya tasowa wacce ba ma fata " likitan ya furta hakan bayan mun zauna a ofis d'in nashi kwantar min da hankali yai tayi ajiyar zuciya nayi tareda mai godiya na koma reception ganin an kira magrib ya sanya muka fara neman wurin sallah 




Muna zaune bayan isha'i ne saiga Arshad yazo duba matar abokin nashi gaishe da su Mamie yayi kafin ya shiga d'akin ya d'an dad'e kafin suka fito da Sahal yana kwantar mai da hankali a lokacin kuma su Fadeel sun zo da abinci gaishe su sukayi suma su ka shiga suka duba jikin nata sannan suka fito zama muka k'ara kad'an kafin muka musu sallama a lokacin ma bacci takeyi haka muka fita Fadeel ne yaja motar har gida 




Kullum da safe sai na duba ta nake wucewa haka ma in na dawo anan nake zama har sai Mamie tazo sai mu wuce tare yau tunda safe da naje jikin Noosrahn ta tsananta don taje toilet ne ta kusa fad'uwa Allah ne ya tsare hakan yasa ban ganta ba saboda ta na tare doctors har wurin 7:30 ba su fito ba hakan yasa na hak'ura na wuce ko da naje office tunani na bai wani jikina rabi da kwata yana tareda Bestie addua nake mata a raina tun ina iya aikin har na ture komai tunani 




Shigowar messages a wayata ne ya katse min tunani na bud'e na farko nayi k'irjina ya na bugawa da k'arfi bana son abunda Noosrah take min ko kad'an don kalamanta suna sawa inji Lamar tafiya zatayi ta barni don mafiya yawan kalmominta sunfi Kama da wasiyya tun jiya take turo min wainnan messages d'in ajiye wayar nayi ina lumshe ido na rasa zan b'ullowa lamarin I know and believe that mutuwa gaskiya ce but yanda take barin min wasiyyar auren mijinta is something I can't do iska na fesar daga bakina ina bud'e idanu tuno cewa muna da meeting by 10:30 ganin da sauran time yasa na janyo file d'in da ke d'auke da project d'in da executive department zasu gabatar a wurin meeting d'in hakan ne ya d'auke min hankali daga tunanin da nake 




 Kiran da ya shigo wayata ne ya katse min aikin da nake a gaggauce na d'aga " bestie ki yafe min,don bana tunanin zaki iso ki tarda ni da rai....." shi ne kalaman da suka daki dodon kunne na bestie ce take fad'in haka cikin galabaita da sauri nace " haba bestie stop saying this zaki rabu da cikin nan lafiya har ki rik'e babyn ki a hannu" cikin muryan tausasawa da kwantar da hankali nai maganar cikin muryar d'azu tace " Kayya bestie baki san halin da nake ciki bane a halin yanzu shiyasa ni dai kizo yanzu ina son in ganki inda hali,kizo please....." 




Daga haka wayar ta katse a firgice na fara dialing number saidai baa dauka kuka na sanya ina mai nufar k'ofa daga ni sai waya a hannu yayinda damuwa da tashin hankali suka bayyana tsantsa akan fuska ta kusan karo mukayi da A.B dake shigowa office d'in cak ya tsaya yana kallo na " lafiya kuwa Miss Sadauki?" Ya tambaya cike da kulawa " I have to see her sir,kar ta mutu ta barni !!" Na bashi amsa ina fashewa da kuka a rikice yace " wace ce?" 




Wayata na mik'a mai ina nuna message d'in da ta turo min kafin ya amsa wayar aka kirani sunan Sahal ke yawo a screen d'in picking nayi " hello Yaya sahal ....." katse ni yayi da cewa " please do come to the hospital now!" Da wata razananniyar voice kafin in yi magana aka zare wayar daga kunne na " cool down man,everything will be okay kaji" yace cikin lallashi banji mai aka ce ba na dai ji yace " da kaina zan kawo ta hospital d'in nothing will happen to your wife,be positive Buddy " katse wayar yayi yana turawa a aljihun shi tare da nuna min k'ofa da sauri na fita har lokacin ban daina kuka ba gani nake kamar kafin in kai asibitin zata rasu 



Arshad's POV




Tun daga ran da matar Sahal ta kwanta a asibiti take cikin damuwa wanda nima hakan ba k'aramin sani a matsananciyar damuwa yayi ba don walwalarta da kwanciyar hankalin ta shi ne nawa a lokacin ne kuma na fara buk'atar sanin relationship d'in dake tsakanin su saboda ko randa naje hospital d'in na tarda brothern ta da wasu mutane 




Damuwar da take ciki yasa aikin ma kawai yi take yi ban da zab'i sai na mata uzuri don nasan she's not her self kuma nasan it is just a matter of time da Noosrah ta sauka lafiya daga ita har Sahal d'in kowa zai dawo dai-dai 




Yau muna da board meeting by 10:30 sai dai wani uzurin gaggawa ya sa akai rescheduling zuwa next week PA na sanya ya tura wa kowa message d'in ta email don yau kam almost a week rabonda ta kunna data saboda damuwa dama kuma tun can ita ba gwanar social media ba ce ina aiki a office ne haka nan jikina ya bani cewa bata lafiya tattare curtains d'in da ya raba mu nayi ina kallon ta a zaune na ganta tayi tagumi tana duba wayarta 




Aje wayar tayi bayan ta kalli wall clock sai ta d'auko file tana dubawa ganin hakan yasa na koma na zauna amma ido na yana kanta da duk motsin ta kiranta akayi ta d'auki wayar a gaggauce sai kuma ta mik'e tana hawaye hakan yasa nai sensing cewa ba lafiya tasowa nayi na rufe k'ofar office d'ina na nufi na ta 




A dai-dai bakin k'ofa muka had'u ji nayi kamar in rungume ta in tambayi halin da take ciki in lallashe ta sai dai babu dama hakan yasa nace " what's wrong Miss Sadauki?" Cike da kulawa fashewa tayi da kuka cikin wani yanayi tace " I have to see her sir,kar ta mutu ta barni !!" Kamar saukan aradu naji zancen nata wace ce zata mutu ta bar ta kuma? da sauri nace 




"Wace ce?" Kasa magana tayi saboda kukan da ya ci k'arfin ta wayarta ta mik'o min zata nuna min wani abu a dai-dai nan kuma kira ya shigo wayar tata d'agawa tayi cikin d'imuwa " hello yaya Sahal...." ban ji mai aka ce daga d'ayan side d'in ba bakin ta naga ya fara rawa hakan yasa na zare wayar don ba zan bari su sake sa ta a damuwa ba " calm down man, everything will be okay " na fad'a cikin muryan lallashi don na lura ya fi Faheemahn Shiga d'imuwa 




Cewa yayi " Buddy ba zaka gane bane,Babe is in critical condition and we have only one option wato ai mata CS a cire babyn,in order to save both of them, but tak'i yarda ai hakan wai sai Faheemah ta zo!! Please let her come to the hospital now!" Wannan wani kalar soyayya ne haka na ayyana a raina a baki kuma na ce " da kaina zan kawo ta hospital d'in nothing will happen to your wife,be positive Buddy " 




"Please do so " ya furta cikin wani yanayi katse wayar nayi na tura a aljihu ina nuna mata hanya gesturing her to move da sauri ta wuce na bita a baya zuciya ta cike da mamakin wannan lamari shin dama Idan matar mutum zata haihu haka yake faruwa ko kuma ita ne nata yazo a hakan ? Ban san komai akan haihuwa ba because yayye na mata ne kuma dukan su sai bayan sun haihu ake sanar min it might be cewa suma suna fama kawai ni ne ban sani ba but I'll ask Ammah about it 




Har muka isa hospital d'in kuka takeyi na rasa kalmar da zan lallashe ta dashi ko parking banyi da kyau ba ta bud'e motar ta fita dafe kaina nayi ina bin ta da idanu vibration naji a chest d'ina da sauri na duba wayar sunan Sahal na gani kafin inyi picking kuma ya tsinke swiping up nayi and luckily wayar ta bud'e jinjina kai nayi ina mamakin rashin sa code a wayar 




Message d'in da ta nuna min d'azu nai arba dashi bugun zuciyata tsananta yayi scrolling up na fara nan na fara karantawa daga farko dafe chest nayi ina mai jin kamar kaina zai rabe biyu ban kai k'arshe ba nai jifa da wayar hawaye naji yana zubo min tuno cewa wai magana za tai da Noosrahn ya sa na fito a gaggauce daga motar na nufi cikin asibitin a k'ofar parlourn na samu 'yan gidan a zaune gaishe su nayi ina kallon su d'aya bayan d'aya babu ita a wurin hanyar d'akin na nufa 




"Bestt gaki ga babe he already agreed zai aure ki yardan ki kawai muke buk'ata please don't say no " shine muryan da ta daki kunne na mugun jiri ne ya kama ni dafe bango nayi ina addu'ar Allah ya sa kar ta amince da maganar shiru akayi sai kuma naji tace " I've told you this bestie ko baki da rai ni bazan iya auren mijinki ba so please ki daina wannan maganar yanzu mu addu'ar mu shi ne saukar ki lafiya nothing more......." 



Katse ta tayi da cewa " ina ji cewa bazan tashi ba uhmm I'm leaving my babe alone but I want to know wacce zan barwa amanar baby na da miji na ina tsoron musu azzaluma kuma heartless woman wacce zata azabtar min da abunda na bari shiyasa nake rok'on ki to be that person to marry him when I'm no more " shiru aka yi sai kuma na jiyo Faheemah saying 




" Stop saying this zaki sauka lafiya and you will be with your husband and baby again ai ciwo ba shine mutuwa ba mata da yawa sun yi ciwon da yafi haka and sun haihu lafiya so kema haka,kawai ki yarda ai miki cs please ki ajiye maganar wani aure ko wani amana " yanzu kuma Sahal ne yace " Faheemah please don't say no if you truly love her then grant her this request tun ba yau ba ta dad'e tana min magana akan ki da kuma cewa kwanciyar hankalinta shine ki samu wanda zaki k'arasa rayuwar ki " da alamun kuka a voice d'in shi ya cigaba da cewa 




"There's nothing wrong in that ni dai na amince and in kina son a wuce da ita theatre room yanzu just say yes please !!" Kasa cewa komai tayi sai can naji ance " promise me cewa ko da raina ko bayan raina you will marry each other and will be together only death will do you apart ....." Tura k'ofar nayi da k'arfi dukan su juyowa suka yi suna kallo na cikeda damuwa nace..........................




Ko me Arshad zai ce kuma?

Wai ma menene aka turo ma Faheemah ma ne a waya ?



Shin kuna ganin Sahal zai auri Faheemah kuwa ?

Anya ita d'in ba RABON Sahal ba ce ?

To in ba tashi bace to RABON waye ?



#Team_Sahal

#Team_Arshad

#Team_Mukhtar

Muga su waye suka fi yawa 




Please manage har yanzu jikin sai a hankali,it was even your prayers and comments ya sa nai typing wannan Fateey Musa thanks for the data Allah ya bar zumunci tun da dai naga alamun zaai wa Arshad k'usa toh in anyi serving d'inshi sai mu baki shi kiyi treating d'inshi kinga sai ki had'u da Raudah 'yar gayu 😂😅 ahh ya naga ana harara ta ne ? ko dai masoyan Arshad d'in tawa ne dasu har haka toh ai shikenan zamu fara saida form masu so suyi applying😅😌


 Thanks once again fateey Deejasmah loves you too😍❤



#vote

#comment

#share

#add

Love y'all😍


Deejasmah🦋🔐❤