KADDARATA CE Page 19/20
Gurin da ake register'n Jamb Jawahir ta je, ba mutane sosai yawanci ɗalibai ne masu son shiga jami'a duk sun zo domin cike form ɗin jamb ta web site, babu wanda ta kula dan tana gefe ita kaɗai a zaune, "Hajiya me za'ayi miki"ma'aikacin cafe ɗin ya tambayeta ganin ta ware ita kaɗai, " Jamb form nazo a cike min" Jawahir ta faɗa tana tasowa.
"okay 1k ne" ya faɗa ya na nuna mata inda zata zauna, file ɗinta ya karɓa ya na dubawa yana ciccike mata komai, sai da ya gama ya bata ya ce " za'a turo miki da date da center'n da zaki je kiyi" ta ce "to nagode kuɗinsa ta ba shi ta tafi.
"To ni zan fita" Baba ya faɗa yana gyara babbar rigarsa wacce ta ɗan kwana biyu, Umma ta ce" to a dawo lafiya Malam" ya fara tafiya kenan Umma ta ce "au na manta Malam gari ya ƙare hakama sabulun wanki" Baba ya ce " haba Aisha meyasa ba za ki canza ba, na sha sanar da ke idan abu ya kusa ƙarewa ki dinga sanar da ni amma sai ki ƙi, to ni yanzu ba ni da kuɗi, sai Allah ya kawo na siyo"
Umma ta ce " a yi haƙuri"
Jawahir ce ta shigo, sakin fuska iyayen nata sukayi Baba ya ce "har an gama abun?" Jawahir ta ce "eh Baba yanzu ance in saurari ranar da zamuje muyi jarabawar da gurin da zamuyi"
Umma ta ce " to waye zai faɗa miki, ku da kuka gama makarantar kuma?" murmushi ta yi tana cewa "ai ta waya za'a turo" canjin 1k ta ɗauko ta ce "ga canjin" ta na miƙawa Baba.
Baba ya ce "a'a auta ki riƙe ko zaki sayi wani abun kinji"Jawahir ta ce "babu abinda zan siya Baba" Umma ta ce " eh dake Mahaifinki ne kina mai da masa da kuɗinsa,ina jiya kika ce min audigarki(pads) ta ƙare, a siya miki wata?" Baba ya ce " zan tawo da ita wannan kuɗin ki sai duk abinda kike so ki ci kinji auta Allah yayi miki albarka" Jawahir ta ce "nagode Baba a dawo lafiya"
Umma ma ta ce "Allah ya ba da sa'a a dawo lafiya"
Jawahir ta ce "ungo kuɗin Umma ni babu abinda zan yi da su"
Kallonta kawai Umma tayi tana tuno baya kafin wannan abun ya faru da ita, son kuɗi ne da ita ga siyayya kamar me, ita ce siyan madara, aya, kantu, kwakwa, awara, waina, rake dasauran kayan kwaɗayi dai haka.Amma yanzu komai ya fita aranta.
Umma ta ce " a'a ki kashe abinki" ta faɗa a hankali cikin sanyin jiki, Jawahir ta ce " to nagode"ta wuce ɗakinta.
Tun jiya take kiran wayar Zainab amma a kashe,
Tanason sanar da ita zata koma karatu, yanzu ma riƙe take da wayar sai ƙara trying take, amma still dai wayan akashe "ko wayar ta lalace ne" ta faɗa ta na tagumi.
"Assalamu alaikum" wata mata ta shigo gidan tana ta sallama, Umma da ke cikin banɗaki ta yi gyaran murya, matar da ka ganta kaga masifaffiya ta zauna akan kujerar katakon da ke tsakar gidan, Jawahir da ta taso dan ganin waye, taga Hajiya ce, gabanta ne ya faɗi sanin a hannunta Baba ya siyawa Zainab katifa, "wa'alekissalam sannu da zuwa ina wuni"
Lafiya lau,ina Baban naku , tun shekaran jiya ya ce zai zo ya kawo sauran kuɗin amma shiru, ni nace ya aurar da ƴarsa da haƙƙin marayu, magada suna jiran kuɗinsu za'a raba musu gado iyee to ba zan amince ba" ta faɗa ta na watsa hannuwa.
Umma ta fito ta na faɗin maraba sannu da zuwa Hajiya.Haɗe rai matar tayi tana cin magani, ta ce "yauwa ki sanar da shi idan ba zai iya biya ba, ya dawo min da katifata" Umma ta ce " kiyi haƙuri Hajiya insha Allahu zai kawo"
Tashi tayi ta ce "ki sanar da shi na baku nan da kwana biyu" ta ta shi ta fice.
Jigum-jigum su Umma sukayi Jawahir ta ce " daman Baba bai kaiwa wannan matar kuɗinsu ba?" Umma ta ce" nima wallahi bansan bai kai mata gaba ɗaya ba, sai da na ce wa Malam ayi amfani da sadakinta ya ce a'a hakkinta ne, ba ita za'a kashewa ba yanzu me ne amfanin haka anzo ana ci mana mutunci akan dubu talatin"
Jawahir da idonta ya ciko da hawaye ta ce "Umma meyasa baku faɗawa Zainab ba, nasan babu abinda zatayi da sadakinta a yanzu ko inje in karɓo dubu talatin ɗin abar mata ashiri?" da sauri Umma ta ce "a'a ki bari ya dawo sai muji abinda zai ce"
Shiru sukayi suna fatan Allah ya rufa musu asiri.
* * *
"Jawahir dai ƙanwar matata ce, ta gama secondary ɗinta wannan shekarar, Alhamdulillah kaima shaida ne suna da tarbiyya sai dai akwai ƙaddarar da ta faɗa mata" cikin zaƙuwa Kamal ya ce " meyafaru da ita Abdul?" kallon Zainab Abdallah yayi, ta kafe shi da ido tana jiran taji me zai faɗa akan ƙanwarta.
Ya ce " abun dai ba daɗi Kamal ƙaddara ce...Zainab ta karɓe wayar ta na faɗin " ashe haka kake Abdallah ba za ka iya rufawa ƴar'uwata asiri ba to ka faɗa masa fyaɗe akayi mata sai me, na ce sai me" ta fashe da matsanancin kuka wanda basu san ranar da zasu daina zubar da hawaye akan hakan ba.
Hankalin Abdallah ne ya tashi ganin Zainab ta na kuka, ya ce "wallahi ba da wani abu na faɗa ba, ce wa yayi yana sonta shine zan sanar da shi gaskiyar abinda ya faru da ita dan kar yaji daga baya ya ce na munafurce shi" ringing wayarsa take tayi Kamal yana ta kira, ba'a ɗauka.
Sosai Abdallah ya yi mata bayani har ta fahimta. ta ce " ni nasan ba za ma ta so shi ba, dan Jawahir ta tsani kowanne namiji a cikin rayuwarta kar ka bari sanadinka mu sami matsala da ita, idan zai iya jira zuwa lokacin da zata ware to, idan kuma bazai iya ba dan Allah yayi haƙuri ya je ya nemi wata" Abdallah ya ce " mekike nufi da hakan, zama za tayi tayi ba aure har sai sanda zata dangana to ba zai yuyuba, zan je na sami Baba na sanar masa duk halin da ake ciki ku daman ba hankali kuka cika ba" ya ɗauki wayarsa
Text yayi wa Kamal na zai kira shi zuwa anjima wani uzuri ne ya taso masa.
Kamal da ke cikin office ɗinsa ya na ta sintiri gami da tunanin meyafaru da ita, ganin text message ɗin Abdallah ya sa ya karanta da sauri, zama yayi yana tunanin Allah ya kawo sauƙi.
GIDAN YARI
Kamar kowanne daren Juma'a rana ce da Hafiz yake yiwa waɗanda suke tare tarihin Annabawa da yanda suka sha gwagwarmayar rayuwa.
Imani ne ya ƙara shiga zukatansu Kure ya ce " ya kamata mu wuce dan akwai labarin da kayi alƙawarin ba mu Ustazu kuma muma mun san mahimmancin cika alƙawari ba re ku ulama'u magada Annabawa" murmushi Hafiz yayi ya na mai ce wa "yanzu kuwa zan sanar da ku malam Sani(kure).
Ni dai sunana Hafizu Aminu Isma'il, Mahaifina haifaffen Bauchi ne ƙaramar hukumar katagum, kasuwanci ya kawo shi Kano inda ya auri Bilkisu (Inna) anan garin na Kano.
Mu biyar ne iyayenmu suka haifa ni ne Babba sai Walida sai Zakiyya sai Isma'il sai kuma autarmu Khadija.
Muntaso cikin neman ilimin addini dana boko nayi karatunN.C.E a Sa'adatu rimi inda na karanci Business administration na sauke alƙur'ani nayi haddarsa tare da hadisai da kuma littattafan addini da dama.
ASALIN LABARI
Abu-Hanifa Islamiyya.
Kowanne aji babu abinda ke tashi sai karatun alƙur'ani daman ƙa'idar makarantar ce idan anshiga da azahar to hadda ake karɓa sannan ayi ƙari, Hafiz ya na ɗaya daga cikin Malaman makarantar kuma mataimakin heard-master dan rabin kula da makarantar a hannun Hafiz yake.
Shi kaɗai ne a cikin office ɗin da ya zama na malamai, dogo ne baƙi ya na da wushirya a tsakanin haƙoransa wanda suke a jere farare tas, matsakaicin dogon hanci ne da shi wanda ya da ce da tsarin halittarsa.
Ƴanmata da dama suna son sa, sai dai ba fuska bare su sami damar sanar da shi abinda ke zuciyarsu.
Wasu ƴan mata ne suka shigo a makare kowacce a tsora ce take.
Malam Hamza ne ke da duty, agogon hannusa ya duba uku harda minti bakwai, ba'a dukan waɗan da sukayi sauka.
Bandaƙi aka ce su wanke, Jawahir da ta duba uniform ɗinta sky blue wanda suke a goge ta hau ba da haƙuri,dan Malam Hamza akwai sakin fuska, washe baki yayi ya ce " to meyasa kuka makara?" Zainab ta ce " Umman mu ce ba tada lafiya shine ni na rakata asibiti, Jawahir ce tayi aikin gidan shiyasa du muka makara Malam"
Malam Hamza ya ce "ayyah Allah ya sauwaƙe ku wuce".
Hafiz da ya ke jinsu kallon fuskar Zainab kawai yayi yasan ƙarya take, daga office ɗin ya fito fuska a ɗaure kamar kullum ya ce " ku wuce ku wanke banɗaki kafin a fito alwala" hypho da klin ya miƙa musu ya wuce, Malam Hamza shi ma ya wuce dan yanzu zai shiga nasa ajin .
Jawahir ta gallawa Hafiz harara ta na nufar inda banɗakunan suke, toshe hanci tayi ta na leƙa wanda babu ƙazanta sosai ko za ta iya wankewa.
Gaba ɗaya yara sun ɓata banɗakunan, fitowa tayi ta zauna a bakin famfo tana faɗin wallahi bazan wanke ba.
Zainab da tasan halin ƙanwarta,ta kalleta kawai, ta cire hijab ɗinta tare da safarta ta bawa Jawahir ta naɗe wandonta ta shiga gyara banɗakin ita kaɗai, sai da ta gama ta wanke hannunta ta sake alwala sannan ta ce "ta so mu tafi" Jawahir ta miƙe tsaf da ita tana ƙara karkaɗe hijab ɗinta suka wuce ajinsu.
Kafin su je ajinsu angama tilawa ana jin hadda, ba su jima da zama ba aka fito sallah.
Hafiz ke limanci yana zuwa aka tashi Jawahir ta ce "ji be shi, shi ba ɗan kowa ba sai faɗin rai, dan yana da ilimi both side yake wani iyayi sai ka ce mace" Azima wacce take kusa da ita ta ce" ke dai ki iya bakinki dan yana da tarin masoya har faɗa ake akansa" dariya abin ya bawa Jawahir ta ce "amma anyi wahalallu meye abinso anan Allah ya kyauta".
kwata-kwata babu jituwa tsakaninsu,tana masa kallon mai iyayi da jin kai, ya na mata kallon mara kunya.
haka suke zuwa makaranta har aka kawo kuɗin auren Zainab.
*****************
Da daddare,Ahmad ya zo zance wajen Walida lokacin bikinsu ya kusa, baifi saura sati biyu ba, Hafiz ya dawo daga sallar Isha ya gansu gaisawa sukayi cikin girmama juna ya wuce ciki.
Baffa na zaune tare da Isma'il da Khadija suna hira dan akwai shaƙuwa sosai tsakaninsu musamman Khadija da tafi son Baffa dan duk abinda akayi a gidan sai ta ba shi labari.
Da sallama ya shiga Baffa ya ce " har ka shigo " Hafiz ya ce " eh kai na naji yana ciwo shiyasa zan kwanta da wuri dan ya ware.
Inna da ke zaune tare da Zakiyya ta ce" ai dole kanka ya dinga ciwo, anyi mutum baya hutawa kullum cikin hidima, ga kwana ba bacci ai ko bacci dole ya tambayeka"
Murmushi yayi ya na zama, Zakiyya ta kawo masa tuwo da miyar ɗanyen kuɓewa wacce ta wadatu da wake da kalwa mai kyau.
Kaɗan ya ci, Baffa ya ce " ka kai kuɗin kayan kuwa?"Hafiz ya ce " eh Baffa har an kammala ma, lokaci kawai muke jira sai a ɗiba akai gidan, abinda ya sa na barsu a can nan ɗin babu inda za'a ajiye su ne" Inna ta ce "gaskiya ne ,Allah yayi maka albarka ya ƙara buɗi"
Amin suka amsa gaba ɗaya.
Walida ce ta dawo daga zance,abinda Hafiz yake jira kenan yaga ta shigo.
ta shi yayi ya na musu sai da safe ya shige ɗakinsa.
Lokacin bikin Walida Hafiz yayi ƙoƙari sosai anyi biki lafiya, kowa yana ta san barka ana ta taya Walida murna.
Soyayya kamar za su cinye junansu, sai da Ahmad yayi sati kafin ya koma kasuwa, Walida tayi tayi da Hafiz ya zo gidanta yaƙi sai ya ce " me zai je yayi, wani lokacin ya zo"
Zakiyya da Khadija kuwa idan sukayi kwana biyu ba su je ba, Ahmad da kansa zai zo, su je su wuni a gidan sun mai da Ahmad yayansu babu abinda ba ya musu duk wani kyautatawa suma suna yi masa hakama iyayensu.
Musaddik shine wanda ake sa ran zai auri Jawahir, ɗan unguwar Kurna ne, ba laifi Jawahir tana sonsa, amma ba wai sosai ba, hakan ne ma yasa idan tayi saurayi ta na iya tsayawa da shi suyi hira.
Yawancin waɗanda suke zuwa wajenta ƴan unguwar ba wai da niyyar aure suke zuwa mata ba, kyanta ne ya ke jansu hakan ya sa bata kula ƴan unguwartasu ta Zage.
Wannan dalilin ya sa ake ganinta mai girman kai.......
``` Domin samun ci gaban labarin ki biya #300 kacal```