Chapter 10
*ZANEN ZABUWA*
©️ *Nana Haleema*
*Page 10*
Tunda suka shiga mota yake wuci Salim bai kula shi ba tuk'in sa kawai yake har suka je gidan, paking d'in motar yayi a compoud d'in gidan ya bud'e k'ofar ya fita ya zaga ya bud'ewa Muhsin yace, "Muhsin sakko mu shiga cikin dan Allah." Bai musu ba ya ziro k'afar sa a fusace ya fito yayi cikin gida kamar zai tashi sama.
A haka ya shiga falon gidan a dai-dai lokacin da Daddy yake tsaye suna magana da Mummy hannun sa rik'e da jaka da alama tafiya zaiyi suka ga shigowar Muhsin a haka ga Salim a bayan sa, "Kai Muhsin zo nan." Daddy ya fad'a yana kallon sa hakan ya saka shi tsayawa cak ba tare da ya dawo ba Daddy ya kuma cewa, "Lafiya kake kuwa?." Shiru yayi baice komai ba hakan ya saka Salim yace, "Daddy wani ne ya b'ata masa rai a school shiyasa ka ganshi a haka." Mummy tace, "ya b'ata masa rai? Waye shi da zai b'ata masa rai?."
Salim yace, "wasu ne har marin Muhsin naga yayi."
"What!. Ya mari Muhsin? D'an gidan uban waye shi?." Daddy ya fad'a a fusace yana kallon Salim. "Wallahi Daddy ban san shi ba but sun jima suna samun sab'ani da k'anwar mutumin shine yau ya mare shi."
"Jini na wani banza talaka zai d'aga hannu ya mara? Impossible, Salim yanzu basai anjima ba maza aje a nemo min inda yake da kuma waye uban sa a garin Kano, yau ba sai gobe ba ina so a banbance masa tsakanin aya da tsakuwa dan wallahi sai ya san bakin rijiya ba wajan wasan makaho bane." Daddy ya fad'a a fusace cikin d'aga murya yana kallon Salim.
"Noo Dad ka bar komai a hannu na nine nake so nayi maganin sa da kaina, but Salim kayi abinda Daddy yace yau ba gobe ba ka saka a nemo min waye shi da kuma inda yake zaune." Muhsin na gama fad'ar hakan ya shiga ciki da sauri ba tare da ya sake juyowa ba.
Mummy tace, "Ya cancani ayi masa ko wanne hukunci dan gaskiya bashi da hankali." Mummy ma ta fad'a rai a b'ace tana kallon Salim da yake niyar barin wajan. Gyad'a kai Salim yayi ya fice daga falon ba tare da yace komai ba. Haka Daddy ya tafi ransa a b'ace dan sosai yake jin zafin labarin da aka bashi badan tafiyar tasa nada mahimmaci sosai ba da babu inda zashi haka Mummy ma.
*☆☆☆☆*
Shiru Mufeedah tayi tana kallon wacce take zaune a kusa da ita kafin ta sauke numfashi tace, "Kina ganin hakan shine dai-dai? Kwata-kwata fa ba'a fi sati da fara son sa ba amma kina ganin na furta masa yanzu?." Wacce take zaune kusa da ita tace, "ai tsayawa kallon ruwa shine yake sawa kwad'o yayi maka k'afa, kar ki manta friend a tsaya ya wuce shine yake kawo rabon wani gwara kiyi gaggawar fad'a masa yasan da k'aunar sa a ranki kafin lokaci ya k'ure miki."
Ajiyar zuciya ta sake yi tana kallon Zuhra da itama ita take kallo tace, "Ni tsoro nake ji na fad'a miki da yadda had'uwar mu ta fara bana son ya wulaqanta ni in na furta ina son sa kin san mazan yanzu da mace ta fara cewa tana son su sai suce bata da aji." Zuhra tace, "ba wani rashin aji wallahi, ke fa kad'ai kika san me kike ji a ranki kuma furtawar shine kawai mafita a a gare ki, in kika duba matsayin ki da matsayin sa koda yana sonki zai b'oye ne a ransa da gani zayi kamar kinfi k'arfin sane, amma in kece kika furta hakan komai zai zo da sauk'i. Ba ina baki gurguwar shawara bane k'awa ta ina fad'a miki gaskiya ne akan abinda kike so kar lokaci ya kure miki muzo muna cizon yatsa."
Gyada kai Mufeey tayi tace, "Haka ne friend, yaushe kike ganin zan furta masa abinda yake raina?."
"Ko yanzu ma zaki iya ai ba wani abun bane mai wahala."
"Kai anya zan iya kuwa Zuhra?."
"Zaki iya mana kar ki bada ni mana, kece fa Zainab d'in Mummy da take da confidence a kan komai."
"Toh shikenan zan gwada."
Tv dake mak'ale a bango ta kalla ta hango shi a zaune yana sarrafa computer kamar kullum ya duk'a baka gano yanayin fuskar sa, kallon tv Zuhra tayi tare da yin murmushi tace, "na jima ina addu'ar Allah ya nuna min wanda zai sace zuciyar ki duba da kowa yazo yana son ki kice bai biki ba, sai gashi Allah ya nuna min shi." Itama murmushi tayi bata ce komai ba suka cigaba da hira sama-sama amma hankalin ta na kan sa.
Bayan sallar azahar tana zaune bayan tafiyar Zuhra taga ya mik'e ya d'auki wayar sa da key da alama fita zaiyi hakan ya saka ta saurin kiran wayar sa tace yazo tana neman sa, tana ganin sa bayan ya kashe wayar sai da ya duba agogo kana ya nufo inda take.
Ai da sauri ta mik'e ta gyara fuskar ta ta sake fesa turare ta koma ta zauna tana murmushi ita kad'ai.
Da sallama ya shigo ya k'araso inda take yace, "Madam gani." Ganin yanayin sa fuskar sa d'aure babu alamun fara'a gaban ta ya fad'i amma sai ta daure tace, "ka zauna mana." Ba musu ya zauna kafin yace, "ina sauri ne zanje na dawo."
"Ya mai jiki?."
"Mai jiki da sauk'i, yanzu haka tana school ma."
"Ma sha Allah, Allah ya k'ara lafiya."
"Amin, mun gode da alkhairin ki."
"Babu komai ai an zama d'aya."
Shiru wajan yayi babu wanda ya sake cewa komai kafin tace, "amm Imran zan iya tambayar ka wani abu?." Kallon ta yayi yace, "babu komai ina jin ki." Sai da ta d'an yi shiru kafin tace, "Dan Allah kana da aure kuwa?."
Kallon ta yayi kad'an yana mamakin dalilin tambayar ta amma sai ya shanye mamakin sa jin tace Allah ya saka yace, "A'a bani dashi, wani abun ne?."
Girgiza kai tayi bayan tayi ajiyar zuciya sannan tace, "Babu komai kawai na tambaye ka ne." Baice komai ba sai sake kallon agogo da yayi dan ganin k'arfe biyu ta gota lokacin fitowar Jannat daga lecture har ya wuce, "Dan Allah ko zaki fad'i dalilin kiran da kika min lokaci na tafiya na fad'a miki ina sauri ne."
"Babu komai zaka iya tafiya amma dan Allah ka bani dama anjima da daddare ina so mu had'u sai mu tattauna tunda yanzu sauri kake." D'an jim yayi yana mamaki da kuma tunanin maganar da zasuyi, ganin yayi shiru ya saka tace, "Dan Allah badan ni ba."
"Babu komai Allah ya kaimu."
"Amin. nagode da amincewar ka, anjima zan maka text d'in wajan da zamu had'u da kuma lokacin da zamu had'u d'in."
"Ba damuwa." Ya fad'a yana mik'ewa bai sake cewa komai ba ya fice ta bishi da kallo tana jin ina ma kar ya tafi ta dawwama tana jin muryar sa.
Koda yaje makarantar ya duba ta bai ganta ba yasan ta tafi gida kenan ransa ya sake b'aci ya shiga motar maimakon ya koma company kawai sai ya nufi gida domin ran sa b'ace yake ainun.
Yana tsayawa da motar ya shiga gidan Gwaggo yana neman Jannat take shaida masa tana gidan Umma bai ce komai ba ya juya ya nufi gidan nasu ya ganta a zaune a falon Umma suna hira kasancewar tsakar gidan akwai rana.
Kamar an cillo shi haka suka ganshi kawai a kansu kafin wani yayi magana yace, "Jannat meyasa kwana biyu bakya jin magana tane ne? ban hana ki hawa napep ba,? D'azu kin hau kinje school yanzu ma kin hau kin dawo me kika d'auke ni? Kin mayar dani abokin wasan ki right? Sau million nawa zance miki bana son hawa napep bana so amma sai da kika yi dan kawai ki b'ata min rai ko?."
Cikin fad'a yake magana hakan ya saka jikin ta rawa sosai tace, "nazo da safe baka nan kuma yanzun tun k'arfe d'aya muka gama lecture nake jiran ka ban dawo ba sai yanzu da naga baka zo ba." Ta fad'a cikin sanyi domin yanayin sa ya bata tsoro sosai.
"Zaki min shiru ko sai na mare ki,? baki da number ta da baza ki kira ni ki fad'a min kun gama lecture ba? In baki fad'a min ba ta yaya zan san kin gama lecture d'in?."
Idon ta ya ciko da kwallah ta kalli Umma da take kallon ikon Allah kafin ta k'ara dawo kallon ta ga Imran d'in tace, "na kira ka bata shiga ba shiyasa na tawo kar na dad'e kayi min fad'a." Ta fad'a hawayen na sakkowa a idon ta bayan ta sunkuyar da kanta k'asa.
Zaiyi magana Umma ta riga shi tace, "to tunda ta fad'a maka uzurin ta ba sai kayi hak'uri ba wannan fad'a da kake mata haka kasan fa ba lafiya ce da ita ba."
Had'd'iye abinda yayi niyar fad'a yayi kawai ya juya ya fita bai sake cewa komai ba. Kuka ta fashe dashi sosai tace, "Umma fushi yake dani tun jiya ko magana baya yi min." Umma da tayi murmushi kad'an tace, "to me kika yi masa yake fushi dake haka? Ban tab'a gani yana yi miki fad'a haka ba." Idon ta ta goge tace, "Tambaya ta yayi na fad'a masa gaskiya shine bai yadda ba tun jiya yake fushi dani har yanzu."
"To ki daina kuka kinga ba lafiya ce dake ba ki bari in anjima in ya wuce kije ki same shi ki bashi hak'uri nasan zai hak'ura." D'aga kai tayi alamun to ta cigaba da goge fuskar ta. Haka ta wuni ranar a gidan Umma jikin ta sanyaye gashi ta zauna dan ta ganshi amma ko k'urar sa bata sake ji ba har magariba bata koma ba tana gidan Umma hatta assignment d'in ta a gidan tayi.
Bayan sallar magariba ya shigo gidan da sallama ya nemi waje ya zauna tare da fad'in, "Umma kunyi waya da Kawu kuwa?." Umma tace, "eh munyi ya shaida min bikin y'ar wajan sa Wasila ya tawo."
"Yauwa daman sak'on da yace na fad'a miki kenan tunda kunyi wayar ma shikenan, abinci fa Umma?."
"Yana madafa, Khadija shiga ciki ki d'auko masa."
Sai a lokacin ya kalle inda take ta rakub'e a cikin bango kamar marainiya ya d'auke kansa ita kuma ta mik'e ta shiga ciki. Bata jima ba ta dawo ta ajjiye masa abincin ya bud'e ya fara ci ba tare da ya kalle ta ba.
Umma duk tana kula share ta d'in da yake yi sai tayi murmushi kawai dan tasan tabbas zasu shirya a daren dan ba'a shiga fad'an su.
Text ne ya shigo wayar sa ya d'auko ya duba yaga Mufeedah ce duk da bai yi saving number ta ba amma ganin text d'in yasan itace, yatsine fuska yayi dan shi ya manta ma sunyi zasu had'u gashi lokacin da sukayi ma yayi.
Har ya kammala cin abincin tana so tayi masa magana amma ta kasa sabida yadda ya tsare gida sai kallon Umma take yi wai ko zata yi masa magana amma taga hankalin ta bama ya kansu. Bai cinye abincin ba ya ture dan ya k'oshi ya d'auko k'aramar wayar sa yana dannawa, ba wani abun kirki yake yi ba kawai baya son kula tane shiyasa yake neman hanyar share ta dan in ya zauna baya komai sai dai kawai yaji yayi mata magana na tare da ya shirya hakan ba.
Umma ta kalla tayi mata alamun tayi masa magana sai tayi y'ar dariya tace, "Baba na wai me ya had'o ka da k'anwar taka ne haka?." D'agowa yayi ya kalli Umma yace, "Wani abun kika gani?."
"Gashi ma ina ta gani ka share ta ko magana baka yi mata ba."
"Babu komai Umma." Ya fad'a yana mik'ewa ya sake cewa, "bara naje na dawo." Yana fad'a ya fita Jannat ta kasa jurewa yana fita itama tabi bayan sa da sauri ta hango shi a kusa da motar sa yana niyar bud'ewa ya shiga.
"Dan Allah kayi hak'uri Yaya na ka daina fushi dani." Ta fad'a tana niyar fitowa gashi ko mayafi babu a jikin ta.
Kallon inda take yayi duk da wajan da duhu kasancewar babu wuta amma ana ganin ta yace, "Baki da hankali zaki fito babu mayafi?." Sai ta fashe da kuka tare da d'urkusawa a wajan tana shashsheqa.
Ya dafe kai ya cize baki yace, "Tashi kije ki d'auko mayafin ki kizo ki raka ni." Ba musu ta mik'e da sauri ta koma gidan Umma bata jima ba ta dawo ta samu har ya shiga motar itama ta shiga ta kulle k'ofar tana cigaba da goge idon ta.
Kallon ta yayi bayan ta zauna yaga yadda take ta mitsiltsila ido sai abin ya bashi dariya yayi murmushi kad'an ya kawar da kai yana murmushi, Jannat jinin jikin sa ce ya sani ko kusa bazai tab'a iya fushi da ita na dogon lokaci ba sai dai kawai ya daure dan ya hukunta ta amma ba'a son ransa ba.
"Kayi hak'uri ka daina fushi dani bazan sake yin abinda baka so ba." Ta fad'a kanta a k'asa a hankali tana sake goge idon ta. Numfashi ya fesar ya mayar da hankalin sa kanta kana yace, "firstly ki fara goge idon ki ki tabbatar babu hawaye sai muyi magana."
Kamar jira take ta saka hannu ta share idon ta ta kalle shi shima a lokacin ita yake kallo yayi murmushi kad'an yana kallon ta da manyan idanun sa da suke a bud'e tarr dasu.
Wani irin shauk'i taji tun daga kan ta har farcen k'afar ta ya tsirga mata tsigar jikin ta ta tashi ta kasa daina kallon sa tana murmushin itama, ganin kallon nata kamar yayi yawa ya saka shi bud'e idanun sa tare da d'age gira d'aya yace, "kallon fa?." Murmushi ta kuma yi tace, "Rabon da kayi min murmushi har na manta shiyasa nake farin cikin ganin sa a fuskar ta ka."
Bai san lokacin da murmushi ya sake kubce masa ba har haqoran sa suka bayyana hakan yaja ta ga sauke ajiyar zuciya wacce ta zo mata da fad'uwar da kuma bugawar zuciya mai k'arfin gaske. "Raina ne kawai a b'ace shiyasa."
"To na baka hak'uri ai in sha Allah kuma bazan sake ba." Baice komai ba sai kallon ta da yake yi ta fahimci mai yake nufi hakan ya saka tace, "Kuma abinda na fad'a maka shine gaskiya kaine kake ganin kamar nayi maka k'arya a kan hakan amma kayi hak'uri dan Allah."
Tab'e bakin sa yayi dan ba yadda ba kawai ya k'yale tane kuma zai bincika da kansa yace, "is okay ai ya wuce, last warning zan miki a yanzu dan ko nan gaba kika sake Allah bazan d'aga miki k'afa ba, babu ke babu keke napep na farko kenan, na biyu kar na sake ganin kin fito koda soron gida ne babu mayafi in kika sake na kama ki wallahi tallahi ranki zaiyi mugun b'aci kuma nayi fushi dake bazan wuce ba."
"In sha Allah bazan sake ba Yaya na."
"Good girl." Ya fad'a yana lakuce mata hanci da murmushi mai kyau a fuskar sa har kana ganin kyakykyawar wushiyar sa.
Farin ciki take ji yana zaga ko wanne sassa na jikin ta har ta kasa b'oyewa ji take kamar tayi ihu sabida farin ciki. Tamke fuska ya sake yi kana yace, "yauwa meye sunan d'an school d'in nan naku?."
"Muhsin naji ana ce masa."
"Jannat!". D'agowa tayi ta kalle shi jin yadda ya kira sunan ta a tausashe tace, "Na'am."
"Bawai shawara nake baki ba ba umarni nake baki akan wannan d'an makarantar naku, babu ke babu shi Jannat kar ki shiga harkar sa koda ya shiga taki ki daure ki share, kinga ke mace ce yanzu sai sunan ki ya b'ace a school d'in ace kina fad'a da maza kuma wannan tambarin sai yayi affecting d'in ki har auren ki, dan haka umarni nake baki babu ke babu shi kar ki sake wani abun ya sake had'a ku har ya kaiku ga cacar baki balle ya dake ki ko ya rik'e miki hannu, bana so Jannat ina jin zafin hakan ki daina dan Allah."
Gyada kai tayi tace, "in sha Allah Yaya na bazan sake koda kallon inda yake ba, daman shine yake zuwa har inda nake d'azun ma ina zaune naji ya mare ni ba tare da nayi masa komai ba, amma in sha Allah ko me zai min bazan sake kallon inda yake ba tunda baka so."
D'an murmushi yayi cikin jin dad'in kalaman ta yace, "kiyi min alqawari akan baza ki sake sauraron sa ba, kome zai ce miki baza ki kalle shi ba balle ki bashi amsa" Ya fad'a yana mik'o mata hannun sa kamar yadda y'an india suke yi. Ba tare da tunanin komai ba ta d'ora nata a kai tace, "nayi maka wannan alqwarin yaya na babu abinda zai sake had'a dashi koda ba fad'a ba ni Khadijah bazan saurare shi ba, nayi maka wannan alqawarin kuma bana fatan na sab'a shi har abadah."
Rik'e hannun nata yayi a cikin nasa kamar sun gaisa kana yayi murmushi mai kyau kafin ya zura hannu a aljihu ya d'auko wata azurfa mai kyau siririya mara girma sosai kalar mata ya zura mata da tsaya kusa da k'arami yace, "to ga zoben alqawarin nan duk ranar da kika cire kin karya alqawarin." Kallon azurfar tayi tana murmushi domin ba karamin kyau tayi mata a hannu ba tace, "bazan ma cire ba balle ya kai ga na karya alqawarin in sha Allah."
Kallon sa tayi kafin tace, "Yaya na d'azu nayi mamaki da naga kana fad'a harda marin sa naga kayi." Juya idon sa yayi a cikin idon ta ya sake rik'e hannun ta yace, "Jannaty kenan, baki san ya nake ji bane in na ganki kina kuka shiyasa kike cewa haka, ke jinin jiki nace Jannat."
Kyakykyawan murmushi tayi tana jin dad'i a zuciyar ta dan da dama babu abinda zai hana bata taka rawa ba.
Sakin hannun nata yayi jin wayar sa na k'ara alamun ana kiran sa kafin ya kai ga d'aukowa ta katse Jannat ta kalli wayar bayan ya d'auko tace, "Yaya na ya kamata ka canja wayar nan."
Y'ar dariya yayi kad'an yace, "ke ana ta kai wa yake ta kaya? Ni waya bata dame ni ba tunda ke kina da ita ai shikenan." Zata kuma maganar wayar ta sake shigowa ya kalli number koda bai saving ba yasan Mufeedah hakan ya saka ya d'auki wayar tare da fad'in, "Assalamu alaikum." Shiru yayi alamun yana sauraron abinda ake cewa kafin yace, "na manta ne amma yanzu in kina nan sai na tawo." Shiru ya sake yi kana yace, "okay gani nan in sha Allah." Ya fad'a yana kashe wayar ba tare da ya kalli Jannat ba yace, "Jannty jeki gida zanje wani waje na dawo." Jannat da tunda ta jiyo muryar mace taji kuma yace gashi nan gaban ta ya fad'i hankalin ta yayi k'ok'oluwar tashi kishi na taso mata tace, "ina zaka je?."
Yadda yaji maganar ta na rawa ya saka ya kalle ta yace, "alqawari na dauka zanje na sauke shi."
"Ina ne wajan?."
"Wajan wani cin abinci ne a can nasarawa."
"Yaya zan raka ka."
Kallon ta yayi sosai kafin yace, "A'a dare yayi ki shiga gida ma had'u gobe in Allah ya nuna mana." Ta sake cewa, "kodai zance zaka je?." Sai ta bashi dariya yayi dariya kad'an yace, "ni babu zancen da zanje."
"To indai hakan ne muje tare dan Allah." Ta fad'a tana fara dire masa k'afa tare da k'okarin fara yi masa kuka.
Hankalin sa ya tashi ganin ta fara kuka da gaske hakan ya saka yace, "shikenan jeki gida ki tambayi Abba in ya barki muje sai ki wanke fuskar ki kizo muje." Kallon sa ta sake yi tace, "baza ka tafi ka barni ba?." D'aga mata kai yayi alamun eh ta balle murfin motar ta fita ya bita da kallo har ta shiga gidan su.
Murmushi yayi bayan ta shiga ya lumshe ido yana kallon lokacin da take masa murmushi har yana kallon fararen haqoran ta, murmushi ya cire hular kansa ya shafa kansa yana jin wani irin farin ciki a duk lokacin da suke tare da ita yana jin kamar kar su rabu haka ji a jikin sa, buga glass d'in da yaji ana yi ya dawo dashi daga tunanin da yake ya kalli wajan yace, "A'a Nura". Ya bashi hannu suka gaisa yace, "ina zuwa haka?." "Wallahi wani waje zanje ina jiran Jannat tazo muje."
"Okay in ka dawo zamu tattauna."
"To shikenan." Daga haka suka rabu Nura yayi gaba.
Ganin fitowar Jannat ya saka shi yayi murmushi dan yasan daman baza'a hana ta fita dashi ko ina zasu je kuwa domin iyayen ta sun amince dashi matuk'a, bud'e murfin motar tayi ta shiga tace, "an barni." Kunna motar tayi kafin yace, "na d'auka ai baza a barki ba." Dariya tayi kad'an tace, "ai ko musu ma Abba baiyi ba ina cewa zamu fita yace a dawo lafiya kar dai a jima." Murmushi yayi yana jin dad'in yaddaa iyayen ta suka bashi yarda ta ko wacce fuska akan ta hakan ya saka yake sake k'aunar su dukkan su.
Tafiya suke suna hira sama-sama can sai tace, "Yaya na." Ya amsa da fad'in, "Na'am Jannaty."
"Wai kana da budurwa kuwa?."
Kallon ta yayi kafin ya mayar da hankalin sa kan titi yace, "meyasa kike tambaya ta?." "Babu komai ina so na sani ne kawai."
"Bani da ita, amma dai kwanan zanyi."
Shiru tayi bata ce komai ba shima kuma kamar wanda aka hana baice komai ba tafiya kawai suke yi har suka isa, a waje yayi parking d'in motar ya kalle ta yace, "bara na yi sallar i'sha sai mu shiga ciki." Yana fad'a ya fita ya barta a cikin motar.
Ita kuwa jikin ta duka yayi sanyi tana jin ina ma bata biyo shi ba haka ta zauna shiru har ya dawo yace, "to muje." Tace, "Yaya kaje ni ina nan bana jin dad'in jiki na."
"Subahanallahi, meya same ki?."
"Kaina naji yana yi min ciwo."
"Ayya sannu." Ya fad'a yana d'auko wayar sa ya koma gefe da alama waya yake. Can ba jimawa bayan ya gama wayar Mufeedah ta fito tayi kyau cikin doguwar riga ta shadda blue tayi mata kyau matuk'a ta nufo inda yake da murmushi a fuskar ta tace, "Sannu da zuwa."
"Yauwa sannun ki."
"Meyasa baza mu shiga ciki ba? Nayi mana order abubuwa da yawa ka daure muje."
"Sauri nake yi ne a nan ma zamu iya tattauwa."
Abinka da kai kake nema dole ta amince tace, "Daman magana ce a kan..." sai tayi shiru ta kasa k'arasawa. Kallon ta yayi yace, "ina jinki fad'i mana."
"Da dai munje ciki abin zai fi."
"No ina jin ki fad'i kawai." Sai da ta sauke ajiyar zuciya ta fara wasa da yatsun hannun ta tace, "Imran tun ranar da kazo office d'ina zuwa na farko Allah ya d'ora min qaunar ka, naso na b'oye hakan amma na kasa shiyasa na yanke hukuncin fad'a maka dan b'oye maka bashi da amfani sai cutar dani da yake yi, Allah ya sani da zuciya d'aya nake son ka kuma auren ka nake so nayi in Allah ya amince."
A lokaci d'aya zuciyoyin mutum uku suka k'ara kaimi wajan bugu kamar zasu faso k'irji su fito, Jannat da take jin komai dan glass d'in motar a sauke yake hankalin ta yayi kokoluwar tashi jikin ta ya soma rawa haka zuciyar ta kishi mai zafi yana taso mata daga cikin zuciyar ta, b'angaren Imran d'in shima hakan take domin sam baiyi tunanin abinda zata ce ba kenan ya d'auka abinda ya shafi company ne da babu abinda zai kawo shi, sosai kalmar ina Qaunar ka ta ratsa shi har ya rasa abinda zaice sai kallon ta kawai da yake yi, Mufeedah kuma tsoron amsar da zai fito daga bakin sa shine ya saka zuciyar ta take bugawa da sauri-sauri jikin ta har rawa yake.
Ajiyar zuciya yayi ya zuba mata ido kawai yana kallon ta kafin ya d'auke kai ya lumshe ido ya bud'e, ya bud'e baki zaiyi magana Jannat ta saki wata irin k'ara da ta dakatar dashi da fad'ar abinda abinda yake niya ya juya da saurin gaske yana kallon tagar gefen da take.
Free page😁
_Wannan labarin na kud'i ne ki biya naira 300 kacal ki karanta cikin nutsuwa da kwanciyar hankali, domin biya tuntub'i wannan number but only WhatsApp. ***_
Wattpad @ Nana_haleema
Arewabooks @nanahaleema11.