7&8
*AL'AMARINMU*
*Na*
*AMINA ABUBAKAR YANDOMA*
( _Meenart A Yandoma_)
Wattpad: Meenat_A_Yandoma
ArewaBooks: Meenatyandoma
*Labari ne wanda ban taba tabo irin wannan jigon ba, labari ne daya banbanta da sauran kada in cika ku da labari domin hausawa sun ce gani ya kori ji muje zuwa.*
*🌍MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION📚🖊*
______________________________
*TSOKACI!*
*LITTAFINA NA KUƊI NE AKAN FARASHI 300 ZAKI RURO KATIN WAYA MTN KO KUMA KI TURO TA ACCOUNT AISHA ABUBAKAR 2151366600 U.B.A BANK, DAN ALLAH IDAN BAKI SHIRYA BA KADA KI TABONI🙏🏻*
*TALLAH*
Albishirnku mata munzo maku da magani na gargajiya wanda zai saukarmaki da ni,ima yaqara maki lfy yawanke miki dattin mara daduk wani sanyi dake damunki,
Ina amare dake shirin yin aure kafin kifara shan komai yakamata kifara da mgnn sanyi domin matuqar bakishaba kayan ni,ima bazasuyi tasiri ajikinkiba,
Ina masu jego gadama tazo,Atafasa asa lipton da sugar da mada asha 2 times Muna katsina muna tura kaya ko ina yankatsina free deliver ne 1500 zaimiki 1month, ga masu buƙata muna bayar da rabin bokiti,Ku tuntube mu akan wannan number *** 🤸🏻♀️🤸🏻♀️🤸🏻♀️
Typing...✍🏽
10/1/2023
@2023 January
Free fages👇🏻
*PAGE 7️⃣&8️⃣*
...Cikin tsananin tashin hankali yake kai kawo daga bakin ƙofa zuwa tsakar gidan,amma ya tsorata da lamarin Asabe yana tsoron rasa matar shi domin baƙar wahalar da take sha tayi yawa.
Unguwar Zoma ce ta fito tana rarraba ido tamkar ka kama bera a buta, da saurin Ɗan ladi da mahaifiyar shi suka ƙarasa wurinta suna tambayar ba'asi.
"Ta haihu amma bata cikin yanayi me kyau,ruwa ya huci zuciyoyinku, tana buƙatar ganinka kafin ta shaƙi numfashi ta na ƙarshe."
Kafin unguwar zumar ta ƙarasa maganar tuni Ɗan ladi ya afka cikin ɗakin a gigice, kwance cikin jini ya taras da Asabe ga jinjira a saman ƙirjinta.
"Sannu Asabe Ruwa ya duba lamuranki."
Dogon numfashi ta ja kafin ta fara magana.
"Ɗan ladi ka gafarce ni domin ina ji a jikina nima kashe ni zasu yi kamar yadda suka kashe na bayana, ina da tabbacin duk rintsi jinjirata ba zata rasa rayuwarta ba domin jikina na bani ita ce wadda zata kawo ƙarshen matsalar wannan gari namu, Ɗan ladi ka aureni ba tare da sanin ni wace ce ba, amma kada ka damu na haifa maka wadda ita ce wadda zata haska rayuwar ka zata zamo alkhairi a gare ka domin ita ɗin fitila ce me matuƙar haske ko a cikin fitulu, zata bayyana maka ni wace ce zata sadaka da duk wasu alkhairai sannan ita ce me ɗaukar mani fansa, Ɗan ladi ga amanar abinda na haifa nan na damƙa maka kada ka bari tayi kukan rashina idan ta tambayeka ina nike kada kayi kuskuren ce mata wurin haihuwarta na rasa rayuwata domin faɗar hakan ba alkhairi bane a wurin ta, kace mata tana jinjira na mutu."
Asabe ta ƙarasa maganar a galabaice domin ko wane second ɗaya azaba ce ke ƙaruwa a jikinta.
"Asabe kaina ya ƙulle kin jefa ni cikin kogin tunani ta hanyar faɗa mani wasu ƙullallun al'amarra, ba zaki mutu ba asabe ki daina fadar zasu kashe ki domin ina tare dake babu wanda ya isa ya kashe ki."
Murmushin ƙarfin hali ta saki.
"Yanzu haka tsaye suke a kusa dani ka ɗauke jinjirar nan daga jikina domin kada su cutar da ita."
Hannunshi na kyarma ya ɗauke jinjirar, ɗauke ta keda wuya Asabe ta fa ra wata irin kyarma tamkar wadda aka ɗaurama lantarki a jiki jini ya fara fita ta hanci da kuma baki, idanunta ne suka kakkafe.
Wata irin kururuwa Ɗan ladi yayi wadda saida ilahirin yankin su ya amsa tuni mutane suka nufo gidansu a gigice domin wannan alamace dake nuna anyi mutuwa.
Da ƙyar aka raba Ɗan ladi da gawar Asabe.
Kasancewar mahaifin Ɗan ladi shine sarki a wannan gari da suka kasance babu abinda suke bauta sai ruwa.
Sudai wannan gari sun kasance inda aka haifi Jinjira uwar shi ta mutu wurin haihuwa to alamace ta babu alkhairi a tattare da jinjirin kuma wasu musibu na nan tafe.
Fada aka ce aka sanar da sarki abinda ke faruwa cewa sirikar shi ta haihu amma ta mutu, fadawa aka tado domin lokacin tashin sarki a fada baiyi ba.
Gidan mutuwar kuwa cike yake da ƴan gari sai faman koke-koke suke wasu suna zaga tufafinsu, hatta Tabawa Mahaifiyar Ɗan asabe birgima take yi tana kurma ihun mutuwar sirikar tata.
Ɗan Ladi kuwa kuka ya tamkar mace ga jinjira rungume a hannunshi ko kaya babu a jikinta sai wani baƙi yaɗi da aka nannaɗeta a ciki.
Sai da yamma sannan me martaba ya dawo gida nan ya taras da tashin hankalin da ake ciki, jinjirar ya amsa tare da ƙare mata kallo.
Idanunta a rufe suke babu alamun ta buɗe su bakinta kaɗai ke motsi shima in ka lura sai ka ga tamkar wani abu ake bata take sha domin sai haɗite yawu taje tana tsotse-tsotse.
Tsawa ya daka ma mutanen gidan sai ga gida tayi tsit duk masu kukan sun daina.
"Kamar yadda kuka sani a al'adar wannan gari inda uwa ta mutu tabar jinjira alamune na babu alkhairi a tattare da ita dan haka tun daga rana me kamar ta yau zamu fara bukukuwan mutuwar Asabe ita kuma wannan jinjira anan taje zamu zamu saka mata suna domin dole ne mu saka wannan jinjira a ɗakin baƙin ciki har sai tayi kwana ɗaya gobe mu fiddota mu kai ma Abun Bauta Ruwa ya saka mata albarka, a matsayina na Mahaifin Ɗan asabe kuma Sarkin wannan garin na sakama wannan jinjira suna Samu."
Yana rufe bakin shi wata baiwa tazo da tafashasshan tuwan zafi domin yima wannan jinjira wanka, amsarta tayi a gaban mutane aka fara yi mata wanka kamar yadda aka saba amma abinda ya ba mutane mamaki shine tunda aka fara yima jinjirar wanka bata buɗe idanunta ba, shidai wannan ruwa da aka saka Samu ciki haka ake yima duk wani jinjiri wanda indai aka saka yaro ciki zai fasa kuka har sai an gama ma shi wankan.
Amma Samu ko ɗar bata yi ba hasalima idanunta a rufe suke, ana gama wankan aka miƙa ma Ɗan ladi domin mahaifin jinijirar da kanshi ke saka ts ɗakin baƙin ciki ya rufe har sai ta kwana da gari ya waye sai a fiddota.
"Me martaba na roƙe ka ka gafarceni kada a saka yarinyar nan ɗakin baƙin ciki domin babu abinda ya shiga cikin ta."
Ɗan Ladi ya faɗa yana hawaye.
"Wace maganar banza ce kake gaya mani kana matsayin ɗan sarki amma kake wannan maganar, buɗe kunnuwan ka da kyau ka saurareni ba gudu babu ja da baya dole a zartar da hukunci a kanta."
Wani dogari ne ya amshi samu Sarki da kanshi ya saka ta cikin wani rumbu wanda shine ake kira ɗakin baƙin ciki.
Babu yadda Ɗan ladi ya iya haka ya zuba ido aka saka ta cikin wannan rumbu.
Shi dai wannan Rumbu muddun aka saka jinjiri ciki haka zai riƙa tsala kuka har gari ya wane lokacin ake fiddo shi ya galabaita sai a kai ma ruwa ya saka ma shi albarka, amma tunda aka Saka Samu ciki shuru kake ji har aka gabatar bubuwan rufe gawa aka binneta amma Samu bata yi kuka saba.
Ɗan Ladi kuwa tunda aka dawo daga rufe Asabe yana jikin Rumbun cike da tausayin ɗiyar shi.
Ganin har yanzu Samu bata fara kuka ba nan fa mutanen gari suka fara ƙananun maganganu.
Ɗan Ladi kuwa babu Yadda ta bawa bata yi dashi ba akan ya koma makwancin shi ya kwana amma ya ƙeƙashe ƙasa ya kwana nan bakin rumbun da aka kulle Samu.
Gari na fara Haske dandazon mutane suka fara taruwa bakin ƙaton kogin garin wanda tsabar ruwar dake cikin shi baka ganin ƙarshen ruwan.
Sarki da fadawan shi sai kuma Ɗan ladi rike da Samu haka suka nufi kogin.
Sarki na isa wurin ji kake kowa yayi tsit!
"Kamar yadda kuka sani a al'adar wannan garin bayan haihuwar jariri da kwana ɗaya muna kawota mu saka a cikin wannan kogi domin ruwa ya saka mata abarka, dan haka Ɗan ladi da hannunka muke so ka saka wannan ɗiya taka."
Sunkuyar da kanshi yayi ƙasa.
"A gafarce ni domin bazan iya saka ɗiya ta cikin ruwa ba."
"Me kake faɗa haka, tabbas ruwa na gaf da la'antar ka in kayi wasa, maza ka jefa yarinyar nan kafin fushina ya sauka a kanka."
Sarki ya faɗa a fusace.
Dan ladi bai motsa daga inda yake ba balle kuma a saka ran zai aiwatar da abinda aka saka shi.
Nan fa hankalin mutane ya karkata kanshi suna tsumayin abinda za'a zarta ma shi.
Wani dattiju ne ya fara magana a fusace.
"Kana so ka janyo mana fushin abun bauta, shin a kanka aka fara saka yara cikin ruwa ko mu duk da muka saka namu finmu son su kayi"?.
"Dan kana dan sarki ba zaka karya mana doka ba in ba haka ba dole ne ka karbi hukuncin abinda ka aikata."
"Ku dakata!"
Sarki ya faɗa a matuƙar fusace.
Kafin Ɗan Ladi yayi wani yunƙuri tuni Me Martaba ya fizgi jinjirar ya jefa ta cikin ruwan...
*SAURA PAGE ƊAYA FREE PAGES SU ƘARE.*
*MEENART............✍🏽*
***