JINNUL KAMIL(A TRUE LIFE STORY OF ALISHA)
7
by @milhaart
Bayan sun gama lesctures ɗin a tare suka fita, suna hiran lectures ɗin da akayi musu a haka har suka isa hostel ɗinsu ,gun metron suka nufa domin ɗauko kagan jamila sabida zuwa ta kenan ta shiga lectures, da taimakon wasu secuirities suka kwaso kayan har kofan ɗakin su.
Alisha ce ta zaro key a ɗan madaidaicin jakae ta ta buɗe kofar,tana buɗe wa kuqa yarinyar da suka gani a tsyae tub dazu a gun ta cusa kai zuwa ɗakin baki a buɗe suke kallon ta cike da mamaki,handbag ɗinta ta ajiye kana ita na ta fito ta fara shiga da kayanta,haka suka cigaba da jidan kayan babu wanda ya kula kowa a cikin su,Alisha bata zauna ba sai da ta taya jamila arranging kayanta tas kana ta shiga ban ɗaki ta wasa ruwa tsawon mintuna goma ta ɗauka a ban ɗaki bata fito ba sai da ta ɗauro alwala tana fito wa birjimemen hijab ɗinta ta ta saka kana ta shimfiɗa sallah kasantuwar lokacin har an idar da sallar azahar,Jamila ma ta faɗa ban ɗaki tayi wanka tayi alwala tana fita ta tarar Alisha har ta idar da sallan ta kuna risho kasantuwar dokan hostel ne ba a bari ayi amfani da gas cooker, girki ta farayi hankalin ta a kwance,gabatar da sallah tayi bayan ta idar alisha ta dire musu girkin da tayi a gaban ta dama indomie ne shiyasa bata ɗauki lokaci mai tsawo ba ta gama, wannan yarinyar da ta shigo sai aikin kallon su take ta kasa kasa, a zuciyar tace "Lalle ma baza su min magana ba zanyi maganin kune"
A gaggauce suka ga cin abincin nan da na suka sanya kaya suka fuce daga ɗakin kasantuwar suna da lectures karfe biyu don a lokacin har biyu ya gauce,tafiya suke da ɗan sauri sauri ,jamila takasa hakuri tace "Alisha yau naga ikon Allah kiga yarinyar nan yanda ta kusa bangaje ki, kuma sannu baza ta iya ce mana kawai ta kama ta shige mana ɗaki"
"Uhmn nima dai ta bani mamaki tunda kiga haka to fa ita ɗakin nata ne so bamu da bakin magana"
"Haba abin nata dayawa gaskiya ai ko sallama zata mana ko sai kace ba musulma ba?"
"Ki kauda idon ki akan ta ai na tabbata yanda muka nuna mata bamu san tana wajen ba abin zai dame ta,ba sai ka kula kashi ba bare kasan yana wari ko?"
"Umm hakane"
Alisha riko hannun ta tayi tace "kinga yi sauri mu shiga kar malamin ha riga mu shiga ace first day a disga ka don nasan lecturers ɗin nan wasun su ba mutunci bane dasu"
Ba musu ta bi bayan ta da sauri suka shige,zaman su ke da wuya sai ga shigowar malamin ai kuwa yana shiga ya bada umurni aka rufe kofar ,ganan ɗalibak dayawa a waje suna tsaye daga bisani suka hakura ganin baida niyan barin su su shiga, Jamila tace "Allah ha taimake mu"
Alisha ta amsa da "wallahi kuwa"
*KUMO*
Head district na Akko local goverment, dake cikin jahar gombe,garine wanda ake kiwo da kuma kasuwanci, fulani sunfi yawa a garin duk da cewar akwai hausawa a garin.
"Inna lillahi wa inna ilaihir'raji'un" shine abinda naji na furta tana yarfa hannu haɗe da kallon wace ta nufo ta,ta rike haba tace "Wai ke dan Allab wace irin mayyace wai duk inda nayi sai kin bini?"
"Haba Mariya wallahi nifa ba da sharri nake bibiyar ki ba wallahi so nake ki zama qawata amma bakya kulani ban san me na miki ba kika tsane ni har haka"
"Qawancen ne nace bana so jimin yarinyar nan fa ana dole ne? Kulu Ko ana dole ne nifa ba sa'an ki bace yauwa"
Wace naji ta kira da kulu har matsar kwalla take ta juya ta fara tafiya ranta babu daɗi dum sanda tazo mata ta maganar nan sai taci mutuncin ita ita dai kawai Mariya burgeta take,Binta da wata kallo mariya tayi "Mtsww mayya kawai ni ban taba ganin mutum irin ta ba wallahi"
Tafiya take tana jin jina al'amarin yarinyar nan it aa dole so take ta zama kawarta amma mariya taki idan zata magana sau duba to sai ta zage ta sau duba.
Tafiya take tana tsalle tsalle ta ɗauki kara tana wasa dashi ta nufi hanyar gida,tsaye tayi tana kallon shi har ya gifta ta inda take hannun sa rike yake da ruba cike da goruba da alama talla yake,yaro ne wanda bazai wuce shekaru 12 ba, cike da tsiwa tace "Kai zonan" tasa hannayen dukka a biyu a kwankwason ta ko kallon ta baiyi yiba ya cigaba da tafiyar sa kasantuwar yasan wace ce mariya da abinda zata iya aikatawa a karo na biyu ta kuma faɗin "Kam bala'i kai don uwar uban ka ba da kai nake ba nace ka zo nan wallahi kasanni sarai idan na kama ka sai na karya maka hakori zo nan nace" fuskar ta babu alamun wasa a ciki ita ala dole an 'bata mata rai.
Sum sum sum ya zo shi ya tsaya a gaban ta kansa a ƙasa ya ƙasa haɗa ido huɗu da ita, rankwashin sa tayi ji kake kwas kwas ya buɗe baki zai sa ihu a tsawace "Ka min kuka sai na yanka maka bakin nan naka" ta faɗa haɗe da murɗa masa bakin da hannun ta ji kake guut ya haɗiye kukan "Bani goruba na hamsin"
"To ina kuɗin?" murya sa a sassarke alamun yana son yin kuka.
"Dallah zan baka kasan dai nafi karfin naira hamsin"
"Mariya na ranan ma fa baki bani ba kika sa inna ta tamin dukan tsiya" ya karasa maganar yana share guntun hawayen da suke kokarin zubawa
"Hahaha Allah ya kara maganin mara kunya kenan,ka bani na hamsin nace kana bata min lokaci" ganin bayi da niyar bata tasa hannu ta buɗe marfin roban ta ɗauki guda biyar tace "Maza ka tafi" Allah sarki babu yanda ya iya haka ya juya ya fara tafiya sai da yayi nesa da ita har ta juya ta fara tafiya ya kwala kiran sunan ta "Ke Mariya!!!! Waigowa tayi tana gutsiran goruban dakuwa ya mata haɗe faɗin "Kinci uwaki muguwa azzalamu kawai wallahi sai na faɗawa mamana,kuma Allah ya isa rankwashina da kika yi shegiya kawai" ya ari na kare.
Ciza lebenta tayi tace "Zaka ci gidan kune idan na kama ka sai kasan ka zage ni" ta juya ta cigaba da tafiyar ta, akan hanyar ta na komawa gida ta zagi wannan ta tsokani wanchan idan kuma kana nan yarane ta ci zalin su ta cigaba da tafiyar ta.
Cike da masifa da ɗaga murya yake faɗin "Shiyasa fa nace miki bana so yarinyar nan tana fita,idan tasa ƙafa ta bar gidan nan sai an gata gashi nan tun dawowata yarinyar nan bata gidan nan gashi ahr magriba tayi"
"Haba malam kasan halin mariya fa sarai bata jin magana kai kaɗai kake gaya mata magana taji babu yanda banyi da ita ba amma ta fita saida ma ta bari na shiga sallah ta fita tun fa azahar ta fita har yanzu bata dawo ba"
"Iyee wato ma har faɗa kike tun azahar to na rantse idan wani abu ya sami yarinyar nan sai na sa'ba miki, haka kawai ni banga amfanin ki a gidan nan ba......"
"Assalamu alaikum wa'alaikumussalam" ita kuma haka take sallama tayi sallama kuma ta amsa da kanta, muryar ta ne ya katse sbi ya kasa karasa maganar da yake da niyar yi. Ai kuwa ya shiga washe baki yana dariya kamar mai tallan toothpaste "Wa alaykissalam Mamana an dawo kennan,ya hanya anje wasa kenan?"
Mama baki a buɗe take kallon sa tace "Yanzu malam ka gama masifa akan ina barin yarinyar nan ta na fita kai da zaka tambayeta da ina take amma kake cewa ya hanya malam?"
"Ke ke talatu kinga bana son iya yi, ina ruwanki da maganar da muke da mamana"
"Malam yarinyar nan fa girma take ace yarinya katuwa da ita amma wani abun kamar na ɗna shekara 5 amma kai kullum duk abinda tayi akan dai dai take shekarunta fa 16 malam sa'annin ta dayawa suna gidan mazajen su wasu har sun haihuwa amma ita tana nan tana ta shiririta"
Mariya ta faɗi akasa ta hau birgima tana ihu tana faɗin "wayyo Allah na wayyo na shiga uku na wayyo za'a rabani da gidan ubana,wayyo Allah baba wallhi matar nan bata sona"
"Kinga abinda kika ja ko? Nace kinga abinda kika ja ko? Wai Meyasa bakya son farin cikana da na yarinyar nan a gidan nan?"
Inda sabo ta saba, duk sanda tayi magana ta rushe da kuka tana ihu kamar ta yanka tane,girgiza kai tayi ta shige ɗ'akinta ta bar su a wajen yana ta aikin rarrashin ta.
Sai da ya samu ya rarrashe ta tayi shiru kana ya samu kanta cikin muryar shagwaba tace "Baba nifa matar nan bata sona shiysa nima bana son ta"
"Kaaai maman nasha faɗa miki ki daina ce mata matar nan, mahaifiyar ki ce fa itace ta haife ki, kin taba ganin uwa ta haifi ɗanta kuma taki shi?" girgiza masa kai tayi alamun a'a "To tana son ki"
"Amma ai kullum cikin faɗa take min ba kamar kai ba ai da rarrashi kake min magana"
"Haka mahaifiyar ki take ki mata uzuri ki rika jin magana kinji?"
"Toh"
"Kuma dan Allah ki daina fita idan ta hana ki, kuma idan kin fita ki tabba kin dawo da wuri kinga ke mace ce bai kamata kina yin ma ba"
"toh baba amma zaka saya min tsire?" dariya ma ta bashi sabida yanda tayi masa maganar kamar yar shekara biyu yace "Eh zan saya miki idan na dawo daga masallaci"
Da murna ta mike ta ce "Toh sai ka dawo" ta shige ɗakinta shi kuma ya nufi mallaci.
Bayan sallar isha a kofar gida ya tarar da ita tana zaune tana jiran sa ,duk wanda ya wuce sai ta nemi tsokanar ba yara ka ɗaiba har manya mariya bata bari ba, tana ganin sa kuwa ta wafci ledar ta shige cikin gida ɗakinta ta nufa ta shige ta rufe ta cika ta zauna a kasa haɗe da bajewa ledar tun kan ta kai bakin ta ta fara haɗiyan yawu,nan ta hau ci bata gama hadiye na bakinta ba sai ta kara wani.
baba girgiza kai yayi ya shige ɗakin mama ganinta yayi akan sallaya tana azkar zama yayi a bakin gado bayan ta gama ta mike ta ajiye masa abincin sa a gaba sa ta koma kan gado da niyar kwanciya,murmushi yayi kana yace "Toh Su Tala haryanzu fushi ake dani ne"
Uhmn kawai tayi tayi kwanciyar ta,har ya buɗe abincin ya rufe jawo ta yayi kusa da shi yace "Haba uwargida kuma amaryata meyasa kike son bata min kyakkyar fuskar kine? Baki san fushi sam bai dace da fuskar nan taki ba?"
"Uhmn Malam kenan dole kaga fushina ,dole na yi fushi sam yadda kake goyon bayan yarinyar nan ba dai dai bane kwata kwata hakan bai min ba wai ace yarinya kamar wannan yar shekara 16 tana neman shiga 17 bata da aiki sai wauta amma kai sam baka ganin laifin ta ni.........."
"Assalamu Alaikum"
Sallammar da akayi ne ta katse mata maganar da take bakin ta,wani sallaman aka sake yi da karfi.
Baba yace "Waye wannan haka da daren nan?"
"Kuma fa kamar muryar mace nake ji fa"
"Assalamu Alaikum wai babu kowa ne a gidan?"
Zumbur mama ta mike haɗe da dafe kirji "Ya kamar muryar mero dillaliya nake ji?"
Shima baba mikewa yayi yace "Ya naga duk kin fita hayyacin ki? bashi take bin kine gashi kije ki bata" ya karasa maganar haɗe da zaro kuɗi daga aljihun sa masu yawan gaske.
Kai ta girgiza masa haɗe da faɗin a'a malam bata bina komai kawai dai duk inda kaga Mero dillayi fa to ba alhairi bane bare yanda nake jin take sallamar nan kamar ba lafiya ba"
Wani sallaman aka kuma yi wannan karon ba daga waje ba a tsakar gidan ta tsaya.
Baba yace "Muje muji da me ta zo" ya maida kuɗin a aljihun sa suka fice a tare.
__________________________
Milhaat ce
Ƴar Terawa✍🏻