KADDARATA CE

KADDARATA CE Page 21/22

by @zinariya0102



Bayan wata biyar da bikin Walida, tafe suke akan lipan ɗin da Ahmad ya siya ta ce " idan na gama awo zan zarce gida inyaso sai ka biyo mu tafi" 

Ahmad ya ce " angama ranki ya daɗe" dariya tayi tana mai ƙara jindaɗin yanda mijin nata yake ƙoƙarin faranta mata a ko wane lokaci.

Har cikin hospital ɗin ya kaita sannan ya nufi kasuwa. Sai da ta gama komai ta nufi gidansu.


Zakiyya ta samu tana shirin tafiya Islamiyya, cikin murna suka rungume juna, ɗakin Inna  ta nufa ganin sallah take yi, ya sa ta zauna tana faɗin "bari nima na tashi nayi" duk ta gaji.

Abinci Zakiyya ta kawo mata, shinkafa da wake har da salad ta ce "bari in zauna muɗanyi hira idan an fito sallah na shiga" 

A'ina zaki zauna, wuce ki tafi sai yayanku ya zo ya ga baki je ba, kin san dai haɗuwarki da shi ai" Walida ta yi dariya ta ce "ina nan har ki je ki dawo sai dare zan tafi" da murna Zakiyya ta yi musu sallama ta tafi makaranta.


Har bacci Walida tayi kafin dawowar ƴan gidan nasu, Khadija da Zakiyya ne suka fara dawowa, sai kusan magriba Hafiz ya shigo, fuskarsa cike da gajiya ganin Walida a gidan ta yi kyau ta ƙara yi masa girma a idonsa.


Da murna Walida ta yi masa sannu da zuwa suka gaisa, nan yake tambayarta babu wata matsala da kwarin guiwa ta amsa da jindaɗi, "lafiya ƙalau wallahi Yaya" ita ke binsa hakan ya sa akwai shaƙuwa mai ƙarfi tsakaninsu, danma ba mai wayan magana ba ne.


Sai da akayi sallar isha, Ahmad ya zo, har cikin gidan ya shiga nan akayi ta hira da shi, Ahmad ya kalli Hafiz wanda yake shirin fita, ganin ana ta kiransa a majalisin da suke karatu, ya ce " Yaya munyi fushi fa yanzu saboda Allah ace baka zo mana ba" murmushi Hafiz yayi ya ce "zan zo insha Allah" Walida ta ce "ai kullum haka ka ke cewa" alamar ba ta jin daɗin rashin zuwan nasa" Baffa da ke ɗakinsa ya yi murmushi ya na mai godiya ga Allah da ya ba su siriki nagari.


Tun da ya fita yaji gabansa ya faɗi addu'a ya ke karantawa a ransa har ya isa majalisin inda yake harabar masallaci ne.


Gaba ɗaya jikinsa babu ƙwari a haka ya daure suka fara karatun tare da abokansa su Gaddafi, da Abubukar da sauran ɗalibai.....





***************

Jawahir! Jawahir! a ina kika ajiye maganin sauron ne, na duba banganshi ba" Umma ta faɗa ta na fitowa daga ɗakinta.

Har ta fara bacci kasan cewarta mai saurin bacci ta jiyo kiran Umma, da sauri ta tashi ta na amsawa "na'am" ta fito sanye take cikin doguwar riga ash colour, mai dogon hannu rigar mai ɗan kauri ce, " ina maganin sauron yake?" 

Umma ta faɗa tana kallonta, marairaicewa tayi tana raba idanu ta ce " uhm wallahi Umma na manta ban siyo ba, bari yanzu in je shagon Ali in siyo" ta juya da sauri ta ɗauko hijab.

Zainab da ke waya da Abdallah ta ce "ina zakije?" da sauri ta amsa "maganin sauro zan siyo" ta fita.


Umma ta ce " ki yi maza ki kawo" 

Jawahir ta ce to, ta tafi.

Da ke lokacin sanyi ne ƙarfe tara ne amma kamar goma ta wuce duk sahu ya ɗauke kowa yana gida sai ɗai-ɗaikun mutane haka, shagon Ali ta je, ganin a rufe bayanan ya sa tayi gaba.


Wasu Samari ne su biyu, tafe a mota ɗayan ne ya ce "kai guy kaga wata can" wanda ake nunawa ya juya ya kalli wajen babu kowa sai ita, "bi ta" 

Bayanta su ke bi har ta isa ɗayan shagon, abun kamar haɗin baki shi ma bayanan.

Cikin gajiya ta dafe kanta ta ce yanzu sai naje titi mtsww, ta miƙi hanya ita kaɗai dai-dai wani lungu waɗan nan Samarin suka  cimmata, gani tayi an buɗe mota an fizgota, baƙi ta buɗe ta kurma ihu, ji ta yi an ja motar da ita.


"Ku taimaka min, jama'a ku taimake ni!" abinda take faɗa kenan cikin tashin hankali, motar tinted ce kuma a rufe glass ɗin ya ke babu wanda yake jinta.


Kokawa suka shiga yi da wanda ya riƙeta, ɗayan da yake driving ya yi parking, a dai-dai wani kango ta baya ya daki kan Jawahir, ta ke ta sume, ta faɗi kamar matacciya.


Ɗaukarta suka yi suna rangaji dan a bige suke, su ka shigar da ita kango, yar da ita sukayi a ƙasa, wanda yake driving ya fara zare velt ɗin jikinsa, a maye ɗayan ya ce " haba guy ba haka mukayi da kai ba, ai ni na fara ganota" 

Saurayin ya ce " sai kuma aka ce ni zanci ragowarka never, i'm the boss" ya jefa masa agogonsa a fuska, Jawahir da ke halin suma, ba ta san abinda ke faruwa ba, wani zafi ne ya ratsa jikinta wanda yayi sanadiyyar farfaɗowarta, wanda ake kira guy kuwa duk neman matan da suke bai taɓa jin mace mai ɗanɗanon kamar wannan ba.


Ƙoƙarin ihu take jin bakinta a rufe yake an ɗaure shi, hakama hannuwanta, ya sa ta ƙara shiga tashin hankali, azaba take sha wacce bata taɓa sanin akwai irintaba.


"kai ɗaga ta hakanan, nima na yi, wai kai meyasa ka fiya son kanka ne" ya na zaune hankali kwance ya na shan sigari, da ƙyar ya ke iya ɗaga idonsa saboda buguwa.


Tun Jawahir na ganewa har ta ƙara suma, ga duhu, ba tausayi suka yi mata fyaɗe har su biyu.

kusan ƙarfe tara da minti hamsin na dare suka tashi daga karatun Malam Hamza ya ce " ya kamata mu je mu duba Malam Lawan ɗin dan tun ɗazu na so mu yanke karatun nan, saboda yanzu lokacini sanyi ne" Hafiz ya ce "anya kuwa ma je a yanzu, may be ma yayi bacci mu barwa gobe" Wayar Malam Hassan ce ta yi ringing ya na dubawa kuwa yaga Malam Lawan ne, ya ce " ga shi ma yana kira, assalamu alaikum" 

Daga can Malam Lawan ya ce " ina jiranku fa tun da akayi isha nake jiran zuwanku" 

Malam Hamza da ke kusa da Malam Hassan ya ce " gamu nan zuwa insha Allah" Hafiz da ke zaune ganin sauran sun dage sai anje, ya ce" mu je dare yana ƙarayi" sauran duk sun tafi sai su. 

Suna tafe suna hira har gidansu Malam Lawan, a ƙofar gida suka tsaya a waya suka sanar da shi sun shigo.


Shi ya fito ya shigar da su gidan,gaisawa sukayi da Mahaifiyarsa suka duba shi tare da yi masa addu'ar samun sauƙi.

Ba su jima ba suka tafi, Malam Hassan ne ya fara yi musu sallama ya nufi hanyar gidansa, Hamza da Hafiz ne suka rage, suna tafe su na hira.

Hamza ma ya je kan layin gidansu ya ce " to malam Hafiz sai da safe" 

Hafiz ya ce Allah ya bamu alkhairi. 

Ya ci gaba da tafiya, nishi ya fara jiyowa sama-sama a dai-dai kango, ana ƙoƙarin ihu sai gurnani ake da ƙarfi, dubawa yayi babu kowa a wajen ga dare dan goma har da kwata, 

Har ya wuce ya ƙara jiyo nishi da gurnani da alama a galabaice akeyi.

A hankali ya nufi wajen, wayarsa ya haska dan ganin waye, Mace ce kwance an ɗaure mata baki, cikin hanzari ya nufi inda take, idanunta a rufe suke wannan nishin kawai take iyayi da hancinta.


Rasa abinda zaiyi mata yayi, ƙoƙarin kwance mata baki yayi, hannunsa na rawa ya kwance mata baki ya na faɗin "subhanallahi, me ya kawo ki nan, sato ki akayi, innalillahi wa'inna'ilaihirrajiun......Wayyo Allah ku taimake ni za su ka she ni, ihu take ta na riƙe da wuyan rigararsa, gigicewa Hafiz yayi yana ƙoƙarin kwace wa daga hannunta, Zamewa yayi tsabar tsoro ya faɗa kanta, rigarsa ta ta ja ta keta ta, har ƙasa, ruɗewa sosai Hafiz yayi ya na ƙoƙarin kwace kansa, ihu take ta na riƙe shi.


Maƙota ne suka jiyo ihu, take kowa ya fito daga gida, hasken wayan Hafiz ne ya sa aka nufi cikin kango, kafin wani lokaci an cika a kangon, riƙe Hafiz akayi samari suka fara neman dukansa.


"Ku tsaya ku tsaya" wani dattijo ta faɗa yana kare Hafiz, Jawahir da ke kwance a sume, aka duba ganin fyaɗe aka yi mata ya sa aka kira ƴansanda.


Mata ne suka yayyafa mata ruwa ajiyar zuciya ta sauke, wasu na kuka wasu na zagin Hafiz ana sai sun ƙonashi, a samasa taya, yana faɗin "wallahi ba ni bane wa....Naushin sa wani saurayi yayi take hancinsa ya fara jini, iya tashin hankali Hafiz ya shiga a wannan daren.

Wata babbar mace ce ta ce "ke waye yayi miki wannan aikin?" batasan fuskar kowaye ba, Hafiz da ke tsare a hannun wani mutum ta ɗaga hannu ta nuna shi, cikin mawuyacin hali take.


Da wa Allah ya haɗasu kuwa dukansa suka hau yi, kafin ƴan sanda su iso anyi masa jina jina, a galabaice polices suka iso ɗaukansu akayi aka nufi station da Hafiz, Jawahir kuma akai hospital da ita, har sha biyu na dare mutane na ta magana akan su Hafiz, ana ta tsine masa.




Tun da Jawahir ta fita Umma ke jira shiru-shiru har goma babu Jawahir ba alamarta, Zainab ce ta fito ta ce " wai har yanzu bata dawo ba?"

Umma ta ce "nima hankalina bai kwanta ba nan nan fa kantin Ali na ce mata ta je" Zainab ta ce "Allah ya sa lafiya" amin ya Allah" rife gidan sukayi dan Baba baya nan anyi rasuwa kawunsa ya rasu a Katsina a can zai kwana.


Sun je shagon Ali bata nan, gaba sukayi duk kantinan da ke kewayen sun je bata nan. Nan hankalinsu ya tashi, salati kawai Umma take, Zainab sai kuka take tana faɗin " har ta fara bacci aka ce ta siyo wani maganin sauro, wasa-wasa har sha ɗaya su na nema, maƙota suka dinga bi suna bugawa dan jin ko ta shiga nan ma ba ta nan, haka akayi cirko-cirko a ƙofar gida, wasu su ce ko saceta akayi.Dare sai ƙarayi yake Zainab ce ta yanke jiki ta faɗi jin ance ko an sashe Jawahir, hankalin Umma ne ya ƙara tashi, maƙocinsu Alhaji Usman ne ya ɗauko mota aka sakata aka nufi asibiti...




Bayan Ahmad ya ɗauki Walida sun tafi, hira su Inna suka ci gaba da yi a ɗakinta, duk jiran shigowar Hafiz sukeyi dan ko abinci bai ci ba ya fita majalisinsu.

Duk inda goma tayi ansan sun tashi ya shigo gida, amma har sha ɗaya bai dawo ba, kiransa Baffa yayi wayar tana ringing amma ba'a ɗauka.


Su Zakiyya duk sun tafi sun kwanta bacci, Baffa da Inna ne kaɗai a zaune, Inna ta ce " ina ya tsaya haka har sha ɗaya ni Aishatu" Baffa ya ce "yo wa ya sani ne gashi na kira baya amsawa" shiru sukayi gajiya Baffa yayi ya fito da kansa, masallacin ya je dan ganin ko ba su tashi ba ne. Babu kowa sai Hashim shima wajen mai shayi zai je a dafa masa indomie nan suka gaisa Baffa ya ce "ina su Hafizun naga babu kowa a wajen" Hashim ya ce " tun ɗazu suka tafi duba Malam Lawan, bari in kira su, Baffa ya ce "na kira shi amma baya ɗauka" 

Hashim ya ce "bari in kira Malam Hamza" 

Har ya fara bacci yaji kiran wayarsa, ganin Hashim ɗalibinsu ya sa ya ɗaga wayar da sallama, gaisawa sukayi ya ce daman Baffa ne yake neman Malam Hafiz  ko kuna tare?" Wattsakewa Hamza yayi ya ce" ai tun ɗazu ya dawo ba mu jima a can ba" nan fa hankali ya tashi, Hamza ya kira wayar Hafiz ɗin nan ma ba'a ɗauka ba, su Malam Gaddafi da Abubakar suma sai suka tashi.

Gaddafi ne ya ji labarin an kama wani yayi wa wata yarinya fyaɗe, sai zancen mutane sukeyi ana da an barsu sai sun kashe shi. 


Matsananciyar faɗuwar gaba Malam Gaddafi ya ji, ƙarasawa yayi ya na musu jaje, wani ne ya ce " ni fa nasan guy nan malamin su Maryam ƙanwanta ne, ashe ba malami ba ne a daren nan ya kawo yarinya ya lalata musu ƴa" innalillahi wa'innailaihirrajiun, abinda Gaddafi ya ke faɗa kenan.


A daren ya nufi gidansu Hafiz, ganin Abubakar da Hamza da wasu a tsaye tare da Baffa, ya na zuwa ya ce " wai har yanzu bai dawo ba?" Baffa ya ce "wallahi har yanzu"

Kwantar musu da hankali yayi ya ce " naji ance ƴan sanda sunyi kame ɗazun nan ina tunanin yana station" Abubakar ya ce "tabbas dan naji jiniyar motarsu ta wuce ɗazun nan" Baffa ya ce " amma indai haka ne ba su kyauta mana ba" 

Lallaɓa Baffa sukayi ya koma gida.

Nan ya sanar da Inna abinda ya faru, hankalinta dai ya ƙi kwanciya a daren ta ce su je su duba ya ce ta bari zuwa da safe.

Daga Inna har Baffa ba suyi bacci ba a daren, hakama Gaddafi da yake cikin tsoron abinda ya ji...........