🌼🌼ZUBAR HAWAYE NA🌼🌼

Episode 7-8

by @gimbiyaayshu2503

🎡🎡ZUBAR HAWAYE NA🎡🎡


STORY AND WRITTEN BY 


(GIMBIYA AYSHU)  


     WHATPAD NAME 

     * AISHAMAARUF*




ELEGANT ONLINE WRITER'S 📚




PAGE 4


________________________Buta Nasreen ta dauka ta shiga bayi, bayan ta fito ta daura da alwala, daki ta shiga ta tada sallah, "itama tsauri take ta tafi gida" bayan ta sallame inna ta shigo da abinci, yi maza kici kafi ki tafi kinji diyata, mama dare nayi zanci innan koma gida, A'a wlh zauna kici kina bata lokaci, zama Nasreen tayi jikin ta na rawa har tara ruwa idan ta yayi, ita ba wai dan wani abu bane yasa take gudun dare a'a, fassaran da za'a matane bata so, batasan sanda hawaye ya gangaro mata ba, hannu tasa ta share hawayen, " ki dai na kuka kinji insha Allah wata rana sai lbr, Aisha ce ta karashe maganan tana share mata hawayen ta hadi da runguman ta" bayan sun kammala cin abincin, kitchen takai kwanon sannan ta fito ta wanke hannun ta, godiya tayi ma inna da irin kwaunar da take nuna mata, "nace ki dai na gode min, ki dauke ni a matsayin mahaifiyar ki, ki gayamin duk damuwanki zan share miki hawaye insha Allah kinji, bar Zubar da hawaye, Allah miki Albarka ya kareki daga sharrin matsu Shari yayima rayuwanki Albarka" da Ameen ta ansa haka ma Aysha dake tsaye itama ta amsa da ameen, daki Nasreen ta shiga kayan jikin ta ta cire ta miyar da Wanda tazo gidan dashi,Aisha ce ta shigo dakin ta same ta tana shiri, Nasreen tafiya zakiyi?, ki kwana a nan mana, zaro ido Nasreen tayi tace" kinasan aci kanin ubana kenan, 'tabdi', I in ban kai ma mama kudin tallan ta ba sai ta ci ubana ita bata damu da komai nawa ba, ko na kwana ko karna kwana, damuwan ta kawai shine kudi, kinga ko in bataga kudin nan ba ba zaman lfy, bazama tayi barci ba sai ta jira dawowa na, yanzu haka ina komawa zai na sha zagi in ma ba'a hada min da tsaraban duka ba, dan Kona bata kudin wanibi sai an min duka", ta karshe magana tana daukan tiran abincin ta, dagowan dazatayi sai taga Aysha na kuka, bude baki Nasreen tayi tana kallon ta, mai ya faru? Na miki wani abu ne? Yi hakuri inna bata miki rai. Karasowa Aysha tayi da dan gudun ta ta rungumi Nasreen ta fashe da matsanan cin kuka harda majina, rungume ta Nasreen tayi tana dan murmushi Wanda ake kira da "yafi kuka ciwo" tana shafa bayan ta kiyi hakuri Aysha, ki daina kukan kinji, ba kuka ya kamata kimin ba Addu'an ki kawai nake bukata, nawa jarabawan kenan a Rayuwa, saboda haka Addu'a kawai zakimin, Allah ya bani ikon cinye jarabawan, girgiza mata kai kawai Aysha tayi tana kokarin tsayar da hawayen ta. Inna fake tsaye a bakin kofa tun da suka fara zancen ne ta tsaki labulen da ta dan daga, jin gina tayi da jikin bango tana ko Karin miyar da hawayen da ya taru a idan ta, Allah tsarki Nasreen taki jarabawan kenan a Rayuwa, Allah baki ikon cinye wannan jarabawan ya baki hakuri da juriya, da wata ce a irin wannan halin da ta dade da shiga cikin wani halo na Rayuwa mara kyau, "ya Allah ka dubi baiwan ka da idan Rahma, ka kare ta daga dukkan sharri, ka tsare gaban ta da bayan ta ya Allah, ka kawo mata a gaji, Barin bakin kofan tayi ta nufi dakin ta dan taga alamun zasu fito" fitwo sukayi daga dakin suka nufi dakin inna, sallama suka yi inna ta amsa musu, shiga sukayi da murmushi a fuskan su dan kar inna ta gane abin da ya faru, inna zan tafi, "har zaki wuce diyata, bazaki bari anjima ba ko gobe? " zaro ido waje Nasreen tayi tana rike haba, kai! Inna, inna kuskura banje gida ba kashina ya bushe, dan sai an karaira yani, ko yanzu ma nasan ana cigiya na, " girgiza kai kawai inna tayi dan tasan ba cigiyar Arziki ake mata ba, toh shike nan ga wannan, tana miko mata wani dan laida" "nagode inna" tsororo inna ta kalle ta tace bangane kin gode ba, maza ansa kafin ranki ya baci yanzun nan, "Amsa tayi tana godiya"sallama sukayi inna sannan Aysha ta rakata har kofan gidan su, sukayi ban kwana suka rungumi juna, kafin Aysha ta juya ta fara tafiya, tanayi tana waiwayan Nasreen, da sun hada ido sai Nasreen ta daga mata hannu har ta bace ma ganin ta, cikin gidan ta shiga bakinta dauke da sallama, tana shiga da mama ta fara cin karo, wata arniyar kallo mama ta auna mata tace zannu da zuwa uwar gantalallu, kin tsiyar da abincin duka koko kin rage na uwar ki ta karasa ragowan daya rage, "A'a na tsiyar mama" kai kai kai!!! Ki dai na kirana da mama, danni ba uwarki bace, duk cikin yarana babu mayyah, shegiya kawai, ban kudina tana warce kudin hannun Nasreen, "tsake mata Nasreen tayi, tana murza hannun ta dan taji zafin warcewan da tayi a hannun ta, har gwarjewa sai da tayi", zaki matsa a gabana ko sai na mangare ki,kuma kije Kiyi wanke wanken nan, gashi chan yana jiran ki, dan babu baiwar ki a gidan nan ehe!" Sim sim Nasreen ta nufi wurin da aka tara tulin kwanonin ta fara wanke su ba kama hannun Yaro, dan in bats yi tsauri ba sai tayi dare sossai, ta rasa yanda ake an fani da kwanoni a gidan nan su ba yawa ba kwata kwata su shida ne, amman in kava kwanonin wani lokaci zaka ce gidan da aka tara yara 20 da mata hudu ne,tana cikin wanke wanke sa'ade ta shigo da gyle a kafada, sai cin cingum take jikake kas.. Kas... Kas... Tayi daurin ture kaga tsiya da dan gashin ta a katsan daurin akwai gashi dai ba laifi, hannun ta rike da laida har hudu, duk a cike da kayan makulashe, sai tafiya take laidan na janta dan yai mata nauyi, "sannu dazuwa diyar Al-barka tana daga zaune" haba mama bazaki tashi ki zo ki taimkan ba kinga ina fama da abu, amman in anzo ci kinfi kowa san a baki dayawa, "haba diyar Al-barka, I ba kin tashi nayi ba, naga kaman kin karaso ne tana amsan laidan dake hannu daya, iko tana dauka sai da tadan yi kara, kai-kai laidan nan da nauyi wlh, sai kace an tsaka kan mutun a ciki, wai Allah yayi ma mutumin nan Albarka, diyata tayi goshi, irin wannan kayan haka wai- wai" daki takai kayan, zaman dirshen tayi ta fara bude laidodin, haba mama ki bari mana inzo in bude haba mama, ta karasa da jan tsaki ta nufi hanyyan kofa, " tohhh! Na bari, tana mikewa tsaye ta bi bayan sa'ade. 


Ba Nasreen tagama wanke wanken nan ba sai 10:15, tana share wurin lauratu ta shigo tsanye da dogon riga da jaka a rataye da gyale a hannun ta, sai tafiya take tana wani rangwada da yauki, zannu da gida mama, ta daga mata hanu irin yan da en gayu keyi, *alamun hy" tana tafiya, bata tsaya ko Ina ba sai da takai daki, tana shiga batayi wata wata ba ta cire kayan jikin ta tayi daura kirji, fitowa tayi da dan kwali akan ta, k zuba min ruwan wanka, "da toh! Nasreen ta amsa dan tasan da ita ake, roban wanka ta dauko ta nufi bakin rijiya, ruwa ta debo ta cika roban, bayan ta gama ta nufi wurin lauratu, dukawa tayi a gaban ta tace na cika" toh! Dauka kikai bayi da kwandon wanka, "toh! tashi tayi ta nufi bakin rijiyan ta dauki ruwan da kwandan wankan dake ajiye a gefen rijiya ta nufi bayi da shi ajewa tayi ta fita a bayin, Anty na kai ruwan, ko amsa ta bata yi ba, Nasreen naganin haka sim sim ta bar wurin ta nufi bakin kofan ta ta zauna, tagumi tayi tana kallan kofan tsoron gidan, baba ne ya shigo gidan da sallama a bakin shi babu Wanda ya amsa banda Nasreen, "ina wuni baba" ko kallon ta baiyi ba balle tayi tunanin zai bata amsa haka ya nufi dakin shi baiyi ma kowa magana ba, k dau abincin chan ki kai mishi, da toh! Nasreen ta amsa, tashi tayi ta nufi kitchen, abincin shi ta dauko Wanda ke cikin wani kwanon samira an kulle shi da marfi, dauka tayi ta nufi dakin baba, sallama tayi a bakin kofan amman shiru ba'a amsa ba, ta kara yi har tsau uku amman bai amsa ba, yaye labule tayi ta shiga da sallama a bakin ta, karasowa tayi ta ajiye abincin a gaban shi, baba ga abinci, shiru bai amsa ba, kaman ma babu kowa a dakin, dama tasan ba amsa mata zaiyi ba, tashi tayi idan ta na taruwa da hawaye, fita tayi a dakin ta shiga dakin ta, zama tayi ta dinga rusa kuka kaman Allah ya aikota, ta share minti 15 tana kuka, mama ne ta kwala mata kira, hannu tasa ta share hawayen ta da tsauri, katsan zanin ta, tasa ta share hawayen idan ta, fitowa tayi mama gani, dan ubanki kina jina kika min shuru, "A'a mama na amsa wlh" okh wato dan ubanki ni nake karya kenan, A'a mama ba haka nace ba, kiyi hakuri, zo ki saka ma yayyin ki abinci, mai idan mujiya, mai tsuffan mayu kawai, tsaki taja ta nufi dakin ta, hawaye ne ya tsauko mata, hannu tasa ta share tana jan hancin, kitchen ta nufa ta dau kwano biyu ta dauriye, tuwo tasa sannan ta zuba miya a sama, dauka tayi ta nufi dakin mama da shi, sallama tayi a bakin kofa, aka amsa da shigo, shiga tayi ta ajiye kwano daya a gaban Sa'ade daya kuma a gaban lauratu, ta juya, har ta kai bakin kufa, taji muryan sa'ade taji tace uwarki ce zata kawo mana ruwa, girgiza kai Nasreen tayi alamun A'a, k ina miki magana kina daga min kai, A'a kiyi hakuri, fita tayi a dakin ta dibo mutsu ruwa ta kawo, fita tayi a dakin bayan ta ajiye, buta ta dauko ta nufi rijiya ta dibo ruwa ta zuba a buta, alwala tayi ta nufi dakin ta.................. 


COMMENT IS NEEDED 


BY GIMBIYA AYSHU. ❤❤❤📚📚📚


🎡🎡ZUBAR HAWAYE NA🎡🎡


❤❤❤LOVE AND DESTINY   STORY❤❤❤


Ladi tace"Bazaki taba Auren mai kudi ba sai talaka, talakan ma tukuf Wanda sai kun wahala zaku samu abinci" "yarana ne kawai zasu Auri mai kudi"


Matsiyaciya mai kama da mayya, yar tsintarciyar mage " Ba abinda Nasreen keyi banda hawaye"................. 


Sai dai abin da mama bata sani ba shine in Allah ya kaddara abu bawa bai isa ya chanja shi ba. 


Zuwan safwan rayuwan ta a matsayin dan talaka tukuf ya zeme mata Alkairi, dan ganin shi a haka da mama tayi ta zata ba dan kowa bane kuma ba komi ba face kaskan tance, talaka irin Wanda takesan Nasreen ta aura, ba batasan tayi kuskure ba ta kaita in da bataso............ 


Toh! Masu karatu ku biyo ni dan karanta wannan labarin. 


Duk zaku sami wannan littatafan daga taku Gimbiya Ayshu marubuciyar "LAILAH" and now "ZUBAR HAWAYE NA" a farashi mai tsauki dan jin dadin ku. 


Kada ku tsake a baku labari dan it gonna be like 🔥🔥🔥. Gamai buka tan littafan, the payment are as follow:


Daya:150

Biyu:250

Uku:350

Hudu:400

Biyar:500


In kina bukatan duka zaki biya daribiyar(500) ta wannan bankin:


Aisha Nura Murtala 

GT bank

Account number 

0623151889


Evidence of payment ta wannan number 

***


*NIHLAH

*IDAN ZUCIYA TAYI WAKE

*TUGGU BIYU

*ZUBAR HAWAYE NA

*MATA A YAU


Kar ku bari a baku labari, kuyi hanzarin siya dan ku nishadan tu. 


Ga matsu turo kati kuma sai ku turo ta wannan lanban 

***.


Karku manta zafafa ne sai kunzo ❤❤❤


Ga mai bukatan ZUBAR HAWAYE NA. Ga


Account name

Zainab Yahaya

Fcmb

Account number 

7410207015


Evidence of payment 

***


Ga mai bukatan NIHLAH. Ga Account number 

2215749011

Name 

Saratu kabir 

UBA Bank


Evidence of payment 

***


Ga mai bukatan MATA A YAU. Ga Account name

Hafsat Yahaya 

First Bank

Account number 

3140418863


Evidence 

***


Ga mai bukatan IDAN ZUCIYA TAYI WAKE. Ga

Account name

Halima Nuru Murtala

ECO Bank

Account number 

3090183528


Evidence 


***


Ga mai bukatan TUGGU BIYU. Ga

Account name

Aisha Idris Abdullahi

Wema Bank


Account number 

0241707861


Evidence 

*** 


Kuyi hanzarin tsiya insha Allah zakuji dadin littattafan kuma zaku wa'azan tu, nishadan tu da dai tsauran su........... 


Bye GIMBIYA AYSHU💞💞💞.