🌼🌼ZUBAR HAWAYE NA🌼🌼

Episode 9-10

by @gimbiyaayshu2503

🎡🎡ZUBAR HAWAYE NA🎡🎡


STORY AND WRITTEN BY 


AISHA MA'ARUF(GIMBIYA AYSHU) 


ELEGANT ONLINE WRITERS 📚


WHATPAD NAME 

*AISHAMAARUF*


📚📚PAID BOOK 📚 📚 


*FREE PAGE*



PAGE 5


__________________________ wani sallaya dayaga duniya ta dauko ta shinfida sannan ta dau wani kodaddan hijab ta saka, sallah ta tayar, tana cikin sallah taji mama na kwala mata kira, tsauri ta farayi dan ta idar, bayan miti daya ta fito a dakin ko hijabin bata cire ba, mama gani, mai kikeyi da baki amsa ni ba a!, "mama kiyi hakuri, wlh sallah nake san da kika kira ni, ko Addu'a Banyi ba na taso" salati mama ta rapka har sai da su sa'ade suka fito daga daiki. Mama lfy irin wannan salati haka, tayani ji fisabilillahi, wai ni wannan diyar zatace ma tana sallah san da nakira ta, kuma wani karin zunubin shine wai ko Addu'a bata yi ba ta fito, ni zata gwada wa Addu'a, yaushe ma ta iya sallah bare Addu'a, "tsaki Sa'ade da lauratu suka ja atare" lauratu tace "ni nazata wani abun kirki ne ya faru, toh! Bata kai Addu'a bane, kiga yarinya tafara kirgan dangi kice bata iya sallah ba bare, toh in bata iya ba yaushe zata iya, yarinyar da kila nan da shekara biyu wani zai dauke ta tunda babu abin da ta rasa, ga kyau, gashi, haske kaman ita tayi kanta, yarinya tun tana karama diri har ya fito mata I kinga ba'a magana" "wannan ko dan president takai tayi dai-dai dashi, class din manya kike gani, balle ma inta kara girma, I kofan gidan ku baza'a samu hanyyan wucewa ba, dan ma Allah yayi ta da kamun kaiiii! hmmmmmm!, kada kai tayi ta nufi cikin daki". 


Mama data tsake baki tana kallon tane tace"Amman Allah ya tsine miki lauratu, dan ubanki ni zaki ma wannan fatan, amman Allah tsine miki, lauratu kinci ubanki, tana fashewa da matsanancin kuka harda dukawa kasa. " toh! Meh! Abin kuka I naga dai gaskiya lauratu ta fada, in dai kyau ne da komai k ma dai kinsan ta fimu, in za'a ajeta da mu yanzu kafin a zabe mu sai mutane 30 sub zabe ta, takarasa tana shigewa daki. Mama ne ta kara fashewa da kuka tace" Amman ku kam anyi en iska wlh, wait har fada kuke ta fiku da abu, k kuma mai shegen baki harda cewa wai sai an zabe ta sau 30 kafin a zabe ku, toh! Zaku gani dan uban ku, toh! bazan yarda, shegu kawai, tana tashi daga kasa, ta nufi hanyan dakin ta, "mama gani" wani irin juyowa mama tayi tace kinci kutumar ubanki, dalla bace min da gani mayyah kawai, shegiya, "sim sim Nasreen raja kanta zuwa daki, daman ba yunwa taje jiba balle tace zata nemi abinci, tana shiga ta kulle kofan dakin ta, darduman data bari a shinfide ta daga ta linki shi, ta ijiye, hijabin jikinta ta cire ta linke, cire kayan jikin ta tayi ta daura dani sannan ta saka wani dan vest daya kode tayi hannu daya ma ya tsinke tasa wani yadi ta hada ta daure, hawa kan dan gadon ta tayi, Addu'a tayi kafin ta kwanta, baifi minti 5 ba barci ya dauke ta saboda a gajiye take. 


Mama na shiga daki taga su Sa'ade da laidan nama a gaba, wani miyau ta hadiye, ji kake makut tana sudan baki, share fuskan ta tayi da kyau tana kirkiro murmushi dole, ahhhh! Shine baku kira ni ba, da ban shigo ba fahhh! "Ahhhh! Bakin tsaya mastifa bahhhh! Je kicigaba dayi I, A'a ba mastifa nake bahh! Gaskiya na fada,"lauratu ne takusa kwarewa tace wani irin gaskiya, haba mama kiji tsoron Allah! Son zuciyar ki ya fara yawa fahhh! Kinsan duk abinda Allah ya kaddara sai ya faru"eyeeeee! Ni zaki gwada ma Allah, yaushe aka haife ki, wlh baki biyo halina ba, kodai chanja min k akayi, Sa'ade dake goyon baya na ma yanzu naga tafara karkata hanyya, toh! Wlh karyan ku bazaku zuba min katsa a ido bahhhh! Aheee!, suna cikin haka ne salmanu ya shigo ko sallama babu, su Sa'ade na ganin shi duk suka boye laidodin dake gaban su suna murmushin yake, kai daka gansu kasan basu da gaskiya. Kanshin mai nakeji haka,Sa'ade ne tayi karap tace "wlh kaza mukaci,tana dunkule wani laida, sai wani kumbura hancin take ta busa shi" marowatan banza kawai shine ko ku rage min, tabe baki kawai Lauratu tayi tana juya kanta, tawani aza kafa daya kan daya tana karka ta shi, toh! Naga kai baka dawowa da wuri ne shiyasa , cewar Sa'ade. Wani wawan tsaki yaja sannan ya bar dakin. Yana fita Sa'ade ta tashi da hanzari ta kulle kofan harda zira makulli ta ciki. Shegu kawai I nasan karya kuke baku cinye ba, karuwan banza kawai en iska, ya karashe maganan yana fita a gidan. Ko kula shi Sa'ade batayi ba ta nufi wurin data boye laidan kazanta, zama tati ta gwale kafa, irin zaman en bori, tissue da aka da a ciki ta dauko, Wanda idan ka gama ci zaka share baki da shi, daukan cinya daya da hakarkari biyu tayi tasa mata, toh! Mama gashi sai a kore kwadayi, kamar mayya haka mama ta mataso ta amshi Kazan har tuntube take wurin amsa. Lauratu ma ta emmata acikin nata. Bayan sun gama party su, suka fita da laidodin Kazan da abubuwa da suka sha. Wanke hannuwan su sukayi Sa'ade takoma ciki Lauratu ko ta shige bayi, bayan ta fito ta shiga daki ta kulle kofa. 


Ba salmanu ya shigo gidan ba sai karfe 1:30 na dare, shima da kyar ya shigo yana tangal tangal, kai da ganin shi kasan yayi mankas. Yana shiga dakin shi ya zube a kasa wurin sai barci. 



Wani hadadan tsaurayi naga yana tsaukowa daga saman bene sai kira mummy yake, mummy dake kitchen tare da masu aiki ne ta leco tace ya akayi ne Arif irin wannan kiran haka " mommy wallet dina nake nema ban gani ba kuma nasan na dawo dashi gida, dan dana fito a mota yana hannu na, yanzu kuma nazo zan dauka ban gani ba, ya karasa yana turo baki irrin na sangartattun yaran nan, dungure mishi kai tayi, kaban ajiya ne?" A'a mommy tanbayan ki nake ko kin gani, yana marmar da ido. "Jiya ka yar dashi, nima dana tsauko ne nagani, je ka duba drawer na yana ciki" tsauke ajiyan zuciya yayi ya rungumi mommy yace " thank u mommy na naji tsoro wlh, nazata zakice min baki gani ba ya karasa yana tsakin mata peck a goshi tare da cewa luv u mom, tsakin ta yayi ya nufi up stairs zuwa dakin mummy"girgiza kai mummy ta yi tana murmushi sannan ta koma kitchen ta cigaba da abinda take. Tsaukowa yayi hannun shi daya rike da wani dan jaka mai bala'in kyau, dayan kuma rike da coat. Tsaukowa yake da tsauri dan ya kutsa makara. Mummy na wuce ya fada yana nufan hanyyan fita daga parlorn. Toh! Son Allah ya tsare ya kiyaye, kabi a hankali banda gudu kaji kohhh! Toh! Mummy insha Allah bazan yi ba, bye luv u sai na dawo,ki dafa mun best food dina mummy. A'a nikam rashida zata dafa ma. Tabdi bazan ci ba kenan. Dariya mummy ta yi tace karka tafi ka biye min babu ruwana in dad dinka yama fada. I baze min komi ba ni da nake oga, I sai sanda naga dama zan tafi"Ahhhh! Koh! Toh! Jira ka tsaya surutu, sai in kira dad in gaya mishi, kai! kaman ta kuna da meeting kohhh! " salati Arif yayi yace na shiga tara, wlh mummy na manta, dole kice dad zaimin fada ashe kina tsane, nikam na tafi ya karasa maganan yana bude kofan parlor" Toh! Allah kara yaya hanyya a kula, da Ameen ya amsa, ya nufi parking space da tsaurin shi. Wasu guard ne su biyar suka taso, oga ina kwana, da lfy lau ya amsa musu ya tan baye su ya suke. Daya saga cikin sine yace oga kawo mukullin, A'a ka barshi karka damu, shiga motan shi yayi ya bashi wuta, dama tun fitowan shi mai gadi ya bude mai gate. A hanyyan shi na zuwa ne ya hadu da go slow a ta wurin kasuwa, wani mota ne yayi hatsari,kuma ya riga ya shiga ciki balle ya chanja hanyya, wayan shine ya fara ruri, yana jin ringing tone din yasan waye ya kira shi, dauka yayi yayi sallama, dad ya amsa mai acikin wata kamilalliyar murya, gaishe shi Arid yayi, dad ya amda mai yana cewa " son ina ka tsaya ne kasan munada meeting yau koh! "Ehhhh! Dad, wlh yanzu haka ma ina hanyya, anyi hatsari ne a ta wurin kasuwa, so ba hanyya, amman ana clearing wurin, ya karasa yana dago kan shi, idan shi bai tsauka a ko ina ba sai akan wannan yarinyar da ya gani ranan, kallon ta yake yama manta cewa yana waya ne, dad yai ta magana yaji shiru ba sa amsa, sai da ya kira shi dadan ihu "Safwaaaaaaaaaaaaaaaan" firgigit Arid yayi yace" Na'am dad inajin ka, tunanin mai kakeyi son ehhh!, A'a dad ba tunani nake ba, toh! Mai kake yi ummm babu komi, okh! Tunda kace haka ya hanyyan yanzu, ehhh! Ya fara dan Washe wa nan da minti 30 zan karaso insha Allah, "toh! Allah kawo ka lfy" Ameen Ameeen dad. Kashe wayan dad yayi, tsauke wayan shi yayi da tsauri yana maida direction dinshi zuwa inda ya ganta dazu, amman bai ganta ba kalle kalle ya fara yi chan ya hango ta ta fito daga wani shago, kallon ta yake har ta karaso wurin tiren abincin ta, dai-dai nan aka bude hanyyan, key yayi ma motan shi yana kallon ta yana tuki har ya bar ganin ta. 


Karfe 9:00 dai-dai yayi parking a gaban wani babban company mai sunan "Safwan Textile", fita yayi daga motan shi ya nufi liftan dazai sada shi da office din shi kai tsaye, yana shiga office din direct wurin laptop din shi ya nufa ya zauna P.A din shi ya kira yasa ya kawo mai schedule din shi, baifi minti 3 sai gashi ya iso, knocking yayi, ya bashi izinin shiga, shiga yayi da sallama, Arif ya amsa mai, gud mrng boss, " mrng hw u" am fyn sir, "GM nanan" yes sir yana nan, "okh! Toh! Sai anjima" fita P.A yayi a office din, duba schedule din tayi, bayan ya gama ya tashi rike da wayan shi a hannu ya fita daga office din shi, liftan dazai sada shi da office din dad ya hau, baifi minti 5 ba yakai, finger dinshi yayi anfani da ya bude kofan sannan ya shiga da sallama, samun dad yayi yaba ma kofan baya, "dad najin muryan shi ya juyo yana amsa sallaman" "masha Allah, kana ganin Arif kaga dad kaman yayi kaki, suna tsananin kama, babancin kawai shine dad ya dab tsufa" har ka iso son " ehhh! Dad nayi minti 10 da shigowa company ma" okh! Dad yace yana duba agogon hannun shi, tsaura minti 20 a fara meeting, inda abinda zaka dauka je ka dauko kazo, juyawa yayi ya nufi bakin kofa, muryan dad yaji yana cewa kazo da laptop dinka, "toh"dad yana fita daga office din.................... 


COMMENT IS NEEDED 


BY GIMBIYA AYSHU❤❤❤📚📚📚.