๐ŸŒผ๐ŸŒผZUBAR HAWAYE NA๐ŸŒผ๐ŸŒผ

Episode 21-22

by @gimbiyaayshu2503

๐ŸŒผ๐ŸŒผZUBAR HAWAYE NA๐ŸŒผ๐ŸŒผ


STORY AND WRITTEN BY



GIMBIYA AYSHU ๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž



ELEGANT ONLINE WRITER'S ๐Ÿ“š๐Ÿ“š๐Ÿ“š




PAGE 10



__________________________Meeting din aka Fara ba Bata lokaci,basu suka fito a meeting ba sai karfe hudu,gaisawa duk sukayi aka rabu lfy,daganan masallaci Mafi kusa suka nufa,bayan duk sunyi sallah suka Kama hanyyan company,karfe 4:37 suka Isa company,ko da Arif ya Isa bai zarce ko Ina ba sai Office din daddy,shiga yayi da sallama, bayan ya gaishe da daddy ya fayyace mishi Yanda akayi a gurin meeting,bayan ya gama bayani,suka Dan tattauna da daddy sannan ya nufi office din shi,Yana shiga ya rataya coat din shi akan kujera,dakin dake cikin office dinshi ya shiga,dakin ya tsaru komi na cikin dakin blue ne da fari,royal bed ne a dakin yasha gyara da bed sheet Mai taushi,cire kayan shi yayi ya nufi bayi,bayan kaman minti 20 ya fito daure da bath rope fari Kal,da wani Dan karamin towel a hannun shi Yana share gashin kanshi da shi,hand dryer ya dauko ya busar da kashi, ya gyara,Bayan ya Gama ya shafa mayukan shi masu tsada,Tulare ya dauka ya feshe jikin shi da shi, drawer ya nufa ya dauko wani kananan Kaya farin riga Mai guntun hannu da wandon jeans navy blue,Tulare ya dauka ya fesa bayan ya Gama shiryawa,kallan kanshi ya yi a madubi, murmushi yayi sannan ya juya ya fita daga dakin.




12:00 Nasreen ta shigo gida bakin ta dauke da sallama,mama ta iske a tsakar gida da Anty lauratu suna girki,gaishe su tayi,Suka amsa,Anty lauratu ne tace sannu da zuwa,yau kin dawo da wuri,Masha Allah, murmushi kawai Nasreen tayi tana Mika ma mama kudin hannun ta,kwace kudin mama tayi tana hararan Nasreen,dauke Kai Nasreen tayi ta nufi inda ake ajiye kwanoni ta ijiye tiran.Buta ta dauka ta wuce bayi Bayan ta fito ta zo takama musu aiki.Da musalin karfe 12 da minti 55 Suka kammala girki,Anty lauratu tasa ma kowa nashi na baba Kuma akasa a cikin cooler. Tashi duk sukayi sukayi Alwala mama ko daki ta nufa Dan ita sai taga dama take sallan,bayan sun idar da sallah sukaci abince,tattara kwanon Nasreen tayi ta nufi waje,ruwan wanke wanke a hada ta fara,fitowa Anty lauratu tayi ta Fara tayata,sunayi suna Hira har suka Gama,bayan sun kammala wanke wanken Nasreen ta share tsakar gidan tas ta gyara ko Ina.


Tun da Nasreen ta kammala Aikin gida ta kwanta barci ba ita ta tashi ba sai karfe 4:30,tana farkawa ta duba lokaci,tana ganin time ta mike da tsauri da Addu'a a bakin ta,fita tayi ta saka ruwa a buta bayan ta fito tayi Alwala ta Yi sallah,bayan ta idar da sallah tayi Addu'a ta yima Ammin ta ma Addu'a,bayan ta kammala,ta cire hijabin ta sannan ta fita sakar gida inda ta tadda Anty lauratu na gyara wutan da za'a daura sanwa,tayata Nasreen tayi sukayi girkin,da misalin 6 saura suka kammala,tuwan masara da miyan kubewa bushashe sukayi,raba abincin sukayi yanda aka saba.


Cikin dare da misalin karfe 2 da minti 36 na dare Anty lauratu ta farka a firgice, bakin ta dauke da Addu'a,ta hada uban zufa sai zare Ido take,jikinta na rawa,ta Kai minti 10,a haka kafin tadan Fara samun natsuwa,juyawa tayi ta kalli Nasreen hawaye na tsauka daga idanta,shafa kanta tayi tayi Mata Addu'oi sannan ta shafa Mata,ba ita ta koma barci ba sai karfe 3 da minti 15,tana kwantawa barci Mai nauyi ya dauketa.......


Nasreen ce ta Fara tashi da Addu'a a bakinta Mirza idan ta tayi ta kalli a gogo taga karfe 5 da minti 15,Kiran sunan Antyn ta tayi Amman Bata amsa ba,hannu tasa ta jijjigata tana Kiran sunan ta,sai data yi mata hakan sau uku kafin ta iya tashi,tashi tayi tasa hannu biyu ta rike kanta da shi tana Addu'a,dago kanta tayi ta kalli Nasreen,sai mafarkin da tayi ya Fara dawo Mata,saurin kawar da mafarkin daga zuciyar ta tayi tana Addu'an naiman tsari, Nasreen ce ta katse Mata tunanin da take da fadin "Anty lauratu Mai ke damun ki kanki na ciwo ne, girgiza Mata Kai Anty lauratu tayi alamun ehhhhhh! Langwabe Kai Nasreen tayi kaman zata zubda hawaye tace sannu kinji Antyna, murmushi Mai Hadi da Hawaye Anty lauratu tayi ta rungume Nasreen tana kuka kasa kasa,Hawaye ne ya sauko daga idan Nasreen,tace"Baki da lafiya ne,Mai yasa kike kuka,nayi Miki wani Abu ne,in nice Dan Allah kiyi hakuri ki yafe min ta fada tana fashewa da kuka" cire ta Anty lauratu tayi daga jikin ta a rikice tace Dan Allah kibar kuka bakimin komi ba,kawai dai kaina ne ke ciwo,Amman Babu komi Bayan haka ta karasa tana share hawayen dake idan Nasreen,sannan tace "Baki taba min laifi ba kanwata,illa taimakon da Kika ma rayuwa ta,zuwan ki rayuwa ta Alkairi ne kuma babban ni'ima ce nagode ma Allah daya hadani dake,ta fada tana murmushi" murmushi Nasreen tayi har fararan hakoranta Suka bayyana, rungume juna sukayi suna murmushi da Hawaye,"itako Anty lauratu zuciyar ta sai suya yake,ba abinda take tunani kaman mafarkin da tayi, Addu'a take Kar Allah ya tabbatar da mafarkin da tayi"Basu suka saki juna ba sai da wayan Anty lauratu tayi Kara,tashi sukayi Suka nufi waje inda Nasreen tafara shiga bayi bayan ta fito Anty lauratu ta shiga,Bayan sun idar suka Fara aikin yau da kullum,"inda Sabo yaci ace sun Saba"Basu suka Gama aikin gidan ba sai karfe 9:20,shiryawa Nasreen tayi Dan ta wuce talla,bayan ta Gama shiri harta dau tiran a Kai ta Kai bakin kofa,Anty lauratu tayi saurin tare ta,tace tayi Addu'a Bayan tayi tabata wani ruwan Addu'an Tasha,sallama sukayi sannan ta wuce, tsayawa Anty lauratu tayi a zaure tana kallan ta har ta bace ma ganin ta,komawa ciki tayi jikin ta a sanyaye.



Wurin karfe 6 da minti 50 Nasreen ta shigo da tiren abinci,ta siyar Amman saura guda daya kawai,tana shiga taci Karo da mama a sakar gida,gabanta ko sai faduwa yake Dan ta manta Rabon da taci duka,Mika ma mama kudin tayi ta kirga,sannan tace saura kudin daya,zare Ido Nasreen ta farayi sannan tace ban siyar bane,kallan ta mama tayi a kaikaice tana mikewa tsaye tace bangane Baki siyar ba,ja da Baya Nasreen ta Fara yi,tana girgiza Kai,janyota mama tayi ta wanka Mata Mari dama da hagu sannan tace banace karki Kara dawomin da kwante ba, "da ehhhhhh! Nasreen ta amsa murtan ta na rawa", Riko ta mama tayi zata Fara duka Anty lauratu tayi saurin rike hannun mama tana rokon ta,mama tace Zaki sake min hannu ko sai naci ubanki,kin saki Lauratu tayi illa cigaba da rokon da tayi,hankada ta mama tayi ta fada gefe ta bugu da bokitin karfe,Kara ta saki Mai razanarwa,Wanda ya firgita mama da Nasreen,sakin Nasreen mama tayi da sauri,dukawa duk sukayi inda lauratu ke kwance bayan tayi ihu,jijjigata mama take tana ihun sunan ta,Amman shiru kakeji ko alaman motsi,fita mama tayi da gudu ta nufi wajen gida inda Nasreen ta cigaba da jijjigata tana kuka,dawowa mama tayi da makota Mata biyu sai Namiji daya,wani matashi ne ya shigo yace ga Mai adedeta nasamo,mama ne tace asata ciki,daki ta nufa da gudu ta bincika duk inda tasan tana ajiye kudi,ta kwaso tare da daukan gyalen ta dake rataye a kan kofa.


Basu zarce ko Ina ba sai wani Dan karamin Asibiti dake Dan gaba da kwayen su,da sauri aka amshe ta aka Fara Bata taimakon gaggawa,bayan kaman minti 30 doctor ya fito Yana share zufa, " yace wacece mahaifiyar ta" da sauri mama tace nice,"wato patient din ta bugu sossai a kugun ta da Kai Amman da sauki mun shawo kan abin sai dai mu Bari inta Farfado muga yanda abin zai kasance" Yana Gama bayanin shi ya Kara gaba.........






Ba Lauratu ta Farfado ba sai washe gari da misalin karfe 4 da minti 50 na yamma, "bude idan ta da yayi Mata nauyi sossai ta Fara Yi a hankali har ta Dan bude shi kadan,sunan Nasreen ta Fara ambata tace"Nasreen Ina kike,ya naji jiki na yayi nauyi,kara tasaki da Dan karfi a sakamako juyawan da zatayi, Nasreen ce tayi saurin tashi ta matso inda take tace Anty lauratu ya jikin ki,karki motsa da yawa kiyi a hankali kinji,girgiza Kai Lauratu tayi hawayen a zuba daga idan ta. Nasreen ce ta Miki ta nufi wurin Dan karamin flask din su ta zuba ruwan zafi a cup ta hada Mata tea Mai kauri,rikewa tayi a hannu ta dinga fifita shayin,har shayin yayi Santi yanda za'a iya Sha,ajiye cup din tayi ta nufi wurin ta ta saka Mata pillow a baya ta gyara Mata Zama da kyau yanda zata jidadin Zama,juyar da kanta tayi sukayi Ido hudu da mama,wani irin harara mama ta auna mata,saukar da idan ta Lauratu tayi sannan ta bude Baki a hankali tace Ina kwanan mama,shiru mama tayi Bata amsa ba sai da Lauratu ta maimaita har sau uku kafin ta amsa ciki ciki kaman an Mata dole,sannan tace ya jiki ta na hura hanci,amsawa Lauratu tayi da da sauki hawaye na fita daga idan ta,daukan cup din shayin tayi ta nufi wurin ta ta zauna a gefen gado sannan ta Fara Bata shayi a Baki kadan kadan,"mama ne taja wani dogon tsaki sannan tace karere kawai,bude kofan tayi ta fita rai a bace,binta da Ido duk su kayi,babu Wanda ya furta wani kalma a cikin su,ta Sha shayin sossai Dan yafi Rabin cup,Lauratu ce tace zatayi sallah, "Nasreen tace Zaki iya" Anty lauratu ta amsa da ehhhhh! Insha Allah,riketa Nasreen tayj ta sauko daga kan gado,sayawa Nasreen tayi ta Dan huta kafin su nufi bayi,tana mikewa sai ga nurse ta turo kofa,da sauri nurse din tace ya haka,Mai yasa ta tashi,Nasreen ce tace cewa tayi zatayi sallah shine nace zata iya tace min ehhh! Shine na rikota Dan na Kai ta bayi,kallan ta Nurse din tayi tace Zaki iya kuwa,daga Mata Kai Anty lauratu tati alamun ehhhhh! Riketa nurse din tayi tace ma Nasreen ta gyara inda zatayi sallah,da toh Nasreen ta amsa,bayan sun fito ta kaita har wurin da aka gyara mata Dan tayi sallah,hijabi ta amsa a wurin Nasreen ta saka,a zaune tayi sallan,sai da ta Rama duka sallolin da ake binta,bayan ta idar tayi Addu'oi ta shafa, Nasreen ce ta taimaka Mata ta kaita gado.


    


       BAYAN SATI DAYA


Jikin Anty lauratu yayi sauki sossai, Doctor ne ya shigo yace masha Allah jikin patient da sauki,wani takarda ya Mika ma mama yace ga shi na sallama ne zaku iya tafiya gida Allah ya Kara sauki,Yana Gama fada ya fita daga dakin,amsa mama tayi ko uffan bata ce ba, Nasreen ne ta Fara tattara kayan su wuri daya,fita tayi ta tari Mai napep sannan ta dawo ta kwashe kayan ta Kai cikin napep sannan ta dawo ta rike Anty lauratu ta fita da ita waje,shiga duk sukayi suka wuce gida.Ruwan wanka Nasreen ta daura musu a wuta,bayan yayi zafi ta hada ta Kai Mata bayi,Bayan ta Kai ta zo ta sanar mata.tattara gidan tayi ta gyara ko Ina Bayan ta Gama ta shiga wanka,Bayan ta fito ta shafa Mai ta shirya,bayan ta Gama shiri ta fita ta dauko abincin su.




       BAYAN SATI DAYA 


Shiri Nasreen take tana hira da Antyn ta Mai debe Mata kewa,Mama ne ta kwala Mata Kira tare dacewa Mai kikeyi a daki da bazaki fito ki wuce ba,saurin zura rigan Nasreen tayi ta dau hijab ta saka,fita sukayi tare da Anty lauratu ta rakata har kofan gida,tasata tayi Addu'a kafin ta wuce,ba ita ta bar kofan gidan ba har sai da Nasreen ta bace ma ganin ta............................





COMMENT AND SHARE


BY GIMBIYA AYSHU ๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž.