🌼🌼ZUBAR HAWAYE NA🌼🌼

Episode 25-26

by @gimbiyaayshu2503

🌼🌼ZUBAR HAWAYE NA 🌼🌼


STORY AND WRITTEN BY


GIMBIYA AYSHU 💞💞💞


ELEGANT ONLINE WRITER'S 📚


WHATPAD NAME AISHAMAARUF

FACEBOOK NAME AYEESHA ASHRAF MUHAMMAD

FACEBOOK PAGE HAUSA NOVEL BY GIMBIYA AYSHU

FACEBOOK GROUP HAISA NOVEL BY GIMBIYA AYSHU.

AREWABOOKS 2503.


GA MASU ACCOUNT A WA'INNAN WURIN DANA LISSAFA DAN ALLAH SUYI FOLLOWING DINA.


PAIDBOOK

FREE PAGE


PAGE 12/13


____________________________Haka Suka cigaba da Zama har aka Kira sallan magariba Bata Farfado ba, Daddy ne ya mike Suka fice masallaci tare da Arif,Basu suka dawo ba sai karfe 8 da minti 50,hannun Arif rike da laida biyu en madaidaita,shiga dakin sukayi da sallama,Zama duk sukayi,Arif ya gaishe da mummy sannan yayi Mata sannu da Zama,gaishe da Daddy mummy tayi tamai sannu da zuwa, Daddy ne yace "Yauwa sannu da tsayawa da daughter mu" kallan shi mummy tayi da murmushi a fuskan ta,"murmushi Daddy yayi Dan yasan taji Dadi ko Bata fito ta gayamai ba,ko Mai ya tuna!sai kawai ya girgiza Kai,"Kallan su Arif kawai yake Yana murna Amman fa a zuciyar shi, a fuskan shi ko kadahan kadaham,haka dai suka cigaba da hiran su gwanin ban sha'awa,sai wurin karfe 11 su Daddy Suka tafi,yayi yayi mummy tabi shi Amman Taki wai zata zauna da ita tunda doctor yace zuwa dare zata tashi,haka dai Daddy ya hakura ya barta Suka tafi da Arif."A bangaren Arif ko bai so ba Dan yaso ace ya kwana tare da ita a Asibiti,haka dai ya hakura yabi Daddy shi tunda dai mummy tace ba zata bishi ba".


Zaune mummy take Akan sallaya da misalin karfe daya da minti Sha biyar '15'bayan ta Gama Addu'oin da take ta mike ta linke darduman,ta ajiye shi akan Dan table din dake dakin,matsowa tayi zata shafama Nasreen Addu'oin da tayi,sai taga Kam an ta motsa,tsayawa tayi Dan taga ko dai idan tane ke Mata gizo,har ta cire rai sai Kuma taga ta miss idan ta tare da motsi da Hannun ta, murmushi Mai hadi da Hawaye mummy tayi ta fita daga dakin sauri sauri gudu gudu, office din doctor ta nufa ta sanar mishi da tana motsi,tashi yayi da sauri tare da daukan stethoscope ya Mara ma mummy baya har dakin,duba ta ya farayi sannan ya Yi Mata abin da ya kamata,ya duba duka vital signs tare da yi Mata physical examination,Alhmd komai lafiya sai dai yanzu abin da ya rage shine mu tabbatar da lafiyan kwakwalwan ta,juyawa yayi Yana kallan Nasreen,karasowa mummy tayi tana kallan su,daga Mata hannu yayi yace ykk baby,sannan yace Mai sunan ki,kallan shi tasaya yi,takai sawon minti 3 tana kallan shi kafin ta bude Baki a hankali tace sunana,kallan juna sukayi da doctor da mummy,kallan ta ya Kuma yi yace Mai sunanki baby girl,kallan shi tayi batace komi ba,harsun cire Rai da amsan ta sai su kaji tace "Nasreen" daga nan Bata Kuma cewa komai ba,kallan mummy doctor yayi yace tasamu memory lost Amman zata iya recover in taga wani data sani ko Kuma Kara a kusa da kwakwalwan ta,shawaran Yan da za'ayi doctor ya Bata sannan ya fita daga office din,karasowa mummy tayi kusa da ita ta zauna gefen gado tace baby ykk,kallan mummy ta sayayi Dan Bata taba ganin fuskan taba,chan tace lafiya Lau Ammi, murmushi mummy tayi hawaye na zuba a idan ta,shafa kan ta mummy tayi tace Allah yayi Miki Albarka babyna, murmushi Nasreen tayi har wushiryar ta ya fito,tashi zatayi mummy ta Yi saurin mikewa ta rike ta,dagata tayi tasa pillow a bayan ta tagyara Mata Zama da kyau,wurin flask mummy ta nufa ta hada Mata tea Mai kauri ta dauko da bread,fifita shayin take suna Dan Hira da mummy har shayin ya Dan huce,diba ta farayi da spoon tana Bata a Baki,diban bread tayi takai Mata Baki Amman Nasreen Taki Amsa,tea kawai Tasha Rabin cup sannan ta kawar da Kai alamum ta koshi,Zanyu fitsari Ammi,tashi mummy tayi ta cire Mata drip sannan ta rikota har bayi ta sata fitsari bayan ta gama tayi Mata sarki tayi Alwala Suka dawo daki,darduma mummy ta shinfida Mata tasa tayi sallan a zaune,sallan take a natse kaman wata babba,Bayan ta idar tayi Addu'a ta tashi a kan darduman,mummy ne ta rike ta ta Kai ta har kan gado ta kwantar da ita,tace kiyi barci kinji dare yayi,girgiza Kai Nasreen tayi,ta kulle idan ta,kallan ta mummy tasaya yi har na tsawon minti 15,da mama taji dai Bata Kuma motsi ba har na tsawon wannan lokacin sai ta tashi ta nufi kushin din dake dakin ta kwanta tana kallan Nasreen,tunanin zuci ta farayi har barci yayi awon gaba da ita,da misalin karfe 5:00 dai-dai Nasreen ta farka,mikewa tayi ta jingina da gado,kallan dakin ta farayi,chan idan ta ya Kai kan mummy,ta shi tayi a hankali ta nufi inda mummy take sugun nawa tayi tace Ammi Ammi,amsawa mummy tayi da na'am little kin tashi, da ehhh"Nasreen ta Amsa tace,lokacin sallah yayi,bude Ido mummy tayi tana kallan ta da mamaki yarinya karama Amman ta iya ta shi sallah,mikewa mama tayi ta rike hannun ta suka nufi bayi bayan Nasreen tayi fitsari da Alwala ta fito, mummy ma tayi nata ko da ta fito Nasreen ta sallame,bayan an tada sallah ta mike tayi sallan Asuba,bayan ta idar tayi Addu'a ta shafa,juyawa tayi ta kalli mummy tace Ina kwana Ammi, murmushi mummy tayi sossai har hakoran ta na lobawa tace lafiya Lau little Dina ykk,lafiya Lau Ammi,tashi Nasreen tayi ta nufi kan gadon ta kwanta,tana kallan mummy har ta kulle idan ta,tashi mummy tayi ta nufi inda Nasreen take ta gyara Mata kwanciya,komawa tayi kan kujera,tana ta kallan Nasreen.


Da misalin karfe 10 su Daddy Suka Isa Asibiti,ko da Suka shiga dakin samun Nasreen sukayi zaune akan gado itada mummy,juyowa sukayi suna kallan Wanda ya shigo,kallan su kawai Nasreen take Dan Bata San su ba,shiga su kayi Arif ya gida mummy,mummy ta gaida Daddy,Gaishe su tayi muryan ta a sanyaye,amsawa Daddy yayi da fara'a a fuskan shi,yace ya jikin ki baby girl,da lafiya Lau ta amsa,Arif ko Daddy kaman ya kashe shi da yaga ta farka,Amman yanda yaji tana magana yaga alamun ta Dan samu masala, Daddy ne ya nufi office din doctor,shiga bayi mummy tayi,ya rage daga Arif sai Nasreen a dakin,matsowa yayi ya kalle ta,yace Hy Angel,dago idanuwan ta tayi ta kalle shi,"Angel y silent," sunana Nasreen ba Angel ba,"yace kin sanni," kallan cikin idan shi tayi na tsawon minti 5 'biyar' kafin ta girgiza Kai alamun a'a bata San shi ba,girgiza Kai yayi Yana jimamin abun,Kara matsowa yayi yace,kinsan hanyyan gidan ku,kallan sama tayi tana tunani,chan tace gidan muuuu!, ban sani ba, "ajiyan zu ciya Arif ya sauke Yana kallan ta,yace Ni yayan ki ne kinji sunana Arif,ki dinga ce min Yaya Arif",daga Kai tayi kaman wata kadangare,Hira suke mumy ta fito daga bayi darduma ta shin fida tayi sallan walha,tana idarwa Daddy na shigowa daki,Zama daddy yayi yayi ma mummy bayanin abin da doctor yace,"Arif najin su Kuma uffan baice ba," "Daddy ne yace Bari na tanbaye ta muga ko tasan gidan su if she could be able to remember their house then she could recover her brain in not less than a week" 'girgiza Kai kawai mummy take alamun haka ne,Amman a zuciyar ta batasan ta rabu da yarinyar sai dai ya zatayi tun da ba nata bane Laura ne ya hada su,' "Daddy ne ya tashi ya nufi gadon da Nasreen take yace baby,dago Kai Nasreen tayi tace Ina kwanan Abba, murmushi Daddy yayi yasa hannu Yana shafa kan Nasreen ya amsa da lafiya Lau ya kike diyata"lafiya Lau Abba,Hira Suka Fara Yi da Daddy cikin Hira Daddy ya tanbaye ta ko tasan gidan su,yasa data tasa a Baki tana tunani,chan tayi saurin cewa I gidan mu daya Abba kasan gidan mu i,ga Yaya ba ga Ammi na,girgiza Kai kawai Daddy yayi a zuciyar shi yace,Ya Allah ka bamu ikon samun iyayen yarinyar nan da wuri" Ameeeen,Hira suka cigaba dayi tare da Nasreen gwanin ban sha'awa,ta saki jiki dasu sossai.............


BAYAN KWANA BIYAR


Nasreen ce zaune akan gado da misalin karfe 2 'biyu' na rana suna Hira da Ammin ta,"Arif ne ya turo kofa hannun shi rike da takarda,zuwa yayi ya Mika ma mummy yace mummy na doctor yace zamu iya tafiya gida ya sallame mu tunda patient ta warke sossai,sai dai a kiyaye Abu Mai Kara a kusa da brain dinta, wato ' kwakwalwan ta',saboda in aka samu Kara daya affecting brain dinta zai iya sa tayi loosing memory again ko Kuma tayi regaining memory din ta daya cikin biyu,shiyasa doctor yace a bi a hankali da ita,yanzu the best thing is ba'a San Kara,"' girgiza Kai mummy tayi tana jinjina abun' Fara tattara kayan su Arif yayi,Yana kaiwa cikin mota,mummy ko ta gyara Nasreen ta saka Mata hijab,rike Mata hannu tayi ta saukar da ita daga kan gado ta gyara gadan,"Arif ne yace Angel zo muje",turo Baki tayi tace zanbi Ammi,daga Kai yayi Suka hada Ido da Ammi,saukar da nashi idan yayi da sauri ya juya zai fita sai yaji muryar mummy tace ' ki bishi little',Nasreen najin Abinda mummy tace batayi musu ba ta bishi Suka fita daga dakin, mota Suka nufa,bude booth yayi yasaka kayan dake hannun shi sannan ya zagayo ya bude mata back seat ta zauna Shima ya zauna Hira Suka farayi abin su Dan sun shaku a en kwanakin Nan sai dai sun cika fada Abu kadan ke hada su,suna cikin hiran ne ya hango mummy ta doso su,fita yayi ya kulle kofan ya koma driver seat,bude ma mummy kofa yayi ta ciki ta shiga ta kulle.key yayi ma motan ya jata sai gida.


Suna Isa gida mummy ta bude kofa ta fita baya ta bude ta riko hannun Nasreen ta fito da ita,rike ta tayi Suka shige cikin gida Nasreen ko sai surutu take ma mummy,abin nasa mummy farincikin da nishadi sossai,Mai aiki ne ta bude musu parlor door,dukawa tayi ta gaishe da mummy,amsawa mummy tayi da kulawa tace ya gida da Alhmd ta amsa,gaishe da Mai aikin mai suna 'salame' Nasreen tayi,amsawa salame tayi da murmushi a fuskan ta,amsan jakan hannun mummy tayi ta raka ta da shi har daki,umurni mummy ta Bata akan ta haÉ—a ma Nasreen ruwan wanka mai zafi bayan ta gama haÉ—awa ta fito,fita tayi daga dakin ta nufi kitchen,bayin mama ta shiga ta duba ruwan sannan ta zuba mata ruwan Tulare a ciki,bayan ta gama drawer ta nufa ta dau sabon towel ta ba ma Nasreen,amsa Nasreen tayi ta tube ta daura towel din sannan ta shiga bayi,bayan ta fito mummy ta Bata mayukan ta ta shafa,ta bata wani dogon riga ready maid Mai kyau kalan ja da digon stone a jikin shi,sai singlet da pant da legis,amsa tayi,tayi godiya ta saka," murmushi kawai mummy take Dan tanasan taga farin cikin Nasreen,"wani lokacin har mamakin don da take ma yarinyar take",bayan ta gama mummy ta saka mata kwalli da kanta,Nasreen na ta bari ta iya Amman mummy Taki,haka Nasreen ta hakura dan ba yanda ta iya da mummy,bayan mummy ta saka mata ta feshe ta da tulare,sannan ta bata hijab ta saka,"kallan mummy tayi bayan tasa hijabi tace Amma bayi kyau",daga mata Hira mummy tayi tace unnnnn!my little kinyi kyau sosai kina kama daaaaa.........sai tayi shiru ta kasa karasawa,"zauna ki Kur'ani bari nayi wanka na fito,"da toh! Amma Nasreen ta amsa",mika mata waya mummy tayi ta shige bayi, bayan ta fito ta shafa mai ta shafa humra ta saka wani dogon riga na antanfa mai tsada,kwalli kawai tasa bancin shi bata shafa komi a fuskan ta ba,daukan gyalan da zai shiga da kayan jikin ta tayi sannan ta dau hand bag dinta wani dan locker ta bude ta dau Atm ta kulle,wurin takalma ta nufa tasaka wanda zai shiga kayan,wani ka'ida ta bude ta fito ma Nasreen takalmi ta bata taska,fita sukayi daga dakin,dining Suka nufa suka ci Abinci,suna cikin ci sai ga Arif ya shigo da sallama,amsawa sukayi,karasowa dining din yayi ya gaida mummy,amsa mishi tayi da fara'a tace ya gajiya da hidima,"dan dariya yayi yace haba mummy u duty nane"murmushi mummy tayi tace Allah yayi maka Albarka son,"turo maiki Nasreen tayi tace Ni ba'ayi min ba,dariya duk sukayi munmy tace mai za'ayi miki,turo baki ta karayi tace Allah ya maka Albarka kuma Amin,dariya duk sukayi "Arif ko harda kyakyatawa",hada rai Nasreen tayi dan asan da gaske take,'da mama taga ta kara hada fuska shine ta bar dariya takara lallashin ta sannan tasa mata Albarka,bayan sun gama,mummy ta tashi tana yaga gyalan ta,"Arif ne yace mummy fita zakiyi ne?"da ehhh! Don mummy ta amsa tana mai cigaba da abinda take,muje toh! mummy tunda ba abinda zanyi,toh!muje inka shirya,"i Ni a shirye nake kawai muje"murmushi mummu tayi ta riko hannun Nasreen suka fita daga parlor,wani bakin Land Rover ya nufa ya mata key ya shiga,mummu da Nasreen kuma suka zauna a back seat,kunna motan yayi ya nufi gate,Mai gadi naganin tahowan shi ya bude motan tun kafin ayi horn, Addu'a mai gadin ya ringa musu,1000' dubu daya Arif ya Ciro ya Mika ma Mai gadi,yana bashi ya ja motan suka fita ko saya amsa godiya da mai gadi k Mai baiyi ba,yana cikin tuki yace ma mummy Ina zamuje,"amsa mishi mummy tayi da dama shopping zanyi ma little dina," "da okh ya amsa yace wani zamuje mummy" ' duk Wanda kaga ya dace' "daga haka bai kuma cewa komi ba ya kama hanya zuwa wani babban ShopRite din da ake ji dashi a garin Kaduna,suna isa wurin ya naimi wuri yayi parking,fita duk sukayi suka nufi cikin mall din,basket mummy da Arif Suka dauka suka fara kiran kaya baji ba gani,"Arif duk abinda ya gani ya mai kyau dauka yake wani abin ma bai san mai nene ba Amman ya dauka sai da ya cika basket manya guda biyu" mummy ma diban kaya tayi sossai masu tsada da quality,sai data cika basket uku makil da kayan kwalliya dana sawa,wani basket Kuma ta dauka ta zabi takalma da jaka shima sai da ta cika shi,kwashe basket din sukayi zuwa tun da ake biya,cire kayan duka akayi aka lissafa kudin gaba daya ya kama dubu dari 500 dai-dai,mummy ne ta bude jaka zata dau Atm ta bayar taga Arif ya Mika nashi,"dagowa tayi ta kalle shi tace ya haka",' murmushi yayi yace mummy ki barshi na biya',girgiza kai mummu tayi tace Sam ban yarda ba,magiya ya fara mata akan ta barshi Itako taki,a karshe dai suka saya a fifty fifty wato zata biya rabi shima ya biya rabi,bayan sun gama biya,aka kwashi kayan aka bisu da shi, booth din motan ya bude aka cika shi da kaya makil..........................


COMMENT AND SHARE


ACCOUNT NUMBER:2245462427

ACCOUNT NAME:AISHA MAARUF

BANK NAME:UBA

EVIDENCE NUMBER:*** VIA WHATAPP


BY GIMBIYA AYSHU 💞💞💞.