🌼🌼ZUBAR HAWAYE NA🌼🌼

Episode 27-28

by @gimbiyaayshu2503

🌼🌼ZUBAR HAWAYE NA🌼🌼


STORY AND WRITTEN BY


GIMBIYA AYSHU 💞💞💞


ELEGANT ONLINE WRITER'S 📚


             PAID BOOK

             FREE PAGE


PAGE 14/15


_____________________________Shiga duk sukayi ya ja motan ya bar haraban mall din,Bai zarce ko Ina ba sai wani hadaddan bakery,parking yayi a haraban wurin,mummy tace suje da Little ita bazata shiga ba,Atm ta mika mishi yaki amsa ya fita abin shi,rike hannun Nasreen yayi suka shiga ciki,kayan kwalama ya siya laida biyu ya fito da su,Nasreen na biye da shi sai surutu take zuba mai,bude back seat yayi ya saka laidodin aciki ya kulle,front seat ya bude ma Nasreen ta shiga ya rufe, zagayawa yayi ya shiga driver seat,ya tada motan suka nufi gida,dai-dai yana parking ana Kiran sallan Azahar,daukan laidodin ice cream kawai yayi ya nufi parlor da shi,fridge din dake parlor ya bude yasaka laidan ice cream a ciki,bayin parlor ya shiga yayi tsarki sannan yayi Alwala,fita yayi da sauri yanufi masallaci dan an tayar,yana shiga Masallaci aka yi ruku'i,da sauri ya shiga layi ya kabbarta sannan ya bisu,bayan an idar bai tashi a wurin ba sai da yayi Addu'a sossai.


************************************


A bangaren Anty lauratu kuwa tunda Nasreen ta fita talla gaban ta yake ta faduwa, Addu'a kawai ta dinga yi,a ranan ko sukuku ta wuni har mama ta tambaye ta ko lafiya,tace lafiya kalau kawai dai gaban ta ne ke faduwa,Allah ya kyauta kawai mama tace ta cigaba da abin da ke gaban ta,bayan sallan magariba shiru shiru Nasreen bata dawo ba har aka kira sallan isha'i,tashi Anty lauratu tayi tayi sallan bayan ta idar ta zauna tasa agogo a gaba bini bini zata duba lokaci,ko motsi taji zata leka,haka ta dinga yi har tara '9' ta buga,iya tashin hankali Anty lauratu ta shiga,dan tunda 9 ta buga taga dai ba alamun Nasreen hankalin ta ya fara tashi,fita tayi daga dakin da waya a hannun ta ta zauna a kan kujeran tsugunno tana duba agogo taga har tara da rabi Babu alamun Nasreen tuni zufa ya fara keto Mata,dama da hijabi a jikin ta,gidan su Aisha ta fara zuwa dan ,ta duba ko tana chan Amman aka ce mata rabon data zo gidan ma sun manta,tanbayan ta maman A'isha tayi akan mai ya samu Nasreen din ba'a ganta bane, amsawa Anty lauratu tayi da bangan ta ba tana kuka,mikewa mama da Aisha sukayi a tare,salati mama ta saki tace ma A'isha ta dauko mata hijabi a daki,juyawa A'isha tayi da gudu ta nufi dakin mama,dama ita da hijabi a jikin ta É—an bata jima da dawowa daga aike ba,fita sukayi daga gidan,a zaure suka ci karo da baba,bayani mama tayi mai a sassaye ta wuce,tafiya suke suna dube dube,har kasuwa su kaje amman babu Nasreen babu kaman ta,kuka Aisha da Anty lauratu suka fashe da shi,Anty lauratu ko harda dukawa tana kuka sossai,daga ta mama tayi tana bata hakuri,komawa sukayi suna duddubawa,Aysha ko sabar rudewa harda tanbayan masu wucewa take,basu suka koma gida ba sai karfe 10'goma' da rabi,ranar Anty lauratu batayi barci ba yanda taga rana haka taga dare.A bangaren mama ko batayi barci kirki ba,Aysha ko kuka ta dingayi,idanuwan ta sun kumbura abinka da farin fata,batasan san da barci barawo yayi awon gaba da ita,kiran sallan farko a kunnen ta.


Raya daren Anty lauratu tayi tana sallah tare da Adduo'i sossai,bayan tayi sallan Asuba barci ya dauke ta akan darduma,batafi awa biyu da kwantawa ba ta fara jin surutun mama,farkawar tayi ta zauna,hannu biyu tasa ta rike kanta da shi tana salati saboda wani irin sara mata da yayi,shigowan mama dakin taji,dagowa tayi ta kalle ta,gaishe ta tayi,ko amsa mata mama batayi ba tace "ina wannan shegiyar yarinyar mai idan mujiya,kallan ta Anty lauratu tayi ta kasa magana,ba dake nake magana ba ehhhhhh!" Dagowa Anty lauratu tayi hawaye na zuba daga idan ta tace"bangan ta ba",kallan ta mama tayi tace ban gane baki gan ta ba,"share hawayen idan ta tayi tace"bata dawo gida ba tun jiya",kallan ta mama tayi a kaikaice tace kina nufin bata kwana a gidan nan ba,daga mata kai Anty lauratu tayi kuka nasan cin karfin ta,tafi mama take tana surutai,tace wato yanzu wiyan ta ya isa yanka har tasan ta kwana a waje,gaskiya ne,wato yanzu ta dadin iskanci,wiyan ta ya isa yanka zata dawo ta same Ni,haka ta dinga bambanci har ta fita waje,a ranan sun sha mita.


Da misalin ƙarfe 9 na safe maman Aisha da Aisha Suka shigo cikin gidan su Nasreen da sallama a bakin su,suna shiga suka iske mama nata banbancin fadan ta,gaishe da mama kawai Maman Aisha tayi haka ma Aisha,tsayawa mama tayi ta kasa tanbayan mama ko an dace an ganta,amman da jin abin da mama ke fadi tasan bata dawo ba har yanzu,Anty lauratu ne ta leka sakamakon jin Muryar maman Aisha, muryar Anty lauratu da maman Aisha taji ne ya sa ta juyawa bangaren da taji Muryar,amsawa mama tayi tana karasowa inda take tace kunga idan ki kuwa lauratu,ba dai kuka kika ci haka ba,i ba kuka ya kamata kiyi ba Addu'a za kiyi mata Allah ya tsare ta a duk in da take,da Ameeen Lauratu ta amsa tana daga kai,takasa rike kukan ta,Aisha ma sai Taya ta take,mama dake jin su tayi shewa tace kunanan kuna bata lokacin ku akan yarinyar da bata masana kuma yi ba,yarinya ta tafi kasuwanci kunanan kuna Allah ya tsare,zan ga yanda zai sare ta na wurin sabo,wani irin mugun kallo Aisha ta aika ma mama da shi zata yanka maman ta tayi saurin hana ta,juyawa kawai Aisha tayi daga gidan tana kuka Dan in tasaya komai ma zai faru,kallan tan Inna wato maman Aisha tayi tace duk abin da kike tunani ba shi bane,nasan yarinyar nan bazata taba aikata abin da kike fada ba,insha Allah sai dai baki ki ya sari danyan kashi,kuma Allah zai tsare ta a duk inda take,kuma yasa tana hannun na gari,inna na kaiwa nan ta dubi Lauratu tace ki bar kuka hakan kar kija ma kanki wani ciwon kinji,kawai abin da nakeso da ke ki dinga mata Addu'a,girgiza mata kai kawai Lauratu take hawaye na zuba a idan ta,fita mama tayi daga gidan.


**********************************


Zaune suke dukan su a dining table suna cin Abinci,Nasreen ko ba wani abincin kirki ta ci ba,bayan sun kammala suka nufi parlor, fridge Arif ya nufa ya dau laidan daya saka a ciki,budewa yayi ya dau roba daya ya ba ma Nasreen sannan ya mika ma mummy,kafin ya dau na shi,irin flavour Nasreen,sai da Nasreen ta sha guda biyar zata kara mummy ta hana tace ta bari sai anjima,haka ta hakura ba dan taso ba,tashi sukayi suka gyara wurin ita da Arif,bayan sun gama ya kara zuwa waje,kayan da suka siyo ya cire a booth gaba daya bayan ya Gama ya Kira masu aiki suka kwashe zuwa cikin dakin da aka gyara dan Nasreen,zube su akayi a filin dakin,mummy ne ta shigo tare da mai aikin su,shirya kayan tayi a cikin drawer gaba daya,sai da drawer ya cika makil da kaya,bayan ta gama dama already mummy ta Ciro Mata daya wanda zata sa,bayi ta shiga ta hada mata ruwan wanka,bayan ta fito Nasreen ta shiga,mintin ta 10 a bayi ta fito,mai ta shafa ta aka inners tasa kayan ta,zaunar da ita mama tayi ta fara tsefe mata gashi,bayan ta gama tayi comb ta kama mata,sannan tace za suje salon gobe,da toh Ammi Nasreen ta amsa.


Washe gari da misalin 11 suka fita salon,Arif bai bisu ba saboda ya fara zuwa office,yayi yayi mummy ta Bari su tafi tare ina yaso gobe ya fara fully ba fashi amman mummy taki,haka nan ya tafi ba yanda ya iya. Da misalin ƙarfe daya suka dawo daga salon dadi kaman ya kashe Nasreen an gyara mata gashi sai kuri take tayi da gashin,ranar ko ko dan kwali ba'a kuma sawa ba,duk wanda ya shigo sai ta nuna mai,da daddy ma ya shigo i da gudu ta nufi wurin shi tana murna,nuna mishi gashin ta tayi tana murna, murmushi Daddy yayi ya shafa kumatun ta,Arif ne ya bude kofan parlor ya shigo da sallama,Nasreen najin sallaman shi ta tashi da sauri ta nufi wurin shi tana nuna mishi kan ta, unnnnn! yayi kyau sossai saura kitso,turo baki Nasreen tayi tana kallan shi,dariya yayi yaja kumatun ta yace wato bakisan kitso ko daga mishi kai tayi alaman ehhh!, murmushi kawai yayi ya riko ta suka nufi gurin su mummy.


      BAYAN WATA DAYA


Anyi binciken inda za'a samu en uwan ta ko kuma wanda ya san ta amman abin ya citura, shiru kakeji ba labari,tsawon sati Uku kenan,hakura daddy yayi yace insha Allah Allah zai bayyanar da iyayen ta lokacin da ya dace.


Arif ne kawai zai iya bada details din inda za'a iya sanin wanda ya santa,Amman kashhhh! Anyi rashin Sa'a Arif baya gari,kuma ko da wasa daddy da mummy basu taba yi mishi zanchan ba.


Wani matashin saurayi na hango yana saukowa daga matattakalan jirgi,sanye yake da kananan kaya farin riga mai gajeren hannu sa bakin jeans,bayan shi rataye da jaka,saukowa yake fuskan shi dauke da murmushi sakamakon hango su mummy da yayi.


Tsaye su mummy suke a cikin filin jirgi,daddy da mummy sun jingina da mota,Nasreen kuma ta jingina da jikin Mummy,ba sufi minti 10'goma' da tsayuwar ba sai ga jirgin su Arif ya sauko,tunda Nasreen taga jirgin a kasa ta kura ma jirgin ido kaman idan ta zai zazzage ya makale a jikin jirgin,tana hango Arif ta cire hannun mama daga kafadan ta ta kwasa da gudu,gudu take bata duba hanyya,a tsakiyan filin jirgin ne wani mota ya kusa bige Nasreen ji kake kiiiiiiiiiiiiiiiiii! Sai da duk wanda ke harabar wurin ya juyo da firgici,hayaki ne ya bulbule wurin,ihuuu! Mummy ta fasa ta nufi wurin da gudu,zamewa gyalen ta yayi Amman Bata ko bi ta kan shi ba,rufa mata baya daddy yayi,Arif dake saukowa daga jirgi da kasaita,fuskan shi dauke da murmushin farin cikin ganin mahaifansa da little Angel dinsa,ganin abinda ya faru ne yasa shi dirowa daga sauran step din ba tare da ya shirya ba,yar da jakan bayan shi yayi ya nufi inda Abin ya faru da gudun bala'i,Mummy ta riga shi isa inda abin ya faru,a duke suka iske Nasreen ta rike kanta da shi jikin ta sai rawa yake,fita driver dake tuka motan yayi ya nufi wurin Nasreen,ya dagota dan ya tabbatar da bai bige ta ba,Mummy ne ta kwace ta daga hannun shi tana dudduba ta,Nasreen na ganin Mummy ne ta rike ta tayi tsaurin rungume ta tana kuka da shassheka,dai-dai nan Arif da daddy Suka karaso a tare,daddy me yace hope ba abin da ya sake ta,daga mishi kai Mummy tayi idan ta cike da hawaye,kokari take kar hawayen ya zuba,wasewa mutanen da suka taru suka farayi,riko hannun ta Mummy tayi suka nufi wurin mota,bin su Arif da daddy sukayi a baya,bayan sun kai wurin mota Arif ya ba ma driver umurnin ya dauko mai jakan shi tare da nuna mishi inda jakan yake,bayan ya dauko ya ba ma Arif jakan,back seat ya shiga,shi da Mummy da Nasreen a tsakiya,Nasreen na rungume a jikin Mummy sai lallashin ta Mummy take,ba karamin firgita Nasreen tayi ba.

Bayan sun kai duk suka fita daga motan, parlor suka shiga gaba daya,Mummy cire gyalen ta tayi tun daga parlor batayi birki a ki ina ba sai bedroom din Nasreen ruwan wanka ta hada mata mai zafin gaske,bayan ta fito tayi mata warning akan karta kuskura ta tsirka ruwan,daga mata kai kawai Nasreen tayi dan ta kasa magana,bayan ta fito Mummy ta bata kayan ta ta saka,riga da skirt na less kalan royal blue Mai shine shine a jikin shi,kwalli mama ta mika ma Nasreen ta saka ta fesa mata tulare,riko hannun ta Mummy tayi suka fito daga dakin.tunda su Mummy suka shiga ciki daddy yace ma Arif ya je yayi wanka amma Arif ya kasa ta shi,bini bini zai kalli kofan dakin Nasreen,haka ya dinga yi har su Mummy suka fito,tunda yaga fitowa su daga daki ya kura ma Nasreen ido kaman zai hadiye ta,mikewa yayi da tsauri ya nufi wurin ta,a tsakiya parlor Suka hadu,dukawa yayi a gaban ta,Mummy na ganin haka tayi gaba abin ta, dining ta nufa,"Angel Dina ykk,hope Mai motan Nan Bai Miki komai ba kohhhh!"daga mishi kai Nasreen tayi kaman yar baby,yace gud Angel Allah ya Kara tsare gaba,"Ameen yaya cewar Nasreen,muryar ta na fita a hankali,Muryar Mummy sukaji tace in kun gama shiriritar kwa karaso,mikewa Arif yayi yana shafa gashin kanshi fuskan shi dauke da murmushi,Mummy ne tace wato kai Arif har yanzu wayo bai ishe ka bako,maimakon kaje kayi wanka kafin mu fito shine ka zauna kana jiran mai maka wankan kohhhh,ta karasa tana kallan Arif,hannu yasa Yana Sosa kan shi yace,ba haka bane mummy, mummy tayi tsaurin katse shi da yaya ne,"shiru yayi ya kasa bada Amsa" sabawa kawai yayi ya fita daga dakin,Mummy ne tace Abban little zo muci abinci,'amsawa daddy yayi da ki bari son ya dawo', da toh kawai Mummy ta amsa,karasowa inda Mummy ke zaune Nasreen tayi ta ja wani kujerar ta zauna ta jingina da jikin Mummy,Hannu Mummy tasa tan shafa fuskan Nasreen kafin tace 'little mai ke damun ki mai yasa kikayi haka ummmmm! Ko dai kina jin yunwa ne?,"girgiza mata kai Nasreen tayi alaman duka babu"Mummy tayi tayi Amman komi Nasreen bata ce ba

Bayan minti 20 sai ga Arif ya shigo kunnen shi manne da waya,yana zuwa ya ja kujera ya zauna a dining har ya Gama call din shi, "bayan ya gama yace Mummy na Gama,"harara Mummy ta dalla mai,Kiran daddy tayi ya nufo dining.

Bayan sun gama cin abinci,tashi Arif yayi ya nufi dakin shi ya dauko Akwatin tsarabar su,akwati daya ya raba ma Mummy da daddy, Akwati daya kuma na Angel,"iko bakin Nasreen har kunne,dadi kaman ya kashe ta,wani town daya tafi da ita ta dauka ta nufi wurin Mummy tana nuna mata",amsa Mummy tayi tace yayi kyau sossai,Amman kince kin gode,girgiza kai Nasreen tayi alamun a'a,toh maza je kiyi godiya,tashi Nasreen tayi da tsauri ta nufi wurin Yaya Arif ta duka ta Mai godiya,"hannu yasa yaja kumatun ta yana murmushi",mummy ne tace sannu da dawai biya son,Allah ya bada lada,"Ameen Mummy cewar Arif" kulle akwatin yayi ya kai dakin Nasreen ya ajiye,bayan ya dawo suka zauna a parlor aka hau jiran yaushe rabo...................................


COMMENT AND SHARE


BY GIMBIYA AYSHU 💞💞💞.