🌼🌼ZUBAR HAWAYE NA🌼🌼
29-30
🌼🌼 ZUBAR HAWAYE NA🌼🌼
STORY AND WRITTEN BY
GIMBIYA AYSHU 💞💞💞
ELEGANT ONLINE WRITER'S 📚
PAID BOOK
FREE PAGE
PAGE 16/17
______________________________Bayan dawowan Arif da kwana biyu aka sa Nasreen a wani private school Mai tsada inda aka sata a jss2, sakamakon interview da aka mata kuma ta ci,matsalan kawai shine turanci da bataji sossai,Amman daddy ya dau mata malamin da zai riga koya mata duk week end,bayan ta dawo makaranta da misalin karfe 3:00 tayi wanka ta ci abinci,bayan sallan la'asar ta saka uniform din da aka dinka mata na islamiyyan da zata fara zuwa,"Arif ne ya shigo parlor da sallama ya ce Angel kin Gama ki fito mu tafi lokaci na tafiya"amsa mishi Nasreen tayi daga cikin dakin da take da ta gama yanzu zata fito,bayan ta fito daga dakin ta ta zarce zuwa dakin Mummy tayi mata sallama,dari biyar '500' Mummy ta dauka ta danka ma Nasreen wai in taji tana jin yunwa ta siya abu,"Amsa Nasreen tayi tai ma Mummy godiya Sossai sannan ta fita daga dakin" wurin Arif ta nufa inda yake zaune akan kujera mai zaman mutum daya,ya kwantar da kan shi akan kujeran ko tunanin mai yake oho! Sai Allah,"Nasreen ce ta tsauko da tsanda a sakamakon ganin irin yanayin zaman shi,tsanda ta dinga yi har ta karaso in da yake zaune tayi tsalle ta buga ƙafan ta da kasa tace woooooo!" 'ko gezau Arif bai yi ba,Dan duk abin da take yana lura da ita,dago kan shi yayi ya kelle ta da idan shi daya dan canja kala daga fari zuwa jaja,dan murmushi kawai yayi yana kallan ta', bata fuska Nasreen tayi ganin bai tsorata ba,Amman ganin kalan idan shi ya sata manta komi tayi tsaurin matsawa kusa da shi har tana kokarin faduwa kan shi tace" yaya Arif Mai ya same ka?,baka da lafiya ne?,mai yasa idan ka yayi ja?,hannu tasa ta taɓa goshin shi taji ya dan yi dumi,cire hannun ta tayi da tsauri ta kalle shi tace kanka na ciwo ne?,"girgiza mata kai kawai yayi dan tanbayan ya fara yawa,kuma ina ba amsa ya bata ba sai suyi awa daya suna abu daya,mikewa yayi bayan ya bata amsa ya nufi hanyyan fita daga parlor sannan yace ta biyo shi a baya"binshi ta farayi da gudu gudu tace bazaka tsaya ka sha magani ba,"girgiza mata kai Arif yayi yace i kan yana bar ciwo",sahgwabe fuska tayi tana kallan shi alamun bata yarda ba,"ohhh! My God Arif yace kasa kasa,sannan ya dau hannun shi yana mammasa kan shi tare da girgiza kan yace kin gani ya barmin ciwo",'kallan shi ta dinga yi irin bata gama yarda ba din nan', " karasowa yayi inda take tsaye yace haba Angel ki yarda dani mana pls,Kinga fa time na tafiya yanzu fa 4:29 kuma bamu ma bar gida ba, ya fada yana langwabar da kan shi gefe daya," gaba tayi ya biyo bayan ta,bude mata front seat yayi ta zauna sannan ya zagaya driver seat ya zauna,'a zuciyar shi yace Angel rigima' ,tada motar yayi suka fita daga gidan,basu zarce ko ina ba sai Islamiyya,mintin su 15 suka isa,parking yayi a haraban makarantar, suka fito,office din principal din makarantar suka nufa,inda nan aka yi mata komi da komi aka sata Aji uku,bayan an gama Za'a tafi da ita class,juyawa tayi tana kallan Arif idanun ta cike da hawaye,daga mata hannu yayi fuskan shi dauke da murmushi mai hadi da damuwan hawayen daya gani a idan ta,haka tabi bayan malamin ba yanda ta iya," yafi minti 5 a zaune ya kasa tashi, sai da principal din yace ko dai baka da lafiya ne,daga kan shi yayi ya kalle shi sannan yace lafiya na lau,mikewa yayi yai mai sallama sannan ya tafi,"driving yake jikin shi a sanyaye".
Da misalin ƙarfe 5:55 dai-dai yayi ma Arif a cikin islamiyyan,da aka tashi ya fito daga motan dan Angel din shi tasan anzo daukan ta,hango student yayi dayawa suna ta fitowa,dayake baisan class din su ba tsayawa kawai yayi,mintin shi 10 'goma a tsaye Amman baiga alaman zuwa Nasreen ba,da mutane suka dan lafa shine ya fara takawa zuwa wurin classes din su,hango ta yayi zaune akan wani dakali, kanta a kasa,takawa yayi a hankali har ya kai inda take zaune,dukawa yayi a gaban ta ya sa hannun shi ya dago kanta,hawayen daya gani a idan tane yasa hankalin shi ta shi,"tanbayan ta abin da ya same ta ya farayi a rikice",shiru tayi tana shassheka taki magana,magiya Arif yayi da lallashin sossai kafin Nasreen ta yarda ta bude baki tayi magana" ' turo baki tayi da muryan kuka tace bakai ne ba bakazo ka ɗauke Ni da wuri ba har sai da mutane suka tafi baaaaa! Ta karasa tana share hawayen idan ta tare da tabe baki', "hannu Arif yasa ya rike kan shi da shi,a zuciyar shi yace,Allah ya hadani da rigimammiya" lallaba ta ya farayi yana mata dadin baki tare da mata Alkawarin siyan abubuwa dayawa, tuni ta wanye ta fara murmushi da dariya jin za'a siya mata abin da take so,ta shi tayi ta kama hannun shi,mikewa yayi ya bita suka wuce,basu suka kai gida ba sai bayan sallan magariba,dan sai da suka biya wurin chop-chop 'ciye-ciye',iko Mummy tayi ta kira ba'a dauka,hankalin ta ya tashi sossai,gashi ba waya a hannun Little balle ta Kira tunda Arif bai dauka ba,ajiye wayan Mummy tayi tai sallah, tana idarwa ko Azkar bata tsaya yi ba ta dau waya ta kara kira, dai-dai nan su Arif Suka shigo parlor,katse wayan tayi fuskan ta a hade tace daga ina?,"ganin yanda Mummy ta hada rai ne yasa Arif yin magana a sanyaye yace Mummy munje shopping ne daga islamiyya",kallan shi Mummy tayi tace toh daga yau karka kuskura ka kara fita da ita daga gidan nan bayan magariba ko kuma magariba yayi muku a waje,kaji ko baka ji ba,"naji Mummy insha Allah ba za'a kara ba,gaishe da Mummy yayi sannan ya ajiye laidan ya fita daga parlor",amsawa mummy tayi kasa kasa,"gaishe da Mummy Nasreen tayi jikin ta a sanyaye ganin anyi ma Ya'yan ta fada,amsawa Mummy tayi tace kai wanna laidan fridge kije kiyi sallah kafin kiyi wanka dan lokacin sallah na kurewa,"da toh Mummy Nasreen ta amsa tayi abin da aka sata ta wuce dakin ta", Ajiyan zuciya mai nauyi Mummy ta saki ta fada duniyan tunani.
Bayan sallan isha'i Nasreen ce ta fito daga dakin ta sanye da dogon riga na Atanfa mai Ado stone a jikin shi,kanta daure da dankwali,down stairs ta sauka ta zauna a parlor ta a kallon Tv,tana cikin kallon ne taji an bude kofan parlor,tsaurin waigawa tayi ta duba wanda ya bude kofan,daddy ta gani,da tsauri ta mike ta nufi in da daddy take fuskan ta dauke da yalwatatchan murmushi,"Welcome daddy",saurin kallon ta daddy yayi Dan ya tabbatar da abin da yaji,girgiza mishi kai tayi hakoranta a waje,dan dariya daddy yayi yace thank You my daughter yakike ya school da islamiyya kinji dadin zuwa kohhhh!amsa jakan hannun daddy tayi suka shigo cikin parlor Suka cigaba da hira,suna cikin hiran ne Mummy ta sauko tace a'a dawowan yaushe,ina wuni sannu da zuwa,amsawa daddy yayi yace banfi 10min da shigowa ba,girgiza kai Mummy tayi ta dau jakan shi ta nufi daki da shi É—an yasan dayan laidan ba kayan da zaije daki bane,tasan duk kwalama ce aka siyo wa little,bayan ta kai jakan tasamo tace Abban Arif bazakayi wanka ba,zanyi kin hada ruwan ne,ehhhh! Na hada fahhh! Da toh toh ya amsa ya mike yace daughter Bari inje in dawo,daga mishi kai tayi tace toh daddy,bin bayan Daddy mummy tayi,cigaba da kallon ta tayi,alamun bude kofa taji,juyawa tayi tana kallon wanda zai shigo,Arif ne ya shigo da sallama a bakin shi,Amsawa Nasreen tayi ta juya ta cigaba da kallon ta,wuri Arif ya samu ya zauna yana kallon tashan da take kallo,dago kanta tayi ta gaishe shi kasa kasa,dagowa yayi ya kalle ta jin yanda tayi maganan,amsawa yayi bai ce komi ba,kallan ta yake yana kallan tashan da take kallo,chan yace Angel Mai ya same ki,girgiza mishi kai tayi alamun babu komi,kallan ta kawai Arif yake baice komi ba,Tashi Arif yayi ya dawo kushin din da take zaune ya zauna, Angel Mai na Miki,y did u change,kallan shi tayi tace banyi ba,i dazu naga Mummy na maka fadan mu dai na kaiwa dare,in dare yayi mu daina magana ta karasa tana turo baki, "rike kanshi Arif yayi yace noooo! Angel, ba Abinda Mummy take nufi ba kenan,bayani yayi mata har ta fahimta suka cigaba da hiran su.................................
COMMENT AND SHARE
BY GIMBIYA AYSHU 💞💞💞.