๐ŸŒผ๐ŸŒผZUBAR HAWAYE NA๐ŸŒผ๐ŸŒผ

Episode 31-32

by @gimbiyaayshu2503

๐ŸŒผ๐ŸŒผ ZUBAR HAWAYE NA๐ŸŒผ๐ŸŒผ


STORY AND WRITTEN BY


GIMBIYA AYSHU ๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž


ELEGANT ONLINE WRITER'S ๐Ÿ“š


            PAID BOOK 

         END OF FREE PAGE



A NAN NA KAWO KARSHEN FREE PAGES DINA, ALHAMDULLAH.


GA MAISON POST SAU DAYA A RANA ZATA/ZAKA BIYA 200

MASU SON POST SAU BIYU 400

COMPLETE NOVEL KUMA 500


ACCOUNT NUMBER   2245462427

ACCOUNT NAME.   AISHA MAARUF

WHATAPP NUMBER FOR EVIDENCE.  ***

BANK NAME   UBA


IN NAGAMA FREE PAGES ZAN BADA HUTUN KWANAN BIYU SABODA WA'INDA BASU BIYA BA SU SAMU SU BIYA DAN A TAFI TARE DUK WANDA BAI BIYA BA HAR MUKAYI NISA TOHH SAI DAI YA NAIMI COMPLETE.


ZAMU CIGABA DA POST INSHA ALLAH RANAR WEDNESDAY BAYAN FREE PAGES.


ALLAH YA BANI IKON GAMA LITTAFIN KAMAN YANDA YA BANI IKON GAMA FREE PAGES.AMEEEEEN.๐Ÿคฒ๐Ÿคฒ๐Ÿคฒ.


BANYARDA A CHANJA MIN KOMI BA DAGA CIKIN RUBUTU NA.






PAGE 18/19


_____________________________ Haka dai rayuwa ta cigaba da tafiya inda yanzu an kwashi wata uku da batan Nasreen,da aka tabbatar da batan Nasreen wato Anty lauratu ta tabbatar ta bata sai da ta sha ruwa laida 10,daga baya ta fauwala ma Allah komi ta cigaba da Addu'an naiman mata tsari,makota ko masu Alhini nayi masu zugi nayi kowa da abinda yake cewa,wasu ko cewa sukayi mama ce ta kore ta wai dama ita ta kashe uwar ta, shine kuma yanzu ta kori diyar,"kumsan mutane sai a hankali kowa da abinda yake fada.


************************************


A yanzu Nasreen ta goge ta zama yar gari,yanzu tana da shekara 14 Amman kaman yar shekara 10 saboda matsalar data samu a kwakwalwar ta.

Tayi bul bul gashi dama tana da tsawo gashi tana da alaman zatayi kiba Amman sai Nan gaba.

A yanzu Nasreen na jss 2 third term,suna exam din promotion,

A yanzu turanci ya zauna a bakin Nasreen sossai,inda inta maka turanci sai ka zata wata yar kasan waje ce musamman in kanta ba Dankwali. Da yake fara ce mai kalan jaja,gata da gashi har baya,ga gashin da laushi.


Zaune suke a parlor ita da Arif da dawowan shi daga office kenan yayi wanka shine ya shigo part din mummy ya iske Nasreen zaune a parlor ta tasa keyan tv tana kallo,Zama yayi a kan kujeran dake kallan nata,gaishe shi tayi ya amsa daga haka suka fara hira, tana yi tana kallo dan Nasreen ba dai kallo ba tayi respecting kallo ba kadan ba,most expecially indai movies,tunda suka gaisa ta maida hankalin ta kan tv, Arif ko yana kallo Amman rabi da kwatan hankalin shi nakan Nasreen,yana kallan tv Kuma Yana Satan kallan ta,haka ya dinga yi har yasa Nasreen ta lura,kallan shi tayi ta tura baki tace yaya mai ya faru kake kallo na,ta shi Arif yayi ya dawo inda take zaune ya duka a gaban ta yace Nasreen,bai taba kiranta da sunan ta ba sai yau,in Bai ce Angel ba zai ce little Amman yafi kiranta da Angel,bude baki yayi ya fara mata magana a taushashe yace," duk wanda yace yana son ki karki yarda,yace karta kuskura ta bashi dama balle har a kaiga magana yayi karfi",hada rai Nasreen tayi dan bata gane mai yasa yake hana ta ba,bude baki tayi zatayi magana yasa hannun shi daya ya kulle mata baki da shi,yace shiru I don't want you to say Anything just obey this instruction kinji Angel,girgiza mishi kai tayi tana kallan cikin idan shi,shima kura mata ido yayi suka dinga aika ma junan su kallan kauna,Amman Nasreen ita Bata ji komai ba, mai gayya ne kawai ke fama da ciwon shi shi kadai.


      BAYAN WATA BIYAR 


A Yanzu watan Nasreen biyar da bata,inda tunda ta bata baba Bai taba bude baki ya ce ina take ba,Anty lauratu ko ta koma islamiyya inda yanzu tazama wata shiru shiru,bata cika magana ba,tun tafiyan Nasreen,dama gidan bata da kowa face Nasreen gashi Nasreen din ta bata,data tuna cewa Nasreen ta bata a ranar wuni zatayi kuka. Haka dai rayuwa ta cigaba da tafiya inda Ahmad ya fito naiman Auren Anty lauratu,da farko dai kin yarda tayi Amman duba da wasu abubuwa yasa ta amince mishi har magana yayi karfi.


Wata rana suna zaune gaba dayan su a tsakar gida bayan an gama cin abinci mama tace ke dai sa'ade kinji kunyya har kanwan ki zatayi aure kina nan kin kasa fidda guda daya daga cikin samarin ki a muku Aure,kallan mama sa'ade tayi a kaikai ce tace mai abin jin kunyya a nan Ni dai ba kunyyan da naji,taje tayi Auren ta Ni bai shafe Ni ba,na daisan ba abinda zata nunamin dan Ni ba abin da bansani ba a toh!, fatihan ne kawai ba'a shafa ba ta fada tana mikewa tsaye,Lauratu dake gefe ko ta tabe Baki tace Allah ya shirya in Mai shiryuwa ce,haka dai suka cigaba da hiran su,Lauratu na gefe ko A bata ce ba,tana dai sauran komi,bayan wata daya aka sa rana,"Ashirin da biyar ga watan bakwai '25/07/2021".


Rana bata karya sai dai uwar diya taji kunyya.Ayau juma'a 25/07/2021 aka daura Auren lauratu Abubakar Muhammad da Ahmad Isma'il akan sadaki dubu hamsin '50',tunda aka daura Auren Amarya ta dinga rusa kuka,anyi lallashin duniya amman abin yaci tura,bayan sallan magariba aka kai Amarya dakin mijin ta,gidan ta ciki da parlor ne sai kitchen da bayi,gidan yayi kyau ba laifi,duk wanda yaga gidan saiya yaba,dan komi yayi kyau Masha Allah,bayan an kai amarya ya rage ita da kawayen ta suna jiran zuwan ango,da misalin karfe 10 na dare Ango yazo da abokan shi su biyar sunyi dressing Mai kyau dan uku daga cikin su ba yan kauyen bane,gaisawa sukayi da kawayen amarya inda su kace sai sun biya kudi kimanin dubu 60 kafin zasu bar gidan,haka abokan ango suka cire suka biya,bayan sun biya Ango yace ga kawayen Amarya a kai su gida,abokan shine sukace Ayi a hankali dai kar a nakasa yar mutane dan naga kaman kana zumudi,duk sauran abokan shi suka kwashe da dariya,bude baki Ahmad yayi yana kallan shi,Abokin ko ya kashe mishi ido daya sannan ya fice, murmushi Ahmad yayi ya girgiza kai,kulle ko ina yayi sannan ya nufi wurin Amaryar shi.


Haka Abokan Ango suka kwashi kawayen Amarya zuwa gidajen su,a wurin sai da duk suka sami budurwa ciki ko harda A'isha kawar Nasreen dan ta fito a matsayin kawar Anty lauratu,dan Anty lauratu da kanta ta naimi Alfarmar hakan.


Haka dai rayuwa ta cigaba da tafiya inda wasa wasa Alakan Mustapha da A'isha yayi karfi kaman wasa har maganan yaje gurin manya,da farko A'isha ta dau abin a matsayin wasa ko yaudara dan tace mutanen birni sun fiye yaudara.


Wata rana suna cikin fira da shi yace mata dan Allah ta sanar ma iyayen ta akan shi zai turo a naima mai Auren ta,jim A'isha tayi ta kasa ba shi amsa,tafi yayi a kusa da ita tayi firgigit ta kalle shi,yace kinji mai nace,girgiza mishi kai tayi alamun taji zata fada,da yauwa babyn musty ya amsa,hiran su suka cigaba dayi har karfe tara dai-dai'9:00' kafin ya tafi.

Bayan ta shiga gida ta sanar ma inna Abinda Mustapha ya fada akan ta fada ma baba,mama ta amsa da toh Allah ya tabbatar da Alkairi,da Ameen Ameen A'isha ta amsa.

Bayan kwana biyu mama ta kira A'isha ta zaunar da ita ta sanar da ita amsan da baba ya bada akan ya yarda ya turo da magabatan shi ayi maganar Auren su,dukar da kai A'isha tayi alamun kunyya, murmushi inna tayi ta fita daga dakin,inna na fita A'isha ta tashi ta fara murna,waya ta dauka ba bata lokaci ta danna mai kira bai dauka ba har wayan ta katse,tana katsewa sai ga kiran shi ya shigo,bayan sun gaisa ta sanar mishi da amsan baba a kunyyace,tana gama gaya mai ta kashe wayan,ajiye wayan tayi akan gado ta fara sallen murnan ta kusa Auren burin ranta.


Bayan sati Daya da maganar sai ga Mustapha da wakilan shi,bai bisu ya shiga cikin gidan ba,dan jagora kawai ya zama,mintin su talatin suka fito daga gidan.


Bayan kwana biyu da yin zanchan aka kawo kayan nagani inaso,zo kuga kaya waiiiii! I ranar an samu abin fada a wannan kauyen,da Duk fadin kauyen kife da kwarya babu wacce ta taba samun irin wannan kayan,iko mutane sai tururuwar zuwa gani suke.


Bayan sati biyu aka saka ranar Auren su inda aka tsayar da date a kan 15/09/2021.


Ana saura kwana biyar a daura Auren aka kawo mata kayan laifen ta na gani na fada,Akwati set biyu,wayyo Allah zokuga kaya masu tsada,masu kyau da inganci.


Rana bata karya sai dai uwar diya taji kunyya, A yau juma'a 15/09/2021 aka daura Auren A'isha Muhammad Hussaini da Ango ta Mustapha Hussaini akan sadaki dubu 100 lakadan ba ajalan ba,ana daura Auren gida ya dau guda yarrrrrrrrrrrrrr!.


Bayan sallan la'sar motoci ne masu rai da lafiya guda goma sha biyar '15' suka jeru a layin,anzo daukan Amarya,karfe 5:00 dai-dai aka gama daukan duk wanda zai je gidan Amarya ciki ko harda Anty lauratu,Amarya kuma tana mota ita da Angon ta ษ—an Ango yace shikam baza'a dauko Amaryar shi ba tare da shi ba,da misalin karfe biyar da minti Arba'in '5:40' motocin su yayi parking a haraban gidan kawayen Amarya ne suka sauko inda suka nufi motan Amarya bayan Amarya ta fito aka yi mata zobe aka sata tsakiya aka nufi parlor gidan da ita,bayan sun shiga sun iske mutane a parlor,tarban su akayi da mutunci,yan uwan ango ne suka rike Amarya suka shiga da ita dakin da aka shirya mata,umurni aka bata akan ta hau kan gadon ta zauna,bayan ta zauna yan uwan Ango ma suka zauna tare da manyan Amarya,Nan dai yan uwan Amarya suka ba ma yan uwan Ango amana inda su kuma, suka karba sukace Allah ya tayasu riko,fita sukayi aka nuna musu ko ina na gidan,bayan sun gama gani sukayi ma amarya sallama,mota suka shiga ya kwashe su ya mai da su,yan uwan ango ma tafiya sukayi bayan dattijan sun tafi,gidan ya rage daga Amarya A'isha sai kawayen ta,suna zaune sai hira ake tayi,da lokacin Sallah yayi masu yi suyi wa'inda basuyi kuma su cigaba da hiran su,haka suka cigaba da zama har Ango da Abokan shi suka zo,zama Abokan sukayi a parlor inda ya shiga ciki ya fito da Amarya, kawayen ta suka yi mata katanga,wai bazai yi mata magana ba har sai ya biya kudin da aka ce,zama duk sukayi a parlor,Abokan Ango sukace zasu ma Amarya da Ango wa'azi bayan sun gama kawayen Amarya suka daura,daganan suka yanke kudi inda su kace sai an biya dubu dari ko kuma sauki bayar da Amaryar, tun kafin su rufe bakin su Abokan Ango suka mika musu dubu ษ—ari biyu kashhhhhh! Shewa sukayi su kace yauwa haka ake so,Amaryar mu mai daraja ce,tashi sukayi duk suka fita waje inda Amarya da Ango suka raka su,duk wannan Abin da Ake Amarya bata bude fuskan ta ba,sallama sukayi inda Abokan Ango suka dau Amarya suka mai da su,komawa ciki su kayi inda Amarya ta nufi daki ta bar Ango da kulle kofa da kashe wuta,bayan Ango ya shigo daki ya hau har kan gado ya bude fuskan Amaryar shi,peck yayi mata a goshi yace Alhmd yau dai kin zama mata ta,hannun ta ya rike ya Kaita har kofan bayi yace tayi Alwala za suyi sallah,har ta bude baki zata ce da Alwalar ta sai kuma tayi shiru ta shige bayin kawai,kayan jikin ta ta cire gaba daya tayi wanka tayi Alwala,daura sabon towel data gani a bayin tayi,bude kofan bayin tayi ta leka,gani tayi babu kowa a dakin,bude kofa tayi da sauri ta fita,bude drawer tayi ta dau hijabin da ta gani a kusa,tana gama saka hijabin ana tura kofa,Ajiyan zuciya A'isha ta sauke tace Allah ya taimake ni,kaya ta fara nema Amman taga duk kayan dake wurin half necked ne, wani dogon riga wanda iya kar shi gwiwa ta dauko,Amman Yana da dogon hannu kuma yana da kauri,rike rigar tayi ta nufi bayi,duk abin da take yana kallan ta Amman uffan bai ce ba, murmushi kawai yayi ya girgiza kai,bayan ta saka ta fito da hijabi a jikin ta,tashi yayi ya hau sallaya itama ta hau ya tada sallah,Bayan sun idar ya juya yana mata tambayoyi akan Addinin ta tana kuma bashi amsa, murmushi kawai yake yana kallan dan karamin bakin ta dake motsi a hankali,bayan sun gama ya tashi ya nufi parlor,kaza ya dauko da plate da duk abubuwan da ake bukata,saka kazan yayi a plate yace taci Amman taki ci wai ta koshi,yayi yayi taci Amman taki,hannu yasa ya dibi kazan ya kai bakin ta,babu abin da zatayi face ta bude bakin,haka ya dinga bata har ta ci sossai dan tayi rabin kazan kuma tasha drinks,ita da tace bata jin yunwa,bayan ya tabbatar ta koshi ya kalle ta yace toooo! Shi kazan nan da kika ci yanzu cikin waye ya shiga,hannu tasa ta rufe fuskan ta tana dariya,inkin gama dariya sai ki bani dan bazanci da kai na ba,cire hannun ta tayi daga fuskan ta da sauri ta gwalalo mashi ido,daga mata kai yayi alamun da gaske yake,hannu tasa ta yanka kazan ta kai bakin shi,bude baki yayi yana kallan ta yaci kazan,haka ta dinga bashi har ya koshi,ya sha drinks,bayan ya gama ya tattara kayan ya kai kitchen,bayan ya dawo yace ta tashi suje suyi brush,mikewa tayi ta bishi suka shiga bayin,bayan sun gama,ta tsaya tana jiran ya fita,gani tayi ya kunna Ac ya kulle kofa,i tana ganin haka a zuciyar ta tace nashiga uku Ni Aisha kashina ya bushe yau,bayan ya gama Al'adan shi na barci ya hau kan gado,kallan ta yayi yace mai kike yi a tsaye kizo ki kwanta,daga ฦ™afan ta ta fara yi daya daya har ta kai bakin gadon zama tayi ta jera kananan pillows a tsakanin su kafin ta kwanta,duka abin da take Mustapha na kallon ta dariya kaman ya kashe shi,hannu yasa ya kashe wutan dakin,cire pillows din ya farayi daya daya yana ajewa a kasa ta bangaren shi,bayan ya gama ya matsa kusa da ita ya rage tazara kadan ne kawai a tsakanin su,janyo ta yayi ya zare hijabin Pleasejikin ta at once,Yana cire hijabi tayi saurin rungume shi a nata wautan,aika mata da manyan sako ya farayi,danaga abin na naiman fin karfi na sai na fita daga dakin nace Asuba ta gari Allah yasa a jefa kwallo a cikin ragaaaaa................................


COMMENT AND SHARE


BY GIMBIYA AYSHU ๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž.