KI KULA NI!! (MALLAKIN ZUCIYAH)πŸ’•

LAST FREE PG 5

by @mssxoxo

*_K I K U L A N I_*

_(MALLAKIN ZUCIYA)πŸ’•_



_N A N A H A F S A T_

    _MSS XOXO_


   


_LAST F R E E - P A G E :005 (SHAFIN KARSHE NA KYAUTA...)_

______


Ya tsugunna agaban Yayan na su . Cikin ladabi yace,


"Ina wunin ku...?"


"Lafiya kalau Junaid ."


"Lapia..."


"Kalau muke maza."


"Kanin mu rabajau kalau mu ke ..."


Suka shiga amsar gaisuwar tasu da yayi... Aqeel ya gyara zaman kishingidawar da yayi yace,


"Akwai hamsin awajen ka?"


Junaid yayi 'dan dum... Yana mamakin irin bushewar zuciya da rashin tashi a nemi na kai na Yayan su Aqeel. Yanzu hamsin dinnan ita kadai ce a aljihun sa kuma akwai abunda ya ke so yayi da ita. Don haka yace,


"Sai dai ashirin Yaya... "


"Ban ashirin din kawai."


Littafin sa ya dakko ya bude tsakiyar shafi. Nera ashirin ya dakko yan nera biyar biyu da nera goma guda daya.


"Ga shi..."


"Yauwa... Idan ka samu ciko ka kawo mun." Aqeel ya fada hadi da cusa ashirin din a aljihun gaban rigar sa.


Junaid yayi murmushi kawai. Halin Yayan nasu sai shi. Wai idan ya samu ciko ya cika masa tamkar ajiya ya bashi. Ko kuma wani aiki yakeyi da ake biyan sa. Mikewa tsaye yayi ya karkade jikin sa.


"Kar fa ka manta idan ka samu cikato ka kawo mun." 


"To..." 


"Idan pi network ya fashe. Wabillahi jeep takwas zan saya ma ka Junaid. Sannan duk wata sai na kai ka Dubai. Bayan wata biyu kuma Saudi Arabia zaka je. Daga nan kayi branching a Egypt..."


Dan murmushi kawai yayi wa Yayan na su..


"To..."


"Karfa ka man ta da cikon" 


"Okay" Kawai yace. Ya wuce hanyar gidah abun sa. 



Γ—Γ—LAYIN MARIGAYI SHEIKH SUFYAN ZUBAIRΓ—Γ—



  Gidah ne babban gidah ginin daaa. Da wasu rassa na ciki da aka buge aka gyara bisa zamani. Dai dai gyaran talaka mai godewa bisaga ni'imomin da Allah yayi masa da buwayar sa da rahamar sa..


Junaid ya sauke nannauyar ajiyar zuciya alokacin da ya shigo layin gidan na su. Ya dubi signboard din da gwamnati ta tallafawa unguwanni da su. 


Kowane layi an saka sunan wanda yafu dadewa a layin. Ko da bako zai zo zai gane inda akai mai kwatance da sunan jikin signboard din da ke layin da ake son zuwa. 


Ya tsaya agaban Mari me soya awara. Tana jingine da signboard din layin na su. Mai sunan mahaifi agare su. Marigayi sheikh sufyan zubair. 


"Ina wuni?" Mari ta gayshe shi tana dashare hakora. 


Fuskar nan tata tayi jagalaf da hoda mai ruwa (foundation) Ta caba jagira hadi da goga jambaki ja. 


"Lafiya kalau Mari ta mu...Aban awara." Ya fada hadi da mika mata nera talatin.


"Ka basshi., " Ta ki karba hadi da janyo farar leda ta cikata taf da awara. Ta debo yankakkun tumatir da albasa dake gefe ta zuba aciki.


"Ga shi...."


Kin amsa yayi. Wato da gaske su Fareeha su ke? Yarinyar nan kaunar sa take? Duk sanda suka gaya masa yadda take basu awara kyauta ko ta kara musu da yawa idan sunzo siya .. Sai suce saboda shi ne. Wai tana tambayar su ya yake tana mai tula musu awarar. 


Abun ya so bashi dariya. Ya langabar da kai hadi da dan rage tsayin da yayi ta hanyar dukawa yace,


"Aa bazan karba ba... Ki bani ta iya kudi na dai..." 


"Nayi niyyah.." Ta fada tana sake murmushi.


Girgiza kai ya yi. Banda shirme irin na yarinta. Dan jarin awaran ma nawa yake.? 


"A'ah Mariya.... Banason musu kinji?"


Ta danyi rau_rau da idanu.. Ya kada kai alamun tabbatarwa. Ba yadda ta iya. Ta cire wadda ta kara din ta mika masa. Idanuwan ta suka cicciko tamkar zata yi ku ka. Ya girgiza mata kai kafin yace,


"A'ah... Kar muyi haka da ke.. Nagode sosai Mariya. Kinji ko?"


Batace komai ba. Sai daga kai da tayi. Bai tashi ba ya sake lankwashe murya zuwa ta rarrashi yace, 


"Ki ce kin amince kinji?" Ya fada. Hadi da zuba mata manyan idanun sa akan ta.


"Na amince..."


"Yauwa yar kanwa tah. Allah ya miki albarka. Ya sawa kasuwancin ki albarka ma kinji?"


"Eh..."


"Yauwa to godiya na ke...." Ya mike tsaye ya shige gidah bakinsa dauke da sallama.


Sashe biyu ne da ka shiga ta kofar da zata saadaka da gidan. Sashe daya na kallon daya. Kowanne dauke da dakuna biyu da dakin girki da bandaki a wadace dai dai karfin talakawa. Dayan sashen mallakin kanin mahaifin su ne. Kawu Ashiru zubair. 


Kan sa tsaye ya wuce bangaren su. Ko'ina tas tas an share an killace komai a muhallin sa. Dakin da yake a matsayin na mahaifiyar sa da yan uwan sa mata ya shiga.. 


"Ummy....." Ya kira sunan mahaifiyar ta su. 


Sallah take yi, Ta dago daga sujjada. 


"Okay sallah kike ummy.? Ga awara ba yawa." Ya ajiyeta daga gefe 


Fita yayi daga dakin ya wuce na sa. Yana shiga bakinsa dauke da sallama ya ajiye littafan sa akan yar katifar sa. Ya bude bokitin ruwan sa ya saka kofi ya ebo ruwa yayi basmala ya shiga sha. Sai bayan ya kammala yayi hamdala ya mike tsaye.


"Fareeha... Fareeha... Madeeha... Madeeha." Ya shiga kiran sunan yan uwan nasa mata. Ganin tunda ya shigo gidan bai ji motsin su ba. 


Fita yayi daga cikin dakin ya nufi wajen bandaki yana kwankwasawa,


"Da mutum?" 

Ya maimaita har sau uku. Rashin amsawar hakan ya bashi tabbatar lalle ba kowa aciki. 


Ya juya ya kallo bangaren kanin mahaifin su. Cikin kuryar kofar dakin ya hango Rahila matar kawun su a zaune akan buhu tana yanke faratan kafar ta. 


Kai tsaye ya wuce bangaren yana kasa kunne. 


"Mama su Fareeha na nan?" 


Yamutsa fuska tayi. Ta kauda kan ta gefe. Hakan ya tabbatar masa da suna ciki ..


"Ba zaku gayamun gaskiya ba? Wacce shegiyar ce acikin ku ta gurgunta mun zakara?" Kunnuwan Junaid suka jiyo masa karar sautin muryar kawun su Ashiru. 


Yaja siririn tsaki ... Shi ko gajiya bayayi da dukan su Fareeha..? Duk sanda ya kwaso bolar bacin ran sa. Babu inda yake saukewa sai akan 'ya'yan Yayan sa marigayi Sufyan.


Har zai tura kofar dakin ya shiga sai kuma ya fasa. Gudun bacin ran ummy mahaifiyar su. Don ta tsawatar masa akan kada ya sake shiga yace zai yi rabiyar tsakanin kawun nasu da kannen sa mata. Uba ne agare su don haka su bashi girman sa. 


Ja yayi ya jingina da bangon dakin. Zuciyar sa na masa zafi da zugi. Ganin yadda kawun na su yake sake kurmama tsawa ga kannen sa.


Ya runtse idanu . Zuciyar sa na tafarfasa.. Jiyo yadda ya daga koma menene ya laftawa daya daga cikin su. Muryar Fareeha yajiyo tana,


"Ka dakeni ni daya kawu... Ba abunda Madeeha ta yi."


"A'ah Kawu... Ni ce nan na kore shi amman ba ruwan Fareeha aciki .."


Takaici ya dankare a wuyan kawu Ashiru. Ya saka tafun kafar sa ya shure Madeeha a gwiwa. Ya sake kai wa gular Fareeha duka. Cikin takaici da bacin rai yace,


"Ku tashi ku fita dan uban ku . Matsiyata. Koma wacece tayi acikin ku. Da girman Allah sai masifa ta hau kan ta. Yan gaba da iska. Ku ta shi..." Zai sa ke kai musu gula suka tashi da sauri suka fita...


Suna fitowa Madeeha ta juya ta hararo kofar dakin hade jan karamin tsaki da Allah ya isa a kasan makoshi..


"To malam ga ta tana wulkita idanu." 

Rahila ta fada tana nuni gare su 


"Wacece acikin su?" Cewar malam Ashiru 


Nan da nan Fareeha ta nuna kanta.


"Ni ce nan."


"Dallah matsa. Kawu ni ce nayi. "


Takaici ya sa kawu Ashiru dago silifas zai duke su suka gudu da sauri. Banda Junaid da ummy mahaifiyar su da kuma su Asmau yaran kawu Ashirun dawasu kawayen na su babu wanda ke gane su .


Kasancewar su din identical twins ne (yan biyu masu kama daya) Babu abunda ya raba kamannnin da suke da junan su sai wata tawadar Allah da ke gefen wuyan Madeeha... Kuma Fareeha batada magana sosai tanada hakuri kuma. Madeeha na da tsiwa, Amman tanada saurin sabo da mutane. ... Banda wannan basuda wani bambamci. Shiyasa idan suka hada kai wajen yin abu. Zai yi wuya agane dayan su.....


"Zo nan Fareeha... Ai har da ke madeeha .. ku zo.." Junaid ya kira sunayen su . Yana gaba suna biye da shi a baya...



_ANAN MUKA KAWO KARSHEN FREE PAGES_πŸ™

---


_Tirqashi.., Mai karatu na san na jefa zukata a kwadayin son karance yadda labarin zai kaya., Tafiyar ta dabance wadda ta dauki rassa daban daban na rayuwar dan Adam ayau da kullum .. Domin tun ran gini tun ran zane. Ha kama kowacce iriyar KULA na ta'ammalli da kaunar da ke cunkushe a rayuka. Haka zalika ita kan tumbatsa ta zama MALLAKIN ZUCIYAH..._


_labarin ya zo da salo na daban. Ya taho da wani launi na kauna marar gaurayeπŸ’•_


_who doesn't love a romantic college love story ? Don't afford to miss this chance.πŸ€ͺ Love is considered to be both positive and negative, with its virtue representing human kindness, compassion, and affection, as "the unselfish loyal and benevolent concern for the good of another" and its vice representing human moral flaw..πŸ’•_



_ZAFAFA BIYAR PAID NOVELS_


_

*RUMBUN K'AYA*πŸ”₯


*DAUDAR GORA*πŸ”₯


*IDON NERA*πŸ”₯


*A RUBUCE TAKE*πŸ”₯


*KI KULANI*πŸ”₯


*_uhmmmm_*😊😊😊😊😊😊😊😊😊😊


*Nasan zakuce ya da murmushi haka?*


*Wanda bai shigo ba bazai gane ba*


*Sai kin shigo daga ciki zaki gane me nake nufi*☺️☺️


*KE DAGA JIN SUNAYEN LITATTAFAN MA KADAI KASAN CEWA AKWAI WANI BABBAN ABU MAI MATUQAR JAN HAKALI TATTARE DASU*


*KINA NEMAN INDA ZAKI HUTAR DA KWANYARKI?*


*KI SAMU ZUNZURUTUN NISHADI DA ILIMI?*


Littafi daya---400

Biyu---600

Uku----800

Hudu-----1k

Biyar din duka----1200


*ZOKI BIYA KUDINKI TA WANNAN ACCOUNT DIN KI ANTAYA JIRGIN FITON ZAFAFA BIYAR*πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯


0022419171

Maryam sani

Access bank


*MTN CARD KO VTU ZASU SAKA TA NAN*


***


πŸ‡³πŸ‡ͺπŸ‡³πŸ‡ͺπŸ‡³πŸ‡ͺπŸ‡³πŸ‡ͺπŸ‡³πŸ‡ͺπŸ‡³πŸ‡ͺπŸ‡³πŸ‡ͺ

*Ina yan uwa 'yan nijer?*

*Zaku saka katin AIRTEL ta wannan number sannan ku tuntubeta*


+22799643131


Littafi daya---450CFA

biyu---650CFA

uku----850CFA

hudu----1050 CFA

Biyar----1250CFA


*A DADE ANAYI SAI GASKIYA!*


*SIYAN NA GARI KUMA MAIDA KUDI GIDA!*


*Thanks for choosing us*πŸ”₯