FANSAR FATALWA 005
*FANSAR FATALWA*
( _Horror Story_💀☠️).
_Tsarawa/Rubutawa_
© *SHAMSIYYA MANGA*
*MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION*
*SADAUKARWA*: _Wannan book ɗin gaba ɗayan shi Sadaukarwa ne gareku Anty Hadiza D Auta, Sis Amira Adam Alkhairin Allah ya kai muku a duk inda kuke ina_ _son ku fisabillillahi_.
*Free book*
-------------------------------------------
*Bissimillahir rahmani rahim*
*005*
____________________________
Da gudu Justice Kabir ya nufi kan ta yana ƙiran sunan ta, amma ina! Hajiya Ikilima ko alamar motsi ba tayi balle ya sa ran zata amsa.
Ihu Justice Kabir ya shiga rusawa yana ƙiran ma'aikatan asibitin yana cewa
"Ku yiwa girman Allah ku zo ku taimaka ku ceci rayuwar matata, dan Allah ku taimaka ni, Ikilima dan Allah ki tashi nasan wasa kike, Ikilima wallahi ƙarya suke mana Azaran mu bata mutu ba tana da rai".
Ya ƙarashe maganar cikin hargowa kamar zai tashi asibitin gaba ɗaya.
Da ƙyar aka ƙira wasu Nurses suka zo suka ɗauki Hajiya Ikilima ɗin inda nan ma da ƙyar Justice Kabir ɗin ya bari aka ɗauke ta ɗin.
Shi kuwa Inspector Rasheed wani irin mugun haushin Justice Kabir ɗin yake ji yana mishi kallon jahili kuma marar hankali.
Lokacin da aka zo za'a shiga da Hajiya Ikilima ɗakin taimakon gaggawa ma nan ma da ƙyar aka dakatar da Justice Kabir dan wallahi cewa yayi shikam sai ya bi su ciki,da ƙyar dai ma'aikatan suka hana shi, sannan ya haƙura, amma duk da haka zarya ya dinga yi a bakin ƙofar ɗakin yana jiran fitowar likita.
Gwajin farko da likita ya yiwa Hajiya Ikilima ya gano cewar rai yayi halin sa ta riga mu gidan gaskiya sai dai muce Allah ya ji ƙanta.
Fitowa likitan yayi daga ɗakin sannan ya dubi Justice Kabir zai yi magana sai dai cikin sauri Justice Kabir ɗin ya riga shi inda ya fara magana cikin tashin hankali.
"Likita ya ake ciki dan Allah kar sanar dani labari mai daɗi game da matata, likita dan Allah ka cemun matata ta farka".
Duk a lokaci guda Justice Kabir ya jefawa Likitan waɗannan tambayoyin.
Zare glass ɗin shi likitan yayi sannan ya dubi Justice Kabir cikin tsananin tausayawa kafin yace.
"Justice Kabir sai dai haƙuri Allahn da ya baka ita ya karɓi abin shi".
Saurin riƙo hannun shi Justice Kabir ɗin yayi yana zaro ido waje kamar zasu faɗo ƙasa sannan yace.
"Likita bangane ba?, Mai kake shirin faɗa mun?".
"Justice Kabir Allah ya yiwa matar ka rasuwa kasan duk wani mai rai mamaci ne ba wanda ya zo duniya domin yayi gadin ta dan haka ay........".
Innalillahi wa'innailaihi rajiun shine abun da mutanen wajen suka fara faɗa cikin tsananin tausayin halin da Justice Kabir ɗin zai shiga.
Sai a wannan lokacin inspector Rasheed ya ɗan ji wani tausayin Justice Kabir ɗin ya kama shi.
Tabbas tsayawa faɗin irin tashin hankalin da Justice Kabir ya shiga ɓata lokaci ne domin kuwa a take ya fara wasu irin surutai marrassa kan gado wasu ma saɓo kawai yake danƙarawa.
Mutanen wajen ne suka kama shi ganin abun nashi yana neman wuce gona da iri sannan aka nufi motar shi da shi, inda wasu kuma suka je suka ɗakko gawar Hajiya Ikilima aka sanya ta a mota domin a je a mata sutura.
Tabbas duk wani mai zuciyar imani sai ya tausayawa halin da Justice Kabir ɗin ya shiga domin kuwa zan iya cewa shima mutuwar ne kawai bai yi ba. Mutane da yawa sun mishi uzuri domin kuwa mutuwar da aka mishi mutuwa ce dai sai mai ƙarfin imani ne zai iya tawakkali,ga ƴa ga mata duk a kwance ba rai.
Su kuwa wasu daga cikin talakawan da suka san halin shi musamman ma'aikatan da suke ƙarƙashin shi take su ka rinƙa Allah ya ƙara duba da yadda daman ba wani kyautata mu su yake ba. Shiyasa a rayuwa duk abun da zaka aikata ka zama ka aikata mai kyau ko dan gudun goben ka. Allah ka kar ka sanya mu daga cikin masu wulaƙanta na ƙasa damu Ameen.
An je an sallaci Hajiya Ikilima inda aka dangana ta da gidan ta na gaskiya.
Har aka je aka kai Hajiya Ikilima Justice Kabir bai bar surutai ba, domin kuwa wasu ma cewa suke ƙwaƙwalwar shi ta taɓu.
*****
A can asibitin da aka kai su Anisa da Amira kuwa sai da suka kwana suka yini ba tare da sun san duniyar da suke ba.
A hankali Anisa ta fara buɗe idanunta da suka mata nauyi tare da jin kan ta kamar zai rabe gida biyu saboda yadda yake mata ciwo.
Wata irin faɗuwa gaban ta yayi sakamakon jin abu kamar ruwa ya ɗiso mata a fuska.
Hannu ta sanya ta gogo wajen da taji ɗisar abun, innalillahi wa'innailaihi rajiun mai Anisa zata gani! Jini ta gani a hannun nata.
Saitin wajen da abun ya zubo mata tabi da kallo duk da irin matsanancin faɗuwar gaban da take ji.
Jini ta gani yana biyowa ta jikin silin ɗin ɗakin da suke kwance ɗin.
Gaba ɗaya saitin wajen da take kwance ɗin jini ne yake ɓullowa har ya bada shape ɗin Star, kafin kuma ya fara ɗisowa ɗis ɗis ɗis akan fuskar ta.
Jikin Anisa idan ban da rawa ba abun da yake yi, wani gigitaccen ihu ta sake wanda ya sanya ma'aikatan asibitin saurin shigowa cikin ɗakin da gudu hankali tashe.
Suna shigowa suka ganta kwance a gadon illahirin jikinta idan banda rawa ba abun da yake ga jini da suka gani a fuskar ta kamar an mata feshi.
Hannun ta ta ɗaga tana ƙoƙarin nuna musu sama sai kuma ta tafi luuuu ta sume.
*****
A ɓangaren Anwar kuwa tun da ya ji labarin mutuwar Azra hankalin shi ya ƙara tashi, take mutuwar Afrah da ta fara bin jikin shi ta sake dawo mishi sabuwa.
Gashi kullum sai Amrah ta zo mishi watarana a fili watarana a cikin bacci, sannan kullum cikin kuka taka zuwar mishi ya rasa dalilin hakan.
Duk ranar da tazo mishi a farke ba'a bacci ba to sai ya suma idan ya farfaɗo kuma to a take zai manta duk wani abu da ya faru ɗin.
Idan kuwa a mafarki ta zo mishi to idan ya farka yana iya tunawa da mafarkin sai dai bai taɓa yunƙurin sanarwa wani ba, shidai kullum cikin addu'a yake.
Yau ma kamar kullum kwance yake akan gadon shi yana bacci lokacin ƙarfe ɗaya na dare ne.
Mafarki ya fara yi wai gashi a wani ƙatoton fili inda ba gida gaba bare baya.
Wata iska ce take kaɗawa ƙarar ta mai cike da abun tsoro, suuuuuiii ka ke jin ta tana wucewa.
A can nesa dashi ya hango ta zaune a ƙasa ta haɗa kan ta da gwaiwa.
Sannu bisa hankali ya fara tafiya har ya ƙarasa inda take ɗin.
Isar shi wajen yayi dai-dai da ɗago kan ta, tare da kafe shi da ido. Murmushi ta fara mishi kafin kuma daga bisani ta fashe da wani irin kuka mai sauti.
A maimakon ya ga hawaye yana fitowa a idanun ta sai ya ga jini hadda guda-guda suna fitowa daga cikin idanun nata.
"Amrah!".
Ya ƙira sunan ta cikin tsananin ruɗani.
"Anwar sun cuce ni!, Anwar sun kashe ni da rai na!, Anwar shin zaka ga laifi na dan na dawo ɗaukar fansa".
Shikam tun da Amrah ta fara magana ya kasa fahimtar inda maganar tata ta dosa, buɗe baki yayi da niyyar tambayar ta su waye suka cuce ta ɗin sai dai kuma take ya fara ganin ƙasar wajen da Amrah ɗin take zaune ta fara zaizayewa, a hankali sai ga wani rami ya bayyana a wajen take kuma Amrah ta shige cikin ramin, shigewar ta keda wuya ƙasar wajen ta koma tare da haɗe kan ta.
A dai-dai wannan lokacin kuma Anwar ya farka daga wannan mafarkin da yake gaba ɗaya jikin shi ya jiƙe sharkkaf da gumi.
Miƙewa yayi zaune cike da ɗumbin mamakin wannan mafarkin da yayi ɗin.
Shin mai yake shirin faruwa ne dashi?, Shin mai yasa Amrah take yawan zuwar mishi a cikin bacci?, Shin su waye suka cuce ta haka har take iƙirarin ɗaukar fansa.
Ganin bashi da amsar tambayar tashi ko ɗaya ne ya sanya ya tashi tsaye tare da shigewa toilet ya ɗauro alawla sannan ya fito.
Sallah ya zo ya tayar kafin kuma daga bisani bayan ya idar ya ɗaga hannun shi ya fara addu'a, sai da ya yiwa Afrah addu'a sosai kafin kuma daga bisani ya tashi ya koma ya kwanta zuciyar shi cike da zulumi.
*MANGA*
_Comment_
_Share_
_Fisabillillahi_.