FANSAR FATALWA 006
*FANSAR FATALWA*
( _Horror Story_💀☠️)
_Tsarawa/Rubutawa_
© *SHAMSIYYA MANGA*
*MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION*
*SADAUKARWA*: _Wannan book ɗin gaba ɗayan shi Sadaukarwa ne gareku Anty Hadiza D Auta, Sis Amira Adam Alkhairin Allah ya kai muku a duk inda kuke ina son ku fisabillillahi_ .
*Free book*
-------------------------------------------
*Bissimillahir rahmani rahim*
*006*
____________________________
Yau kwanan su Anisa da Amira uku a gadon asibiti kuma a yau ne likita ya sallame su suka koma Hostel.
Sai dai har zuwa yanzu mutuwar Azra tana nan a cikin zukatan su ta kasa goguwa duk da kuwa mutuwar daman ba wani lokaci ta ɗauka ba.
A cikin kwana biyu ɗin da suka yi a asibiti babu wani abun tsoro da ya sake razana Anisa ɗin tun na ranar da taga wannan jinin, sai dai kuma kullum zuciyarta cike take da fargaba da tsoro. Gashi sai tayi niyyar sanarwar da Amira abun da ya faru ranar can ɗin sai taji bakin ta kamar an sanya zare an ƙulle shi.
Komawar su Hostel ɗin da kwana biyu aka kafe musu time table ɗin exam wanda hakan ya sanya Suka duƙufa wajen karatu ba kama hannun yaro.
Rana bata ƙarya sai dai uwar ɗiya taji kunya,kamar yadda aka kafewa su Anisa circular ɗin exam ɗin to yau ta kama ita ce ranar da zasu fara exam.
Babban abun da yafi ɗaurewa Anisa kai kuma ya tsorata ta,bai wuce karatu da idan sun yi tana shiga ɗakin jarrabawa zata ji ta nemi komai ta rasa kamar ma ba'a taɓa koya mata ba.
Wannan abun ba ƙaramin tsorata ta yake ba domin kuwa tun tana ganin abun kamar wasa har ta zo ta fara tsorata da lamarin.
Yau ma kamar kullum zaune suke ita da Amira suna karatu, ɗago kai Anisa tayi ta kalli Amira sannan tace.
"Amira nikam akwai wani abu da yake ɗaure mun kai wanda na rasa yadda zan yi".
Ajiye littafin hannun ta Amira tayi sannan tace
"Anisa wannan wane abu ne haka?, kar ki manta lokacin da muke, wannan lokacin ba lokacin da zaki na sanya abu a ranki bane domin kuwa kin fi kowa sanin cewa daga wannan jarrabawar da muke rubutawa sai ta kammalla makarantar mu".
Ajiyar zuciya Anisa ta sauƙe sannan tace
"Hmmm Amira kennan!, wallahi a wannan halin da nake ciki jarrabawar ma ba lalle na ci ba, domin kuwa kullum da kike ganina ina karatu ne kawai amma da zarar na shiga ɗakin jarrabawa komai yake ƙwace mun na rasa mainene dalili".
Anisa ta ƙarashe maganar kamar zata yi kuka.
"Subhannallah Anisa mai nake jin kina faɗa haka!, dan Allah ki bar wannan maganar ma yanzu ba wasa ne ya kamace mu ba".
Amira ta faɗa tana kawar da kai gefe domin kuwa duk a tunanin ta Anisa kawai wasa take mata kasancewar ta san wacece Anisa a kaf cikin ƙawayen su tafi kowa nacin karatu, idan har za'a yi exam to ba wanda yake finta ci daga Azra sai ita sune ƙwarin mate ɗin nasu wanda kowa ya san ƙoƙarin na su duk da kuwa ita ma Amira ba baya ba wajen ƙoƙari.
"Amira kennan kina ɗaukan wannan lamarin kamar wasa ko?,wallahi ba wasa nake miki ba amma koma mainene result zai nuna"
Ta faɗa tana mai miƙewa ta shige toilet ganin duk irin bayanin da zata mata ba yadda zata yi ba.
Yau ita ce ranar ƙarashe ta jarrabawar su zaune suke a exam hall ɗin hankalin kowa yana kan amsa tambayar da take rubuce a jikin question paper ɗin shi amma banda Anisa wadda take zaune in banda juya biro ba abun da take.
A hankali taji wata murya wadda har duniya ta naɗe ba zata taɓa mantawa da wannan muryar ba tana ƙiran sunan ta cikin murya mai firgitar wa.
"Anisaaaaaa! Anisaaaaaa! Anisaaaaaa!"
Da sauri ta ɗago kanta tare da bin wajen da take jin ana ƙiran sunan nata da kallo sai dai tana kai kallon ta wajen taga fitar ta waje.
Kamar wadda aka tsikara da allura haka taji gaba ɗaya zaman hall ɗin ya gagareta inda kuma ta wani ɓangaren taji ba abun da take so kamar ta fita tabi bayan ta.
Miƙewa tsaye tayi sannan ta fice daga cikin hall ɗin inda ba wanda ya lura da fitar ta ta.
Wata hanya daban taga Amrah ta bi inda hanyar jeji ne.
A hankali Anisa ta shiga bin ta domin kuwa da ta tsaya sai taji jikin ta kamar ana watsa mata ruwan zafi.
Haka ta dinga binta har suka ƙurewa ganin mutanen.
Anisa bata ankara ba sai ganin su tayi a wani ƙasungurmin daji mai cike da wasu irin bishiyoyi masu duhu da raishen su kamar zai taɓo sararin samaniya saboda tsawo.
Waige-waige Anisa ta fara domin kuwa shigowar su jejin keda wuya ta nemi Amra sama ko ƙasa ta rasa.
*****
A ɓangaren Inspector Rasheed kuwa sosai ya duƙufa wajen bincike domin gano makashin su Afra da Azra ɗin.
Sai dai har zuwa yanzu ba wata ƙwaƙwarar shaida da ya samu wadda zata taimaka mishi wajen gano wanda yake aikata kisan.
Zaune yake a cikin office ɗin shi yana ƴan rubuce-rubuce, haka kawai jefi-jefi sai ya saki tsaki sakamakon ji da yayi kwata-kwata baya son yin aikin yau ɗin.
Tashi yayi daga kan kujerar sa sannan ya fita bakin kanta inda ya tarar da su kofur Bala a zaune.
Duban shi ya kai wajen Kofur Bala ɗin sannan yace.
"Kofur Bala a fito da mota zamu je asibiti da gidan Justice Kabir da kuma gidan su marigayiya Afrah".
Sara mishi Kofur Bala yayi sannan yace.
"Ok Sir".
Motar aka fito mishi da ita inda suka shiga suka nufi asibitin da gawarwakin su Afrah suke.
Sai dai rashin sani yafi dare duhu domin kuwa inda Inspector Rasheed ya san irin aikin da zai ƙara rattaɓowa kan shi da bai je asibitin ba.
Lokacin da suka isa asibitin kai tsaye suka wuce ɗakin adana gawarwakin.
Kasancewar ma'aikatan wajen sun san shi yasa basu hana shi shiga ba.
Suna shiga cikin ɗakin ya buƙaci da a janyo akwatin gawar da Afrah take ciki.
Abun mamaki da ɗaure kai ana janyo akwatin suka tarar da akwatin wayam kamar ba'a taɓa ajiyar gawa a ciki ba.
Innalillahi wa'innailaihi rajiun shine abun da Inspector Rasheed ya shiga maimaitawa duk kuwa da cewar bai tabbatar da hassasshen nashi ba.
Gaba ɗaya suma mutanen da suke wajen take mamaki da ruɗani ya ziyarci fuskokin su a lokaci guda.
Kofur Bala kuwa ji yayi kamar ace mishi ƙit ya fice a guje domin kuwa shi daman wallahi tun farko ba san wannan Case ɗin yake ba.
Saurin kallon ma'aikatan wajen Inspector Rasheed yayi hankalin shi a matuƙar tashe sannan yace.
"Mai nake kallo haka?, Ina gawar cikin akwatin nan take?".
Ya faɗa fuska ba annuri.
"Ranka ya daɗe ai wannan lamari sai dai mu tambayi juna domin kuwa wallahi ban san amsar da zan baka ba".
Ɗaya daga cikin ma'aikatan Mutuary ɗin ya faɗa.
"Wannan wane irin zancen banza ne kake son gayamun alhalin kune masu gadin ɗakin, idan ban tambaye ku ba wa ku ke so na tambaya?"
Inspector Rasheed ya faɗa cikin tsawa.
Gaba ɗaya wajen shiru ya ɗauka,domin kuwa wannan baƙon al'amari ne kuma sabon abu a wajen mutanen asibitin baki ɗaya, duba da cewar wannan shine karo na farko tun daga lokacin da aka kafa asibitin da aka taɓa neman gawa aka rasa a cikin ɗakin.
"A fito da akwatin ɗaya gawar".
Suka tsinkayi muryar Inspector Rasheed ya faɗa fuska ba fara'a.
Su kam ma'aikatan wajen duk jikin su yayi sanyi aka rasa wanda zai iya tunkarar akwatin da Azra ɗin take ciki balle a buɗe shi.
Kallon su Inspector Rasheed yayi sannan yace.
"Wai ko baku ji abun da na faɗa bane?".
A hankali ɗaya daga cikin su ya nufi akwatin da aka sanya Azra ɗin a ciki ƙirjin shi sai bugawa yake, miƙa hannun shi da yake rawa yayi ya janyo akwatin sannan ya buɗe.
Buɗe akwatin da Azra ɗin take ciki keda wuya mutanen wajen suka shiga tashin hankali fiye da na farko sakamakon tozali da akwatin Azra ɗin da suka yi shima wayam sai wasu irin ƙananan tsutsotsi ne suke shawagi a ciki.
A wannan lokacin da zaka tsaga jikin rabin mutanen wajen to ba zaka tarar da jini ba Saboda yadda suka shiga matsanancin tsoro.
Nan fa aka shiga kallon-kallo a tsakanin mutanen wajen domin kuwa lamarin a yanzu ya daina basu mamaki sai tsananin tsoro.
Duk wanda ka kalla a wajen tsoro ne zaka gani ya bayyana ƙarara akan fuskokin su, idan ka ware Inspector Rasheed kaɗai wanda ya shiga bin akwatunan da kallo ɗaya bayan ɗaya kamar mai nazarin wani abu.
Umarni ya bayar da a buɗe wani akwatin gawar.
Da sauri ƴan wajen suka kalli juna cikin tsananin tashin hankali,kafin daga bisani wani daga cikin su yayi ƙarfin halin janyo wani akwati da yake kusa da akwatin Azra.
Sai dai a wannan karon akwatin da aka buɗe ɗin gawar tana nan lafiya a kwance a cikin akwatin ba alamar wani baƙon abu a tattare da ita.
Shiru wajen ya ɗauka baka jin motsin komai sai ƙarara sauƙar numfarfashin su wanda yake nuni da alamar ruɗani da tashin hankalin da suke ciki.
Can dai inspector Rasheed ya ɗago idon shi da suka yi jawur ya buɗi baki da niyyar yin magana sai kuma ya fasa ya fice domin kuwa a yadda yake jin zuciyarshi tana mishi idan yace zai yi magana za'a samu matsala.
Yana fita daga cikin ɗakin adana gawar kai tsaye office ɗin shugaban asibitin ya nufa domin kuwa wannan lamari ne da dole a san matakin ɗauka tun da wuri.
*****
Haka Anisa ta shiga kai komo a cikin wannan daji mai cike da abun tsoro, ita kam a yanzu ta saddaƙar da cewar mutuwa zata yi wani irin matsanancin tsoro ne ya rufe ta sakamakon tozali da wata bishiya da tayi kaman tana mata dariya.
Bata gama shiga tashin hankali ba sai da ta tabbatar da cewa da gaske fa bishiyar dariya take mata.
Jikin ta ne ya shiga wata irin karkarwa kamar mazari take kuma ta fara jin sautin dariya ta ko ina a cikin dajin yana amsa kowa.
Ɗaga idon da zata yi kawai tayi arba da gaba ɗaya bishiyoyin cikin dajin suna mata dariya, daga baya kuma kawai taga sun fashe da kuka har da hawaye.
Ai Anisa na ganin haka bata san sanda ta durƙushe a wajen ba ta shiga rusa ihu tana neman agaji, sai dai ina babu mai jin ta balle a kawo mata taimako.
Faɗowar abu da taji a kusa da ita ne ya sanyata saurin ɗago kai tare da ja da baya.
Mai zata gani in ba gawar Anisa da Azra ba kwance a gefen ta wasu tsutsotsi suna biyowa ta tsakanin idanun su.
Wani gigitaccen ihu Anisa ta sake sannan ta zube a wajen sumammiya.
Tsananin zafin ranar da ake ne ya buge ta wanda yayi sanadiyar farfaɗowar ta.
Idanunta take ƙoƙarin buɗewa dan taga hasken duniya, sai dai mai duhu ta gani a maimakon taga haske.
Gaban ta ne ya faɗi inda cikin sauri ta sanya hannu ta shafo idanun nata sai dai wayam taji gurbin idon nata a shafe kamar ba'a taɓa hallitar ido a wajen ba.
Buɗe baki tayi da niyyar yin ihu amma kuma muryar tata ta katsea sakamakon dariyar da taji a gefen ta da kuma kuka a lokaci guda suna tashi.
"Dan Allah wacece ke?, Dan Allah mai ya sami idona?,Mai na miki kike son ganin bayana?".
Duk a lokaci guda Anisa ta jefamata waɗannan tambayoyin.
A maimakon taji an bata amsa sai taji an cigaba da ɓaɓɓaka dariyar da kuma kukan har dajin sai da ya ringa amsawa.
Ita kam Anisa zuwa wannan lokacin ta cire rai da sake rayuwa, take kuma duk wani tsoro ya gushe mata zuciyarta ta bushe cikin ƙaraji tace.
"Mai kuke jira da nine da ba zaku kashe ni ba?, Ku kashe ni nace tun da kun raba ni da abu mafi muhimmanci a rayuwata".
Anisa ta ƙarashe maganar cikin sakin kuka mai tsuma rai.
"Anisa mai kike ci na baka na zuba, ai ko baki nemi ki mutu ba to tabbas zaki mutu saboda daman mutuwa ita ta kama ce ki a wannan lokacin kamar yadda sauran ƴan uwan ki suka mutu, amma kafin nan sai kin ɗanɗani baƙin cikin da na ɗanɗana, sai kin fara girbar abun da kuka shuka, sai kin gane cewar cin amana ba abu ne mai kyau ba".
"A.....m......r.......a.....h.....ke.....ce..."
Anisa ta faɗa cikin rawar murya.
Wata mahaukaciyar dariya Amrah ta kwashe da ita sai da ta ɗauki tsawon lokaci tana yin ta kafin tace.
"Kina mamaki ne wadda ku ka zalunta ku ka yi sanadiyar mutuwar ta ta dawo?, Tabbas nice na dawo Ɗaukar Fansaaaaaaaaaa".
*MANGA* ✍️
_Comment_
_Share_
_Fisabillillahi_