FANSAR FATALWA

FANSAR FATALWA 008

by @shamsiyyamanga

*FANSAR FATALWA*

( _Horror Story_💀☠️).


_Tsarawa/Rubutawa_


© *SHAMSIYYA MANGA*


*MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION*


*SADAUKARWA*: _Wannan book ɗin gaba ɗayan shi Sadaukarwa ne gareku Anty Hadiza D Auta, Sis Amira Adam Alkhairin Allah ya kai muku a duk inda ku ke ina son ku fisabillillahi_.


*Free book*


--------------------------------------------

*Bissimillahir rahmani rahim*


*008*

____________________________


Jin wannan mummunan labari da hukumar makarantar suka yi ba ƙaramin dugunzuma hankalin su ya yi ba inda ba tare da ɓata lokaci ba suka ɗunguma suka nufi bayan makarantar.


Innalillahi wa'innailaihi rajiun shine abun da bakunan mutane ya shiga furtawa a lokacin da suka isa wajen suka yi arba da gawar ƴanmata uku rigis kuma aminan junaa kwance cikin jini, sannan gaba ɗayan su ba mai arziƙin sutura a jikin ta.


Wannan abu ba ƙaramin tayar da hankalin mutane yayi ba.


Babban abun da ya ƙara tayarwa da hukumar makarantar hankali shine, su dai sun san cewar gawar Azra da ta Afrah tana can asibiti a adane a ɗakin adana gawa,to amma ya aka yi kuma yanzu suka tarar da gawarwakin a wajen?.


Tambayar da suka shiga yiwa kan su a cikin zukatan su Kennan amma kuma ba amsa.


Kan kace mai labarin tsintar gawarwakin da aka yi a bayan makarantar har ya karraɗe rabin makarantar inda tunin wasu daga cikin ɗaliban suka shiga haɗa kayaryakin su domin kuwa a take mutane da yawa suka ce sun haƙura da karatu a makarantar domin kuwa wannan abun abun tsoro ne,dan haka gwanda su tafi tun da an fara yin ɗauki ɗai-ɗai a ƴanmatan makarantar.


Allah sarki a ɓangaren Amira kuwa har zuwa yanzu bata da masaniya akan gawar Anisa ɗin da aka tsinta a bayan makarantar domin kuwa ita kam tana can bakin gate tana baza ido dan ganin ta wane ɓangare Anisa zata ɓullo.


Ana cikin wannan halin ne kuma Inspector Rasheed suka ƙaraso da shi da muƙarraban shi sakamakon ƙiran gaggawar da ya kuma samu daga hukumar makarantar.


Tun daga shigowar su cikin makarantar Inspector Rasheed ya fahimci ba lafiya ba duba da yadda ya ga ɗalibai suna ta fita da jakanku nan su.


Iso aka mishi zuwa bayan makarantar inda gawarwakin su ke.


Zallan maza ne a wajen domin kuwa matan makarantar ba wadda ta iya tsayawa a wajen kasancewar raunin zuciya da mata su ke da ita.


Darewa mutane suka fara yi inda Inspector Rasheed ya shiga wajen har zuwa kan gawarwakin inda sai a sannan ya fuskanci dalilin ƙiran da aka mishi ɗin.


Zare glass ɗin shi ya fara yi a hankali yana jin zuciyar shi kamar zata fito waje.


A wannan karon duk irin dauriyar da Inspector Rasheed ɗin yake da ita sai da ya ji zuciyar shi ta karye sakamakon tozali da gawar ƴanmata ukun an musu mummunan kisa na wulaƙanci.


Saurin mayar da hawayen da ya ji yana ƙoƙarin zubo mishi yayi gudun kar mutane su lura.


"Innalillahi wa'innailaihi rajiun, Na shiga uku na lalace,wannan wane azzalumi ne yake aikata ma rayuwar mu haka?, Shin mai muka aikata haka wanda ake kashe mu?, An kashe Afrah!, An kashe Azra! Yanzu ga gawar Anisa! Yanzu hakan yana nufin saura niiiiiiii........."


Kasa ƙarasa maganar tata tayi inda kawai sai ƙarar faɗuwar ta aka ji timmm a ƙasa.


Da sauri mutanen wajen suka juya inda suka nufi kan Amira ɗin wadda isowar ta wajen kennan.


Shi kuwa Inspector Rasheed umarni ya bada na a rufe makarantar ba shiga ba fita a yau ɗin gaba ɗaya.


Haka aka ɗauki Amira wadda bata san ina kan ta ya ke ba sannan aka wuce da ita clinic ɗin da yake cikin makarantar.


Tunin labarin mutuwar Anisa ɗin ya isarwa iyayen ta inda suka iso makarantar cikin matsanancin tashin hankali wanda ba zai faɗu ba.


Duk inda tashin hankali ya kai to iyayen Anisa sun shige shi, a nan ne kuma mahaifin ta ya buƙaci a bashi gawar ƴar shi zai wuce da ita gida su mata salla.


Sai dai kuma nan take Inspector Rasheed ya dube shi sannan yace


"Ah Ranka ya daɗe maganar gaskiya ba zamu iya bada gawar wannan yarinyar ba har sai mun gama bincike don gano wanda yake da hannu a cikin wannan kisan".


"Binciken banza binciken wofi wannan ai maganar banza ce, bayan har zuwa yanzu kun kasa ɗaukar wani mataki game da lamarin, ai ba wani maganar bincike don na lura ba abun da zaku iya".


Mahaifin Anisa ya faɗa cikin tsananin ɓacin rai.


Cike da mamaki Inspector Rasheed ya shiga bin shi da kallo tun lokacin da ya fara maganar har zuwa lokacin da ya gama.


"Ranka ya daɗe wannan wane irin magana ka ke faɗa haka?, Kar ka manta komai bisa sannu ake binshi idan aka ce za'a yi gaggawa to out come ɗin ba zai taɓa yin kyau ba".


"Ni dai Wallahi na gama magana babu uban da ya isa yasa na bar gawar ƴata a hannun ku, alhalin ina da labarin gawar ma ba ƙyale ta aka yi ba".


Duk yadda Inspector Rasheed ya so ya tanƙwara mahaifin Anisa ya bar gawar abun ya gagara inda haka suka haƙura tun da ƴar shi suka bashi gawar ya tafi da kayar shi.


Sai a sannan Inspector Rasheed wani tunani ya zo mishi game da wannan zanen tauraron da yake gani a jikin gawarwakin ƴanmatan da kuma farar takardar da ɗazu ya tsinta Kennan hakan yana nufin Anisa ita ce ta uku, tabbas idan kuwa haka ne wannan makashin bai gama aikin shi ba to kar fa ɗayar ƙawar ta su ita ce ta huɗu?, tun da gashi gaba ɗayan su ƙawaye ne".


Aikuwa in dai haka ne to ya zama dole ya sanya ido sosai a kan ta domin a yanzu ita kaɗai ce target ɗin shi da zata iya ɗaura shi akan hanyar gano makashin.


Yana kaiwa nan a zancen zucin da yake ɗin ya juya da sauri ya bar wajen ya nufi clinic ɗin da aka kai Amira.


*****


Yau kwana uku da mutuwar Anisa inda har an kai ta gidan ta na gaskiya.


A ɓangaren Amira ma yau kwanan ta uku a asibitin ba tare da ta san a wace duniyar take ba, numfashin da take ne kawai zai tabbatar ma da cewar tana raye.


Mahaifiyar ta har ta zo tana wajen ta inda jira kawai take ta farka ta ɗauke ta su koma gida, domin kuwa alƙawari ta yi cewar Amira tana farkawa zata wuce da ita gida ta gama karatun kennan haka kawai tana ji tana gani ba za'a kashe mata ƴa ba.


Da mugun ihu ta farka inda ta sanya hannu ta cisge ƙarin ruwan da ake mata sannan ta miƙe zata fita da gudu.


Da sauri mahaifiyar ta da take zaune akan sallaya ta riƙo ta tana cewa.


"Innalillahi wa'innailaihi rajiun Amira ina zaki je?".


"Umma ki bar ni dan Allah na fita, wajen Anisa zan je nasan wallahi bata mutu ba, Umma nasan cewar mafarki nake Umma dan Allah ki taimaka ki sake ni".


Amira ta faɗa tana fashewa da wani irin kuka mai taɓa zuciya.


"Subhannallah Amira ki tsaya dan Allah, jama'a ku kawo mun ɗauki".


Mahaifiyar Amira ta ƙarashe maganar cikin kururuwar neman taimako.


Ma'aikatan wajen ne suka shigo da gudu inda da ƙyar aka kama Amira aka kwantar da ita saboda wani irin ihu da take, ga wasu irin surutai marrassa kan gado da take sai kace hauka sabon kamu.


Allurar bacci likitocin suka mata amma ina!, Kamar an ƙara mata haukar da take, inda da ƙyar wata Nurse ta shiga tofa mata addu'oi kafin daga bisani bacci yayi awun gaba da ita.


Zama a gefen ta mahaifiyar ta tayi tana sharar hawaye cikin tausayin ƴar ta ta.


A can makarantar su Anisa kuwa tunin gwamnati ta aiko da sanarwar a rufe makarantar na wasu lokuta kafin a ga abun da Allah zai yi.


Kafin sannan kuwa daman iyaye da yawa sun samu labarin abin da ya faru ɗin inda suka shiga zuwa suna jidar ƴaƴan su suna mai da su gida a cewar su ba za su bar ƴaƴan su a mahallaka ba.


A ɓangaren Anwar yau ya shirya tsaɓ domin zuwa ya dubo Amira da take kwance a gadon asibiti.


Lokacin da ya isa asibitin Amira kwance take akan gado tana bacci sakamakon addu'ar da aka mata ɗin.


Gaisawa suka yi da mahaifiyar ta inda ya fara magana


"Umma ya jikin Amira ɗin dai?".


Bakin zanin ta ta sanya ta share hawayen da suka zubo mata kafin daga bisani tace


"Jiki Alhamdulillahi ɗannan amma fa lamarin Amira ɗin sai addu'a, domin kuwa kwana mu ke idon mu biyu ba bacci, yanzu haka wannan baccin da kaga tana yi da taimakon wata addu'a da aka tofa mata ne ta samu ta yi wannan baccin, amma kaga jiya yadda muka ga dare haka muka ga rana".


"Bakomai Umma ki cigaba da mata addu'a a matsayin ki na mahaifiyar ta in sh Allah zata samu lafiya, daman dole abun zai zo mata wani iri ganin yadda ta rasa aminan ta guda uku rigis a kusan lokaci guda, tun da kin ga an yi rasuwar Afrah ba'a fi sati ba aka zo aka yi na Azra, nan ma bai fi kwanaki ba aka yi na Anisa, ga mutuwar Amrah a baya wadda tsakanin ta da Afrah wasu watanni ne, to kin ga dole abun zai matuƙar ɗaga mata hankali".


Anwar ya faɗa cikin tsananin tausayawa halin da Amira ɗin take ciki.


Sai da ya kwantarwa da mahaifiyar Amira hankali sosai kafin daga bisani ya mata sallama ya tafi.


*****


Ƙarfe Ɗaya na dare Amira ta farka inda ta waiga gefen ta taga mahaifiyar ta a zaune akan kujera tana bacci.


Da sauri ta miƙe sannan ta zari ɗan kwalin ta ta fice daga cikin ɗakin ƙafa ko takalmi babu.


Tun da ta fita daga cikin clinic ɗin ta shiga tsula gudu kamar mai shirin tashi sama, ƙafafuwan ta kamar za su taɓo ƙeyarta saboda ƙarfin gudun da take ɗin, a haka har ta isa bakin gate ɗin makarantar, jami'an tsaro ta hango tun daga nisa a tsaye cirko-cirko sun zagaye waje da cikin makarantar.


Ras gaban Amira ya faɗi inda ta shiga tunanin hanyar da zata bi domin ta samu ta fice daga cikin makarantar ba tare da sun gan ta ba.


Wata dabara ce ta faɗo mata, inda ta shiga bin jikin bango kamar wata ƙadangaruwa har ta isa bakin ƙofar ɗakin securities makarantar wanda yake can daga gefe kusa da gate ɗin.


A hankali ta leƙa cikin ɗakin inda ta tarar da su a kwance suna bacci kamar gawa.


Saɗaf saɗaf saɗaf ta shiga takawa a hankali har ta isa bakin tagar ɗakin wadda take ta waje.


Hannu ta sanya ta buɗe a hankali sannan ta fara ƙoƙarin haura window ɗin.


Wani security ne taga ya motsa sakamakon wayar shi da tayi ƙara ai take hanyar cikin ta ta kaɗa, bata tsaya wata-wata ba ta dirƙa windon ba tare da ta duba inda ta faɗa ɗin ba.


Dafe hannun ta tayi da taji ya zogi alamar ta kuje amma duk da haka bata dakata da abun da tayi niyya ba, haka ta miƙe tsaye ta runtuma a guje ba tare da ta san inda take jefa ƙafar ta ba.


Gudu ta shiga tsulawa akan titin wanda yake shiru ba alamar motsin wata hallita,ko tsoron daren bata ji ba burin ta kawai bai wuce ta samu ta isa inda take son isa ɗin ba lafiya, sannan ba tare da kowa ya ganta ba.


Haka ta cigaba da gudu tana yi tana waiwaye ko wani yana biye da ita cikin ikon Allah kuwa ba wanda ya ganta ma bare ya biyo ta kasancewar dare ya tsala sosai.


Idan kaga gudun da Amira ɗin take zaka iya cewa ba da ƙafafu take gudun ba saboda yadda take gudun kamar zata tashi sama, tsabar gudun da take ɗin ko gaban ta bata kallo balle ta san inda take jefa ƙafar ta.


Ita dai burin ta da damuwar ta bai wuce ta gan ta a inda take da burin zuwa ba, domin kuwa ko damuwa da duhun daren bata yi ba kai kayi tunanin da rana ne tsaka take wannan gudun.


*Manage it pls yau bana jin daɗi sosai ban ma yi zaton zan muku typing* *ba wallahi* 🥺👏🏻.


*MANGA*✍️.

_Comment_

_Share_

_Fisabillillahi_.