Aduniyar mu 5_&6
by @khadijaumar
Bismillahir'rahmanir'raheem
A DUNIYAR MU
5&6
Mallakar
Khadijah Umar Abdullahi
(Garkuwar Jarumai)💪🏻
""K'warai kuwa wannan ba komai bane, kinsan zan iya rabuwa da kowa akan in talauce, domin wannan yaron neman talautani yake shirin yi,
Kayi haƙuri excellency na tabbata kamal baya a dawa da kai kuma zanyi magana da shi in sha Allah zai fahimta
""wannan kuma matsalar ku ce ke da shi cewar Dady tare da É—aukar wayoyin sa ya fice ya bar momy baki buÉ—e,
tagumi Momy ta rafka tana tinanin inda ya kamata ace ta dosa tsakanin excellency da Kamal tarasa wa zata fuskanta,
---------------------------
Tinda suka baro babu wacce tayi magana a cikin su, agidan Aisha mai kitso suka sauka kowacce da' abinda take saƙawa a ranta Maryam ce tafara yin gyaran murya tace "" kunyi shiru nidai na gama yanke hukunci bazan iya yin zina ina da aure ba, koda sanda nake budurwa da banyi ba sai yazu "" Aisha ce ta katse maryam da cewa"" nidai idan har zan samu naira dubu ɗari biyu a rana wllh zanyi waze sani daga ni sai hajiya Samee sai ku da kuka sani,
kuna gani kitso nakeyi ga yara kullum baya dawowa sai sha biyu wataran a hayyacin sa wataran a buge bai damu da cinmu ba da sham ba bare kuma azo maganar suttura,
ko shekara bayi yake ba to nidai ina so naci me kyau Ć´aĆ´a na su ci mekyau mu kwanta waje me kyau nima naga Ć´aĆ´a na cikin manyan makarantu kamar na hajiya Samee,
ku dubi irin kayan da muke sawa nida yara na saboda haka ni jibi zan koma ""amma Aisha me zamu ce da mazajen mu?
dariya Aisha tayi tace ""nifa ina kitso kuma daman shi a tambaye shi kuɗi ne baya so ni kawai zance masa zan dinga zuwa gidan ƴan siyasa ina yiwa matan su kitso anyi mn hanya kinga shikenan ba kare bin damo na kashe bakin tsanya tafaɗa tana sheƙewa da dariya,
haka jiki a sanyaye duk suka amince inda suka tsaida magana akan jibi zasu koma kamar yanda tace,
Rayuwa mai daɗi ke wakana a gidan shukra wanda a ɓangaren isa so da tausayin shukara ne yake ƙara mamaye masa dukkan ilahirin zuciyar sa a ɓangaren shukra kuwa tana ganin ba tada wani masoyi kamar maman Nabila da ta faɗa mata gaskiya, tinda gashi yana bata kulawa sosai sannan abunda take so shi a keyi,
---------------------------
Bayan sallar isha nura ya aiko kiran jamila, saida ta gama shan ƙamshi sannan ta fita ko sallayar da ake ɗaukar masa yau be samu ba, a bakin ƙofa ta tsaya ta riƙe ƙogu tace ""to gani tsananin mamaki ya hana nura magana banda kallo babu abinda yake binta da shi,
"" kaga idan baka da abinda faÉ—a zan wuce,
mirmushin ƙarfin hali yayi yace "" haba jamila koda babu abida zan faɗa ai babu laifi dan na tsaya ina kallon wife tobe ko?
"Hmm yaya kenan to wllh karka yaudari zuciyar ka don ni wllh ba matar ka bace dubeni fa,
ta faɗa tana juya wa a hasken farin watan da ya haske ƙofar gidan, baki buɗe ya tsaya yana kallon ta kafin ya sake ƙaƙalo wani murmushin yace "" amma you are joking ko? nasan Jamila tawace ni kaɗai nasan babu wanda zai ƙwacemn ke ,
""Allah ko? to bari kaji wllh ni jamila nafi ƙarfin aurenka saboda haka idan ma abinda kayimn a baya kake tinani to ka jira wanda zan aura zai biyaka, mezanyi da kai mekake dashi matuƙin napep ragowar basur dame zaka iya ɗaukar ɗawainiya ta? mezaka bani in saka a jiki na? baka da shi,
saboda haka wllh jamila tafi ƙarfin ka tinda ta fara magana yake kallon ta zuciyar sa na wani irin zugi ba'a taɓa ci masa mutunci kamar yau ba har ta gama rashin kunyar ta tabar wajan bai sani ba saida ya ɗago kansa yaga babu ita a wajan, jiki ba ƙwari yaja ƙafafuwan sa ya nufi gida,
Kamal na shiga É—akin sa ya zauna gefen bed yana tinanin ta yanda zai fafata da Ć´an siyasar da ke zuluntar talakawan dabasu ji ba basu gani ba,
" Khadija
itace ta faɗo masa arai da sauri ya ɗauki wayar sa ya fara danna mata kira saida ta tsinke sannan ya ƙara kira aka ɗauka,
Asslamu alaikum wata zazzaƙar murya tafaɗa,
""wa'alaikissalam matsalarki jan aji wllh kiran farko ma nasa kina gani
"" eh ƙwarai kam ina gani nasan a kwai dalilin da yasa ka kirani amma idan babu wani abu baka nema na "" to ke meyasa bakya nema na
""ina
mace zan dinga neman ka? kaga nifa kafaɗamn abinda yasa ka kira na don zanyi baƙo ne saurayi na ya dawo daga us,
wata irin ƙwarewa kamal yayi ya dinga tari kamar ba zai dena ba ""subhanalla kamal sannu lafiya dai ko ruwa ya ɗauka ya sha sannan ya samu nutsuwa lafiya ƙalau komai norml,
dariya khadija tayi ciki ciki tana jinjinawa miskilanci irin na kamal,
khadija ya za'ai mukawo ƙarshen zalincin da akewa talakawan mu ƴan siyasa sun tattare komai kullm maganar dena shaye shaye ake amma sune suke ordern kayan mayen,
khadija matasa na rasa hankalin sa wasu ma na rasa rayuwar su gaba É—aya a dalilin masu hannu sa shuni,
"" a kwai mafita kamal" a'ina mafitar take?...
COMMENT & SHARE PLEASE